Join Our WhatsApp Group

KYAWUNA JARABTA TA Complete Hausa Novel Document by KYAWUNA JARABTA TA


KYAWUNA JARABTA TA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 55436



KYAWUNA JARABTA TA

Reading Time: 4 Hours

Added On: 18, Sep 2023

Author: Aisha Muhammad Maman Shakur ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 07012181461

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 323.82 kb

File Type: txt

Views: 1728+

Download: 507+

Last download: 14 hours ago

Description/Story: ********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels



Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************

💫 KYAWUNA JARABTA TA💫


✍️M SHAKUR

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAIJINKAI.

LITTAFIN NAN NAKUDI NE BUT FOR NOW INA FREE PAGE SO U ALL CAN SHARE.
subscription is 500 idan kinaso kibiya nasaki a group zaki turo 500 into 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turomin evidence of payment ta watsapp number na 07012181461 sainai adding naki a group din danake posting.



S-SQAURE FASHION AND MORE GIDANE NA HIJABAI DA HADADDUN DOGAYEN RIGUNA NA DINKAWA, KUNSAN MA MENENE TANA WANI PROMO NA FREE DELIVERY KOWANI GARI KIKE IDAN KIKASAI KAYANSU ZATA AIKOMIKI DA KAYAN KYAUTA, DON MAGANA DA ITA KO CHATTING NATA UP DAN SAYAN KAYAYYAKIN SU CLICK ON THIS LINK wa.me/+2347030037697



Free page
EPISODE 1️⃣

Tudun Yola, Kano!
Baban Anguwace kuma sabuwa dan babu mutane haka sosai a anguwan, saidai irinsu uncompleted building da ake kan ginawa dakuma sababbin gidaje da ba'a dade da tarewa cikiba.

Baban gidane dayasha fenti milk color, kana ganin ginin gidan kaga ginin irin family house dinan, tsakar gidan mai bala'in fadi, ga katuwar bishiyan mangwaro a tsakar gidan datai y'ay'a sosai dudda basu nunaba, flat biyune agidan wani babban dankareren flat saikuma wani karamin flat mai kamada boys quarters agefenshi, gidan kana ganinshi kasan bawani gidan mai bala'in kudi bane gidan rufin asiri ne dai namai karfi daidai, motoci biyune parke atsakar gidan wata bus mai kyan gaske milk color saikuma mota sienna ash da mai gadi ke wankewa ga dukkan alamu motar maigida ne sabida yanda ya kuke yana wanketa yanabin wakan sangaya dake tashi a karamin radio daya ijiye kan plastic chair.





Bude kofar karamin flat din dake kusada babban flat din akayi, wani Matashi ne baki dogo baida jiki sosai yana sanye da jallabiya brown hannunshi rikeda makullin mota yafito, takalmi yasaka sanan yasauko daga matattakalan bakin kofarsu yadumfaro babban flat din, da sallama yabude kofa ya shiga ciki.
Babban falo dakeda girman gaske, wani Babban Magidanci ne zaune akan kujera akalla zaiyi 60years kokuma 59, kana ganinshi kaga mai gidan, bakine yanada jiki, hannunshi rikeda jarida dayake budewa yana karantawa.



gefenshi kuma wata Mata ce mai kiba Hajiya Balaraba akalla zatai 40yrs tasaka wani hadadden lace tana kurban shayi a cup, saiga yara dasuke zazzaune akasan carpet suna breakfast kowanne nashan tea da bread da soyayyan egg dinshi, Mata uku ne a tsakar falon da maza biyu wanda duk kasansu daya, Amal that is 14, sai Asiya 13yrs, sai Aneela dakenan 11, Mazan kuma Muhammad dakenan 11 sai Mudasir wanda shine autan gidan 6yrs, gabaki dayan yaran kana ganinsu kaga mahaifinsu tundaga bakin fatar da jikin dan dukansu tuluka tuluka dasu very fat gwanin ban sha'awa kana ganinsu kasan sunacin lafiyayyen abinci, dukansu suna sanyeda uniform din makaranta da alamu hadda zasu danyau sunday.


