Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

MATAR SADIK book 1 Complete Hausa Novel Document by MATAR SADIK book 1


MATAR SADIK  book 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 11535



MATAR SADIK book 1

Reading Time: 0 Hours

Added On: 22, Sep 2024

Author: Zainab Dodo ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION

Author Phone : 09046495943

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 62.97 kb

File Type: txt

Views: 436+

Download: 200+

Last download: 4 days ago

Description/Story: 🧕🧕MATAR SADIK🧕🧕



MALLAKAR
ZAINAB DODO




STORY AND WRITING
BY
ZAINAB DODO( FINANCIAL SECTARY OF THE ASSOCIATION OFFICIAL )




Free book 📖

09046495943


Kuna ina fans ku matso kusa dan jin yarda wannan littafin zai kasance na MATAR SADIK


___________________
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION
💫P.E.W.A💫
Home of perfect writer's together we stand 🤝

ESSENTIAL WRITER'S 📚🖊️*pen 🖊️ is mightier than the sword 🗡️*
_________________
________
________
BISMILLAHI Rahmanirahim
________
Page 1️⃣


Wani matsakaicin gida ne gidan talaka bawan allah, d'akuna uku ne a jere waje daya,sai wani waje da aka zagaye da alama akwai mutum a 'bangaren,Wata kyakkyawar mata ce na hango tsakar gida hannunta rik'e da tsintsiya,ita ba fara ba ita ba bak'a ba irin dai tsaka_tsakar nan ce ga hanci ga idanu bakinta dai_dai ga diri gareta mazaunan ta mutum zai iya d'ora Kofi a kai ba tare da kofin ya Fad'i ba sanye take cikin wata atamfa,tana tsaye tana daddaga tasharar a hannunta irin mutum yayi shara ta d'an saki, wani mutum ne ya fito daga d'aki hannun sa rik'e da hula, fari ne soll ga hanci, yana sanye cikin wani yadi bak'i " Wai harka fito? " Matar ta fad'a,ya bata amsa da "Eh yau ina san naje kasuwa da wuri "Gashi ko naso muyi magana amman ba komai idan ka dawo sai muyi" Okay to yayi" Muje wajen mama" To" ta fad'a tare da ajiye tsintsiyar hannunta suka nufi wani 'bangare da aka zagaye na cikin gidan, a tare sukayi sallama suka ciga cikin d'akin, wata dattijiya ce zaune saman sallaya tana jan carbi, ganin su yasa ta saki murmushi, bayan sun zauna kowannen su ya gaidata ta amsa musu cikin sakin fuska " Auta har an fito?" Eh wallahi mama yau ina San naje kasuwa da wuri ne "To ubangiji Allah ya taimaka ya kawo kasuwa mai albarka" Amin ya rabbi " su duka suka amsa da amin, ya tashi suka fito hannunsu sark'e cikin na juna har bakin k'ofa ta rakasa tace" zuwa yaushe zaka dawo?" To sai munga yarda yanayin kasuwar ta kasance "Okay ka kulamin da kanka allah ya kaimin Kai lafiya ya dawo da kai lafiya ya kawo kasuwa"Amin amin matata "Bakinta ya d'ora a nata ya tsotsa, Sannan ya bud'e gida ya tafi.............dawowa tayi taci gaba da shararta bayan ta gama ta d'auki tsinke da mashaci tayi 'bangaren mama bakin ta d'auke da sallama




"Washhhhhhhhhh" ta fad'a tare da d'ora kanta saman k'afafuwan mama "Sannu "Yawwa mama yau me kike son a dafa ne?" Khadija duk abinda kika dafa "Aah ki za'ba "Aah kiyi kawai"Gaskiya ni sai kin za'ba"ta fad'a tare da bubbuga k'afa irin na shagau'bar nan" To kiyi muna tuwo dan na kwana biyu banci shi ba" To shikenan mama allah nima yau d'in nan da San tuwon na tashi "To kinga shikenan sai kiyi muna shi"Ai kuwa bara na kunce kaina sai naje nayo cefa ne dan ba sauran kayan Had'i "Okay bayan zakiyi ?kawo na kunce miki"Gashi wllh kamar kinsan banasan kunce kitso shiyasama ban cika son yi ba " Ai dan dai kinada gashin ne yasa Baki cika yin kitson ba da bakyada suma dole kije kiyi " Ko mamarmu haka take cewa wai "Ai haka ne ma" ta ciren d'ankwallin sai ga gashin ta ya zuba har a gadon baya manya kitsone ma a kanta kuma ba wani dadewa yayiba, mama ta kar'bi tsinken ta fara kunce mata, ta kunce mata gaba ki d'aya ta shace mata ta kame mata shi........


