Join Our WhatsApp Group

YAR ZAMAN WANKA Book 1 Complete Hausa Novel Document by YAR ZAMAN WANKA Book 1


YAR ZAMAN WANKA Book 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 33400



YAR ZAMAN WANKA Book 1

Reading Time: 2 Hours

Added On: 09, Nov 2023

Author: Maman Afrah ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : FCW

Author Phone : 09030283375

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 164.87 kb

File Type: txt

Views: 1962+

Download: 486+

Last download: 1 day ago

Description/Story: 🤱ƳAR ZAMAN WANKA👩‍🍼

(KWANA ARBA'IN)
NA



MAMAN AFRAH


FCW

🅿️1️⃣


Gabaɗaya ta jibge kayan cikin wardrobe ɗinta a kan gado, sai zuba wa take a cikin wata babbar bakkon kai da gani tamkar ƙaura za ta yi, sai da ta kwashi son ranta ta maida sauran. Akwatin ƙarfe ta ɗakko irin tasu ta mutanen da, kayanta ne na fita unguwa ƴan atamfofinta sabbi. Sai zuba kayan take tana ta faman murmushi gabaɗaya wani irin daɗi take ji a ranta

"Yau sai kwanan binni" Inna Azimi ta faɗa tana ƙoƙarin zige zip ɗin bakkon nata, hango sallayarta ya sanya ta dakata da zige zip ɗin ta ɗakko abin sallar tana cewa


"Kar in je in ke cewa a bani abin sallah dan ni bana son yin sallah sai a kan sallaya ta bare ma su yara da kunya kake bani-bani in da abinka kwa sai dai a ga ka ɗakko" Ta ce tana sanya sallayar ta dannata daƙer ta samu ta shiga saboda cika da bakkon ta yi.


Wanka ta shiga abin ta, tana ta sauri ta fito, kallon ɗakin kishiyarta ta yi ta yatsina fuska a ranta ta ce

" Humm ba zan faɗa miki ba jikata na naƙuda, ba sai dai ki ganni da kayana zan tafi birni in yaso baƙinciki ya kasheki, tun da ke baki da dangi a birni" Ta faɗa har da wani gatsine kamar wata ƙaramar yarinya.Ɗakinta ta shiga sai da ta shafa mai tsaf, ta sanya kwalli sai wani kallon ƙaramin mudubi take tana wani gyagygyara fuska tamkar wata ƴar budurwa. Sai da ta gama tsaf ta ɗakko atamfarta batik a linke a kan gado daman takanas ta fitar da ita saboda ta sanya idan za ta tafi.


Sanyawa ta yi a jikinta ta ɗakko ɗankwalinta irin na tsaffin nan ɗan kantu mai santsi ta ɗaura har da yi gwaggwaro a gaban goshi, ƙasan gado ta sunkuya ta ɗakko takalminta ɗan madina domin shi ne wanda take sanyawa in za ta gidan biki dan shi ne na ganin sarki, ta fiddo shi ƙofar ɗaki ta ajiye, ta ɗauki silifas ɗinta wanda ta cire duk ya wani tsufa ya katale, ta shiga da shi ɗakin ta sanya a ƙasan gado, madarar turarenta ta ɗakko ta shafa abinta, sai ta kwalbar turaren a ƙaramin aljihun bakkon tana cewa.



"Wannan sai ranar suna kuma zan shaga abuna, yo a kan me zan ke wari ranar suna a raina min hankali ganin daga ƙauye nake" Ta faɗa tana taɓe baki.

Sauran goranta ta ɗauko ta ɓantala tana ci ta ƙulle sauran ta saka a ƙaramar jakarta ƴar pos wacce jikarta Sadiya ta bata.



"Yauwa na gama komai bari in je in tambayo Malam, dan ma kar ya ji ya wai dan wallahi tafiya babu fashi" Ta faɗa tana fitowa ta nufi turakar mijin nasu da ke can wajen hanyar zauren gidan.


Kai da tsaye ta danna kai turakar Malam tana mai cewa

"Gafaranmu dai"

"Allah mana gafara" Cewar Malam yana kallonta mamaki bisa fuskarsa ganinta da shirin fita dan ya san biki ma sai na wanda yake da kusanci da ita take saka atamfofinta na adakar ƙarfe, hakan na nufin biki za ta ko sanar masa bata yi b ya faɗa a ransa.

