Join Our WhatsApp Group

HALALCIN SARAUTA Complete Hausa Novel Document by HALALCIN SARAUTA


HALALCIN SARAUTA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 31209



HALALCIN SARAUTA

Reading Time: 2 Hours

Added On: 07, Sep 2023

Author: Benaxir Omar ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 193.89 kb

File Type: txt

Views: 556+

Download: 188+

Last download: 6 days ago

Description/Story: HALACCIN SARAUTA
littafin Benaxir Omar
Ebook created by Shuraih 99%
Punlished at www.hausaebooks.com.ng


benaxir  September 18, 2015
 Hausa Novels  167 Views
HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Aliya yar
kimanin shekara ashirin da daya zaune adakinta wanda
yasha kaya,duk abinda ya’mace budurwa zata bukata toh
akwai shi acikin dakin aliya takardune agabanta dakuma
hotunan mutane wanda take bi daya bayan daya daga dan
zaman da ni benaxir nayi ina lekenta nasamu labarin cewa
Aliya yar asalin garin yombi ne wata babbar masarauta da
ake darajar mulkin sarauta,tanada shekara sha biyar sarkin
yombi ya bukaci akashe duk masu hannu da reshawa
wanda acewarta sarkin yabada sakon akashe mahaifinta
mussaman acikin wannan hargowan don mahaifinta
yakasance shine galadima kuma yana kawo musu matsala
a fadan garin, duk wani abu marar kyau mahaifin aliya
hassan adamu yana kokarin yafidda hakkin musulunci
dakuma hakkin mutane, hakan yasa sarkin garin yabukaci
da akasheshi cikin saa aka kashe hassan adamu da
matarsa alokacin aliya tana makarantan kwana na
yan’mata dawowarta ta tarar da mai aikinsu wanda yabata
wani karamin akwati acewarsa ana gobe mahaifin zai rasu
yace abata, tayi kuka sosai harta bude akwatin anan
tasamu takaranta tarihin komi mahaifinta dama yasan zaa
kasheshin donhaka yamata bayanin komi, dawannan aliya
tayi alkawarin saita rama wa iyayenta abunda aka musu,
barin garin tayi ta tafi abuja gurin yar mamanta inda ta
kammala secondry dinta a shekara sha shida, sannan
tasamu admsn a g.s.u ta takaranta sociology na shekara
hudu sannan taje tayi service dinta,ta kammala komi
tanada shekara ashirin da daya, duk wannan tsawon
lokacin aliya bata saurayi namiji da sunan soyayya ba
acewarta zaibata mata duk wani plans din ta, yar mamanta
wacce tazauna agunta tasan da maganan ramakon da
aliya takesonyi kuma tagoya mata baya duk da tana tsoro
anma taga ita aliyan bata tsoro, aliya agun bautar kasanta
wanda tayi a benue tasamu nasaran samun wani mai suna
ikem zama tayi tayu training agunsa, yakoya mata fada,
yakuma koya mata duk dabaru da abubuwan dake faruwa
acikin gidan sarauta, ya ilmantar da ita da basira dakuma
dabaru dazata kare kanta takuma yi ramakonta cikin
kwanciyan hankali, yabata littafan tarihi dakuma littafan
koyan basira da littafan daya shafi sarautan hausawa
harna yare aliya takaranta tsaf takoya, saan da aka samu
shine aliya macece mai hazaka da basira, batada mantuwa
ko kadan, kallon abu sau daya yakansa ta haddaje abu
batare da ta mantaba, sai abun yasamu daidai sanadin
karanta sociologyn datayi, saita zamto mai nutsuwa gurin
karanta mai dan adam yake ciki yake kuma sonyi, saidata
kammala komi sannan ta tattara takoma gidan antynta
inda tafara shiri antynta tamata waazi anma aliya tanuna
tafiyan shikadai zaisa tamutu lafiya, tabarta aranan aliya ta
tattara tatafi yombi inda tasamu daki tajera kayan alatu
dakomi. Dakin yana wani lungu ne wanda bakowa bane
zaikawo akwai abun duniya aciki, aciki tazauna tagama
hargowanta agarin yombi tana tara labarai gameda fadan
sarki. Tahado kan matarsa,da yaransa daduk wani abu
daya shafi sarkin, sannan tadau niiyan shiga fada, Dafarko
taje tasamu matar dake kwasan bayi takai fada,taroketa
datanason zama afada akan acewa ita yar kwarkwara ce
anma batasan wacece ba,tanason tazauna as baiwa don
tagane ahankali dafarko taki yarda anma da aliya tacire
dubu goma tabata bashiri tace “kije kisaka kaya irin nasu
na bayi mushiga” aliya ta amince da hakan takoma gyda
tashirya tsaf tanemo wasu tsoffin kaya tasaka, sannan
tanufota, matar tace “muje kishiga cikinsu karki fadawa
kowa komi, kina gama nemo mahaifiyarki karki manta
dani” aliya ta amince dahakan ita burinta tashiga fadan
sarki takashe sarki, dahaka suka shige kafanta na dama
tafara shiga fadan tare da adduan Allah yabata saa, gefen
