Join Our WhatsApp Group

NOOR ALBI Complete Hausa Novel Document by NOOR ALBI


NOOR ALBI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 25464



NOOR ALBI

Reading Time: 2 Hours

Added On: 30, Sep 2023

Author: Mamuh Gee ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 09032345899

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 150.42 kb

File Type: txt

Views: 1235+

Download: 489+

Last download: 2 days ago

Description/Story: *_NOOR ALBI_*
_Hasken Rayuwata_

*_Mamuhgee_*

1

*_Bismillahir-rahmanir Raheem_*

Kokarin komawa ta zauna Kan kujerar robar Dake gaban wheelchair dinda mahaifinta yake zaune akai tayi bayan ta aje cup din data Gama basa magani abaki Kan qaramin table din Dake gurin ta dago idanuwanta ahankali cikin nutsuwa ta kallesa batareda tace komaiba ta tsawon mintina biyu kafin ta Dan motsa Bakinta cikin wata nutsuwar ta sakar Masa murmushinda yake narkarda zuciyarsa da tsananin tausayinta da qaunarta Dan kuwa yanajin radadi da zafin dukkanin murmushinta Wanda yariga yasan ba komai cikinsa face damuwa, kadaici,maraici da rashin uwa dakuma rashin uba dukda shi uban gashi a raye Amma tamkar baya raye yake Dan baida wani abun dayake iya yimata bayan nuna Mata zallar qaunarta daga zaune sai kwance.

Ganin irin kallon dayake matane Wanda koyaushe yake nuna gazawarsa amatsayi na uba
Ita Kuma Bata taba yimasa kallon ya Gaza din sbd tasan hakan qaddararsu ce su duka tun daga kan mahaifiyarta da Bata Raye har Momy wadda take ganin itace tafi cutatuwa ato kowane bangare na rayuwarsu.

Sauke idanuwanta tayi daga kallonsa tareda Kai hannu ta zari tissue Mai Dan yawa tahau goge Masa gefen rigarsa da ruwan maganin masu kala suka zuba ta sauke siririn numfashi ahankali ta bude Baki ta furta"

Abba!!
Kadaina kallon kanka da yanayinka amatsayin ka cancanta hakan sbd abunda yafaru,
Kadaina kallon kanka amatsayin Wanda ya lalata rayuwar yarsa yakasa Mata komai bayan Kaine komai nawa,
Nice rabon haihuwata da zuwana duniya ya tarwatsa kwanciyar hankalin rayuwark......

Rintse idanuwa da yayi cikin Jin dacin  zancenta yayi daidai da dafata da akai da hannuwa biyu a kafadarta Dan hanata qarasa zancen.

Ahankali ta sauke ajiyar zuciya  batareda ta dagoba
ta Dan sake sauke numfashi Mai sanyi da rashin sauti kafin ta waiwayo da kyakkyawar fuskarta
idanuwanta basu sauka Kan Yar uwarta Kuma Antynta data dafata sai akan Momy suka fara sauka wadda ke tsaye bayan Anty SA'ADAH din kyakkyawar fuskarta ta Kamar yanda tasanta tun tashinta a daure Babu sakewa Babu fushi sai yanayinta dake sake nuni da har lokacin kallon Rabon daya lalata rayuwarta data yarta take Mata.

Ahankali ta dauke kallonta daga kanta tana Mai Dan Sunkuyar da kanta  ahankali tareda miqewa tsaye daga gurin ta raba gefen Anty Sa'adah ta koma bayanta ta tsaya cikin tattausan muryanta batareda tasake kallon momynba cike da biyayya tace"

Barka da safiya Momy.

Kamar yanda tasani tun tasowarta harzuwa shekarunta na yanzu datake dasu Momy Bata taba amsa gaisuwartaba wanda hakan sabone agareta Kuma baya damunta Kamar yanda ko so daya Bata taba tsallake ranar gashetaba Dan kuwa Bata taba ganin laifi ko Jin haushin momynba,
Kallon uwa Kuma mariqiya take Mata tareda wani girmanta Mai tsanani datake gani.

Qarasowa cikin palon gabaki daya momyn tayi cikin tafiyar nutsuwa ta Isa Kan kujerar dake gurin ta zauna sai alokacin ta kallesa dakyau murya  natse tace"

Barka da safiya!

