Join Our WhatsApp Group

SANADIN PARTY Complete Hausa Novel Document by SANADIN PARTY

SANADIN PARTY

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 13118SANADIN PARTY

Reading Time: 1 Hours

Added On: 03, Nov 2023

Author: Mujahida Matar Malam ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 07064904617

Book License : Free

Category: Horror novels

File Size: 87.96 kb

File Type: txt

Views: 927+

Download: 301+

Last download: 10 hours ago

Description/Story: *SANADIN PARTY HORRO STORY💀☠️*

_FREE BOOK_

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK...(24) RUHIN JINN PAID BOOK.. (25) JAMI'IN SIRRI C~I~D PAID BOOK 300 ONLY.. (26). SANADIN PARTY HORRO STORY
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝```

_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *SANADIN PARTY💀☠️ HORROR STORY*
_Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._*Arayuwa zaka burge wasu Kuma zaka bawa wasu haushi, wasu zasu soka Wasu Kuma zasu k'ika wasu zasu yabeka wasu kuma su kusheka, Haka rayuwa take tafiya idan Kama wani wani bazaka masa ba, dukanin Sak'onninku suna zuwa gareni na Yabo da Akasin hakan, ban Damu da zagin wasu ba Domin kuwa nasan cikakkiyar ni'ima tana Aljanna Amma duk da hakan Ni Mujaheedah Matar mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 nakakce Alhmdllh Domin Alk'alamina A tsalkake Yake bana Batsa ko shashanci ko cin zarafin wani ko Aibatawa, Ina Rubutu Kan tsarin tafarkin Ilimi domin bada Shawara nasiha Fad'akarwa Wa'azantar ilimantarwa, kuma Alhmdllh Sak'ona Yana zuwa daidai inda Allah ya nufa Kuma Yana ban Lada daidai da Aikina, kuma Ina Samun Masoya daidai nufin Ubangiji ✨ Inaaa Alfahari daku Masoyana Kuma Ina sonku Tabbas _BASEERARA ITACE ARZIKINA😍_ Allah ya k'ara wadatamu yamuna K'arshe nainyau yasa mucika da imani yabamu Masoya Nagari ya karemu daga Mak'iyanmu, Allah kabama k'asarmu NIGERIA zaman lafiya da Arziki Mai Amfani..... AmeenAmeen......... Mujaheedah Matar mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 HAUSA NOVELS 📚 TAKUCE🥰🥰*
_BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM_
*PAGE 1 TO 5*......."Nifa ko kayarda ko Karka Yarda wallahi sainaje bikin Nan k'awatace fa She is my best friend Taya zakace bazanje ba Bayan duk Sauran K'awayenmu zasu kawai Kayi hak'uri dear saina dawo"
Tana Gama maganar ta rataya Y'ar jakarta tafice,Girgiza Kai Kawai Yayi A Ransa yana dana sanin Auren Macce Mara Ilimin Addinin yabiye Kyau da Boko yanzu gashi Yana kwasar Bak'in ciki,
"Hello Safa gani nafito fa Kuna ina,"

"Muma gamunan Muna ganinki ma K'araso Kawai motarmu ce gefen titi"
K'atse Kiran tayi tanufe wurin
Ganin motar tayi tashiga da sallma

Ansawa Sukayi, tareda Sakin shewa "Kai Amma Neediy kinyi Kyau Sosai, Ni wallahi Banyi zaton Ammar zaibarki zuwa wannnan partyn ba," Cewar safa

"Cabb Wai bala'i ai wllh Bai sa yahanani zuwa wannnan partyn ba kinsan najima dashi cikin Raina kusan kwana nayi inashirin zuwansa ke harda mafalkai kansa saida nayi,"

Dariya suka saka, "musamman wannan partyn dazai bada record bakin ruwa fa za'ayi Shi,"

"Bakin ruwa kuma,? Amma dai ba nesa bane Sosai ko,"?

