Join Our WhatsApp Group

SAKAYYA Complete Hausa Novel Document by SAKAYYA


SAKAYYA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 110431SAKAYYA

Reading Time: 9 Hours

Added On: 13, Nov 2023

Author: Aisha Ali Garkuwa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 09097853276

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 621.83 kb

File Type: txt

Views: 5008+

Download: 4345+

Last download: 2 days ago

Description/Story: 2:03 Pm.
Friday 4 February 2022.

*SAKAYYAH*
*GARKUWA SABON SALO*
Book One, page 1
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*


*FREE PAGE*


*Komai na rayuwa sai Allah ya nufa, kugafa Time and Date din da na fara rubata littafin nan amman sai Allah ya bani ikon fara sakinshi.*


Wannan littafin nawa mai suna FATTANAH kirkirerren labarine, Amman akwai wasu abubuwan dama da sun faru da gasken gaske, banyi da wata ko waniba, Hakkin mallakarsa nawane AYSHA ALIYU GARKUWA, ban aminceba! ban lamunceba!! ban yardaba!!! ayimin amfani da labarin littafina tako wacce sigaba, har sai in an nemi izinina an samu sahalewata, sabida haka ga number ta 09097853276 kafin ayi komai a nemi sahalewata, komai yafi daɗi cikin mutuntaka zama lfy yafi zama ɗan Sarki!!!..

*Yah Allah ka bani ikon rubuta al'khairai da abinda zai amfani al'ummar fiyeyyen halinta, Ya Allah kayi riƙo da hannayena, tunanina, idona, yatsuna, nazarina, ka hanani samun damar rubuta duk wani abin ƙi da zai zamewa al'ummar musulman masifa ko ƙazanta ko bata tarbiyya, ya Allah ka bani ikon tunasarwa da jan kunne da jan hankali ih zuwa ga nasarar mai tawakkali da imani da riƙo da ibada, Ya Allah ka nuna min ƙarshen littafin nan lfy kamar yadda ka nuna min forkonsa Lfy dani da iyayena ƴaƴana, yayuna, ƙannena, da maƙota makaranta na masu biyana kafin su karanta da masu karanta na sata da dukkan musulmai ya Allah ka nuna mana forkonsa da ƙarshensa lfy kayiwa rayuwarmu data ƴaƴan mu al'barka ka shirya mana ahlinmu ka bawa yayanmu mata maza na gari, mazan ka basu mata na gari, aurarru ka basu zaman lfy da zuri'a ta gari ka tsare mana tarbiyar yaranmu bisa tafarkin dai-dai. Ya Allah kayi mana rufin asiri duniya da ƙiyama, ya rabbil izzati ka dubi bayinka masu buƙatan haihuwa da aure da idanunka masu rahama ka basu masu albarka, marasa lfy Allah ka basu lfy masu juna biyu Rabbi ka sauƙesu lfy masu fama da matsar babu da bashi ya Allah ka yalwata masu ka basu arziƙi mai albarka la basu ikon biyan bashi, Ya Allah ƴaƴan musulmai da tatbiyarsu ke a gurɓace Allah ka shiryesu. Ya Allah ka kawo mana sauƙin wannan zadar rayuwar, ka magance mana fitintinun dake damun ƙasarmu, mahajjatsnmu kasa sunyi hajji Mabruk. al'farmar Annabi da al'ƙur'ani, ya Ubangijin talikai ka jiƙanmu ka yafe mana kurarenmu kayi mana Kekkyawar ƙarshe kasa mucika da kalmar shahada yayin barinmu duniya ka sadamu da mala'ikun rahama masu zaran rai salamun salaman. Yah hayyu ya ƙayyum birahamatika astaƙisu ka jiƙan mahaifiyata Fatima (Deddena) ka sanyaya mata makwanci ta ka haskaka mata ƙabarinta ka yelwata matashi ya Allah kasa tana cikin dausayin jannatul firdausi ya ubangijin kasa can yafi mata nan, ya Allah ka bamu haƙurin da juriyan rashinta. Ya Allah kai mata rahama al'farmar Annabi da al'ƙur'ani🙏🏻😭😭😭*