fannin bayi aka kaisu anan aka bukaci da su zazzauna,
akasa suka zauna aliya tajuya tana kallon wurin dakyau
takuma kalli bayin dake gefenta kowannensu kuka yake
don basuda niyyan zuwa ita kuwa ko ajikinta, acan saiga
matar tashigo tareda wata wacce taji tana kira da “umma
uwar soro” umma uwar soro tace duk sumike acewarta
zata rabasu ne zata zabi masu aiki a fada, da masuyi a
kicin, da na bandaki, dakuma sauran kwarkwaraye dafarko
ta umurci kowacce taje tayi wanka aka basu wani farin riga
susaka, aliya tayi wankan tsaf sannan tafito tajera layin
ana dubiya ne daga fatan jikinsu, sai kuma kyansu, da
yanayin tsayinsu, tafara bi daya bayan daya inta yanke
awani gu zakiyi aiki zaabaki uniform din aikin gurin kodata
iso kan aliya takare mata kallo , aliya doguwa ce bawanda
zaice guntuwa ce, saidai bakace , bakinta mai kyau, tanada
hanci dan daidai da karamin bakinta sai manyan ido,
hakika black beauty ce don yanayin fatarta baacika samun
irin shiba, hannun hajjo tarike dasauri takalleta tareda cewa
“anya ke baiwa ce?” Aliya tayi murmushi don dama
tashirya wa tambayan tace “fatana na gado ne” umma
uwar soro tacigaba da dubata gashin hajjo acunkushe cikin
ribbon ta cire ribbon dim saiga gashi yazubo har gadon
baya, ta girgixa kai sannan tace kumika mata uniform din
fada, anan aka bata blue yard ne anyi dogon riga fittet, sai
dankwalin dan karami hajjo daure kanta tayi duk kokarim
ta cunkushe gashin abun ya gagara. Aka kaita masaukin
bayi aka nuna mata katifanta, dakin ko na karnuka albarka
don baida fasali ko kadan anma yata iya? Tadau niyya,
tana zaune ta gefenta tafara hararanta aliya bata kulata ba
can dai tamiko tareda cewa “keeh zoki wankemim kafa ga
dutsen ce” aliya takalleta sannan tajuya tacigaba da
abunda take yarinyan ta tashi kamo gashin aliya tayi
tasake mata mari wanda ya nutsar da sauran bayin
yakuma janyo hankalinsu tace “nace ki gogemin kafa”
wata dake gefe tacewa aliya kiyi fa. Itace shugabanmu
anan aliya bata musa ba ta tsugunna ta goge sannan
tamike. Azuciyanta tace duk zansami lokacinku bata kanku
nake ba yanzu,ananne umma uwar soro tashigo dakin
sannan tace tunda munsamu sabbin bayi aikin naku zai
canju,keh meye sunanki? Aliya tace “aliya” tohm dake aliya
dake bilki zakuna isa gun yarima yusuf, sauran kuma duk
kunsan wurin zuwa” ficewa tayi alokacin ita bilkin taja aliya
tareda cewa “baki taki saa ba daga zuwa sai gun yarima
yusuf? Bama yarima abdullahi ba. Tafdi zakisha wulakanci
dan wulakancine anma yaka iya kana talaka dakai,” aliya
bata furta komiba don ko bilki bata fada mataba tasan
waye yarima yusuf bashi kadai ba kowa afadan
saidatasani takumasam mezasu iya aikatawa donhaka
tashirya wa yusuf, bilki ce tace tashi muje sunmike tsum
suka nufi kicin kowacce tadauki tray sannan suka nufi
fannin yariman aliya tana hankalce dakomi duk tafiyan
dasukeyi,sun nufi kofan inda dogarai biyu suke tsaye
akofan bilki kai akasa tace “mun isowa da yarima abinci”
daga ciki yace ” kushigo” dogaran ne suka basu wuri suka
shiga falone babba yasha duk wani kayan alatu
dayakamata ace saurayi dan sarki yasamu. Yana kwance
akan kujera, suka sunkuyar dakai suka mika abincin kan
dinning sannan sukaja gefe suka tsaya, wannan ma
aladace bazasu bar falon ba harsai yarima yagama cinye
abincin, mikewa yayi yanufi kan dinning din yana kallon
abincin daya bayan daya,bilki tana rike da serving spoon
tazuba mishi friedrice din sai yamballs da ferfesun kayan
ciki, zobo ma tazuba mar akofin yana danne wayarsa
wacce aliya takare masa kallo, dogo ne wankan tarwada
yanada faffadan kirji,manyan idanuwa wanda taga alamun
kaman shine gadon gydansu dogaye ne masu manyan
idanu,yanada dan dimple saidai baya murmushi wannan
dama tasani tundaga farko, ayadda ta karanceshi akwai
alamun damuwa atattare dashi wanda yaboye babu wanda
yasani, wannan damuwan itace ke hanashi sakewa har
yake matsifa da fadace fadace don baida abunyine
,loneliness yamar yawa, harya gama ci baiyi magana ba
yamike yakoma kan kujera dama tashan bbc yake kalla,
har alokacin yana danna waya sun tattara abincin sannan
suka fito dakinsu suka nufa, aliya tadanci abincin kadan
wanda su bayi suke samu dama asalinta bamai ci bane
hakan yasa tazama sirir[truncated by WhatsApp]

