Join Our WhatsApp Group

NANA KHADIJA Complete Hausa Novel Document by NANA KHADIJA


NANA KHADIJA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 55134



NANA KHADIJA

Reading Time: 4 Hours

Added On: 01, Dec 2023

Author: Binta Umar Abbale ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08089965176, 07084653262

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 297.44 kb

File Type: txt

Views: 1354+

Download: 658+

Last download: 3 days ago

Description/Story: NANA KHADIJA (littafi na daya)


NA

BINTA UMAR ABBALE

(Maman Abdul Wahabu)



NA FARA DA SUNAN ALLAH SARKI BUWAYI ,WANDA YA QAGI SAMA DA KASA SARKIN DA BABU KAMARSHI,

ALLAH KAYI DADIN TSIRA GA ANNABI MUHAMMADU(SLW) WANDA KABAWA YA YADDAR KA ,ALLAH KA KARA TSIRA DA AMINCI A GARESHI DA AHALINSA DA SAHABBANSA TSARKAKA


ALLAH YADDA KABANI IKON RUBUTA LITTAFIN NAN ,LAFIYA INA ROKANKA KASA IN GAMA LAFIYA, ALLAH KA YAFEMIN KUSAKURAI NA NA CIKI.
AMEEN.





WANNAN LITTAFIN QAGAGGE NE DA GA NI MARUBUCIYAR BANYI DOMIN WANI KO WATA BA WANDA YAGA YAYI DAI DAI DA RAYUWARSHI A RASHIN SANI NE




GARGADI



BAN YADDA WANI KO WATA YAYI AMFANI DA WANI BANGARE NA CIKIN LITTAFIN NAN

BA BATARE DA SANINA BA ,DUK WANDA YA TABAMIN WANI SHASHE A CIKI ,ZAMU TSAYA A GABAN HUKUMA





_WANNAN LITTAFIN NA KUD'I MALLAKIN ME SHI NI MARUBUCIYAR TUNDA 1,23,4,5,6 DIN SA BAN MALLAKAWA KOWA BA IN KANA BUKATA SAI KA BIYA KUDIN KARATU ZAKA SAME SHI DAGA FARKO HAR KARSHE HANNUN MARUCIYAR, WALLAHI DUK WANDA YW FUTAR MIN DASHI HAR 'YAN CIMA ZAUNE SUKA SAMU SUKA SIYAR MIN DASHI BAN YAFE MASA BA, NA FADA CEWAR DUK WANDA YACI DA GUMI NA UBANGIJI YAYI MIN SAKKAYA DOMIN BAZAN TABA YAFEWA BA ALLAHI. NASAN ALLAH BA AZZALIMI BANE ZAI BIMIN HAKKINA KAN ZALINTA TA DA AKAYI.




DOMIN SAMUN CIGABAN WANNAN LITTAFIN KAN FARASHI ME SAUKI DARI BIYAR KACAL #500 DAGA 1,2,3,4,5,6 DUK AKWAI A GURIN MARUCIYAR DON HAKA ME BUKATAR KARANTA CIGABANSA SAI YA KIRA WANNAN NUMBAR KAMAR HAKA.

08089965176
07084653262







*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*









Lkace kwabo fada ya rin ca6e tsakanin Dije da indo sai faman ko kawa suke Dije sai faman zagin indo take itako indo sai faman dukan ta take dake dama Dije bata da wani karfi sai aikin tsokanar fada gashi bata da wani jiki indo ta fita jikin girma Sa'a ko sai kokarin rabasu take yi suna hadawa da,ita.

wata irin tsawa! su kaji an ce "kai wannan wane irin iskanci ne kukeyi anan da dabbanci "? cikin sauri Dije ta saki indo sai haki! take ta juyo jikinta sai tsuma ya keyi ganin yaya Ali ne a tsaye a gabansu ,,sai faman zare ido take harara ya banka mata yace "wato ke dan ubanki bazaki daina wannan iskancin ba ko? kitara yara ki ta kokawa a waje dan rashin kamun kai" ya mutsa baki tafara tana kunkuni dashi "to ina ruwanka za kazo ka wani ta kura mana ni banasan a shiga min sabga" duka ya kai mata abakin cikin zafin nama yace "dan ubanki wakikewa haka nisa anki ne " ? cikin sauri ta dafe bakinta hawaye ya na zuba tace "Allah ya isa mugu" cikin kunkunin tayi maganar mari ya kaimata gami da cewa "wato bakin ki bazai mutu ba ko wallahi sai na gyaramiki zama shashashar yarinya kawai stupid " yafada tare da jan hannuta tana turjewa yadaki kafarta ta fadi kasa ya hau janta a k'asa

