Join Our WhatsApp Group

WASIKAR JINI 1 to 8 Complete Hausa Novel Document by WASIKAR JINI 1 to 8


WASIKAR JINI 1 to 8

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 68877



WASIKAR JINI 1 to 8

Reading Time: 5 Hours

Added On: 17, Sep 2023

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 382.53 kb

File Type: txt

Views: 1195+

Download: 865+

Last download: 1 hour ago

Description/Story: 
WASIKAR JINI!!!
Littafi na Daya (1)
Part A
A wani zamani can baya mai tsawo daya shude a
cikin daular kasashen larabawa anyi wani
shararren
sarki mai suna Aiyuba Ibinin Silhar.Masana
hasashe da masu bincike na wannan zamani sun
tabbatar
dacewa babu wani sarki a duniya kaf wanda yakai
sarki Aiyuba tarin dukiya da kuma karfin sihirin
tsafi,saidai kash,ko kadan bai kasance sadauki ba
ko jarumi mai karfin damtse da iya yaki,amma
saboda wannan dukiya daya tara da kuma karfin
sihirin tsafi sai ya zamo dodo ga dukkan
sarakunan dake nahiyar ya zamana cewa duk
tsoronsa sukeji.Komai yawan dakarun yakin sarki
da kuma jarumtakarsu indai sukace zasu yaki
sarki Aiyuba saidai su sha
kashi.Sarki Aiyuba yana da matar aure guda daya
rak mai suna Hufaira wacce sukayi auren saurayi
da budurwa tun kafin ya zamo sarki wato ya gaji
karagar mulki a wajen mahaifinsa kuma kafin ya
tara dukiya taban al'ajabi.Allah bai bawa sarki
Aiyuba haihuwa ba saida ya shekara daya akan
karagar
mulki a sannan idanunsa suka bude akan fadada
harkokinsa na kasuwanci izuwa ko ina a cikin
duniya,ya zamana cewa duk bangaren da mutum
yaje a duniya walau kasar larabawa,turawa da
bakaken fara da kuma bangaren kasar Hindu da
birnin Sin sai yaga gonaki,gidaje,da rumfuna Na
kasuwa anan na sarki Aiyuba Ibn Silhar.Kuma
gaba dayan fatakensa suna amfani da wani
hatimi guda
daya mai taswirar rakumi da takobi a jikin
kowacce irin haja tasa sai kaga wannan hatimi.
Dukkanin yaransa masu sarrafa duniya suna
tsananin tsoronsa
kuma suna adana masa dukiyar domin idan ka
kuskura kaci amanarsa tofa ka rinka ganin masifu
kenan iri iri na cututtuka masu azaba,kuma ka
rinka
shiga bala'i iri iri kenan har sai kazo gabansa ka
kawo wannan dukiya kuma ka tuba sannan zaka
samu kanka.
Wani babban hali na kirki a tare da
sarki Aiyuba shine ko kadan baya wasa da hakkin
yaransa yana biyansu ladan aikinsu kamar yadda
ya kamata,kuma indai ka shekara guda kana yi
masa bauta kaima ka fita daga sahun talakawa
saidai a
saka ka a sahun attajirai.
A shekarar farko daya hau karagar mulki ne
Matarsa Hufaira ta haifar masa 'ya mace
kyakkyawa ta gaban kwatance mai
sunaNuwaira,koda yake sarki Aiyuba yaso ace 'da
namiji ya samu domin ya gaje shi amma duk da
haka saida yayi farin ciki ainun kuma saida aka
shafe kwana saba'in kullum sai anyi walimar ta
farin cikin samun
wannan 'ya.Attajiran sarakai da matsafa saida
sukazo daga kowanne bangare na duniya suka
halacci wannan biki na murnar haihuwar gimbiya
Nuwaira.Batun maroka kuwa duk wanda ya sami
damar shiga gidan sarautar sarki Aiyuba kakarsa
ta yanke saka domin shi da talauci sunyi hannun
riga.Da yawan marokan haukacewa sukayi
saboda ganin irin tsananin dukiyar da suka samu
wacce bama suba hatta jikokinsu da tattaba
kunnensu sai sunci albarkaci,wasu kuwa kuka
suka kamayi domin basu san ta yadda zasu iya
diban dukiyar ba su tafi
da ita,bisa dole komai hadamar maroki yabar
wata dukiya ya kwashi iya wadda ya iya diba.Yan
fashi kuwa dake kan hanyoyin zuwa birnin
Lailatun Harus wato birnin sarki Aiyuba basu taba