Inna Azumi kwa sai da ta gama shigowa ɗakin ta lura da Tasalla da ke zaune a ɗakin sai lokacin ma ta tuna Tasallar ce da girki.

Wani kallo ta yiwa Tasallar ta ce

"Umm in ji mai ciwon haƙori" Ta faɗa tana samun wuri ta zauna. Shi dai Malam har lokacin kallonta yake da mamaki, sai da ta zauna ta ce.

"Sannu Malam" Kallonta ya yi tare da gimtse fuska sannan ya ce


"Yawwa sai ina, dan na san dai zancen gizo bai wuce na ƙoƙi tun da na ganki da shirin fita"


"Haba Malam, dama magana ce nake so mu yi" Ta faɗa tana kallon Tasalla dan so take Malam ya ce Tasalla ta fita dan bata so Tasallar ta san da tafiyar tafi so sai ta fiddo jakarta ta mata bazata.


"Ki faɗi abin da ya kawo ki" Cewar Malam yana kallonta har lokacin babu fara'a a fuskarsa.


Washe haƙuranta ta yi wanda har lokacin da ɗan sauran goron da ta tauna a bakin ta ce

"Dama Halima ce ƴar wajen wannan yaro zan je yiwa zaman wanka sai...


"Zaman wanka kuma Yaushe Halimar ta haihu da har za ki tafi zaman wanka ko faɗa min baki yi ba sai da kika shirya? Shin ma me za ki je ki yi da girmanki da komai?" Malam ya faɗa rai ɓace dan abin ya bashi mamaki bai zaci ma garin za ta bari ba duj tunanisa biki ne za ta je a cikin garin ko wani ƙauyen da ke maƙotaka da su.



Tasalla da farko wani haushi ta ji jin kishiyarta za ta tafi birni, dan duk da sun tsufa amma kishin nan yana nan sabo dal a zukatansu. Amma ganin Malam ɗin ya haƙiƙice sai ta faki idonsa ta yiwa Inna Azumi gwalo.

Inna Azumi wani ƙululun baƙinciki ne ya tokareta ganin kishiyarta tana mata gwalo har da ƙunshe dariya.

"In kin san wata baki san wata ba wallahi sai na yi kissar da sai ya barni na tafi, shegiya ƴar baƙimciki da bata da kowa a birni bare tasa rai wataran za ta je ta sha miyar ɗanyen kaya (jar miya).

"Bata haihu ba fa fama...

"Ban gane bata haihu ba wato shi zaman wankan ma tun kan a haihu ake zuwa yinsa?" Malam ya katse ta da tambaya cikin nuna tsantsar mamaki a fuskarsa.

"Yau za ta haihu"

"Ikon Allah wato dai har ɗan adam ya san ranar da wani zai haihu in ce dai wannan ilimin ubangiji ne, ko su turawan da suka fito da yin hoton ciki (Scanning) Dan a san watanninsa da ranar haihuwar ai ko sun faɗi ranar ba a ita ake haihuwa ba ko dai mace ta rage kwanankin ko kuma ta haura ma amma ke har kin ware ranar da za ta haihu, wallahi Azumi ki fita idona ba na son fitina" Malam ya faɗa yana nunata da yatsansa.

Sosai abin ya yiwa Tasalla daɗi, sai ƙunshe dariya taje tana yiwa Azumi kallon ƙasan ido, wannan abu shi ya ƙara ɓatawa Azumi rai sosai take jin kamar ta fashe da kuka.

"Haba Malam ai ka bari na mutu kafin ka binne ni" Cewar Azumi a ɗan fusace.

"To uwata yi min faɗa ko ki haɗa da duka tun da ke ce mai gidan, kuma ma da kin san ke ce mai gidan ai da baki zo nan neman izini ba da sai ki yi tafiyarki" Malam ya faɗa yana gyara zamansa ya lanƙwashe ƙafafunsa wanda suke a miƙe.