Su indo kuwa tun lokacin da yaya Ali ya mari Dije suka gudo sabuda sun San halinsa harsu zai hada ya Zane babu abinda ya dameshi,,janta yake yana dukanta da kafarsa itako bakin ta baibar yimai rashin kunya ba Nene, CE azaune a tsakargida tana ta faman gyaran wake ta ji ihun Dije tashi tai da sauri ta tana gyara daurin zaninta tana fadin "wallahi na tsani mugunta irin ta "yayan unguwar nan me kuma marainiyar Allah tai musu suke dukanta" kafin tarufe bakinta ta hango Dije a kasa Ali ya na janta kamar yana Jan tsumma Salati ta tabka tace "kai Ali wannan wane irin abune mai tayi maka dan mugunta "? tafada tare da karasawa tana kokarin kwatar Dije daga hannunsa "wai bada kai nake ba kasake ta mana wallahi ka kiyayeni akan wannan marainiyar Allah sa,arkace ita dazaka dunga dukanta iyi"? ,sakinta yayi yana jan tsaki tare da hararar Nene "yace wallahi Nene ke kike daurewa yarinyar nan gindi take yin abinda tagada ma". "to ina ruwanka da,ita iyi?" cewar Nene. cikin 6acin rai ya kalleta tare da daure fuskarsa yace "samunta nayi fa a waje ta tara yara suna ta faman dan be sai kace wasu dabbobi dan nai mata magana tahau zagina wallahi kija mata kune ta kiyayeni kan in bar garinnan sai na canja za mata kammanni da duka"
Harara Nene ta galla masa tace "ka ki yaye ni Ali nifa ba na San ne man magana taya daga zuwan ka zaka ta kurawa yarinya tana wasa da kawayenta gaskiya in dai zaka zo ka ta kura mana ne gwara ka juya ka koma bana son zuwan naka haba ina dalili." Tak'arashe maganar tana gyara daurin zaninta,

Fuskarshi babu Walwala yake kallonsu yana Mamakin Abinda Nene tace tabbas Nene in dai a kan yarinyar nan ne babu da Wanda baza ta 6ata ba ,cikin yanayin maganarshi yace "ae ba gurin ki nazo ba gurin "yan Uwa da Abokan Arziqi nazo wancan Mara kunyar yarinyar bata isa ta Sani na bar garin nan ba batare da na shirya ba"
Harara D'ija ta galla masa tare da murgude baki tana bayan Nene A la6e
Yana kallonta yana Mamakin Rashin kunyar yarinyar,

Nene tace "to babu ruwanka da'ita har ka bar garin to kaji!!

Bai ce komai ba ya Nufi bakin rijiya domin daukar bota da nufin daura Alwala ganin har an soma kiraye kirayen sallahr magari ba

Ya na sane ya zira kafarshi daya wacce ke sanye da takalmi sawu ciki ya mutsikewa D'ija "yan ya tsu yayi saurin dauke kafarsa ya sakai ya fice daga gidan hannushi riqe da bota


Wata kara D'ija ta kurma tana kallon kafarta guda domin Sam bata lura dashi ya take mata ba

Da sauri Nene ta jiyo tace ke lafiyarki kuwa ?Cikin ihu D'ija tace "Nene kunama ce ta har beni yanzu"


Da sauri Nene n ta kafama kafar D'ijan tana duba wa gami da jan yeta da gurin tana sallalami , ta hau duba kafar


Tace" kefa kin fiye sangarta haka harbin kunama yake, ko dai wani kwaron ne ? Tashi ki bani guri in kara duba gurin"

Da sauri D'ija ta matsa gefe tana jan kafa sai kace wacce tayi targaade

Hakadai Nene takaraci dubanta a gun bata ga komai ba juyowa tai gurin dijan tace" Ai sai ki tashi daga gurin ko kije kiyi alwala lokacin sallah yayi na gaya miki kidai nai wa manya rashin kunya kinki ji idan yaje yaji miki ciwo babu ruwa na Ato,,cikin zumbura baki dije ta tashi da ga gun ta nufin inda butocin Al,wala suke ta dau daya dan duk abunta bata wasa da sallah da lokaci yayi take barin abinda take taje tai sallah

Shi kam Ali yana gama alwala wani yaro ya bawa butar ya mayar gidan ya huce masallaci bai dawo ba saida ya jira lokacin isha ya gabatar da ita yai adu'oinsa sannan ya dawo gidan.

