Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

WATA KISSAR Complete Hausa Novel Document by WATA KISSAR


WATA KISSAR

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 107921



WATA KISSAR

Reading Time: 8 Hours

Added On: 28, Feb 2025

Author: Aeysher Cool ,Aisha Humaira ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : PERFECT WRITERS' ASSOCIATION

Author Phone : 07063065680

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 570.36 kb

File Type: txt

Views: 92+

Download: 387+

Last download: 4 hours ago

Description/Story: ✨✨✨✨
        *WATA KISSAR*
                  ✨✨✨✨✨

                      ( *Sai Mata* )

         
*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞.

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️



*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''


______Bismillahir rahmanirrahim
Ban rubuta wannan littafi dancin zarafin wani ko wata ba, nayi shine dan ɗebewa masoya na kewa sakamakon hutun da zan tafi da se Allah ya kaimu September zan cigaba da kawo muku littafin AƘIDA TA, Se dai kash farincikin ku shine nawa, zan baku wannan gajeren labari dan ɗebe muku kewa, ina fatan mu amfana da darusan dake ciki
Amma zamu tafi in random direction ne, babu specific lokacin posting, zan Bismillahir rahmanirrahim
Ban rubuta wannan littafi dancin zarafin wani ko wata ba, nayi shine dan ɗebewa masoya na kewa sakamakon hutun da zan tafi da se Allah ya kaimu September zan cigaba da kawo muku littafin AƘIDA TA, Se dai kash farincikin ku shine nawa, zan baku wannan gajeren labari dan ɗebe muku kewa, ina fatan mu amfana da darusan dake ciki
Amma zamu tafi in random direction ne, babu specific lokacin posting, zan iyayi a kowane lokaci, bazan samu kawo posting akai akai ba saboda uzurrurikan da suka shamin kai, dan Allah include me in your prayers.

                       
* a kowane lokaci, bazan samu kawo posting akai akai ba saboda uzurrurikan da suka shamin kai, dan Allah include me in your prayers.

                       

                           Page 1

Tuƙin Babur ɗin a daidaita sahun sa yake cikin nutsuwa da ƙwarewa, yana yi yana duba agogon hannun sa, ga dukkan alamu yana hanzari ne yaje wani guri, kiraye kirayen sallar la'asar da'ake ne yasa shi yin parking ɗin baburin nasa domin bin jam'in salla.
Koda'aka idar da salla, komawa yayi cikin baburin sa ya cigaba da tuƙi.

Wata ƙaramar Unguwa ya nufa, me ɗauke da gidajen talakawa, wani matsakaicin gida ya nufa yaje yayi parking ɗin baburin sa.

Da Sallama ya shiga gidan, amma yanayin sallamar tasa kaman anyi masa dole ya furta.

Wata babbar mace ce da wasu mata guda biyu kewaye da ita suna hira, da gani kasan 'ya' yan tane, saboda kamar da take da su.

Amsa masa Sallamar suka yi gaba ɗaya, tare da yi masa Sannu da zuwa.

Ba wadda ya kula a cikin su ya shiga ɗakin sa, ya ɗau kusan mintuna Ashirin sannan ya fito ya nufi matsakaicin kitchen ɗin dake tsakar gidan.

Yana shiga ya fara buɗe tukwane, wani uban tsaki yayi ya fito tsakar gida ya kalli inda Mahaifiyarsa da yayyen sa suke yace

"Umma wai ba wani abu se tuwon nan, dan Allah ki dafa min wani abun, ni bana son tuwon nan"

Kallon sa ɗaya daga cikin matan tayi tace "iyeee wai har yanzu Ammar baka dena wannan taɓarar ba? Ayi Abinci amma kai se wanda kake so?"

Haɗe rai yayi yace "ina ruwan ki? Gidan ki ne?"

Ɗayar tace "Taɓɗijan nikam Zanga abunda za'a dinga girkawa a gidan ka, ka fiye ƙaƙale Ammar"

Tsaki yayi yace "Umma dan Allah akwai wani Abincin ne?"

Umma tace "Dan Allah kar kuyi min faɗa, ba yadda zaku haɗu se kunyi rigima, nasan dama ba cin tuwon zakayi ba, duba na dafa maka shinkafa da miya yana ɗakina"

Bece komai ba ya nufi ɗakin mahaifiyarsu domin ya ɗakko Abinci.

"Hmm gaskiya Umma kina sangarta Ammar, Abinci se wanda yaga dama? Har yanzu be dena wannan iyayin ba? Wallahi matar Ammar ta shiga uku, ga masifa da zafin rai, ga jin kai da isa"

"Taɓ lallai Yaya Maryam akace miki zeyi wa matarsa ne? Taɓɗijan ai irin sa in suka shiga hannun mata se yadda akai da shi, baze mata wannan muzuran ba, musamman ya haɗu da yaran zamanin nan masu wankaken ido"

Ammar yana jinsu ya fito ya kalle su yace
"har yanzu ba'a haifi yarinyar da zata juyani ba, ƙare wa ni bazan auri yarinya ba, sena samu wadda aƙa llata kai shekara talatin, dan bazan ɗauki hauka da rawar kai daga kowace yarinya ba, Munafukai kunzo se zigamin uwa kuke, baku da aiki se zarya a gida, wallahi nine mijin ku baku isa ba, bazan yadda da wannan gantalin naku ba"

Yaya Maryam tace
"'yar shekara talatin fa sa' arka kenan? Kana shekara talatin da biyar ka auri 'yar talatin da biyar?"