Sai sannan Azumi ta gane katoɓarar da ta yi aikuwa da sauri ta ɗan karyar da kai tare da sanyaya murya ta ce

"Haba Malamin Malamai, Malamin da ƙauye da rigagen yankin nan ke ji da shi suna alfahri da shi, ni na isa in ja da Malamin da kowa ke girmama shi saboda ilimi da ɗaukakar da Allah ya masa"

Aikuwa Azumi ta harbo jirgi tuni Malam ya washe jajayen haƙoransa, cikin jin daɗi ya ce


"To ai ke ɗin ce Azumi sai kike abu kamar dai ke ce sama da ni amma ai sai ki yi bayani tin farko"

Tasalla wani irin takaici ne ya mamaye dukkan zuciyarta dan bata so Malam ɗin ya sakko ba ta so ayi ta gumurzu, har ayi faɗan da Malam ɗin zai hana zuwa birnin duk da ta san har yanzu bata ji an yi haihuwar ba, ta san kawai riɗin abincin birni ne ya sa ta zazzoɗin son tafiya.


Wani kallo mai haɗe da hara Inna Azumin ta yiwa Tasalla kafin ta juya wajen Malam ɗin ta yi murmushin jin faɗi ta ce.

"Wallahi dama ɗazu ne na kira lambar Babar Halimar dan in ji ya suke, to shi ne fa na ji tana ta sheshshekar kuka tana cewa "Inna ki taho idan da hali muna asibiti an kawo Sa'adiyya tana naƙuda idan ya so sai ki nemo izini agun Malam ki mata zaman wanka, kin san dai bata da wata kakar da za ta mata zaman wanka sai ke kaɗai a duniya" Inna Azumi ta faɗi maganad tana share ƙwallar ƙaryar da ta mammatso daga idanun nata.


"Wato da gasken dai bata haihun ba?"

"Haba Malam wai ya kake maida hannun agogo baya ne, na faɗa maka naƙudar take amma kaƙi yarda sai wasu tambayoyi kake min mau kamar tuhuma, ko dan ka ga yarinyar ba jikar ka bace, amma tabbas ka zama mai manta alheri lokacin yaron nan na da rai haka zai kwaso goma ta arziƙi ya zo ya gaisheka duk da ba kai ka haifesa ba amma shi ne yanzu dan ƴarsa za ta haihu zan je zaman wanka kake nuna mata wariyar launin fata?" Ka san dai shi kaɗai na haifa a duniya, shi ma su biyu ya haifa daga ita sai ƙanwarta, kuma wannan ne karo na farko da jikata za ta haihu amma kana ta yalbatsani a gaban kishiya salon wataran a min gori" Ta ce tana fashewa da kukan makirci har da su fatar majina ita ala dole ta tuno da ɗan mata da ya mutu.


Baki sake Malam ɗin ya ke kallonta, ganin dai ta daddage sai zuba kuka take ya ce

"Ku dama mata kowa ya sanku da goranta abin da kuka yiwa mutum, ko goranta masa a kan abin da wani naku ya masa, da zarar abu ya haɗoku sai ku yiwa mutum gori. In ba haka ba daga magana sai ki fara lissafo abubuwan da ɗanki ya mini saboda ba ni na haifesa ba, to indai tafiya birni ne ki je Allah kiyaye Allah ya sauketa lafiya.


"Haba Malam ba haka nake nufi ba na ga ma har ranka ya ɓaci, kawai ma na fasa tafiya da in tafi kana fushi da ni" Ta ƙara faɗa cikin kissa da kisisina.

"Lah babu komai wallahi, ai mu ma maza wani lokacin da namu laifin sai mu hana mace zuwa abin da bai dace mu hana ba, kin ga wannan ai bai dace ko kusa na hanaki ba, wallahi na aminci Allah kiyaye hanya" Ya faɗa yana sanya hannu a aljihu ya fiddo dubu biyu ya miƙa mata.

Hannu biyu ta sanya ta karɓa tana ta rafka godiya

"Yaushe zan dawo kuma?"


"Kamar ya yaushe za ki dawo ba zaman wanka za ki mata ba ai zan ce kwana arba'in ne ake zaman wanka ko an canja shi daga haka ne?"


"A'a ba a canja ba sai dai da yake haihuwar fari ce ana iya ƙarawa ma a yi arba'in biyu wani sa'in ma in mijin mai sakin fuska ne bai nuna alamar gajiyawa ba har arba'in uku ana yi" Ta ce tana ƴar dariya.