Nene ya tarar ta idar da sallah isha dije kuma tana can gefe itama ta idar da sallahr tana ta faman cin wake da shinkafa wanda tasa nene tayi mata itakam tana bala'in san wake da shinkafa da manja da yaji tai ta zabga yaji tana ci tana zuk'ar baki, ko kallon inda take bai yi bah ya samu gefen Nene ya zauna yana karewa tsakar gidan kallo dan shi kam mutum ne mai tsamtsami abu kadan sai yasayi tashin zuciya yana da bala,in stafta komai nashi a tsare dan baya shiri da kazami gashi da wani irin hali. muskiline sosai sai ya gadama yake magana ko acikin abokansa ma haka dan har suna suka samasa ammafa duk wannan halinnasa bai raina mutum ko mai kankantarshi da iyayansa ya na bala'in sansu da kannansa to suma suna ji dashi sosai sabida ya nai musu abinda suke so Ammafa suna jin tsoransa musaman idan sukasan sunyi wani laifin dan baya musu wasa musamman akan harkar karatunsu, wannnan kenan

Nene ce ta jiyo bayan tagama lazimi tace" to sarki kafi sarki mulki kazo kazaune min yanzu zakafara iyayin naka ko"? tafada tana gallamasa harara
Murmushi ya saki ya kalleta yace " ke ba ayin abin arziki da ke daga zuwa na ko ruwan kirki baki bani nasha ba kina ta wani naiman fada dani" dariya Nene tayi tace" to ai kaine daga zuwanka ka fara halin naka"

Ta shi tai tai nufi madafi wata katuwar kula ta fito dashi ta a jiye a gabansa hade da da faranti tace "gashinan ai mutumin kane nai maka sabida nasan ka ce yau zaka zo" tafada tana kokarin zuba masa tuwon shin kafa ne da miyar taushe wanda taji nama da manshanu sai kamshi ne ke tashi agun tun lokacin da tabude kular ,ta zuba mai ta ajiye a gabansa tace"to gadanga bissimilah"tafada tana murmushi dan in taso tsokanarsa da wannan sunan take kiransa.

Gyara zama yai ya ce "saura ruwa ai cika ladanki uwargidana" gyara fuska tai tace "wannan kuma sai ka tashi ka dauko da kanka wai kai komai sai anyi maka" tafada tana harararsa hade fuska yai yace " sai kiyi ai nikuma bazanci ba indai baruwan kika kawumin ba"/ya fada yana kallonta da murmushi a fuskarsa dan yasan halinta indai baici abinci ba tashin hankalinta zata yi.

Duk wannan abin da suke dije na gefe tana jinsu dan indai da sabo ta saba indai yazo sai sun ta tabkawa da Nene

Nene ce ta kalleta tace" dije na tashi ki dauko masa ruwa a kinji tunda nari ga na zauna bazan tashi"

Wani irin kallo yabi Nene dashi daga ita har dijan yace "har indai wannan yarinyar ce zata d'auko min ruwa wallahi bazan ci abincin ba kina ganin yanxu tagama kazantar ta bayan tagama lashe hannunta ko wanke wa batai ba sabida tsabar kazama ce ita kice ta d'auko min ruwa insha ki kwashe abincinki na fasa ci ya Riga yagama yin sanyi ma" yafada yana Dada gyara kwanciyarsa a gefenta harararshi tai ta tashi tana sababi "wannan yaro halinka sai dai kai matar ka zatasha iyayi da feleke" cikin daki tashige inda firji yake tadauko mai ruwa mai sanyi.

Dije kam tana gefe sai faman harara take aika masa dashi a zuciyarta take fadin " a kwai babban kazami ma irin ka wai kai mai tsafta kadinga wani tsartar da yawu saika ce wata mace"
Harara a duhu Dija take domin shi Ali bai San ma tana yi ba

Nene CE ta,ajiye mai ruwa na roba hade da lemo mai sanyi tace "gashinan to sarkin tsurfa" tafada tana zama a gefensa ,,tashi yai yaje fi ya dauraye hannuwansa duk da cewa ba wani abin ya ta6a ba

Dawo wa yai ya zauna ya jawo plate d'in abinci yai bisimillah ya fara ci ,humm Ali kenan cin abincinnasa ma abin kallo ne cike da tsurfa yake ci yanaci yana ta6e baki yana kallon Nene yana jiran yaji abinda zata ce

