Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

NI DA DR MAHIR Complete Hausa Novel Document by NI DA DR MAHIR


NI DA DR MAHIR

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 61027



NI DA DR MAHIR

Reading Time: 5 Hours

Added On: 03, Jul 2024

Author: Hafsat Bello ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 343.94 kb

File Type: txt

Views: 1431+

Download: 2656+

Last download: less than 1 second ago

Description/Story: ο»ΏCompiled By Umar Dalha Funtua.


Copied By Ummee Garkuwa.


*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S✍🏻*

πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
*HIBBATULLAH*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

Writing by
*HAFSAT BELLO*


Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…

*Am back againπŸ‘―πŸ»πŸ‘―πŸ»*


*πŸ…Ώ 1*

Wata bakar mota kirar Bentley 2019 Mai bakin glass ce ta danno kanta cikin farfajiyar federal hospital dake cikin garin Kano, direct wata rumfa ta nufa wadda ajikin rumfar akayi symbol da babban rubutu aka saka *C. M. D parking lot* anan motar ta faka wani mutum daga gaba ya fito da sauri tare da bude murfin dama.

A hankali ya zuro da farar kafanshi dake sanye cikin wani black cover shoe na companyn Prada, kafin ya idda fitowa gaba dayan sa wooow na fada dan wani classic man ne ya fito sanye cikin wata dakakkiyar designer suit dark blue wadda tayi matukar amsar cikakkiyar halittar jikinsa, tabbas guy din ya hadu over dan kusan kamar shi ya ya zana kansa.

Daya murfin da driver ya zaga ya bude wata classic bab ce ta fito wadda kana ganinta kasan hutu da boko sun zaunar mata tana sanye da wata blue tokish gown ta yane kanta da bakin siririn veil kafarta da sanye da high heels baki mai shegen kyau, tana da kyau amma ba sosai ba ba fara bace amma yanayin Hutu da jindadin da take ciki yasa fatarta ke wani irin glowing.

Wani sihirtaccen murmushi ya sakarwa drivern nasa har sae da siririyar hushiryarsa ta bayyana kafin ya furta.

"thank bukar. "

Matar kuwa sake kicin kicin tayi da fuska ta zagayo tare da shigewa jikinsa cikin wata murya mai dauke da kissa tace..

"baby let's go."

Ba tare da yace mata komai ba suka fara takawa cikin asibitin sakale da juna da kagansu kasan manyan masoyane, duk inda suka ra6a kallonsu ake tare da miko musu gaisuwa, amma shi kawai yake amsawa banda ita matar.

Har office dinsa na CMD ta rakashi sbd tsarinta ne kullum sae ta rakashi kafin ta tafi nata office din, kissing din bakinsa ta danyi kafin ta dago ta kalleshi da kyau tace.

"take care."

Gyada mata Kai kawai yayi kafin tasa Kai ta fice.



Dai dai bakin kofa ta bude kofar kenan sukayi gware da wata matashiyar nurse kyakkyawa number daya tana da shape mai kyan gaske domin boob's dinta a cike suke ga hip dinta nan ma tubarakallah irin matan nan ne da ake kira da full option.

Da sauri taja baya tare da rike files din hannunta da kyau tayi kasa da kanta jikinta na wani irin rawa lkc guda zufa ta rufets ruf tayi kasa da kanta muryarta na shaking tace.

"am..sorry...mah...ban...ban...san...ki....!"

cikin daka tsawa mai firgitarwa tace.

"shut up stub bitch! Are u nonsense?"

Dasauri ta girgiza Kai tana kuma fadin.

"sorry...doc...wllh... "

Mtsww taja wani dogon tsaki cikin isa da izza tace.

"get out of my side dabba."

Da sauri nurse din tabar wajen har tana hadawa da faduwa tabar wajen don tasan halin doctor fina kuma tasan wace ita.



*_MAHIR ABDULMU'IN ABDALLAH dane na uku wajen tsohon NGO na Africa wato Abdulmu'in Abdullah yan asalin kasar sudan ne mahaifiyarsa kuma yar Nigeria ce bafulatanar yola ce, mahir shi kadaine namiji a wajen iyayensa sai yarsa farida da kanwarsa najwa kuma dukkan nusu sunyi aure, family dinsu masu kudin gaskene kuma cikakkun yan bokone._*
*_duk da arziki na iyayensa da family basu baya daga cikin mutane masu dagawa can nuna arzikin da iyayensu ke dashi, yayi krtn shi na medicine a Oxford University anan ya zama kwararren likitan mata mai zaman kasa Mai tsananin basira da sanin aikinsa, yayi aiki da babban asibitin dake birnin London kuma asibiti na biyu a duniya gaba daya kuma yana daga cikin wadanda akeji dashi sosai a kasar indai ta sanin matsalar mace ne, ganin cigaban da yake samawa kasar da ba tashi ba kuma yana ganin halin da tamu kasar take ciki na rashin cigaba da kwararrun likitoci irinsu yasa ya tattaro ya dawo Nigeria domin suma su amfana da shi nan take yana dawowa aka bashi CMD na federal hospital ._*
*_doctor mahir yana kirki sosai ga tausayi da taimakon mararsa shi, kusan duk shekara yana kai mutane da dama saudiya aikin hajj, sannan yana da foundation guda ta tallafawa talakawa a garuruwan arewa dama kasar mahaifinsa Sudan._*
*_doctor mahir yana daga cikin the most eligible bachelor da muke dasu a duniya, wannan dalili yasa matarshi doctor fina ke matukar kishinsa dan da wuya mace ta daura idonta akansa taji batayi wani feelings nashi ba, gaba daya shekarunsa basufi 35yrs ba._*