HALACCIN SARAUTA 2
 benaxir  September 19, 2015
 Hausa Novels  122 Views
HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Tazauna tana
nazarin fadan da yadda komi take, takalli bilki sannan tace
“inane hanyar fadar sarki?” Bilki tajata tareda cewa
“zomuje” kaf saidata nuna mata hanyan fannin kowa
tundaga kan sarkin isa, zuwa ga matansa gimbiya falmata
da gimbiya yakolo, tace “sauran matansa biyun gimbiya
ainau da gimbiya atika sun rasu, kwarkwaransa sunkai
hudu wanda ni kaina bansan sunayensu ba,umma uwar
soro itace tasan kome dake cikin fada ta fannin mata, Aliya
tace “toh fannin yara fa? Bilki tace “yaran sarki su sha
takwas ne, bakwai suna karatu akasan waje, sauran suna
zaune anan,suma don su sukaki tafiya,anan munada
yarima yusuf,yarima abdullahi,yarima shehu,sai fulani
hauwa, fulani hafsat, fulani zainab, sauran kananun yarane,
ihsan,isham,ilham,ashfaq,,ashraf, manyan daga kan
abdullahi, yusuf shehu,zainab ,hauwa hafsat,kowanne nada
bayinsa dakuma fanninsa. Kananun ma sunada fanninsu
agefen na iyayensu, in batun hali ne kuma yarima abdullahi
shine ya gado halin ubansa na dattako, yarima yusuf
yanada wulakanci bar ganin yau yamana shiru gobe zai iya
watsa mana wulakanci, amata kuma zainab itace ta kirki
saidai tacika fada, hafsat da hauwa kuwa girman kai, a
tsakaninsu ma rikici suke, saboda iyayensu daban ne, da
hafsat, zainab da yusuf , ilham , ashfat uwarsu daya wato
falmata, yayinda abdullahi, shehu,
hauwa,ashfaq,ihsan,isham uwarsu daya, wato yakolo,
sauran na kasan wajen yayan atika, da ainau ne bansan
sunayensu ba dai, anma babban dan sarkin shine yusuf, sai
abdullahi, sai wani akasan wajen Tana bayaninta aliya tana
kallonta can tacigaba dacewa kuma kinga anan falmata da
yayanta su suke mulki donhaka kinsan kowa yafi bin inda
akwai tsoka nafi ladabi wa yan dakin falmata kuma nafi
samu” aliya tace “anma ai kinashan wulakanci” bilki tace
wannan dole musha. Haka sukayi ta tadi har dare sannan
suka koma kai abinci sunsameshi zaune yana waya suka
jera abincin akan table sannan suka ja suka tsaya, aliya
najinshi ya idar da wayansa tsaf sannan yataho kan
dinning din bude abincin yayi cikin rashin damuwa yanuna
aliya “ke zonan!” Ta matso ahankali kanta akasa daukan
abincin yayi ya watsa mata!, saiga miyan egusi. Wanda
yasha kamshi tas ajikin aliya, bata dago kanta ba bata
kuma furta komi ba, bilki ce dasauri tanufo gun ta sunkuyar
dakanta akasa tana bashi hakuri itama daukan sakwaran
yayi ya watsa mata, sannan yaja tsaki yabar musu gun,
abinda aliya ta tsana arayuwarta wulakanci, lalle yanaso
taci kaniyanshi, baya cikin lissafinta anma karya bari
tasashi aciki don zaiga ba daidai ba, daukan tray din tayi
tafice, bilki kuma ta tsaya bada hakuri, cikin zafin rai yace
takoma takira aliya, shi acewarsa akan me zata tafi bazata
rokeshi ba,akan me bazatayi ladabi agareshiba,bilki
dasauri tashigo dakin inda tasami aliya tacanja uniform
tasaka wani, dankwalin kanta take daurawa,tace “yarima
yana nemanki meyasa zaki tafi baki bashi hakuri ba?” Aliya
cikin rashin damuwa tace “saboda bazan tsaya jikina a