Itako kallonsa batai ba sabida tasan Neman magana yake ta cigaba da sabgoginta,,

Dije kam tashi daga gun tana faman zumbure zumburen baki taje ta wanke hannunta ta dawo sai taji tana san taci towan gashi cikinta ya cika ba yadda zata yi haka tashige daki ta canja kaya ta haye gadon Nene tai kwanciyarta

Yana gama cin abinci ya tashi daga gun ya canja guri bayan ya wanke hannuwansa. haka Nene ta tashi bayya da ta iya ta kwashe kayan ta gyara gurin tana yi tana sababi shida yai mata shiru a zuciyarsa yace da rigima kenan idan kikaji da abinda nazo garin kenan duk wanann da kike shafar mai ne

Bayan ta gama gyara gun ta dawo ta zauna tana kallonsa tace "tun dazu nake jiran inji dame kazo min yau kuma ?

Murmushi ya saki yace" Nene mu kenan dame nazo miki kuwa inba da alkairai ba"

Washe hakora tayi tace "dan nema to ina jinka" tafada tana tsare shi da ido gyara fuskar sa yayi Alamar maganar da zaiyi mai muhimanci ce yace " sako ne da ga ABBA,
yace kihada kayanki gaba daya inzan koma in tafi dake dake da waccan marakunyar yarinyar.

Wani irin kallo Nene ta watsa masa tace "wallahi ka kiyayeni Ali ka rainani ko bazanje ba"
Tun yaushe ake magana daya nace bazan jeba ya kyalemu anan ina ce wancan satin shima basiru yazo nace bazan jeba saime zaku takuramin sai nabar daki na inatafi wata abuja ban zuwa tafada tana gyara zamanta"

Kallonta yayi yana kwantar da kai dan ya fuskanci inba haka yayi mata ba da akwai matsala dole sai yai aikin rarrashinta,

"Haba Nene wai yaushe zaki gane ne ba fa cewa akai kitafi kizauna acan gaba daya ba zaki dinga zuwa anan lokaci zuwa lokaci ,,kiyi hakuri mutafi kije kidan huta acan kinji uwargidana" ya fada yana murmushi

Ko kallonsa batai ba yace "kinji Nene ,, tai mai banza

Yace "to shikkenan tunda kinza6i atafi da da dijan taki babu matsala ai" cikin sauri tadago kai tana banka masa harara

Dariya ce ta su6uce masa ya din gayi sai da yayi mai isar sa sannan yace " "ai dama zabi biyu ya bayar Abba yace inkice baza kixo ba to a kawo masa dije zai sata a makarantar boko tunda anan kin hana ta karatu"

Kallon sa tayi tace "to ai sai ka jamu ka kai mu abuja nace ni bazan zuwa ahe"

"To ai shikkenan kin san zan iya ko"? ya fada yana kallonta. Ya cigaba da cewa "wallahi kiyarda kawai mutafi in ba haka ba sai ki wayi gari kiga na tafi da wacan marakunyar inga yadda zakiyi" yafada yana ya mutsa fuskarsa

Harararsa tayi tace "to katafin da ita mugani"

"Haka kika ce"? Yafada idonshi a tsaye a kan ta.

"Eh haka Na ce" tafada tana hararsa a karo Na biyu ,taci gaba da cewa munanan in da mukafi wayo babu wata Abuja da zamu ai nan ma tana karatun To! Kaji"!
kallon ta yake yana ya mutse Fuska Na sabo yace"Shikkenan tunda kin fi son A tafi da yarinyar taki zaki wayi gari ki ga ba ta nan domin ba zamu zauna da Yarinya haka ba babu Arabi babu boko kin sangartata"

Sanin Halin sa yasa na kaifi d'aya domin baya magana biyu, tunda taga yana wannan murmushin nashi tasan zai ai kata Ta kalleshi gami da gyara,zama tace " yanzu yaushe zaka tafi"?
Shiru yayi sai da ta qara maimaitawa ,yace" Nan da kwana biyu"
"To shikkenan zan bika Amma bazan Dade ba kwana biyu kawai zanyi in dawo ,domin bazan tafi in bar dakina ba ,da"yan Uwa da Abokan Arziqi"

Cikin zuciyarsa yace "Ai sai kidawo mugani Nene kenan in kika tafi kin tafi kenan,


Mik'ewa yayi yana kallon Agogon dake daure a hannunsa ,ya kalleta Cike da tsokana yace" Daga zuwana duk kin bi kin rikice sai faman fada kikeyi,kinqi ki barni Na huta"


Dariya Tayi gami da gutsirar goron ta tace"ai kai ne Ali halinka sai kai daga zuwa kafara cikin...


Read / Download NANA KHADIJA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album