Shiru sukayi dukkaninsu sbd sanin ba wani iya mgn Abban keyiba musamman da kwana biyun jikin nasa ke Dan sake rikicewa duk da tsawon shekaru masu yawa daya debo daga zaunen da kwancen.

Saida yamata kallon mintuna kamar yanda yasaba yimata kullum kafin ya iya daga kansa ahankali cikin wani irin yanayi na sanyi da jikin dayake Dan ji.

Numfashi Mai sanyi ta sauke ahankali kafin ta dauke kallonta daga kansa cikin sanyin murya tace"

Dr Abbakar yakira akan Yana hanyar qarasowa kana tunanin hakan zai.....

Dakatawa tayi da maganar Tareda yin shiru kafin ta Dan waiwaya ahankali ta kalli inda Sa'adah ke tsaye batareda tace komaiba
Suna ganin hakan suka nufa kofa itace agaba jikinta na qara bayyanarda sanyinta Amma taurin zuciyarta na sake boye hakan.

Kai tsaye dakin anty Sa'adah din Sa'adahn ta jata suka shiga ta nuna Mata bakin gado da ido tana cewa"

Zauna anan Ina zuwa.

Fita tayi ta nufa kicin ta duba abincin da akai Karin safiya dashi taga sauran doyar Dake cikin kular da alama ba'aciba
Ta dauka plate ta zuba Mata farar doyar tareda soyayyar jar miyar dataji albasa ta bude Dan qaramin fridge dinsu daya Dan tsufa Amma Yana aiki ta dauko Mata pure water daya masu sanyi ta nufo dakin ta qarasa har gefenta ta zauna ahankali tareda Kiran sunanta cikin tattausan lafazin dake nuni da irin tsananin son datakewa Yar uwar tata Wanda bayan Momy data haifeta Babu Wanda takeso kamarta.

*_LAYLAH_* Takira sunanta cikin kulawa da sautin Mai Dan girma Kai tsaye tace"

Ahakan Zaki zama likitan kina skipping lokacin cin abinci?
Cinye ki tashi kije ki gyara palon Abba kafin baqinsa suzo.

Kamar yanda yake dabiarta dagowa tayi ta kalli Anty Sa'adah din kadan tareda Dan yaqen guntun murmushi tana daukan plate din tafara cin abincinta a natse.

Qura Mata ido anty Sa'adah tayi tana qarewa kyakkyawar fuskarta zuwa yanayin sanyi da nutsuwarta kallo,
Duk yanda kakai qarshe da sanin halin mutum da yanayinsa bazaka taba iya gane halinda zuciyar *_ZAINAB LAYLAH_* take cikiba,
Yarinyace Mai tsananin zurfin ciki da wata irin juriya da tawakkali,
Bata bayyanarda fushi ko bacin Rai,
Batada hayaniyar da zaka Kuma gane farin cikinta
Abu daya ke bayyanarda halinda zuciyarta ke ciki ko yanayinta shine murmushinta Wanda shine abinda ke bayyanarda zallar 'dacin datake ciki.

Mahaifinta yayi auren sirri da Yar uwar dangin nesa sosai ta Babban amininsa da baida tamkarsa sun taso tare sun girma tare tarin Arziki,suna da daukaka ya rage kusancinsu sbd nisa da aminin nasa yai Masa bawai Dan sun rabu ba haryanxu suna tare matuqar Aminin nasa Yana qasar,
Yayi auren sirri ne da Yar uwar dangi ta Aminin nasa batareda sanin matarsaba wadda dukkanin yardarta,soyayyarta,kaunarta da gatanta suna kansa sbd tsananin yardarta dashi dari bisa dari,
Bata taba zarginsaba ko kawo tunanin zai iya cin amanarta ko ha'intarta takowane bangare musamman sbd sunada 'yarsu daya tak dasuke tsananin so da kauna Sa'adah.,

Saida ya shekara shida da auren ZAINAB cikin sirri Da tsananin so da kauna Mai qarfi da baya iya rabuwa da ita kafin Allah yabata cikin dayayi sanadiyar fitowar auren.