"Inyeee to abin ya zama hauka kuma ba zaman wanka ba, ke yanzu sai ki yi sama da watanni uku a gidan mutane yo ai har yaron ya fara zama ma, amma ana yiwa uwarsa zaman wankan haihuwarsa ai da kunya ma gote-gote da ke ki zauna a gidan yara har arba'in uku"

"Ni fa ba wai cewa na yi zan yi arba'in uku ba kawai dai ina faɗa maka ne abin da ake yi, amma ni kwana hamsin zan yi, sannan jar miya da naman kaza sun ratsa ni" Ta faɗa tana lashe leɓenta dan har yawunta ya tsinke.


"Ko da na ji, Allah kiyaye"

"Amin, amin Malam" Ta ce tana kallon Tasalla da ta cika ta yi fam kaɗan ya rage ta yi bindiga dan baƙinciki.


"To Tasallele, mu zamu tafi birni sai Allah ya ƙaddara saduwarmu, kike sana'ar man ƙuli na da nake yi dan kar kasuwar ta yi ƙasa ganin ana zuwa nema babu sai mutane su ɗauka na daina yi ne kwata-kwata amma in kina yi da na dawo sai in ɗora daga inda kika tsaya, kuma kowa ya tambaye ni ki ce masa na tafi Kano ta dabo tunbin giwa jikata ta haihuwa zan mata ZAMAN WANKA" Ta faɗa tana dariya, Malam dai kaibya girgiza a ransa yana tunanin ranar da matan nasa za su girma gashi dai sun tsufa amma in suka yi wani abin kamar yaran mata.

Haushi ne ya ƙara cika Tasalla wato bayan sana'arta ta waina, hallaw take sana'ar mai da ƙarago ita tana can tana cin shinkafa da miya da nama, har wata ƙwallar takaici ce ta kawo a idonta. Ganin Malam ya kalleta ta daddage ta danne ta ce mata

"Sauka lfy"


"Sana'ar man ƙulin fa?" Ta tambaya da sheƙiyanci.


"Ba zan yi ba" Ta bata amsa a takaice.

"Kin huta" Ta faɗa tana dariya dan ta lura Tasallar ta shaƙa sosai.



"Amma kin san dai yanzu motar kasuwa ta tafi, sai dai ki hau machine ki je Garki ki hau motar Kanon a can ko?" Malam ya katse musu maganar dan ya lura abin na neman zama fitina gwara a rabu lafiya.

"Eh dama yanzu mota ai ta tafi dan rana ta yi sosai dan azzahar ma ta kusa hantsi ya dubu luday"


"Yawwa a gaishe su"

"Za su ji" Ta faɗa tana tashi daga zaunen da take ta buɗe labulen ta fito daga turakar Malam ɗin.


Ɗakinta ta koma ta ɗakko lalle ta sanya a bakkon (Ghana mostgo) Ta ɗaga dakyar ta fito da ita daga ɗakin ta ajiye a ƙofar ɗakin ta ɗakko kwaɗo ta kulle ɗakinta ta sanya mukullan a cikin pos ɗinta. Ƙofar gida ta fita ta sanya Lawwali almajirin Malam ya samo mata mai machine, aka ɗakko jakar za a fice da ita dai dai nan Malam ya fito daga ɗakinsa ya ga Lawwali ɗauke da jakar.

"Azumi lafiyarki kuwa?" Ya tambaya da mamaki.

"Me ka gani Malam" Ta faɗa cikin nuna rashin fahimtar inda tambayarsa ta dosa.

"Wannan jakar ce za ki yi tafiyar da ita, kin shaƙeta da kaya kamar wanda za ki ƙaura can"

"Ba fa kaya bane kaɗai Malam har da bargona a ciki ka san lokacin sanyin nan kar inje ina bani-bani a gidan yara gwara na tafi da abuna" Ta faɗa tana murmusawa.

"To ai shikenan" Ya faɗa, suka fito tare ta hau machine almajiran Malam na ta ɗaga mata hannu, ta tsakiyar ƙauyen suka bi duk inda suka wuce ana ɗaga mata hannu alamar Allah kiyaye dan an ganta da jaka a gaban machine kuma duk yawanci an san tana da ƴan uwa a...


Read / Download YAR ZAMAN WANKA Book 1

START READING

OR

DOWNLOAD TXT NOW
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album