Kitchen aka bude, wata black beauty Matace dan itama ba yarinya bace akalla zatai 38yrs tafito tana sanyeda doguwan rigan atampa mai kyau da akama stonework tana rikeda tray dawasu hadaddun kwanuka ke kai, hada ido tayi da wanda ya shigo dakin dukbasu luradashi ba yasa tace "this children zasusa kayi latti for your program Ya Hamad" kiran sunan shi datayi yasa duka yaran dakowama na falo yadagokai ya kallai, atare duka yaran suka gaidashi "Ya Hamad good morning" batare daya amsasu ba yakarasa shiga falon har gaban Abba yakarasa sanan yazauna agefenshi yace "ina kwana Abba" sanan yakalli matar dake gefenshi yace "Ina kwana Mum" daidai lokacin dayan matar taja coffee table zuwa gaban mijin nasu ta dauramai tray akai tace "your food is ready Daddy Hamad" jaridan ya linke tareda mikamata, karba tayi dayan matan tadauke kai Abba kuma yatura hannu a aljihun sanan yaciro wasu kudi yamikama Hamad yace "inka kaisu kabiya musu kudin makaranta" sanan yajuya yakalli matar dake gefenshi yace "me yaran nan sukeyi asama har yanzu basusan zasu makaranta bane"? dasauri tace "kumafa su tuntuni sukai break, Nanaa, Hawwa" daga chan sama aka amsa, wasu yan mata manya masu jiki guda biyune suka sauko daga stairs, yaran zaka dauka yan biyu ne dan suna kama, irin kama na jini dinnan, Nana itace Babba 26yrs take tana final year a BUK tana karanta Mass Com, sai Hawwa 24yrs tana 300level tana karanta international relation itama a Ado Bayero, Hawwa na kama da Hamad sosai, dukansu suna sanyeda lemon green hijabi na haddan, dukansu ransu abace yake dan sun tsani zuwa hadda suna uni amman suna wani zuwa hadda shikuma Babansu yanuna babu wacce ta isa tabar hadda cikinsu kodako PHD sukeyi, tashi duka yaran sukayi sukama iyayensu bye suka fice, sanan Ya Hamad din yatashi yace "bari nakaisu Abba" gyadamai kai kawai yayi dan haka Babansu yake baifiye son magana ba, sanan yawuce yafice.
Kaman ance tadaga kanta sama taga gittawan mutum dasauri an bude kofa anshige daki batare da an bari sun hada ido da Mami ba. Ahankali Mami tasauke ijiyan zuciya dudda bataga fuskanba but ko amafarki aka tadata tasan waye.





Duk suna zaune afalon harya gamacin dumamen tuwon yadauki ruwa yasha, Dan gyaran murya matan dake zaune kusada shi tayi Mum tace "Alhaji nace bari namaka tuni, kaga duka duka bikin Nana bayan Babban salla da sati uku ne, gashi lokaci nata matsowa yanzu baifi wata daya bikin ba, nasan dama kariga kabada kudin kayan daki, cha kayi daman wanan satin zakaban kudin kayan kitchen, kaga idan kabani nida Zainab saimu shiga kasuwa yau muyo siyayyan koya kika gani Zainab"? Mum tama Mami dake zaune tana sauraransu magana, gyadamata kai tayi sanan tace "eh hakane Abban Hamad" ruwa yadauka a cup yakara kaiwa baki yasha sanan ya ijiye cup din, hannu yasa a aljihu yaciro bandir din yan dubu daya guda biyu yabata yace "kinemi wata kijeda ita kasuwa, Zainab bazata iya zuwa ba itakeda girki, kuma yau lahadi ina gida" yana fadin haka yatashi yawuce sama duk suka bishi da kallo, saida taga yashiga dakinshi sanan tabata rai tace "Alhaji Alhaji bantaba ganin kafaffen mutum irin shiba wlh" tashi tayi batare data kalli Mami ba tai stairs tabude bangaren ta tashige dan saman bangare biyune nata dana Zainab saikuma dakunan yaransu guda uku, na maza kanana dana mata kanana saikuma na yan matan suma dakinsu daban.