Batada labarin aurensa saidai tasamu labarin hadarin daya samu Mai tsananin gaske akan hanyarsa takai Matar asibiti tana nakuda a jahar daba tasuba,
Akaron farko da wani babban alamari ya jijjiga izzarta datake ganin tanada ita a zuviyar mijinta duk wata yardarta da soyayyarsa ta rushe tareda wani irin kunci daya cike zuciyarta tsawon shekarunda take dakonsa har yanzu,
Batasan auren mijintaba saidai gawar matarsa tagani da lafiyayyar jaririya da aka bar Mata wadda kallo daya takasa Mata sbd batason shedan ya ribaci zuciyarta ta cutatarda 'dan kowa,

Bata taba son 'yar ba wadda taci sunan mahaifiyarta Kuma sunanta wato *ZAINAB*
Bata taba sontaba kamar yanda Bata taba Jin qintaba,
Bata kallonta sbd kada ta cutatar da ita,
Ita ba jahila bace tasan Babu haqqi akan yarinyar na abundaya faru saidai Kuma takasa Hana zuciyarta yimata kallon Itace asalin dalilin tarwatsewar rayuwarsu duka sbd rabon haihuwartane yayi sanadin komai,
Tun accident din abban yarasa qafafunsa a zaune yake cikin kujera daga zaune sai kwance tsawon shekarunda sukaja masu tsayi sosai,

Bai taba ganin laifin momy ba Amma Kuma Bai taba daina rokontaba daga kwancen akan ta samu wani fili kadan a zuciyarta da zata saka Masa Laylah sbd batada kowa saishi shikuma Haka tasa qaddarar tazo baida wani Abu dazai iyayi Mata amatsayin uba,

Rayuwar Laylah rayuwace Mai cikeda zallan kadaici da maraici,
Tunda tafara wayo taga yanda Momy Bata taba kallontaba bare amsa ko gaisuwarta Amma Kuma Bata taba hantarartaba saita taso cikin juriya da rungumar rayuwar ahakan tareda yarda da cewa tabbas itace sakamakon cin Amana da haincin da akaiwa Momy Wanda ya rusa rayuwarta da kwanciyar hankalinta na gidan aurenta Dan kuwa tun lokacin Momy ta Rasa miji tunda yakoma baida wani amfani agareta da yarta tun daga kan auratayya har Kan sauran haqqoqin.,

Da wannan zuciyarta take kasa Jin 'dacin Momy sbd takowane sashe tabbas itace mummanar qaddarar data Bata rayuwarsu shiyasa ta sadaukar da kanta da rayuwarta gurin bautawa Momy da anty Sa'adah ko zata iya biyansu ta wani sashen da abinda abbanta da mahaifiyarta da Bata Raye sukai musu,
A rayuwarta cinta da Shanta tareda karatunta momynce ta dauka nauyi abisaga aikin wahalar datake musu tun bayan data girma aka sallami Mai aikin data raineta harta girma ragamar aikin gidan tadawo hannunta tun daga kan girki da tsaftar gidan,

Sam rayuwar Momy a baude take wanzuwar laylah a rayuwarta sbd tuni ta Rasa annashuwa da dariyarta harma da murmushinta,
Rayuwarta Takoma ta wata irin cunkusashiya kasancewarta cikin mutane masu tsananin riqo a zuciya shiyasa duk tsawon shekarun Bata tabajin sassaucin abunda takejiba akan al'amarin.

Babban abunda yake tattareda rayuwar Layla na nutsuwa da kwanciyar hankali shine tsananin kauna da soyayyar da mahaifinta ke Mata Mai tsanani da wadda 'yar uwarta Anty Sa'adah ke Mata Dan kuwa anty Sa'adah itace gatanta a fili da boye sbd itace ta tsaya Kai da qafa agurin mahaifiyarta ta roqu alfarmar bawa laylan damar karatu bisaga neman alfarmar zata karba ragamar aikin gidan,
Da wannan Laylah tasamu tayi karatu a makarantar gwamnati Mai dama dama harta samu ilimin bokon datake dashi sabanin ita Sa'adah datai karatun private school Mai kyau,

Anty Sa'adah ce gatanta a duk abinda ya danganci haqqin dake rataye akan iyayenta na kula da ita shiyasa koyaushe Abba ya bude idanuwansa akan Sa'adah yake Mata godiya cikin ganin qimarta itada momyn sbd koma yayane da dukiyar momyn Sa'adah ke yiwa Laylah hidima Wanda itama momyn rufin asirine kawai na 'yar kasuwancin buga buga datake Dan tallatawa rayuwar yarta da abban da yarsa dasuka zamar Mata wani babban jarabawan rayuwa.

