Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

BUDURWAR ZUCIYA Complete Hausa Novel Document by BUDURWAR ZUCIYA


BUDURWAR  ZUCIYA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 26415



BUDURWAR ZUCIYA

Reading Time: 2 Hours

Added On: 15, May 2024

Author: Shamsiya Adam ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08160375544, 07043185799

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 158.67 kb

File Type: txt

Views: 428+

Download: 255+

Last download: 2 days ago

Description/Story: ο»ΏBUDURWAR ZUCIYA 2020
Na Shamsiyya Adam
Bismillahir Rahmanr Rahim
Allah kamana dakyau don Annabi s a w

BUDURWAR ZUCIYA
Awani gari mai suna kainuwa. Garine maikyawun gine gine da ababan more rayuwa daban daban kasancewar garin cike yake da tarin attajirai damanya manyan 'yan kasuwa da masu aikin govnati. Akwai anguwar talakawa babbar anguwa anfikiran unguwar dasuna fukara'u
Munadaya daga cikin masu xaman anguwar fukara'u
Sunana Ismat 'ya ga malm musa da mama kareema inashekara 13 mahaifinmu yarasu lokacin kanina Ayman nashekara 8,bakaramin girgixamu rasuwar mahaifin namu tayi ba kasancewar ko lokacin dayake raye acikin talauci muke domin dakyar yake iyasamomana abin da xamu ci koda kwa sau 2ne arana, gashi yanxu yatafi yabarmu waxaibamu ga kawu bala baya taimakon su tundaran babanmu duk da kasancewar kawu bala daya daga cikin masu kudin garin. Amma baruwan sa damu yanxu shekarar Ismat 15,ayman kuma goma.