~Aisha Alto, Mom Bobo, kune wanɗa nake ganin kamar kunsan ciwon da nakeji a raina a duk sanda na tuna banda mahaifiya, domin kusan lokaci daya muka rasa iyayenmu. Allah yayi musu rahama yasa sun huta, ina tunawa a lokacin nafi son yin mgn daku fiye da kowa a social media, domin gani nake kun san yadda nakeji a zuciyata, Aisha Alto addu'o'in da kikeyi min dani da mahaifiyata yasa nakejin ke ta dabance mom bobo kuwa munsha kokawa tare, mu rasa mai lallashi wani tsakaninmu~


*Littafin SAKAYYAH na kuɗine 1k ne kacal wannan Free page, yar uwata ki biya ki karanta abinki cikin Salamah 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. In baki da account zaki iya bada a P.O.S ki Basu 100 na su turo 900 wasuma 50 suke amsa, ko kuma ki sayi katin Mtn sai ki copy number's ɗin katin ki turo min ta WHATSAPP. Banda V.T.U. dan Allah.*


A hankali ta turo ƙofar ɗakin nata, cike da jin nitsuwa da salamar, sanin ta yanke baccinta ne ta tashi cikin talatainin daren, domin neman aminci da yardar ubangijinta daya halincceta ya bata rai da lfy, cikin rashin tsoron da ko yaushe in ta tashi tsakiyar dare, Allah ke yaye matashi, duk da kasancewar makaken gidane bila haddin wanda ke kewaye da tsirrai, kana ga wutsiyar kogin Gembulan na jihar Taraba da yayiwa gidan zanen harafi C, yayinda kuwa su biyu ne rak suke rayuwa a cikin ƙaton gidan.
Koda yake tazarar dake tsakanin ɗakinta da sade ɗin jikanta Modibbo tazarace mai yawan gaske, sai dai suna raya gidan da Ambaton Allah a koda yaushe, shiyasa ubangiji yake saukar musu da cikekkiyar nitsuwa salama.

Numfashin ta fesar a hankali tare da gyara ɗaurin zaninta, kana ta gyara riƙon da tayiwa yar butar dake hannunta.

Ido ta lumshe tare da buɗe su a hankali, sabida wani irin sassayan iska mai masifar daɗi da ratsa jiki da taji yana ratsata da sakar mata wani irin nitsuwa, salama, da farin ciki.
Juyowa tayi ta kalli yamma sabida ganin wata ta faɗi alamun dare ya tsala, domin watan tayi kwana goma sha ɗaya ne, faɗawanta ke nuni da biyun dare ko ɗaya da rabine.
Kai ta ɗan juyo gabas ta kalli ƙofar safe ɗin Moddibo wanda yake can nesa da ita sosai, yayinda wasu sassayan fulawowi yayiwa ko ina na gidan ƙawanya.