bace agunba” toh dai kizo muje kibashi hakuri” aliya tayi
shiru tabita suka koma wanda yana zaune akan laussasan
kujerarsa yahade kafa daya kan daya, gashin kansa ya
kwanta luf luf sunkuyar dakai sukayi akasa, bilki tafara
bada hakuri anma aliya bakinta tsit” bilki tafara tunkude
aliya domin itama tayi magana anma aliya kam taki cewa
komi, can dai yace “ke dago kanki naganki”aliya bata dago
ba bashiri bilki taja kanta wanda saida dankwalinta yafadi
akasa gashin kanta yaxubo yarufo mata kai, cikin rashin
damuwa yakalli bilki tareda cewa “aina kuka samo wannan
bakan? Kije ki aske mata gashi banison ganin gashi, balle
yazubemin a abinci, aliya wani murmushi tayi wanda
itakanta sai Allah sukadai sukasan meke ranta, ni kaina
benaxir na tausaya mashi sosai,ficewa sukayi bilki jikinta
na bari, suna shiga dakin tace don Allah yazamuyi?” Aliya
tacire kanta tareda cewa “aske zuwa yanda yakeso”bilki
taji. Hauahi har ranta anma babu yadda ta iya tarage
gashin aliya yadawo dan daidai yanda sauran nasu yake,
sannan suka zauna, bilki tayi mamakin ganin aliya bata
damuba,anma aliya tace mata “ke indai gashin kainane
kibashi sati biyu zakiga yadda zai dawo” tadai bari aranta
dahaka suka kwanta bacci, washegari dassasafe suka nufi
fannin sa yana bacci donhaka saida suka jirashi ya idda
baccinsa,sannan suka shiga yayi wanka abincinsa suka
basa, sannan suka hau gyran dakin, suka share sukayi
goge goge sannan suka gyra mishi lallausan gadonsa
dakin tuni yagume da kamshi alokacin harya fice da
dogaransa, sunfito kenan aliya rike da roban dasukayi goge
goge kanta akasa tanadan sauri, sai jitayi tabugi mutum,
tuni wani dogari yayo kanta zai maka mata sandanshi
anma cikin zafin murya taji ance “rabu da ita” bai juyo
yakalleta ba yaci gaba da tafiyansa bilki cikin tsoro tace
“waike meye matsalanki? Yarima abdullahi nefa wannan
kinci saa ba yayan bane da yau saikinyi tsallen kwado”
aliya taja numfashi tabi yadda yabi dakallo sannan suka
fice, Umma uwar soro ce tabukaci dukkan bayi masu aiki
dasu hallara wanda aliya tashiga cikinsu tana sauraro, cikin
izza tace ” munsamu labarin akwai wanda basa aikinsu
dakyau, yau yarima yusuf yamin bayani akan yanason
canjin masu masa aiki, donhaka kuzo kudauki hukuncinku
kafin naci gaba da magana bilki da aliya ne suka fita inda
suka mike akabasu bulala hamsin hamsin, gwara bilki
tasaba anma aliya tunda uwarta ta haifeta zunguri bata
taba sha mai lafiya ba, nan da nan jikinta ya kumbura
fatanta yattatashi, dakyar akayi daki da ita, zazzabi ne mai
zafi yarufeta wanda saida umma tanufota tareda cewa
duka hamsin kacal shine kike mana ciwo? Kimike yanzu a
kicin zakina aiki, agun zaki dauwama, bilki har hawaye
tayiwa aliya anma babu yadda ta iya , aranar saida aliya
tanufi kicin yadda taga girman tukwanen saida cikinta
yakada saura kadan ta tsure, wasu manyan tukane ne.
Dasu ake girkin gydan, ga kicin din uban zafi, haka dai
aliya tadaure, iyakacinta kicin sushiga dasafe sushiga
darana suzo kuma sushiga daredare ciwon baya da ciwon
jiki yasaka aliya takar ramewa, takara dawowa baka,