πŸ’šπŸ’šπŸ’šπŸ’šπŸ’šπŸ’šπŸ’šπŸ’š
Xaune take tana sawuta ga murhun dake gabanta, wanda ke dauke da tukunya 'yar madaidaiciya akai, tukunyar bayanta yayi baki sosai kuma ta tsufa dayawa daganesa ma bakace xata iya dafa wani abuba sbd lalacewa.
Wani kyakkyawan farin yaro nagani yafito daga wani daki dake ta bayan budurwar yanufo wajenta hannunsa dauke da tiren roba yakara so
Anty Ismat yunwa nakeji cikina sai ciwo yake tamkar xai fuje
Dago kai tayi idanunta jaxur sbd hayaki dayagama bule mata ido wasu siraran hawaye ne suka xubo daga idaniyarta
Karka damu Ayman ka kara hakuri ainakusa gamawa danagama xakaci kaji
Hannu yakai xaibude tukunyar sabd bayajin gaskiya tafadamasa
Tarike hannunsa sbd tasan bakomai aciki face ruwa kawai data xuba take ta dafawa mamansu tunsafe tafita don tanemo musu abindaxa aci kuma balallai tasamo ba tayi hakane sbd takwantarwa da Ayman hankli yaxata ko abinci take dafawa
Jikinta yafada yana sakin wani marayan kuka
Wai anty wannan wanne irin abincine tin la'asar akedafa shi baidafu ba har mangaruba, dan Allah anty kifada mun inbabune wlh yunwa tamkar takashe ni
Fashewa tayi dakuka mai karfi tana rumgumesa ajikinta sosai
Inna nillahi wa inna ilaihir raji un Allah kayanke mana wannan igiyar wahala tatalauchi don manxon Allah s a w. Ayman bakoma acikin tukunyar nan face ruwa sbd shine kadai ayanxu muke dashi Allah ya axirtamu. Yau donhaka Allahamdulillah Allah shine abin godiya abisa diikkan abin dayaxar tar
Hakane anty yanxu ruwan xamu sha
Eh saimu kukkurba daxafi xafi kamar shayi kaga xamuji dama dama, kuma kaga inna tafita tin axahar neman mana abinci ataskar Ubangiji kuma in sha Allahu baxamu rasaba,
Daukomana kofina maxa
Dagudu yaruga yadauko musu adaki taxuba masa itama taxuba suna fifitawa suna sha Ayman yakalleta
Anty wai menene yasa kawu bala baxai taimakemuba yakaimu gidansa
Rike baki tayi tana cewa
Kaiitab lallaima yakaimu gidansa fa kace, hum um baxai iyaba tunda kaga kyamatar mu sukeyi su duka 'yan uwan abban mu, kuma bansan nima meyasa ba amma bari mama tadawo saina tambayeta,
Sallama tayi tashigo dafara arta saibakar leda dake hannunta babba, dagudu Ayman da Ismat suka ruga gareta dukkansu tahada ta rumgume tana farincikin samunsu datai cikin koshin lfy
Oyoyo maman mu
Ayman yafada yanakara kankameta tamkar wani xai kwace masa ita
Allah sarki Ayman dina har yanxu bakuci komai ba ko Ismat?
munsha ruwan dumi mama ai
Ismat ta ce tana amsar ledar hannunta tare dayimata sannu daxuwa cikin nutsuwarta dakuma yanayin tausayawa ga maman nasu
Ismat kuyi hakuri dan Allah nafita nabarku bakuci komai ba kingani ma tindana fita nakefaman neman taimako nako nera 100,ne nasiyo mana ko kwaki ne madanjika musha damuxauna haka amma hakan sam baisamuba sai gabda mangarubar nan nasamu wani bawan Allah yabani sadakar dari 500shima kaya naga yadauko su aboot in motarsa data lalace masa abakin titi xaishiga unguwar tasu natafi dasauri natare sa ina kama kayana nace
Dako ne yace aa nace dan Allah yataimaka min nadaukar masa nakai masa indaxashi yadan bani lada ko kadanne dan Allah damamaki afuskarsa nagani ina mace kuma ina neman dako yagirgixa kai yana bani nadauka nabisa abaya harkofar gidansa sannan na aje yamiko min dari biyar nai godiya yace miyasa nake dako nace marayu ne dani navarsu kuma tinsafe basu ci komai ba yatausayama na yakuma nemi kwatancena akan xairinka aiko manada sadaka insha Allah naigodiya nataho abakin layi natsaya kantin inuwa nasiyo mana kwaki rabi da mai na 50,ragowar chanjin nasiyo mana taliya 'yar awo kwata
Mungode sosai mama Allah yasakawa wannan mutumi da alkhairi mafifici
Cewar Ismat tana sakin murmushi
Mayafinta mama ta cire tana cewa
Amin bari nawanke mana kwakin sai akwadanta yanxu aci
Aa mamanmu kawo kiga ninakwadanta baxai yuwuba kidawo yanxu daga wannan tafiyan akafaba kuma sannan kixo kina wahalar aiki aibanwa kaina da kuruciyata adalciba
Mama tai murmushi
Allah sarki ismat Allah yamiki albarka don albarkar ANNABI s a w. Bakomai hakkinkune akaina amma tunda kindage shikennan dauki kije saiki deba mana wanda xai ishemu yanxu ki aje sauran saikuma gobe