Mahaifiyarta ta rasu tabarta a ranarda ta haifeta Dan Haka batasan wani shaquwaba ko sake tayi Wasa tareda wani,
Mahaifintane Kuma kwance ta bude ido tagansa,
Anty Sa'adah Kuma kallon wadda ke tallafe da rayuwarta take Mata duk da a zuciyarta matsayi da girman kaunar datakewa anty Sa'adahn daban ne.
#MAMUH#

*_NOOR ALBI_*
*_Rabo sai Mai shi...Bata taba saka ran shigowarsa ko zama jigo a rayuwarta ba sbd kallon datake Masa amatsayin Uba,Abokin mahaifinta,Amininsa Kuma Mariqi.!_*
*_Soyayyace tashiga tsakaninsu Mai girma da qarfi batareda sun ankare da hakanba bayan dukkaninsu sun haramtawa kansu hakan,Shin ta yaya zata kalla mijin yayarta,Yar uwarta wadda ta riqeta tamkar yanda uwa me riqon 'da amatsayin nata mijin?_*
*_Qaddararsu wannan kokuwa itace rabonsa tun farko?_*
*_NOOR ALBI Hasken rayuwata_*
_Littafina dayazo muku da wani salon na dabam Wanda soyayyarsa ta kere sauran labaraina,salonsa ya bambanta da sauran,nishadinsa da shauqinsa na musamman ne_
_Fata dai ku kasance taredamu kuji zafi zafin damuka dawo muku dashi_
*_NoorAlbi#MAMUH_*


*_FOLLOW ME@_*
_Mamuhgee_
Wattpad
*_ArewaBooke@_*
_Mamuhgee_


*ZAFAFA BIYAR*


*_KUFAN WUTA_*
_Safiyya Huguma_

*_BAQAR INUWA_*
_Billyn Abdul_

*_RAYUWAR MACE_*
_Hafsat Rano_

*_MASARAUTA_*
_Miss Xoxo_

*_NOOR ALBI_*
_Mamuhgee_

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*

09166221261



*_NOOR ALBI_*
_*Mamuhgee*_



2
Ajiyar zuciya anty Sa'adah ta sauke lokacinda taga laylan na aje plate din gefe daya alamar ta koshi
Ta dauki ruwan dake da sanyi sosai
Saikuma ta maida ta aje Dan batashan ruwa Mai sanyi sosai sbd lafiyarta na daya daga cikin abubuwan datake kiyayewa badan kantaba sai Dan kula da Abban da gidan gabaki daya Dan kuwa idan ta kwanta ciwo komai cak yake tsayawa a gidan duk da ba wani babban gida bane ko gidan taro su kadaine agidan Wanda yakeda iya nasa girman na masu rufin asiri.

Miqewa tsaye tayi batareda ta kalli Anty Sa'adah ba ta nufi kofa daukeda plate din da ruwan cikin sanyi tana cewa"

Zanje nafara aikin abincin Rana
Lokaci yafara ja.

Ficewa tayi tabar Anty Sa'adah na bin bayanta da kallon Kamar koyaushe cikin jin qauna irin ta jini dakuma tsantsar burgewa da laylan ke Bata akoda yaushe Dan kuwa Babu abinda Layla ta baro mahaifiyarta tun daga kalar fatar,da jikin,da tafiyar dama sanyi da nutsuwa Wanda hakan kesa Koda mugun kallo Momy Bata kaunar kallon fuskarta sai da dalili Wanda kallo daya take Mata ta dauke Kai,
Ita kanta anty Sa'adah so daya taga fuskar mahaifiyar Laylah
Shine lokacinda sukaje asibiti tareda momyn da aka Kira cewan Abban yasamu hadari aka kaisu har gadon mahaifiyar Laylah alokacinda ta haifeta,
Kallon mintuna masu tsayi Momy tayiwa ZAINAB da jaririyarta kafin suka juya suka fice Bata sake ganin fuskarba har yau saidai Akan fuskar Laylah.