Matsawa"ni wllh matsala ta dake kenan saurin sarewa, tokoma meye idan mukaje kyagani, badan wannnan Cikin nakiba wallahi sai a d'auka ke budurwa ce,"

Shafa cikin tayi, tareda Murmushi"Kuma wallahi Inason Abuna sosai kinsan duk iskancina Inason mijina wallahi shikuwa yasa Rai Kan cikinnan Sosai,"

"Hunmm to Allah ya sauke lafiya kema musha party"

"Ameen Amma banda party domin kunfi kowa Sanin Mijina Ustax ne mlm ne da badan Yana sonaba ai bazan rik'a Masa wannnan rashin kunyar ba,"

"Gaskiya Kam Ammar yana Sonki,"

Gidansu Amarya Suka tsaya Koda suka isa kowa yashirya dan har Ango yaturo motocin wasu har sunshiga motocin ita kanta Amarya tafito dan Shiga mota nan suka gaisa taci wanka cikin wani yadi Mai net tayi kyau Sosai d'inkin ya Kamata sosai shiga Motar tayi inda shima Angon yana ciki, cikin motar tasu Anisa tashiga sai Rahila Sauran kuwa suka shiga tareda Samarinsu,

Rahila d'ayar k'awarsuce duk tare sukayi karatu musamman a islamiyya nasiha datake yawan yimusu yasa basu cika shiri da itaba, amma duk da hakan sunshak'u sosai da Anisa donin Anisa tana d'aukar shawara saidai tafe rawar kaine,

"Banzata zakizo ba Rahila,"

"Wallahi har gida Amaryar taje ta rok'o Umma da Abba Kan subari naje wannnan yasa nazo amma wallahi Anisa gaba bugawa yake duk nawani tsorata kamar Kar naje,"

Hahahaha"dan bakisaba bane yarinya shiyasa ni Wallahi sai yanzu Dear yadawomin Araina nakejin ban kyautaba Bari namasa text,"

Wayaeta tajanyo tarubuta text na neman Afuwa ta tura masa, sannna ta kashe wayar

Sosai sukayi tafiya sannan Suka Kai, parking Sukayi duk suka fito Sauran matan suka fara shewa da ihu, masu had'a kayan kid'an Suka fara kowa ya Soma nashi Aikin,

Tinda Suka fito cikin Motar duk tsaurin ido irin na Anisa kasa matsawa tayi zuciyarta ke halbawa da k'arfi yayinda takejin wani tsoro yana shigarta, lurada hakan yasa Rahila Kama Hannunta tace"kema kinsoma jin Abunda nakeji ko,? Yanzu kin gasgata cewa bawai Dan Ina Sabon shiga bane,"

"Hakane Rahila bansan Meyasa Haka kawai Hankalina Yakasa kwanciya da wurin nan, gashi inata sake Kiran wayar Ammar Amma tak'i zuwa ga Alama wurin Nan ba network"

"Allah zai fitar damu in Sha Allah Kawai kada mushiga cikinsu mutsaya Anan muyita Anbaton Allah"

Yarda da Shawararta yasa Suka bud'e motar kawai suka zaune suna hangensu Angama shirya komai sunsaki kid'a sun Soma rawa, ba yarda Amaryar da safa basuyi ba kan sushiga filan kid'an Amma sukak'i hakan yasa dole suka kyalesu.............
KUYI HAK'URI DA SAMUN PAGE'S DINA MARASA TSAYI HAKAN TANA FARUWA NE SABODA BANDA LAFIYAR IDO WALLAHI BAN IYA JURAR KALLON HASKE DA YAWA KUYI HAK'URI KUBINI AHANKALI NAMUKU TYPING YARDA ZAN IYA, KUMA KUTAYANI ADDU'A ALLAH YABAN LAFIYAR IDANUWANA..............

KADA AMANTA DA COMMENTS DAMA SHARING PLEASE..
_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_WhatsApp number 07064904617

*SANADIN PARTY HORRO STORY💀☠️*

_FREE BOOK_

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK...(24) RUHIN JINN PAID BOOK.. (25) JAMI'IN SIRRI C~I~D PAID BOOK 300 ONLY.. (26). SANADIN PARTY HORRO STORY
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝```

_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *SANADIN PARTY💀☠️ HORROR STORY*
_Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._*Arayuwa zaka burge wasu Kuma zaka bawa wasu haushi, wasu zasu soka Wasu Kuma zasu k'ika wasu zasu yabeka wasu kuma su kusheka, Haka rayuwa take tafiya idan Kama wani wani bazaka masa ba, dukanin Sak'onninku suna zuwa gareni na Yabo da Akasin hakan, ban Damu da zagin wasu ba Domin kuwa nasan cikakkiyar ni'ima tana Aljanna Amma duk da hakan Ni Mujaheedah Matar mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 nakakce Alhmdllh Domin Alk'alamina A tsalkake Yake bana Batsa ko shashanci ko cin zarafin wani ko Aibatawa, Ina Rubutu Kan tsarin tafarkin Ilimi domin bada Shawara nasiha Fad'akarwa Wa'azantar ilimantarwa, kuma Alhmdllh Sak'ona Yana zuwa daidai inda Allah ya nufa Kuma Yana ban Lada daidai da Aikina, kuma Ina Samun Masoya daidai nufin Ubangiji ✨ Inaaa Alfahari daku Masoyana Kuma Ina sonku Tabbas _BASEERARA ITACE ARZIKINA😍_ Allah ya k'ara wadatamu yamuna K'arshe nainyau yasa mucika da imani yabamu Masoya Nagari ya karemu daga Mak'iyanmu, Allah kabama k'asarmu NIGERIA zaman lafiya da Arziki Mai Amfani..... AmeenAmeen......... Mujaheedah Matar mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 HAUSA NOVELS 📚 TAKUCE🥰🥰*