πŸ’š
Bayan kwana biyar alhaji sanam yayo musu aike da shinkafa kwano da jakar maggi sai500 sunji dadi sosai don haka mama bayan sallar mangaruba taje gidansa domin tayimasa godiya maigadi ne yace mata yana ciki tashiga sallama tayi kofar falon ya amsa tare da yi mata ixinin shigowa
Akasan falon taxube suka gaisa sai lokacin yakalle sosai data dukar dakai kasa yaga kyanta wanda yadauki hankalinsa mama dama ba tsohuwa bace macace kykkyawa wacce wacce baxata wuce shekara 33, doguwa maikira. Dayawa alhaxawan kainuwa nakawo mata hari amma tanaki sbda ba abin duniya take nema ba aa mutumcin yaranta dakuma tsoron matansu sbda batasan yasuke ba bataso kuma yaranta su samu tsamgwama ko kyara awajen kishiya shiyasa mataki aure ta gwammace taitaxama dasu ahaka suna nema ataskar Ubangiji maigirma
Dadama kuma wasu iskanci suke nemanta dashi ba aure ba, amma bata da ra ayin bakar rayuwa irinta.
Jin shurun yayi yawa yasa tadago kai daga dukar dashi datayi tana mikewa tsaye
Toh Alhaji ni xankoma mungode Allah yasaka da alkhairi ainaso ma nasamu maidakin naka mugaisa naigodiya
Yayi murmushi tare dakara kafeta da idanunsa masu daukar hankali
Uhum har xaki tafi dakin xauna nakawo miki ruwa ai andan kara gaisawa ko?
Ai nabaro yara shiyasa kumadama cewa nai bari naxo muyi godiya da aike mungani mungode mungode
Da amin ya amsa tanajuya baya yabita da kallo tare da lashe dikkan labbansa yana saki murmushi mai cike da ma anoni daban daban wadanda shikadai yabarwa kansa sani.
πŸ’šRanar alhamis bayan la asar yaje gidan yana xaune amotarsa saiga Ayman yafito yana gara gare gare bude murfin motar yayi yana kiransa dasauri yaxo yana gaidashi
Mamanka na nan
Ayman yadaga kai
Eh tana nan yanxu tadawo daga gidan wanki
Tohm jeka kace mata tayi bako alhaji sanam
Aikuwa dagudu Ayman yakoma yana samunta xaune kan karamar kujerar cikin gida tana yiwa Ismat kitso ita kuma banda rakin xafi xafi ba'abin datake, sabda batason kitso maman ce ke tilas tamata xama ayimata amma don ta ita ne sai kanta yayi wata biyar ba kitso, adankare don kuwa ko taxar arxiki baya samu daga gareta balle kitso, kuma gashi Ismat irin matannanne masu cukowar gashi mai roba marar tsayi sai uban yawa su tsefe yayi musu ham aka
Maman mu waikinyi bako alhaji sanam
Ayman kenan ya ida maganar sa yana karasowa gabansu
Kareema ta kallesu tana mamaki Alhaji sanam kuma mai basu taimako shine kuma yaxo gidanta tohm lfy kuwa Allah yasa dai lafiya
Ismat tace
Maman mu kamar fa sunan alhajin dayake aikomana da shinkafa da kudi ne
Shine nima ai mamakin danake dakuma naji shine dakansa Allah yasa lfy
Mama lfy mana kidaina tsoro dan Allah kikasani ko wani taimakon ne yakawo mana dakansa amatsayin mu na mabukata xai tunanin ko abincin mu yakare yanxu bamu dana sawa abakin salati
Mama taja wana dogon numfashi tana jan hijabinta dake jikin kauren kofar dakin ta tana sawa
Tohm Allah yasa bari naje saikixo soro kimasa shinfida kikawo ruwa
Tom mama
Tafice tana tunanin irin kallon dataga yanayimata ranar dataje gidansa yimasa godiya baison tagansa ba da alama akwai manufarsa akanta amma Allah xaimata tsari dashi
Takarasa inda yake jikin motarsa tare dayanke tunanin datake
Daddana waya yake sallamar tace ta katse masa game din dayake bugawa mai dadi ya amsa sallamar tare dasakar mata murmushi kasa tayi dakanta
"Lfy klau ya yara kuma?
Lfynsu klau alhaji ya office
Allahamdulillah
To madalla Allah yadada arxiki da girma
Amin malama
Yafada yana kara fadada murmushin sa dake kwance afuskarsa tundaya daga kai yayi toxali da kyakkyawar fuskar dayake marari,
Shuru ne yaratsa tsakaninsu kafin tace
Alhaji kashigo daga ciki
Yayi dariya har saida jerarrun hakwaransa suka fito reras farare tas dasu tamkar baitauna abinci dasu . Sbda abinda yake nema kenan maganar xatafi idan aka samu aka xauna anutse don haka tana yin gaba...


Read / Download BUDURWAR ZUCIYA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album