idonta yakara fitowa, tuntana shan wahala har tasaba,
Watarana tana zaune a kicin babu tunanin da batayiba,
yakamata tabar kicin dinnan takoma wani gu daban
inbahakaba zuwanta yazama na banza, jakadiyan gimbiya
falmata ce tanufo kicin din bashiri kowa yamike yanuna
ladabinsa, tabi su daya bayan daya sannan ta je wa aliya
“kizonan” aliya tabita basu nufi ko ina ba sai fannin
falmata, macece wacce bata wuci arbain ba,fara ce
kyakyawa saidai daga kallonta kasan ba karamar makira
bace,cikin kissa ,kissisina da izza take rayuwanta, zuwan
aliya yasa takalleta sama da kasa sannan tacewa jakadiya
wannan kika samo? Jakadiya tace “itace tayi saura a masu
ilmin bayin” falmata takalli aliya sannan tace “da alamu
kingaji da kicin din?” Aliya wacce ta durkusa kanta akasa
tace “ae ranki shi dade” falmata tace “zan aikeki karki bude
aikan inkinkai lafiya toh zaki dawo gefena da aiki” aliya
tace “komi kikace ranki shidade” jakadiya ce tamika mata
takarda tareda cewa” zaki kaiwa umma uwar soro” takarbi
takardan sannan tafice harta kusa isa zuciyanta yaraya
mata data bude takaranta budewanta taga anrubuta “ki
kasheta” abun ya tsorata aliya, metayi wa gimbiya? Babu!
Toh gimbiya na gwadata ne duk yadda akayi, tunda taji
tace “itace tayi saura a masu ilmin bayin” gwajine!
Donhaka ta nannade takardan tanufi gun umma uwr soro
wacce tabude takaranta cikin izza tamike ranta abace tace
kinsan mekika kawomin kuwa? Kinfa kawomin cewa za’aje
akashe gimbiya falmata ne, aliya aranta tace “bahaka bane
tabbas gwajine” waya baki ? ” babu bansan wayeba” babu
yadda umma batayiba har kiran dogarai tayi suka dirke
aliya taji jiki sosai anma taki magana, candai saiga
jakadiya tazo takarbeta fannin falmata takaita, falmata tayi
murmushi sannan tace “kinwuce gwaji” donhaka na
amince dake zan ci gaba da aiki dake, zakibar kicin kidawo
fannina, sannan ungo wannan tamika mata wani kullin
magani, inaso kije kisaka a abincin da zaakai fannin
abdullahi naji labarin ke kike zubawa”aliya tace “komi
kikeso rabki shidade shizanyi” dahaka tamike tafice
dakinsu tanufa tana tunani, lalle makirci da duk wani kissa
da izza yakare a maitan son mulki wato tasan danta yusuf
baida hankali tunda shaye shaye yake bazaa bashi mulkin
garinba gwara takashe abdullahi ahankali sai shehu, oh
Allah, dahaka har yamma tayi tafita da kullin jakadiya
nabiye da ita tana leka ta, ahadin abincin yamballs ne saita
zuba, tana zubawa jakadiya tafice, bashiri taxubar da
wannan kwabin sannan takarayin wani, tashirya tsaf aka
kaimishi, sannan tanufi fannin falmata tana durkushe kanta
akasa sannan tace “na zubo ranki shi dade” falmata tayi
murmushi sannan tace “kullum zakina sakamishi, maganin
tsotse jinine, zaisamishi karamin hauka, kinga idan
yahaukace bawanda zai karbi mahaukacin sarki gwara dan
shaye shaye,” aliya tayi murmushi sannan tace ” gidan
shikenan har abada yazama naki gimbiya, mata mai ran
karfe, wanda yatabaki yataba zakanyan jeji mai cutar
hauka,...


Read / Download HALALCIN SARAUTA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album