samun ganima ba a rayuwarsu irin ta shekarar da
aka haifi Gimbiya
Nuwaira,wasu ma da yawansu sanadin daina yin
fashin su kenan.
Bayan an kwana saba'in ana walimar murnar
haihuwar ta gimbiya Nuwaira sai baki suka watse
suka koma izuwa kasashensu,a lokacin ne fa
labarin Gimbiya Nuwaira dana mahaifinta ya sake
yaduwa da fantsama a ko'ina cikin
duniya,sunayensu ya zamo abin kwantace,daukak
arsu ta shafe duk wani mai sharafi a zamanin.
Wani babban abin mamaki da yake daurewa
mutane kai dangane da sarki Aiyuba shine babu
wanda yasan a inda yake tara dukiyarsa ko
yake boyeta,
Amma duk sa'adda yaso yayi amfani da dinare
ko lu'u lu'u ko makamancin su kawai zaice aje
guri kaza ne a dauko,ana zuwa kuwa za'a ga
dukiyar koda yawanta yakai cikin gari guda,kuma
koda an san cewa babu komai a wajen,mafi
yawan
wuraren dayake cewa aje a debo dukiyar ma
wulakantattun wurare ne marasa daraka inda
babu
tsaro kamar kududdufai ko inda ake tara shara.
Haka dai arzikin sarki Aiyuba yaci gaba da
habaka ya zamana cewa kullum a cikin gyara
birninsa yake da gine gine na kawa da kasaita
har saida takai cewa a duniya kaf babu wata
kasa data kai tasa
kyawu,tsaruwa da kawa,fadarsa kuwa aljanar
duniya ake kiranta domin komai na cikinta da lu'u
lu'u aka yishi.
Lokacin da gimbiya Nuwaira takai shekara bakwai
a duniya sai kyawunta ya ninka nada,al'amarin da
yasa iyayenta suka kara son ta
kenan ainun fiye da koyaushe.'Yayan masu fada
a ji
kuwa tun daga sannan suka fara kamun kafa ta
neman aurenta saboda matsayin ubanta da kuma
kyawunta,amma sai sarki Aiyuba yayi biris da
bukatarsu komai irin dangantakar dake
tsakaninsa
da iyayensu kuwa,wannan shine abu na farko
daya fara jefa hassada a zukatan sarakunan dake
nahiyar suka fara tsanar sarki Aiyuba.
A yamma da birnin Lailatul Harus wato birnin
sarki Aiyuba akwai wata kasa mai suna
Hirama,sarkin dake mulkin kasar Hirama ya
kasance gagarumin sadauki mayaki mai tarwatsa
maza a filin daga,ana kiransa da suna
Murwatu,shima matsapi ne na gaske,amma bai
kama farcen kafar sarki Aiyuba ba,domin ya taba
jarraba karfin tsafinsa akan na sarki Aiyuba yaji
ba dadi,harma saida ya durkusa bisa gwiwoyinsa
a gaban sarki Aiyuba ya nemi gafara don kada ya
rasa rayuwarsa.
Al'amarin ya faru ne a wata shekara da akayi fari
a kasar Hirama ya zamana cewa
yunwa,fatara da talauci ya addabi mutanen kasar
har takai cewa kananun yara da masu rauni suna
mutuwa.Lokacin da al'amarin yayi tsamari ainun
sai sarki Marwatu yasa aka rubuta wasika ya
tashi
manzo izuwa ga sarki Aiyuba a cikin wasi kar ya
nemi taimakon abinci mai yawa gami da aron
kudade masu yawa domin ya bunkasa harkar
noma a kasar tasa,dama babbar matsalar kasar
itace kasarsu bata da dadin noma sai masana
kasa sunzo sunyi mata aiki sannan kuma suna da
karancin
ruwa,dole ne a buda hanyoyin ruwa daga
kasashen ketare su shigo,kuma a nemi iri mai
kyau na
shuka.
Sarki Marwatu ya dauki alkawarin cewa bayan ya
shekara guda zai dawo da duk kudin da aka ara
masa kuma zai bayar da riba kaso guda cikin
uku.
Lokacin da wannan wasika ta riski sarki Aiyuba
yana zaune akan karagar Mulki a fadarsa ana
tafiyar
da harkokin mulki,ga Gimbiya Nauwara zaune a
cinyarsa kumaga fadawansa da sauran jama'ar
gari sun kewayeshi.
A tsakiyar fadar wadansu kyawawan 'yan mata
ne su bakwai suna ta tikar rawa anayi musu kida
don debe kewa.
A wannan lokacin sarki Aiyuba yana cikin nishadi
da walwala don daka dubeshi kasan cewa farin
ciki ya cika zuciyarsa.Bayan magatakarda ya