Wayarta ta dauko ta Danna Kiran umma Jamila yayar Momy Wanda ke ji da Sa'adah din itama Kamar itace ta haifeta sbd ita Bata taba haihuwaba.

Dan madaidaicin kicin dinsu ta Isa ta ajiye plate din hannunta tareda Dora ruwan data dawo dasu akan fridge su huce kafin tasha
Ta tattara kayan da akai amfani dasu tafara wankewa cikin Dan sauri sbd lokaci yaja Mata sosai.
Tana gamawa ta goge kayan ta saka a kwando ta dauko tukunya ta kunna lafiyayyan risho dinsu babba ta Dora abincin Rana ta fito ta nufi palon gidan Wanda yake daukeda dakin Momy a gefe saina anty Sa'adah a gefensa sai nata daga can gurin hanyar fitowa palon.

Tsaf tagyare palon ta nufi dakin Momy ta gyaro takoma dakin anty Sa'adah ta gyara kafin ta fito ta nufi palon abbansu Dake dayan gefen tashiga da sallama duk da tasan suna daga kurya Momy na magana dashi Wanda sai babban al'amarine kesa Momy magana dashi Dan haryanxu babu Wanda yasani akan akwai aure tsakaninsu haryanxu kokuwa zaman rufawa Kai asiri suke? itadai abinda tasani a gidan shine zaman alfarma take.

Gyaran palon takeyi cikin nutsuwa saiga momyn ta fito ta fice har lokacin Bata dagoba Saida tagama gyarawa kafin ta nufi dakin Abban da sallama idanuwanta akansa ta qaraso tafara gyaran dakin duk da Babu inda dauda ko rashin tsafta yake a dakin kullum tana gyarawa hakama kullum sai Abdullahi yazo yayiwa Abban wanka da wasu abubuwan tareda wankin kayansa.

Daga zaunen dayake kansa a langabe gefe ya zuba Mata ido cikin yanayin Mai tsananin 'daci da damuwa tareda tausayinta Mai tsanani,
Akan idonsa 'yarsa da zainab ta taso cikin bauta da rashin walwala,
Ta taso cikin kadaici da maraici,
Badan Sa'adah ta tallafi rayuwarta ba da zuciyarsa bazata iya kawo yanzu tana daukan tsananin baqin ciki da damuwarta ba
Shiyasa har abada bazai daina godewa Sa'adah da momyn ba ko Yayane dai sun tallafa rayuwarta alokacinda baya iya tsinana Mata komai amatsayinsa na mahaifinta...

Saidai babbar gagarumar damuwarsa shine shin wane Hali zata shiga idan babusa?
Tayaya zatai rayuwa Kamar kowa tasamu farin ciki?
Ya tabbatarda rashinsa zai qarasa juyarda duniyartane gabaki daya sbd har abada zata qare a bauta da wahalar gidan Dan kuwa kowane lokaci Sa'adah Dake tallafarta zatai aure ta tafi tabarta.

Hawayene suke bin gefen fuskarsa suna gangarowa zuwa kan kafadarsa da kayansa
Zuciyarsa na tsananin quna cikeda damuwa.

Ajikinta taji kukan mahaifin nata
Ta waiwayo ahankali a natse ta kallesa da idanuwanta da ako yaushe suke hasko Masa mahaifiyarta ya rintse ido hawayensa na tsananta gudu alamar kukane Mai tsanani yakeyi na zuciya Dan baida lafiyar fitar sautin kukan ne.

Qarasowa tayi gabansa a natse cikin sanyi ta zauna tareda Dan sauke kanta qasa tsawon mintuna batareda tace komaiba,
Tissue dage gefe ta zaro guda uku ta dago fararen idanuwanta dasukai ja take batareda hawaye sun taru cikinsu ba kokuma suka gangaro ta zubawa Abban takai hannu ahankali tafara share hawayensa Wanda hakan yasa hawayen nasa Suka sake barkewa ba kakkautawa,

Yanajin radadi da zafin Zuciya ba damar furtawa kokuma bayyanawa,
So yake ya bude Baki yasaka Mata albarka tareda Bata hakurin yanda quruciyarta da yarintarta take neman qarewa agurin dawainiya dashi.

Batace komaiba sai share hawayensa datakeyi ahankali tana...


Read / Download NOOR ALBI

START READING

OR

DOWNLOAD TXT NOW
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album