"eh' yar shekara talatin ɗin, wadda tasan meye zaman Aure, ba wannan banzayen yaran masu rawar kai da fitsara ba"

Amina tace "mhmm wai Mune munafukan, Allah ya bamu rai da lafiya, zamu ga matar Ammar, zamu ga irin zaman da za'ayi, 'yar shekara talatin din tayi maganin ka yarinya ba tayi ba"

"Ba' a haife ta ba, macen da zata juya Ammar babu ita"

Yaya Maryam tace "to ina batun Amirar gidan Baffa salmanu, ai kaga ita da girman ta dan zata kai shekara ashirin da biyar, da ko ita seka aura"

"Nine zan auri wannan yarinyar? Banda hauka da yarin ta babu komai akan ta, ko ciwon kanta bata gama sani ba"

"shekara Ashirin da biyar ɗin ce bata san ciwon kanta ba?

Umma tace "dan Allah ya isa haka, ku idan kun haɗu baku da aiki se faɗa, jeka kaci Abincin ka, ni ɗazu gidan Malam Lawan sunzo, sunce dan Allah ranar Lahadi zaka kai musu 'yan ɗaukar Amarya, ka faɗi nawa zasu baka"

Yamutsa fuska yayi "ɗaukar Amarya kuma?"

Umma tace "Eh mana, ko ba kaji me nace ba?"

"Bazani ba" ya bata Amsa
"me yasa?"
"Ni bazan ɗauki wannan mahaukatan yaran ba, in tafi titi suna hauka da ihu a cikin babur ɗina ba, dan sam hankali be ishi matan unguwar nan ba, daga su har iyayen su, basu da kintsi, duk gayyar ballagazai, bana san shirme ko nawa zasu bani ba zani ba"

Maryam tace "hada mu kenan? Tunda muma 'yan unguwar ne"
Wani mugun kallo yayi mata yai gaba abun sa ba tare da ya bata amsa ba

**********

Tafiya take a sannu uniform ɗin ta na makaranta sun ɗau guga, dukda lokaci ya ƙure kusan tara da rabi na safe, ta makara sosai amma tafiyar ta take cikin nutsuwa.

Tana isa makaranta ta shiga kanta tsaye ba tare da fargabar komai ba ta nufi hanyar Ajin su.

Ji tayi an ƙwala mata kira daga bakin staff room "Mufeeda" tsayawa tayi ta dai daita nutsuwar ta sannan ta juyo ta nufi inda ake kiran ta, yanayin tafiyar ta zaka kalla kasan bata da lafiya.

Discipline Master ne tsaye shida megadi tana zuwa ta zube har ƙasa ta gaishe shi, ya amsa ransa a haɗe ya kalle ta

"ke se yanzu ake zuwa makaranta?"
Cikin sanyin murya tace "Sir am sick that's why I come late"
Ta faɗa tana ɗan yamutsa fuska tareda ƙwalla a idon ta alamar tana jin jiki.

"Meyasa kika zo bayan kin san baki da lafiya"?

"Naji na ɗan samu sauƙi ne shiyasa"

"Shikenan jeki Allah ya sawwake"
"Ameen thank you sir"

Ta miƙe tana juya masa Baya ta kama dariya tareda gwali ta tafi Aji.

Bayan an fita break an dawo, class ya kaure da surutu da hayaniya, prefect ne suka zo sukayi magana a class ɗin akan principal yace ayi shiru yana da baƙi, sannan a rubuta masa noise makers duk wanda sunan sa ya fito a 'yan surutu akwai horo me tsanani .

Hakan yasa ajin yin tsit, dan ko kwakwaran motsi kika fiye yi se a rubuta sunan ki, saboda punishment ɗin principal ba sauƙi.

Mufeeda ta kalli ƙawar ta Fati tace "Kin san meyasa na makara yau?"

Fati ta girgiza kai, Mufeeda tace "Anguwar su Anty murja na biya, naje na samu Yaya Usman me mana ɗinki nan ƙanin mijin ta na sauke masa kwandon bala'i, na gaya masa an jima da yamma zan koma ya bani dinki na kona masa rashin mutunci, dan wulaƙanci biki saura sati ɗaya amma be gama min ɗinki na ba, Anty murja ta hanani kuɗin mota wai tunda nayi wa ƙanin mijinta rashin mutunci ba zata bani kuɗin mota ba, ni ko nai amfani da kuɗin makaranta na, nai taho wata"

"Mufeeda wallahi zan rubuta sunan ki, tun ɗazu kike surutu fa" cewar class captain ɗin su

Cikin tsiwa mufeeda tace "eh da yake nika ɗai kika raina ba, karki fasa saka sunan nawa"
Aikuwa aka rubuta sunan Mufeeda cikin masu surutu.

"Fati dan Allah bayan la'asar zanzo gidan ku ki raka ni, idan be gama ba koda me yake yawo seya bani kayana"

Seda Mufeeda tayi surutun ta me
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download WATA KISSAR

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album