gama karanta wasikar sarki Marwatu sai sarki
Aiyuba ya tuntsire da dariya irin tasu ta sarakai
masu jin izza sannan ya dubi 'yarsa Gimbiya
Nauwara yace,'yata kinji
bukatar da sarki Marwatu yazo mini da ita,shin
kin amince na taimaka masa ko kuwa na rabu
dashi?
Kisani cewa duk wannan dukiya dana tara a
duniya badan kowa na tara taba sai domin
ki,kece kadai
kike da ikon fadin abinda za'ayi da ita.Koda
fadawan sarki Aiyuba da sauran jama'arsa sukaji
wannan
batu sai suka cika da mamaki sukayi zaton ma
ko sarki Aiyuba ya sami dan tabin kwakwalwa ne
domin basu ga dalilin da zaiyi wani abu da
dukiyarsa sai ya tambayi 'yarsa wacce ta
kasance yarinya karama 'yar shekara bakwai.A
lokacin da gimbiya taji tambayar da mahaifinta
yayi mata saita yi murmushi sannan ta
dubi sarki tace,yakai Abbana kayi sani cewa kana
daarzikin da zaka iya ciyar da gaba dayan
kasashen dake nahiyar nan tamu kuma ka
wadatar dasu da arzikin da zasu tsira daga
talauci to amma nafi so
kayi taimako a inda ya dace abinda nake nufi
shine wannan sarki Marwatu yana daga cikin
wannan
sarki Marwatu yana daga cikin irin sarakunan da
sukayi maka girman kai,
baya daga cikin sarakunan da suke zuwa
gaisheka duk shekara duk wani abu na farin ciki
idan ya sameka baya zuwa ya tayaka sai yanzu
da bukatarsa ta taso sannan zai nemi
taimakonka.
To kasani cewa bazamuki taimakonsa ba,kasa
akai masa abinci mai yawan gaske kuma a bashi
kudade masu yawa wadanda zasu isheshi ya
gyara harkar noma amma bisa sharadin zai
biyaka kuma ya biya ka riba bayan cikar shekara
guda kamar yadda ya
sharadanta da kansa.In har ya karya wannan
alkawari to duk abinda ya biyo baya kada ya
zargo
kowa face kansa.
Baya ga wanann inaso ka gaya masa a cikin
amsar wasikarsa cewa kai mai arziki ne kuma
attajir uban sarakai inda ma ya nemi kyauta da
an bashi amma rashin biyayyarsa ce ta sanya a
bashi aro.
Koda Gimbiya Nauwara tazo nan a
zancentsa sai gaba dayan mutanen dake fadar
suka cika da tsananin mamaki bisa yadda akayi
Nauwara ta zamo yarinya mai kaifin hankali da
tunani haka, shi kuwa sarki Aiyuba sai ya kamu
da tsananin farin ciki ya dubi 'yan majalisa
yace,kunga wannan yarinyar dole ne ta kasance a
cikinku domin ko babu ni zata iya baku
shawarwari akan harkokin mulki wadanda zasu
amfane ku su amfani kasa gaba daya,kuma duk
abinda ya taso na kudi zata taimaka muku
dashi,saboda zata gaji duk dukiyarta bisa wannan
dalili daga yau dinnan na mika matsayin
Galadima a hannun Gimbiya Nauwara tunda shine
matsayi na kula da duk harkokin kasuwancinmu
da sarrafa kudaden kasa,koda jin wannan batu
sai idanun Galami suka zazzaro hankalinsa ya
dugunzuma kuma ransa ya baci.Ya dubi sarki
Aiyuba cikin alamun tsananin damuwa a lokacin
dayai sauri ya durkusa a gabansa zai fashe da
kuka yace,Haba yakai dan uwana ya za'ayi kace
gimbiya ce zata karbi matsayina alhalin
shekarunta basu kai ta ruke wannan mukamin ba
kuma idan ta karbi wannan
mukami ni kuma wane matsayi zan rike a wannan
majalisa ko kuwa so kake na karayin kasa ne?
Koda jin wannan batu sai sarki ya mike tsaye
daga kan karagarsa ta mulki ya sauko har kasa
inda galadima ke durkushe ya kama kafadunsa ya
tashe shi tsaye ya dubeshi cikin murmushi
yace,Yakai galadima kayi sani cewa har abada
bazan taba wulakantaka ko
kaskantar dakai ba saboda kaine kadai dan
uwana na jini daya rage a wannan duniya,a kan
wane dalili
zaka damu da mukami a cikin wannan fada
alhalin ko yanzu na fadi na mutu kaine zaka gaji