Tsarin ginin gidan tsarine, wanda ko a ƙasashen turawa na musamman ne,
Ƙaton gidane mai yalwar fili.
Daga can bakin gate ɗin gidan filine mai girma wanda zai iya ɗaukar motoci shida ba tare da wata ta gogi wata ba, ko matsi wataba, ɗakine mai ɗan girma a bakin gate ɗin wanda ke haɗe da bayi a ciki, da yar baranda alamun ɗakin mai gadi, saidai babu kowa a ciki.
Daga gefe kuwa watsu tsala-tsalan bishiyoyin na mijin gwanɗa ne masu masifar tsawo da ganye mai duhu a can sama sune suke jere reras a jikin katangar gidan baki ɗaya, daga ƙasansu kuma, wasu tsirran fulawowi ne masu masifar kyau da sanyi masu collor's blue, red, and yellow.
Tsakanin farfajiyar gidan da can cikin gidan kuma, akwai wani katanga a tsakiyar da kuma ɗan madaidacin gate shima ɗin mota zai iya wucewa ta nan,
Cikin katangar shima zagaye yake da bishiyoyin dabino ta wajen ta cikin kuma in bishiyoyin mangoro ne guda biyu sai daya gefen kuma na goiba, ne da kuma cabɓulle (Tsada) akwai fili ta gefen hagu, inda motoci biyu zasu iya tsayawa a wurin.
Sai gefen dama kuma, wani ɗan siririn hanya ne, wanda fulawowi ne yazama kamar katangar wurin, tafiya kaɗan zakayi ka riski part din Moddibo, irin ginin nanne mai tudu, duk da bawai bene bane amman ginin a sama sosai yake, forko daga wurin baranɗace mai girma, da tudu wacce ke malale da tayis mai masifar sheƙi, a bakin barandar anyi wasu steps guda bakwai masu faɗi, kafin hawa barandar,
A gefen dama da hagunsa kuwa wasu fararen ƙarafun silver ne masu kyau sukayiwa barandar garkuwa, a ƙasansu kuwa, wasu. Tukwanen ƙasane masu tsirran fulawowi masu masifar kyau da ƙamshi, kana a kan ko wanne step akwai tukanen a gefen hagu da daman a jere, guda bakwai-bakwai kenan.

In ka gama haurawa saman barandar kuwa ka juyo ka kalli bayanka ras zaka hango tekun Gembilan kwance a can, da tsirran bakin Kogin.
A can bayan Part ɗin nashi kuwa wani tamfatsetsen garding ne mai masifar kyau da ƙamshi, sai wani tabkin wanka mai kyau kujeru guda bibbiyu a kusurwowin alƙibila, sai kuma gado a gefen dama da hagunsa,
Cikin Part ɗin nasa kuwa, wani tamfatsetsen parlour ne mai kyan tsarin ƙasaitattun kujeru da labulaye da kayan wuta, komai na ciki farine tas,
tambarin shaidar tsananin tsabtar ma-mallakin wurin kenan, sai ɗan ratsin sky blue, wanda hakan yasa in ka shiga falo sai kayi zaton a sararin samaniya kake shawagi.
Sai dinning area, da kuma kitchen, sai wani yalwataccen corridor'n wanda ke gefen dama da hagu ko wanne bedroom ɗaya ne a ciki, sai can mashigar falon nanma akwai wani ɗan madaidaicin bedroom.

Hatta cikin falon kuwa kewaye yake da fulawowi, shaidar ma-mallakin wurin masoyin sirraine da sanyi da kamshi window palon irin manyan nanne har kusan ƙasa, haka yasa yana iya hango bakin tekun daga cikin palonshi.

Daga Part ɗin nashi kuwa gefen hagu akwai wata hanyar mai kewaye da tsirrai, wacce ke sadashi da can cikin gidan.
inda ɗaki ɗaya ne rak, na kakarsa Innayi wacce tace ya isheta rayuwar duniya.
Sai kuma kitchen nata a gefe mai tsarin gargajiya, kana da bayan gidanta can gefe, domin sam taƙi yarda ayi mata bathroom a cikin ɗaki, acewarta kada santsin tayis ya ƙaryata, dole haka Modibbo ya haƙura da tsarinta komai na gargajiya, hatta gadonta taƙi a sauya mata.
Sai dai ta amince da tsarinsa na zageyesu da tsirran shuke-shukensa da zuba mata tattausan Turkey carpet mai masifar taushi, tsarin dakin nata komai ya fito kamar na gidan sarakai shuke-shiku kuwa ba dama.
Daga can gefen hagun side nashi, wani wurine mai ɗan tudu wanda akayiwa rumfa irin ta gargajiya rumfar bunu, gefenta zagaye, da tsirran, cikinta kuwa wasu tsala-tsalan kujerune masu masifar kyau guda hudu da table a tsakiyar su, sai ɗan dandamali na al'adar mutanen Gembilan wanda suke hura wuta a ciki sabida rage tsananin sanyin da ake tsula musu.