Ahankali Mami ta tashi ta tattare duka kwanukan takai kitchen sanan tasa Mai aikinsu Uwani tazo tashare falon ta kunna turare sanan tai sama itama bude dakin mijin nata tayi tashiga bata wani dade aciki ba sanan tafito, direct dakin yan matan tayi ahankali tabude kofar, dakin nada dan fadi gashi a gyare Kal Kal, gadaje ne guda uku irin nayan boarding jere adakin kowanne da bangaren nashi saiga wardrobe na bango da kayan kowa keciki, bin kan gadajen tayi da kallo ganin babu kowa kai yasa takarasa shigowa dakin tareda maida kofan tarufo sanan tashigo ciki takaraso tsakiyan dakin saikuma ta tsaya turus tai shiru tana kallon gaban gadon dake tsakiyan dakin, wata faran budurwan yarinyace azaune akasa tabama dakin baya tana kallon bango tadaura kanta kan kafafuwanta ta, nimai rubutu M Shakur banmasan mutum bane awurin ba saida naga Mami ta tsaya turus tana kallon wajen, wani irin silk black gashin kaman na yar India ne zube awajen yana taba tiles din kasan daki sabida yanayin zaman datayi tsabagen tsayin gashin, sai farin kafanta sol mai bala'in kyau da dogayen fararen farcenta dababu komi akai sai uban haske kaman ana wankesu da madara. "Du'a" jin ankira sunanta yasa tadago kanta daga kifen dasuke akan kafafunta dasauri batare data waigoba jin muryan Mamin ta, dan Jim Mami tayi tana binta da kallo sanan asanyaye tace "inkin gama kukan ki tashi ki tattare gashin nan naki ki kulle kisa a hijabi kije Abban ki nakiranki yana dakin shi" tana maganan tawuce tafice daga dakin tarufo musu kofan.



Ahankali takai fararen hannuwanta tashare fuskanta sanan tamike tsaye ahankali, wani iri mahaukacin cokacola shape Allah yamata gawani irin pointed curvy ass gareta daya fito sosai cikin doguwan rigan material din dake jikinta, itama kaman sauran yaran gidan tanada dan jiki danbazaka taba kiranta da mara kiba ba amman batakai su Nana kibaba, saidai tafisu diri, ga gashin kanta dabaida banbanci dana yan India har waist dinta, juyowa tayi ahankali TSARKI YA TABBATA GA ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA WANDA YA HALLICI SAMAI DA KASSAI DAKUMA HALITTUN DAKE CIKINTA!!!! yarinyar nan koda ace itace tayi kanta banjin zatai kanta tai kyan datake dashi yanzu hakaba dan My Lord!!! dan itace definition of tacika goma cip cip tamakai sha uku, farace Kal fuskanta babu pimple ko daya idanunta sun kumbura sunyi ja sabida kukan datayi wanda haryau takasa sabawa dan by now yakamata ace tasaba duk sanda yan uwan ta zasu makaranta boko ko islamiyya saitai kuka, tanada wani irin long pointed hanci ga pink lips, gashin idanunta dogaye kuma acike sun jikeda ruwa, ga kirjinta awani irin cike kaman wacce taje tai surgery ga flat tummy kaman bata tabacin abinci ba, Allah yamata ass amman waist dinta kona jariri albarka her waist is so tiny, ahankali take tafiya har zuwa gaban madubin dakinsu ribbon dinta dake wajen tadauka sanan ta kulle kanta da kyar sanan tashiga bayinsu wanko fuskanta tayi tafito tadauki dogon hijabin ta maroon tasaka tafito daga dakin ahankali.


Cikin wata irin siririyan cool melodious voice tai sallama gaban dakin Abban su, daga ciki taji yace "shigo" ahankali tabude kofa tashiga kanta akasa, yana zaune kan couch din dake dakin yabita da kallo tazo gabanshi tazauna tareda saukar da kanta kasa ahankali tace "Abba gani" zama ya gyara tareda bude Al Qur'ani dake kan cinyanshi sanan yace "biyomin haddanki" gyara zama tayi sanan tafara rairomai suratul Yusuf shafa'i ukun dayabiya mata last week, shi karan kanshi idan tana biyamai hadda baiso tadena dan muryanta Allah yay mata dadi saida tagama tsaf sanan yakara mata wasu shafa'i ukun kafin yamata tajweed sanan yace "tashi kitafi" tashi tayi ahankali tai hanyar kofa yasake binta da kallo harta daura hannunta kan handle din kofa taji yakirata anatse. "Du'a" dasauri tajuyoda kanta ta kalleshi saikuma tasauke idanunta kasa tace "na'am Abba" ahankali yace "nariga nasaman miki wata sabuwar malama, daga gobe zata fara zuwa In sha Allah, ki shirya" gyadamai kai tayi sanan tajuya zata bude kofan saikuma tajuyo ahankali batare data budeba ta kalleshi hada ido sukayi hakan yasa takasa magana tajuya zata bude kofan tafice cikin muryan nan nashi nabawasa yace "mekikeso ki fada"? Dan juyowa tayi ta kalleshi saikuma tasauke kanta kasa kirjinta na bugawa fat fat tashiga wasa da yatsunta tsabagen how nervous she was tama kasa magana, dan idan Abban su yakureka da ido zamaka iya fitsari ajiki baka saniba, shifa kokadan baida wasa kuma yanada zafi sosai, gashi kaifi daya saisa duka yaranshi ke tsoron shi. Ganin takasa magana yasa yace "I'm listening" rawa sosai muryanta yafara tanama bude baki maganan yakasa fitowa saikuma tasaki hannunta ta shiga chakuda hijabinta da hannu duk yana binta da kallo hijabin tarike gamgam sanan da kyar tasamu maganan yafito ahankali tace "Ab.....ba ni......maisa ake barina agida kahanani fita kowaje, Abba ni nafison naje school kaman su Ya Nana......" saikuma tasake hadiye wani irin dry miyau hawaye yawani zubo daga idanunta suka sauka akan hijabinta cikin wata irin murya na wacce ke gabda fashewa da kuka kuma take a bala'in tsorace tace "Ab....ba ni maisa baka sona kaman yanda kake son su Ya Nana da Hawwa da....d....." Du'a!! taji anwani irin kirata da kakkausar murya dayasa tadaga kanta da sauri ta kalli inda taji muryan, Mami ce tafito daga bedroom din Abba da alamu tuntuni take ciki maybe gyaramai dakin take dan taga karamin rag na goge goge a hannunta, cikin wani irin tsananin bacin rai tace "Du'a are you questioning your father? eh? mahaifin ki kika tasa agaba kina tuhuma haka?" girgixa mata kai tayi dasauri saikuma tasaki kuka dasauri tajuya tabude kofa tafita daga dakin dagudunta.



💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫




✍️M SHAKUR

UMMI COLLECTION is a whole world of turaruka, both na wuta dana feshi, exquisite burners na electric dana charcoal, and oils, turarukan wanka da sauran su. kunkosan kwanan nan UMMI COLLECTION na promo free delivery, hehehe banso kuyi missing this mad offer just click on this link danyin magana da ita directly.
wa.me/+2348186968736



free page
EPISODE 2️⃣
Azuciye Mami ta jefar da rag din dake hannunta tace "nikema yarinyar nan magana tafice tabarni sabida batada kunya Dadyn Hamad" tataho cikeda bacin rai zatai wajen kofa tabita Abba dake kallonta tunda tafara masifan yace "ina zaki"? Turus ta tsaya tana kallonshi takasa koda motsi, anatse yanuna mata bedroom dinshi yace "koma kicigaba da abinda kikeyi" dasauri tace "but......" "no buts ki koma kicigaba da abinda kikeyi nace" yay maganan babu alamun wasa akan fuskanshi hakan yasa bata karacewa komiba tawuce takoma ciki ranta abace, jaridanshi yabude ahankali yacigaba da karantawa bazaka gane takamaimen wani yanayi yake cikiba dan fuskanshi bata nunawa.


Dakinsu tabude dagudu tashiga tafada kan gado tana kuka sosai, tayi kuka nakusan awa daya sanan bacci yay awon gabada ita akan gadon.
Hayaniya yatadata daga baccin datakeyi, bude idanunta tayi ahankali saikuma ta yunkura ta tashi zaune tana kallon dakin nasu, Nana da Hawwa ne kecire kayan jikinsu sundawo daga hadda duk sunyi zufa, ahankali tace “Ya Nana kundawo daga makaranta” danjuyowa Nana tayi takalleta tana kokarin daukan zanin dazata daura tashiga wanka tace “eh yanzu muka shigo”"sannu da zuwa" tafadi ahankali sanan tajuyo da kanta Hawwa ta kalla taga Hawwa tadauke kai dasauri tana batarai, daidai lokacin aka bude kofan dakinsu, Aneela ce tashigo wacce take kanwarta, dan Du’a ce yar Mami tafarko, sai Aneela, sai Muhammad da Mudasir su Hudu Mami ta haifa, itakuma Mum itace mahaifiyar su Hammad, Nana, Hawwa, Amal, da Asiya yaranta biyar.


Ko kadan Aneel bata kama da Du’a inba ma angayamaka ba bazaka zaci uwarsu dayaba dan tafi kamadasu Nana black beauty ce itama, kyakkyawan yarinya bakutu da ita, zama tayi kan gadon takalli yayartata tace “yauma saida kika kara kuka sabida muntafi makaranta banda keko” Hawwa data zauna kan gadonta tana ciro wayanta daga jaka tana kunnawa tace “asheko xakita kuka har karshen rayuwanki dan Abba yace konan...


Read / Download KYAWUNA JARABTA TA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album