karagata,tunda babu yadda za'ayi gimbiya tayi
mulki bisa dokar wannan masarauta tamu?
Idan kana kwadayin dukiyar da take kai kawo ne
a ofishinka na
kasuwanci idan ka zama sarki komai na
hannunka,ka sani cewa gimbiya babbar
gudunmawa
zata bayar a gareka kuma da babban taimako na
kudi ko nawa ake bukata tunda arzikin da zan
barmata ya ninka duk arzikin dake cikin kasashen
nan na nahiyoyinmu sau goma,daga yau ka koma
matsayin wazirina tunda ka sani cewa tunda na
hau mulki kujerar wazirci babu kowa a kanta,koda
jin
wannan batu sai farin ciki ya lullube galadima ya
kama godiya kamar bazai daina ba,amma yana
hada idanu da gimbiya Nauwara sai ya murtuke
fuska kamar wanda aka aikowa da sakon
mutuwarsa,ita kuwa saita risina a gareshi kuma
ta tayashi murna bisa samun wannan sabon
mukami na waziri.
Nantake sarki Aiyuba yasa aka rubuta wasikar da
sarki Marwatu ya aiko da ita kuma akayi bayani a
cikinta kamar yadda Gimbiya Nauwara ta
bukata,daga nan
sai aka shirya buhunhunan abinci a kalla miliyan
uku bisa keken shanu da rakuma gami da
buhunhunan dinare duba arba'in bisa rakiyar
dakaru dubu dari aka baiwa manzo na sarki
Marwatu suka kama hanya suka durfafi birnin
Hirama..........
Dafatan littafin yayi.?
Kasancewar korape-korapen da najima ina samu
akan cewa ayi wani littapin yaki nikuma banida
lokaci daman kun sani, wannan dinma nayi
rubutun ne tun 2015 yana ajiye shiyasa nace to
ko akwai wanda basu karanta ba wasu kuma
zasu so sake karantawa...
Ina patan zaku bani hadin kanku mu gudu tare
mu zira tare.
WASIKAR JINI!!!
Littafi Na Daya (1)
Part B
.
Aka baiwa wannan manzo na sarki Marwatu suka
kama hanya suka durfafi birnin Hirama.
Al'amarin waziri Ridwan bin Silhar kuwa lokacin
da fada ta watsa sai ya tafi izuwa gidansa cikin
tsananin farinciki tamkar an mallaka masa
duniyar gaba daya
nan take yasa aka shirya walima ta musamman
ya gaiyaci duk manyan abokansa na birnin da
kauye. Washe gari kuwa gidansa ya cika makil ya
batse da jama'a maza da mata,ba'a fara walimar
ba sai bayan anje fada an gama bikin
nadashi,babban abinda ya bakantawa waziri
Ridwan rai shine ba sarki ne ya nada masa
rawani ba na wazirci,Gimbiya Nauwara ce ta
wakilci sarki kuma tun a fada yaga komai ya
sauya na irin ikonsa da karfinsa akan harkokin
arziki na kasa.Hatta dukiyar da ake ajiyewa a
Baitul Mali a gabansa mai kula da dukiyar yazo
gaban gimbiya da lissafin komai kuma yayi bata
bayanin yadda ake sarrafa dukiyar bisa tsarin
tsohon galadima,koda ta fahimci cewa tsari ne
nason kai da son zuciya,domin akwai wadansu
kudade da suke shiga aljihun galadima a banza
maimakon su rinka zuwa hannun talakawa
mabukata,sai ta dubi ma'ajin baitul Malin
tace,yau zan canja tsarin komai na dukiyar dake
cikin baitul Mali kuma zan kirawoka na baka
komai a rubuce bisa yadda nakeson a rinka
tafiyar dashi.
Koda waziri yaji wannan jawabi na gimbiya sai
zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone
kuma yaji ya sake tsanar gimbiya fiye da ko
yaushe,ba komai ne ya janyo hakan ba face ya
san cewa da zarar gimbiya ta sauya tsarin komai
na
dukiyar baitul mali shike nan ya daina samun
kudade masu yawan gaske wadanda dasu ne
yake sharholiyarsa a garin yake yin duk abinda
yaso har ma ake shakkarsa.
Da farko attajiran garin sun dauke
cewa sarki Aiyuba ne yake baiwa dan uwansa
Ridwan kudade shi yasa yake tafiyar da rayuwar
mai
mugun tsada a gidansa da harkokinsa,amma a
yanzu da aka sauke shi daga matsayinsa na mai