*_doctor Nafisa Alkasim dan baiwa, 'yace d'aya tilo a wajen shugaban kasa mai ci a ynz wato alkasim dan baiwa, mahaifiyarta hajiya kuye kuma tsohuwar manager ce ta NNPC, asalinsu yan Nigeria ne nufawan Mina, nafisa Fina tayi krtn ta na medicine a kasar Cyprus inda ta karanci abinda ya shafi hanci hunhu mak'ogwaro, tana da kwarewa sosai a aikinta Kuma tana daga cikin manyan likitocin da ake takama da su a Nigeria kmr mijinta._*
*_doc nafisa kwatata bata da mutunci bare da'a tana da jinkai da nuna isa da son asan ita ko wace, bata harka da kowa sai uwarta domin bata yarda da kowa ba sai dai tana da wani amintaccen yaronta guda daya wanda shine yasa kusan dukkan surrukanta, tana da kishi Mai zafin gaske wanda ita kanta batasan wane iri bane domin zata iya aikata komai idn kishinta ya motsa, tana da gayu da kwalliya gata komai nata sak na yan bariki domin har tattoo ne da ita a wuyanta._*
*_tunda ta auri doctor mahir sbd tsananin soyayyar da take masa kasancewar mahaifinta aminin mahaifinsa ne, ba laifi shima yana sonta sae dea sam baya son halinta da dabi'unta, wajen aiki guda suke aiki sbd tsabagen kishinta duk wata staff mace daga patients har doctors nurses babu wanda bai san halinta ba, shi isa duk mai son kansa da arziki da zaman lfy ba Mai shiga sabgar mijinta._*

Wannan kenan

Jikinta na tsananin rawa ta sauka daga benan CMD din ta nufi department dinsu na labour room, office dinsu ta shiga tare da ajiye files din hannunta ta zauna shirif tare da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya.

Daya daga cikin matan office din dake zaune tana rubutu a register ta ajiye beron hannunta tare da fadin.

"sister *HIBBATULLAH* lfyrki kuwa kika shigo haka kamar anjefoki ko biyoki akayi ne."

Wadda take gefe tana danna waya tace.

"kema dai sister rashida kamar bakisan daga inda take ba, wata kila tayi karo da madam."

"mtsw."

Kakeji wadda aka kira da Rashida taja tare da fadin.

"wllh kuna bani mamaki kun dauki tsoron duniya kun daurawa waccan ajawon mai siffar karuwai, ni banga abin tsoro a tare da ita ba."

Dasauri dayar ta tareta da fadin.

"aikuwa doctor Fina ita ke da abin tsoro, karfa ki manta ubanta ke da kasa."

Tsaki rashida taja kafin tace.

"aikin kutmar uba dan ubanta ke da kasa amma ai bashi ke da duniya ba, shikkenan dan tana matsayin yar shugaban kasa sae kuma akace ta taka kowa, wllh bari kiji ras nake da ita bana tsoronta ni wllh har so nake ma wani uziri ya kaini wajen CMD tym din kuma tana wajensa, tayi attempting yi mini wani Abu wllh sae na zubar mata da jini in yaso tasa a haka rijiya gaba dubu a jefani."

Hibba dake ta sauke ajiyar zuciya tayi bayyanan nan murnushi wanda ya fito da zahirin kyawun halittar da fuskarta ke dauke da shi sannan tace.

"um um dai sister Rashid banda cika baki."

"bar matsiyaciya sister hibba duk wannan zafin kan nata tasan doctor Fina taci uwarta iya shi."

"hmmm maman boy kenan ku zuba ido very soon rabb ya hadani da ita Zakusha mamakina."

"Allah ya hadaku kuwa."

cewar maman boy tana cigaba da abinda take, yayin da hibba ta Mike ta janyo dayar register ta fara cike cikenta...






*toh my fans ya kukaji labarin a cigaba ko a dakata....for commentsπŸ‘‡πŸ»*
08125544850



Vote
Share
Comments




Oum AfafπŸ–€πŸ”₯
[9/22, 2:32 PM] Ummee Garkuwa: *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S✍🏻*

πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
*HIBBATULLAH*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

Writing by
*HAFSAT BELLO*



*πŸ…Ώ 2*

Wani hamshak'in parlour ne da girmansa zeyi 100by100 fadin tsarin parlourn is weste of time kawai kuyi imagining kyawu da tsaruwar parlon shugaban kasaπŸ€£πŸ˜›.

Tana zaune sanye da skinny jeans da half vest ta daure gashin dokinta da akayi mata kananun kalba da shi tana danna wayarta kirar iPhone x-mas, karar taunar cingum dinta kawai ke tashi hade da tashin wakar dake fita a decorder.

A hankali yake saukowa daga stairs din parlon yana sanye da wasu designer english wears red T-shirt da black trouser ya zuba hannunsa daya cikin aljihu dayan kuma rike da car key dinsa da wayanshi.

Har ya karaso cikin parlour hankalinsa na kan wayarshi da yake dannawa a gabanta ya tsaya tare da duban Rolex watch din dake tsintsiyar hannunshi yace.

"baby ni zan dan fita."

Wani irin kallo tayi mishi mai dauke da ma'anoni iri iri sannan ta Mike tsaye tare da
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download NI DA DR MAHIR

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album