_Thursday 5/10/2023 October_*Aduk Yarda kuka Sami k'arancin Typing d'ina Dan Allah kuyi hak'uri Kada ku kusheni wllh banda Lafiyar idanuwane inajima kamar zandaina Typing duka saboda Lafiyar idanuwana, so please Banda zagina game da karancin Typing kunji dalilina lafiyar idoce banda kutayani Addu'ar Allah yaban lafiya*
*Page 6 To 10*

.......Yana fitowa masallaci Yaji k'arar Wayarsa alamar shigowar sak'o baisami damar duba sak'onba Saboda d'alibanda Suka tsaidashi d'aukar karatu haka yake duk Akayi sallah sai wasu sunsaidashi d'aukar karatu, sai kusan magarib Suka gama sukashiga sallah baidawo gida Saida yayi isha dama hakanne k'a'idarsa, Gaisawa sukayi da maigadi yawuce yayi mamakin ganin haryanzu batadawoba zama yayi d'aya daga cikin kujerun palourn ya d'auko wayarsa kiranta text d'inta yagani murmushi kawai yayi Afili yafurta "My Anisa rigima" kiranta yasa amma not reachable hakan kenuna indatake ba network, ganin bazaisametaba ya hak'ura, har yakwanta yana gwada kiran amma maganar d'ayace not reachable, hanakalinsa yakasa kwanciya domin duk biki batakai 10:00 gashi yanzu 12:00 yanacikin tunani bacci ya saceshi bashiri,.******""""**********

"Safa zo, dan Allah kisaka saurayinki yakaimu gida nidai nagaji wallahi gashi inakiran Ammar wayar tak'ishiga saboda nan ba network Kuma inajin wani iri kutaimaka ku maidamu gida dare yayifa yanzu 12:00 kunata Abu d'aya inada tabbacin yanzu hankalin mijina yatashi,"

"Cabb yanzu kinatunanin wurinnan akwai wanda zai iya matsawa ba'a gamaba? Wallahi konace yaje bazashiba bakisan halinsa bane dason casu kuyi hak'uri agama ankusa ai,"

Muryar MC sukaji yana Fad'in "za'ayi kid'an K'arshe Sai kowa yakama gabansa dare yayi,"

Aikuwa dagudu Safa ta isa wurin akasake wata banzar wak'a suka shiga Suka Soma rawa da rungume rungumen juna, wasunsu ma harda kisses kumafa saurayi da budurwa,

("WA'IYAZUBILLAH, WANE IRIN BALA'I NE ACE SAURAYINKI ZAIYI KISSING D'INKI KIBARSHI? KODA BAN FAD'ABA KEMA KINSAN HAKAN HARAMUN NE BAIZO CIKIN ADDINIBA ANCE MACCE TA KAME KANTA AMMA SABODA LALACEWAR ZAMANI DAGANIN WAYEWA TA BANZA ANDAINA AMFANI DA FAD'AR ALLAH DA MANZONSA SABODA ME ZAMUGA DAIDAI? WLLH TINDA MUKA KAUCE FAD'AR ALLAH DA MANZONSA TO BAZAMU SAKE GANIN DAIDAI BA, MATA MAZA MUJI TSORON ALLAH, MUTUWA ZUWA TAKE BATA NEMAN IZINI KO SANARWA ZUWA KAWAI TAKE DATAZO DOLE AJE KODASHIRI KO BABU TO MUJI TSORON ALLAH MU GYARA GOBENMU" WANNNAN SHAWARAR MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 KAWAI,")

Iskatasoma k'ad'awa dak'arfi take duhu ya maye gurin duk wani Abu dakewurin iskatasoma d'aukeshi su kansu mutanen Bata raga musu ba d'aukarsu take tana jefawa ruwa wasu kuwa saidai ta katsesu gida biyu tamkar rake jini yasoma zarya wurin ihu kawai ketashi na Mutane sai Ihun neman taimako suke,