Bayan sun gama taje tayi Shirin zuwa kasuwa , tazo ta bama mama mukullin d'aya d'akin wanda firij d'in ta suke ciki, dan mace ce mai san Sana'a duk unguwar ita kad'ai keda firij ai kuwa koda yaushe cikin ciniki take, tana siyarda ruwa, zobo, kunun aya,k'ank'arar zak'i........................kuma mace ce da bata dogar ga miji sai ya bata zatayi Abu ba cikin kud'in ta take fitarwa ta siya har cefanen gida ita keyi wani lokaci, ba ruwanta idan ya bata ta amsa tayi godiya idan bai bataba ba ruwanta haka take gareta, yana d'aya daga cikin abinda yasa sadik ke k'ara k'aunar ta,sannan tana bama Mahaifiyarsa girman ta su zauna suyi wasa da dariya wani lokacin idan kaga suna wani abu zaka rantse kace tobassai ne akan shak'uwarsu, yayun mijinta har fad'a suke da mama aka ganin irin sagartar da take mata, sai dai abu d'aya wanda yake damun mama da sadik shine rashin haihuwarta har yanzu kusan shekarar su uku da watanni da aure amman ko 'bari bata ta'bayi ba, ga matar da akayi auren su tare mak'otansu har ta haifi yara biyu amman ita haryanzu Shuru ka ke ji.......



Bayan ta kaimata mukullin ta fito ta samun abun hawa tayi kasuwa, cefanen ta tayi mai rai da lafiya, har ta gama cefanenta ta joyo kenan sukayi kaura da wata mata "Subhanallah yi hak'uri dan allah ban ganki ba" matar tayi mata kallan sama da k'asa tare da cewa" Bangane nayi hak'uri ba saboda wawanci kana tafiya bazaka Kalli hanyarka ba "Yi hak'uri dan allah"Khadija ta sake fad'a"Mtsssssssssssssssssss to idan nace bazan hak'ura d'inba fa" yi hak'uri dai" ta sake fad'a duk da ranta ya 'baci na ganin sai faman bata hak'uri take tana gaya mata maganar banza duk da ma ba laifin ta bane dan ita ta jiyo ne ita kuma matar tana tafiya tana dannar waya, " To bazan hak'uraba" Matar ta fad'a irin cikin izzar nan tare da rik'e k'ugu "Bazaki hak'ura ba? "Eh bazan hak'ura ba" khadija ta aje cefanen hannun ta tare da cire nik'ab d'inta ta jefa cikin ledar ta shak'o wuyan matar ta yarfa mata mari tare da fad'in "Dan kutumar ubanki idan kika hak'ura allah bai godeba bura ubar banza kawai dan ma kin samu ana baki hak'uri shi ne harda k'ara botsarewa to ubanki yaci ubansa idan kin hak'ura" nan take idanun matar nan suka kawo ruwa ga Marin da Tasha ga matsarda take sha, ko kafin kace me tuni mutane anzagayensu ana 'ban'barar hannun khadija amman ankasa,wani mutume da yake gefe yana kallansu mussaman ma khadija yana kallan mazaunanta yarda suke rawa akan jijjigar hannunta da akeyi, ya tako a hankali ya tsaya bayan khadija ya zuro hannuwansa ta gaba a yarda ya tsaya yanajin yarda tudun mazaunanta suke sai ki ci niyar rik'o hannuwanta yake wai shi yazo raba fad'a, khadija jin namiji a bayan ta yasa ta saki matar tare da saurin juyowa ta d'auke sa da mari tare da fad'in " Da aure na da yagiyata uku akai dan kana d'ebabben albarka zako kana ta'bani wallahi yanzun nan sai na kullah ma sherin da ba ubanda ya isa ya fitar da Kai dan iskan banza da wofi asararre"ta sake juyowa ta Kalli matar wacce banda Maida numfashi ba abinda take tace" Dan Allah gobe ki k'ara banza y'ar tasha " ta duk'a ta d'auki kayanta tayi gaba abun ta.....................








Idan naga anyi comment mai yawa zan rik'ayin typing mai tsawo




Bayan ta dawo,ta fara aikin ta,tana aiki ana ta zuwa siyen kaya, duk wanda yazo sai dai tace yaje ya d'auka robar kud'i na ciki ka kad'a kud'i ka d'auka, wasu su kad'a wasu kuma su k'i kad'awa kuma su d'auki kaya............


Cikin k'ank'anin lokaci ta kammala girkin ta sai k'amshin miyar keyi, ta d'auki na mama taje ta kai mata ta dawo ta kai sauran abincin d'aki, ta shiga toilet tayi wanka ta shirya cikin wata doguwar riga,mai kyau,bayan ta gama bada jimawa ba,sai ga sadik ya dawo cin abincin rana, ta tarbesa irin yarda ya dace ta kai masa ruwan wanka a bayi yaje yayi wanka ya fito ta d'auko masa wasu kayan, ta kawo masa abinci, lomar farko sai da ya runtse ido tare da kyad'a kai "Allah dai ya miki albarka ya k'ara miki zak'in hannu kiyita yimin irin wad'an nan girkin mai dad'i" Amin Amin mijina" Yawwa wace maganar ce kika ce kina son muyi?" Daman akan maganar gadon nanne da aka raba aka bani nawa shi ne nayi wani d'an nazari akan mezai hana na arama kud'in ka k'ara cikin Sana'a ka ka juya,tunda ni kaga ina da sana'a bare nace jari zan ja "To matar sadik amman kina ganin ba matsala " Ba matsala" kinyi shawara da inna ne" Aah ai Wannan kud'i na ne ni keda ikon yin duk abinda nake so da su bare kuma nasan inna zata goyi bayana akan wannan abun "To shikenan allah yasa musu albarka"Amin" ta fad'a tare da Mik'ewa taje ta bud'e wardrobe d'in ta ta d'auko wata
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download MATAR SADIK book 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album