ALLAH kuma ya yelwata hannunsa da al'barka duk abinda ya shuka sai ya tsiro a yalwace.
(Moddibo kenan)

Numfashi Innayin ta sauƙe lokacin da ta gama ƙarewa farfajiyar gidan da lukkunan gidan kallo,
duk da ba hasken farin wata, babu kuma na taurari sosai, sakamakon hadarin gajumaren da yayiwa sararin samaniya ƙawanya.

Juyawa tayi ta nufi, ɗan bayan gidanta dake, nan gefenta kaɗan, tana maiyin taku cikin yanayin tsufar da ya cinmata, tare kuma da taka tsantsan gudun kada santsin simintin dake malale a farfajiyar sashin nata ya kadata.


A bakin ƙofar bayin ta ɗan tsaya tare da yin, addu'a shiga bayin.
“Allahumma inni'aauzubika minal kuɓsi wal kaba ihsi?.
Kamar yadda Moddibo ke nusar da ita mahimmancin addu'a ako wanne lokacin.

Bayan ta fito ne, da addu'a a bakinta, ta zauna bisa, wani dutse mai kyau dake bakin barandar ɗakinta, ta fuskanci gabas.
Tare da fara al'wala.

A can side ɗin Moddibo kuwa, kwance yake, harshensa jiƙe da ambaton Allah, duk da cikin bacci yake.
Saidai baccin, ba baccine kamar na kowa ba, domin bacci yake cikin wani irin yanayin daya gaza tantancewa, shi ba bacci ba, kuma ba ido biyu ba, ba kuma mafarkiba ba kuma zahiri ba, ba kuma a sumeba wasu abubuwan da lokuta da dama yana riskarsu cikin bancinsa yake fuskantar su.

Ita kuwa Innayi a hankali ta gyara zamanta, tare da juyowa ta kalli bayanta, da sauri sabida wani irin haske da taga ya gilmawa ganinta, sai kuma tayi saurin juyowa gabanta ta, kalli gabas saitin ɗakin Moddibo domin a zatonta ko an dawo da wutar nepa ne.
Ga mamakinta kuwa, babu alamun hasken wutan nefan sai wani irin sanyi mai ratsa jiki.
Haka nan taji wani yanayi na rufeta,
wanda yafi kama da tsoro abinda bata taɓa fuskarta sa acikin gidanba duk duhun dare.

Hakan yasa tayi saurin sunkuyar da kanta taci, gaba da yin al'wa'ar, hannunta ta wonken, kana ta ciko tafin hannunta na dama da ruwa, zata kai bakinta domin kuskuran baki kenan.
Wani irin saurin ɗago kanta tayi ta kalli gabanta, sabida ganin wani irin masifeffen haske mai firgitarwa da taga ya haska illahirin duniyar har hasken yana haska cikin ruwan dake tafin hannunta.
Cike da tsoro ta zubda ruwan tare, da juyawa ta kalli.
Gabas da yamma Kudu da Arewa.
Babu mutun ba dalilinsa, babu kuma alamun ta inda hasken ke fitowa.
Kana kuma ga kuma hasken dake tsananta.

Da wata sassayan iska mai ratsa jiki da sanyaya zuciya.
Wacce tasa Moddibo gyara kwanciyarsa tare da ci gaba da wani irin bacci mai mayataccen daɗi da yaji ya dannesa da kuma shigo masa da wasu sabbin ababen gani a idanniyansa, yayinda harshensa kuwa ke nanata addu'o'in masu tarin yawa.