Iyarud'ewa su Anisa sun rud'e Bayan motar suka lab'e suna rik'e dajuna ita da Rahila duk wata Addu'a datazo bakinsuyi suke,

Anjima cikin wannnan halin Kafin Haske yabayyana na farin wata, Koda suka duba gurin jini yayi Anbaliya har cikin ruwan ga gawarwakin Mutane zube duk an Ragargazasu bakyawon gani, sun tsorata iya Matik'a sun rud'e ihu Suka kurma suduga Sauran domin Yanzu bazasu wuce Ashirin ba sama da talatin duk sun hallaka, juya idanuwanda Anisa zatayi tahange Amarya sarkafe dawani tsinin icce tamkar k'warangwal haka tadawo bakinta saijini kefita, k'ara Anisa tasaki tana nuna musu da Hannu, Koda suka waiga sukagani suka k'ara shiga tashin hankalin, motsi ruwan gulbin suka fara dawani haniniya tamkar dawakai zasu fito cikin, cikin tashin Hankali suka rugu cikin dajin suna gudun ceton rayukansu, Aikuwa Aljanun Suka mara musu baya domin kuwa duk mutanen da suka kashe dawowa sukayi k'warangwal sukabi bayansu, gudu suke Sosai na fitar hayyaci k'afafunsu sai taka k'aya suke domin tuni suka jefarda takalmi amma tsabar tashin Hankali bawanda yakecin zogin k'ayar, dukansu suna tare wani k'aton dutse Suka gani cikin sauri suka shige cikinsa Duka suka b'uya, Koda k'warangwal d'in sukazo basu gansuba Suka wuce, duk sunyi tsit bamai motsi bamaijin bacci dukansu danasanin zuwa wannnan partyn suke, bacci B'arawo ne Kawai yayi nasarar sacesu,
Kiran sallar Assubah ne yatashi daga Mugun mafalkin da yake firgigit yatashi da Sunan Allah abakinsa saida yasake dubawa amma batadawo ba hakan yatabbatar Masa ba lafiya ba, sallah yayi Yajima yana Addu'a yau ko tsayawa karatun baiyiba yadawo gida kiranta yacigaba dayi amma yakasa samu, zaune yayi rafka Uban tagumi, yana Addu'a Allah yatsare matarsa da d'ansa, jiran haske yabayyana yake yaje gidansu yagani,.
Sanyi da iskane yatashesu Koda suka falka sukaga gari ya waye tar masu Sauran imani sukayi taimama sukayi salla da Rok'on Ubangiji yafiddasu cikin wannnan bala'in

Huci suka somaji daga bayansu Koda suka waiga wani k'aton maciji sukagani idanuwansa manya manya bakinsa tamkar rame nufosu yayi cikin tashin hankalin suka ruga waje shima yabisu kamar ta iska haka ya dira gabansu tareda cafkar saurayin Safa, yasoma kalaci dashi domin kuwa had'eshi yasoma yi kanajin k'arar karairayewar k'asusuwan jikinsa da macijin ketaunewa, ihu suke shikanshi saurayin ihu yake iya gigicewa sun gigice, sake rugawa sukayi sukabar saurayin wanda yajima da mutuwa Domin tamas macijin yamasa Yacinyeshi, koda yagama cinyeshi yaga basunan yabi bayansu Yana nemansu,

Sosai suke gudu cikin tashin Hankali sunyi nisa sosai Suka tsaya suna maida numfashi, kuka safa tasaki tana Fad'in"nayi Dana sanin zuwa partynnan nayi Dana sanin sanin k'awancena da diza nayi nadamar k'injin mahanar
Iyayena Danayi nazo Nan gashi *SANADIN PARTY* munata halaka"

Dukansu kuka suke kowa yana tuna yarda Yafito wasu da dama ance kada suzo wasu kuwa sunfi k'arfin iyayensune wasu kuwa dama su fand'ararrune,

Dafe cikinta Anisa tayi tana kuka da danasanin bijirewa mijinta gashi dakanta tawo kanta inda zasu halaka Kuma Abun Bak'in ciki inda ko gawarsu baza'a samuba Kuma su mutu *SANADIN PARTY*

Motsi sukaji suna waigawa sukaga wata Y'ar tsohuwa tanufosu tana tafiya da k'yar da Y'ar sandarta............................
_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_
WhatsApp number 07064904617

*SANADIN PARTY HORRO STORY💀☠️*

_FREE...

Read / Download SANADIN PARTY

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album