Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

AISHAH SIDDIQAH Complete Hausa Novel Document by AISHAH SIDDIQAH


AISHAH SIDDIQAH

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 37616



AISHAH SIDDIQAH

Reading Time: 3 Hours

Added On: 10, Feb 2025

Author: Sumayya Abdulkadir Takori ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 07030137870, [email protected],

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 210.68 kb

File Type: txt

Views: 154+

Download: 122+

Last download: less than 1 second ago

Description/Story: 
AISHAH-SIDDIQAH



1






SUMAYYAH ABDULKADIR
[email protected]
[email protected]
TUNASARWA/JAN HANKALI
Ba’a rubuta littafin AISHAH-SIDDIQAH don cin zarafin kowacce kabila ba, ko don nuna wata kabila ta fi wata daraja a tsakanin kabilun Najeriya ba.
Kyakkyawar manufar dake kasan labarin itace dabbaqa kalmar WA-ZO-BIA da fadakarwa cikin nishadi akan kabilancin da ake nunawa ita wannan kebantacciyar kabila dana dauka, da kuma wanda suma suke nunawa ga kabilar hausawa.
Labarin AISHA-SIDDIQAH labari ne da aka gina shi kacokam akan manyan kabilun Najeriya guda uku, don son samar da fahimtar juna da rage tasirin kabilancin da yayi katutu a zukatanmu ga junanmu.
Asali mun san cewa Najeriya kasa ce bata kabila guda ba, bata yare ko harshe guda ba. Bincike ya nuna kusan kabilu 371 da yarurruka sama da 500 suka hadu suka mallaketa, wadanda suka fi yawa sune Hausa, sannan Yoruba, Igbo da kuma Fufulde.
In haka ne kenan babu wadda ya kamata ace tana faharin tafi wata, ko tata itace kan gaba ko mafi daraja, in dai Allah daya muke bautawa sai mu rike ayar “Inna akramakum Indallahi Atqaakum”.
Idan kuma ba addini daya ya hadamu ba, sai mu dauki ayar “Lakum Deenukum Wa liya Deen” nan ma sai kaga an zauna lafiya da juna.
Fatan marubuciyar shine Hausawa mu daina kabilanci, in bazamu iya dainawa ba mu rage shi, sauran kabilun suma su rage nasu kabilancin ga hausawa, ta hakane kadai za’a samu hadin kai da fahimtar juna a tsakanin WA-ZO-BIA wadda zata iya zama jagora wajen cigaba da haifar da auratayya da kyakkyawar mu’amala tsakanin kabilun musulmai a duk inda suke a kasar nan. Don haka kada kayi tsalle ga tafiya karshen labarin ko ka dauki wani abu ya zama cin zarafi ga yarenka ko kabilarka ba tareda ka ga karshen littafin ba. Taku har abada.
–Takori Sumayyah AbdulQadir.
SADAUKARWA
Aisha-Siddiqah ta sadaukar da labarinta ga daukacin mambobin whatsapp group na TAKORI’S LOUNGE bakidayanku. Allah ya bar zumunci da kauna har ‘ya’ya da jikoki.
KIYAYEWA
Hakkin mallaka abin kiyayewa ne ga marubiciyar littafin, ban yarda a karanta shi a kowacce kafa ta sadarwa ba tare da rubutaccen iznina ba. Yin hakan ya sabawa doka ta shari’ah kuma abin tuhuma ne daga lauyana Barr. Sadiq Rufa’I Wali.
GODIYA DA JINJINA
Godiya da jinjina ga aminan kwarai wadanda suka taimaka matuka gaya wajen shawarwari, tacewa da gyarawa (editing) Dr. Amina Jafaru Musa, Barr. Azima Musa Abdullahi, Aisha Muhammad, Maryam Yusuf Abubakar, Haj. Zainab M. Ahmed da Bilkisu Askira.
In tsaya ina ce muku na gode kuma kunsan yayi kadan, saidai kawai in jinjina muku bisa namijin kokarinku akan ingantuwar littafin AISHATU SIDDIQAH.

KAFIN MU FARA INA TALLATA MUKU AISHA LAME (ORIGINAL ORIFLAME AMBASSADOR)
Kina neman jakadiyar oriflame ta kwarai? Kinason mayuka da zasu dace da launin fatarki a wannan lokacin na zafi kona sanyi? Kinason kamshi na alfarma? Kinason supplements ingantattu na wellness and meal replacement ga masu bukatar weight loss and weight control? Kayan kwalliya na kerewa sa’a? Kina bukatar zama Dawisu sarkin ado? Kawai tuntubi AISHA LAME a lambar waya 07036662633 zaki samu duka wadannan cikin farashi mai inganci da kyakkyawar mu’amala. Aisha Lame karshe ce wajen baiwa fata hakkinta ku tuntubi Aisha ku zo ku bani labari.
-Takorinku