Yayinda ita kuwa Innayi, wani irin tsuma jikinta ya farayi lokacin da taga gaba ɗaya duniyar ta ɗauki wani irin mashahurin haske mai kyan gani.
Wanda ta rasa ta ina yake fitowa.
“Innalillahi wa innailaihi raji'un hasbunallahiwani'imanwakil?.
Ta fara maimaita cikin firgici lokacin da ta ɗago kanta, ta kalli sararin samaniya.
Wani irin kerma da makerketa mai cike da tsananin tashin hankali, firgici, tsoro, da karkarwa jikinta ya farayi, sabida yadda taga ubangijin talikai, yana wanzar da ikonsa da buwayarsa a sararin samaniya.
Wasu irin masifaffun hawaye masu zafi wanda irinsu kan tsinkowa ɗan Adam lokacin da yaga tsananin abin tsoro da shiga firgici da ƙudurar Allah.
Kar-kar haka jikinta yake rawa, ganin yadda taurari.
Suke fizgowa sunayin wani irin haske mai kashe idanun ɗan adam, wanda sune take ganin duk sun cika sararin samaniya da haske tamkar rana.
“Ya hayyu ya ƙayyum birahamatika astaƙisu, ya Salam, innalillahi wa innailaihi raji'un, la haulawa ƙuwta illabillahil aliyul azeem?.
Sune tasbihai da furucan da ubangijin ya bata ikon furtawa, lokacin da ta fara ganin taurarin sunayin ƙasa tamkar zasu faɗo, ƙasa domin gani take kamar sai sunzo har ƙasa sosai kamar zasu taɓo rufin kwanon ɗakin Modibbo, sai kuma taga ubangijin ya janyesu sun koma sama da azaban sauri tare da tartsatsin haske mai kyan gani.

Fadin halin tsoro ko tashin hankali ko firgici da ɗimuwar da take ciki ya zarta zaton mai zato, ya wuce tunanin mai tunani ya shallake nazarin mai nazari, wasu irin wahaye ne ke kwaranyo mata.
Yayinda ta koma baya ta jingina bayanta da jikin filan barandar ɗakinta dake bayanta, ta jingina kanta tana kallon sama.
Tare da fara nanata kalmar shahada.
Domin ta gama sallamarwa cewa, lokacin ta yayi, ma'ana mutuwa zatayi.
“La hailahaillahu Muhammadu Rasulullahi sallahu alaihi Wasallama?.
Shi ta fara maimaitawa can ƙasan maƙoshinta domin.
Komai na jikinta ya fara tsayawa, sabida azabebben tsoron daya rufeta da cikekken imanin kaɗaita rabbissamawati wal ardi zuwa yanzu tama fara ɗimautan shin anyama kuwa a raye take?.

A ƙalla 30 minute ubangijin talikai na wanzar da ikonsa! Da kuma, buwayarsa!! Can kuma sai ta fara ganin gaba ɗaya duhu na meye hasken.
Duhu mai cike da sassayan iska.
Wani irin tsorone ya kuma rufeta wanda ya diro mata da zazzafan zazzaɓi mai haɗe da masifeffen ciwon kai.
Wanda ya tilasta mata kife kanta bisa guiwowinta tare da rumtse idanunta tamkar zata liƙesu da juna.

A can cikin masarautar Gembilan kuwa, Gimbiya Dadu ce, ke kwance bisa tsakiyar gadon ta, wani irin masifeffen mafarki mai tada hankali takeyi.
Wanda yasata ihun neman ceto, wanda bata saninba har ya fito fili.
Fitarsan ne, yasa hadimarta saurin shigowa tare, da tadata. Ai kuwa cikin tsananin firgici da tsoro ta farka tana mai karkarwa, lokaci guda kuma zazzafan zazzaɓi ya rufeta.

A nan gidansu Moddibo kuwa.
A hankali ya fara buɗe idanunsa tare da...


Read / Download SAKAYYA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On SAKAYYA
avatar
hajara-ahmad

6 months ago

Reply

Nice novel

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album