kula da bailtu mali sai komai ya sauya ya kasa
cigaba da bushasha kamar yadda ya saba duk da
ci
gaba daya samu a majalisa ba baya ba.
Bayan an dawo daga fada an fara walima mutane
maza da mata,sarakai da attajirai,da masu fada
aji suna ta ciye ciye da shaye shaye a cikin
babban falon gidan Waziri Ridwan amma shi mai
gaiyatar babu shi a wajen sai matarsa Gimbiya
Ra'isa wacce itace take
karbar baki tana sawa ana kaisu inda ya kamata
su zauna,koda Ra'isa taga an shafe kusan rabin
sa'a da fara walimar amma mijinta bai gama
shirin ba ya fito daga cikin turakarsa sai ta tafi
izuwa turakar tasa da sauri.Tana shiga sai ta
iske shi a zaune bisa kujera
ya kifa kansa akan tebur yana ta sheshshekar
kuka,al'amarin daya dugunzuma hankalinta kenan
ta ruga gareshi ta dago da kansa suka dubi juna
tace,Haba yakai Abul Zainur yaya zaka zauna
anan kana kuka alhalin yau rana ce ta farin ciki
bisa babban mukamin daka samu,ga masoyanka
can fa
sun taru a falo ana tayaka murna.Koda jin
wannan batu sai waziri Ridwan ya kyalkyale da
mahaukaciyar dariya,al'amarin daya firgita Ra'isa
kenan ta danja da baya ta kura masa idanu
kawai.Take Ridwan ya tsuke bakinsa ga barin yin
dariyar ya dubeta cikin
yanayi na bakin ciki a lokacin da hawaye ya zubo
masa yace,Yake matata kiyi sani cewa dan uwana
sarki Aiyuba ba matsayi ya kara mini ba tauyeni
yayi domin wannan kujera ta waziri daidai take
da ajiye ice ko dutse abinda bashi da rai wanda
bazai iyayin
ko motsin komai ba,kin sani cewa bani da wani
buri a wannan duniya face na zamo gagarumin
attajiri
wanda babu kamarsa a duniya a tarin dukiya
dajin dadin komai na barwa duniya abin tarihin da
baza'a
taba mancewa dashi ba.
A da nayi tunanin cewa da zarar dan uwana sarki
Aiyuba ya mutu zan cika wannan buri nawa tunda
ni kadai nake da gadon duk abinda ya mallaka
amma a yanzu daya sami haihuwa sai dukkan
burina ya ruguje tunda gimbiya Nauwara zata
gaje dukiyar ce wacce a halin yanzu babu wani
mahaluki a doron kasa daya mallaki a
dadinta.bani da ikon batar da gimbiya Nauwara
ko na kashe ta domin duk abinda zan aikata a
boye sai ya gani da karfin sihirinsa na tsafi.
Babban abin bakin cikina shine na fuskanci cewa
wannan matsayi
na galadima da sarki ya rabani dashi yafi
kowanne mukami daraja da muhimmanci akasar
hatta karagar sarki kuwa...
Dalilin da yasa na fada miki haka shine gaba
daya harkokin kudi na kasar yana cikin wannan
matsayi haka kuma galadima shine da jan
ragama ta zabin sarki kuma shine mai baiwa
sarki shawara akan harkokin mulki,kinga kenan ko
na hau kan karagar mulki gimbiya Nauwara ce
mai jagorantar mutane a fakaice idan tayi aure ta
sami haihuwar 'da
namiji,danta zai iya zama sarki kinga kenan a
karshe nida duk iyalina zamu tashi a tutar babu,ki
tuna cewa a yanzu danmu Yarima Zainur da
shekaru biyu kadai ya girmi Gimbiya
Nauwara,yaushe ne
shima zai girma kuma yaushe ne nima zan hau
karagar mulkin kasar nan har ya gajeni?
Koda Waziri Ridwan yazo nan a zancensa sai ya
fashe da kuka,al'amarin daya karya zuciyar Ra'isa
kenan taji ta kamu da tsananin tausayinsa don
haka sai ta rungumeshi ta shiga rarrashinsa tana
cewa,
Ka kwantar da hankalinka yakai Mijina kayi sani
cewa komai nisan jifa kasa zai fado tunda idan
babu
mutuwa ai akwai tsufa da cuta,da...


Read / Download WASIKAR JINI 1 to 8

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On WASIKAR JINI 1 to 8
avatar
abdulrasheed-yusuf

4 months ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album