SHIMFIDAR LABARIN
WAIWAYE ADON TAFIYA (1)
Dr. Murjanatu, wadda kowa a gidansu da danginsu bakidaya da “Taiwo” yafi kiranta, kannenta kuma suce mata “Aunty Taiwo”, abokan karatu su ce Murjanatu Akanni. Murjanatu baka ce ba sidik ba, bakin da akewa lakabi da (chocolate beauty) sabida sanyin kyawunsa da haskensa, doguwar mace mai ‘yar kyakkyawar kiba ta jikin hutu, irin kibar da batayi munin da za’a ce mata lukuta ba.
Saboda duk da kasancewar ingarman jiki keda Dr. Murjanatu to suffar jikinta mai tsari ce duk da kibarta, gata da doguwar fuska irinta fulani da dara-daran idanun yarbawa masu haske, Taiwo-Murjanatu, nada dogon hanci sambal irin na Kakarta ta wajen Uwa wadda ta kasance bafullatanar jihar Gombe da suke kira “NANI OUMMANA”.
Sannan tsayin ta masha Allah shima bai wuce misali ba. Komai na Dr. Taiwo kamar ita ta aunawa kanta ta kuma zaba. Domin dai a fasalce baza’a kira Aunty Taiwo doguwa irin sambal ba, saidai ace kamar kwalbar nan ta coca-cola ga kauri ga tsayi da dirin jiki mai zati, tana a ma’aunin daidai na tsayin da akeso a tareda mace.
Shekarun Murjanatu na haihuwa a wancan lokacin da muka waiwaya talatin cif. Murjanatu-Taiwo Akanni ga tsayi ga zati irin na mace mai aji da kasaitar nasaba, girman jikinta mai ban sha’awa ne don bai sa mata muni ba. A takaice komai na jikin Taiwo irin na matasan matan kabilar Yoruba ne, wato daga kabilar Yarbawa ta fito.
Tafiyar Taiwo mai daukar hankalin mai kallonta ce, domin tana tafiya ne cas-cas akan tsinin dugaduganta, cikin rangaji na jan aji da kasaita sanna ga iya ado mara misaltuwa, kullum haka take cikin tsantsar gayu da yawan ado, duk yadda ta motsa ko tayi magana ko murmushi sai kaga wannan ajin na musamman irin na jinin sarautar gidansu ya nuna kansa a tareda ita.
Kallo daya zaka yiwa Taiwo da dabi’unta da iya kasaitarta kasan ta hada jini da sarautar Yarbawa mai tushe, ko daga yanayin takun tafiyarta dinnan mai kayatar da idon mai kallonta kamar Dawisun da ya baza adon jikinsa yake tafiya.
Tafiyar Murjanatu cikin kasaita da iya sarrafa jikinta da yake mul-mul irin na kosassun ‘ya’yan kabilar Yoruba da suka ci suka tada kai.
A daidai wannan lokacin da Murjanatu ta shigo gidanta, yamma ce lis, hadari ya gangamo, sararin samaniya yayi duhu, sai cida da iska ke kadawa, gab ake da kecewa da ruwan sama mai karfi.
Wannan na faruwa ne a cikin daya daga manyan biranen Najeriya mafi yawan al’umma da kabilu daban-daban, wato birnin Legas ko Ikko da aka fi sani da jihar Lagos.
Gidan nata matsakaicin gidane kyakkyawan (Duplex Mansion) wanda anan Dr. Taiwo da iyalinta ke zaune tun dawowarsu Jihar Lagos da zama daga Ilorin, gidan yana nan a shiyyar babbar unguwa mai tsari ta masu hannu da shuni ‘Eko Atlantic’, gidan Murjanatu nada farin fenti mai dan duhu da ratsin ruwan madara-madara (off-white/milk), kuma gida ne da in ka gani ko daga nesa kasan masu shi sun jima da kama kasa.
Zamu iya kimanta lokacin da misalin karfe shidda na yamma, daidai lokacin da Taiwo-Murjanatu, ta shigo da kan motarta kirar ‘Hyundai Creta’ harabar gidannata, bayan tasowarta daga asibitin da take (housemanship) acan, wato asibitin koyarwa na jihar Lagos.
(Murjanatu-Taiwo Akanni, dalibar likitanci ce a Lagos State Teaching Hospital).
A wannan lokacin duk tunaninta da hankalinta na kan karamar diyarta (Kiki) wadda ta baro a gida hannun sabuwar mai rainonta Bunmi, tun bayan data fara housemanship ta samo Bunmi ‘yar kabilar Ibira suke zaune tare.
Kiki ‘yar kimanin shekaru uku wadda saboda son da dan uwanta yake mata, yasa a yawancin lokuta bata dauka cewa ita ta haifeta, tafi dangantata da ‘yarsa shi kadai, ko cewa zata yi Kiki sai ta hada da inkiyarshi, tace “Kikinshi” ko “Kikinsa”.
A lokuta da yawa idan ana hirarsa, kasancewarsa ‘Polo Celebrity’ ne, ‘yar uwarsa Murjanatu data fi kowa kusanci dashi ta kan gayawa kawayenta daliban LUTH, musamman wadanda ke bibiyar kallon wasan shi a kafar talbijin ta “Global POLO TV, suke kuma mayatar son jin wani abu da ya shafeshi personally, Taiwo kan basu labarin irin son yaransa ne, ta kan ce da dai ace maza na haihuwa da kansu, ba mata ke haifa musu ba, da tasan shi zai yi nakudar Kiki ya haifeta, wato da bazai bar mata ta haifota ba, saidai shi da kansa, saboda sonda yake mata a matsayin karamar diyar ‘yar uwarsa, wadda duk duniya bashi da makusanci, amini, amar ita ‘yar uwarsa Taiwo. Ya sha gaya mata cewa ya raina adadin kulawar da take baiwa Kiki, tunda har ta zabi karatun likitanci akan zaman gida ta kula da kyautar ‘ya’ya biyun da Allah ya bata.
Tana basu labarin irin yadda yake bata lokacinsa in yana gaban Kiki, don mayar da shekarunsa yake daidai da nata, su taru suyi ta zuba
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download AISHAH SIDDIQAH

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album