Join Our WhatsApp Group

ABRAHAM Complete Hausa Novel Document by ABRAHAM


ABRAHAM

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 81042



ABRAHAM

Reading Time: 6 Hours

Added On: 21, Dec 2023

Author: NoorEman ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 07082281566

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 441.74 kb

File Type: txt

Views: 536+

Download: 436+

Last download: 2 hours ago

Description/Story: 🍇🍇ABRAHAM 🍓🍓


*First edition*


#NoorEemaan





*WATTPAD*
@NoorEemaan



Am back again🚴♀️ it has been a while now....


All characters and lifestyle in this story are all drawn from my imagination, any resemblance of story should be considered as a coincidence!


⚠Caution ⚠️
Wanna liittafin Hakkin mallakan NoorEemaan ne! Ban yarda a juya min novel ta kowacce siga ba, idan kunne yaji...



The writer of
Rayuwar faheemah
Mijin ammina ne sila
Kyautar koda
Papi ne and now 👇
ABRAHAM...



*Wanna book din na so yin shi a matsayin paid book, amma saboda yanda masoyana suke ta tambayar :Noor yaushe zaki fara mana sabon novel ya sanya zan sakar muku shi a free domin Jin dadinku my fans, comment dinku kadai nake bukata, sannan wattpad fans dina kada ku manta da following dina sannan voting nagode...


*( bari na Baku wani takaitaccen labari game da book din ABRAHAM dazan fara in sha Allah...*

*Few days back ina cikin keke napep zuwa gidan mu, kwatsam naji labarin yazo brain dina, it's funny RIGHT? Yeah it's! Ni kadaina murmushi na saki domin abin yazo min a bazata, buh trust me guys zaku ji dadin shi fiye da zaton ku, ku dai ku rikitani da comments dinku kana kuyi following dina a wattpad.)*


_In sha Allah daga yanzu har zuwa lokacin dazan ajiye alkalamina wanna emojis din grapes da strawberry (🍇🍓) zan dinga amfani dashi a dukkanin novel dina kamar yadda kuka gani a sama, Dan haka masoya matukar kuka gan wanna emojis din 🍇🍓 toh tambarin novel dina ne_

*Note*
_Wanna shine second to the last novel dina Dana Yi, so ina ƙara reposting ne, ba sabo bane_

https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din



In the name of Allah, most gracious most merciful


Chapter 1-2


IMO OWEERI STATE NIGERIA

_WORDBANK ESTATE_


Unguwar wordbank na daya daga cikin unguwanin masu hannu da shuni a jihar imo. Wani Had'add'en gidane mai sassa daban-daban na hango, Ana wa gidan lakabi da ABRAHAM MANSION, sannan shine gida mafi kyau, haduwa, hadi da girma a Unguwar wordbank din gabadaya, cikin wani sashe na gidan na nufa....

Wata farar matashiya ce tallafe da katon cikin ta wanda yayi girma sosai, fridge ta nufa domin dauko Eva table water sakamakon kishirwan da take ji, balle murfin ruwan tayi ta fara sha, lumshe ido tayi kewar Mijin ta na nukurkusanta, Sosai take bukatar ya dawo, sai da ta shanye duka ruwan kana ta cilla Goran cikin dustbin, hanyar part din su ta nufa domin dauko wayar ta saboda ta yi Kiran mijinta, mutum mafi soyuwa a duniyar ta gabadaya baya ga iyayen ta, miskilancin sa kadai da ta tuno ya sata sakin murmurshi, she loves everything about him...

Har ta gifta sitting room ta dawo da baya sakamakon muryar mummy(madam Gloria) dake tashi, wani mugun murdawa dan cikinta yayi sakamakon abinda kunnuwanta suka jiyo mata...

"Sarah (babbar aminiyar madam Gloria) bazan taba bari wanna damar ta wuce ni ba, dole ne na salwantar da Nonye da Abinda ke cikinta, wanna aikin kuma zamu yi shi cikin daren yau kafin dan taurin ran ya dawo, domin matukar ya dawo komai ya lalace min , kin san cewa yana da wayo sosai basai na gayamiki ba, Dan haka ki shirya karfen biyun dare zamu aikata lahira, sannan na fasa ihun kukan mutuwar ta da safe, bayan na gama da ita, sannan a hankali zan aika Abraham lahira shi ma, daga nan dukiyar ABRAHAM ya dawo mallakina kaf, abinda na dade ina buri Kenan" madam Gloria ta fada da yaran igbo tana sakin dariyar zallan mugunta.



Nonye dake tsaye a bakin kofa ta saka dukkanin hannayenta ta rufe bakinta, sakamakon kukan dake k'ok'arin kufce mata, sosai zallan al'ajabi ya kamata, da mutum ne ya gayamata cewa madam Gloria nada irin wanna mugun halin sai inda karfin ta ya kare, amma gashi da kunnuwanta taji, azahiri ba wai a duniyar mafarki ba...


Kokarin barin bakin kofar take domin wani mugun duhu ke kokarin ratsa idanun ta, burinta ta isa dakinta domin Kiran Abraham ko da ita da Dan cikin ta basu rayu ba, amma zata so Abraham ya san da wacce yake zama, sai dai tana daga kafa daya tayi luuuuu zata fadi, sak'amak'on haka kofar ta girgiza, a kuma daidai lokacin ne madam Gloria da aminiyar ta Sarah suka kai idanun sa ga kofar a firgice, domin basa son kowa ya San da nufin su har su aiwatar dashi

Ta bangaren Nonye kuwa zaro fararren madaidaitan idanun ta tayi cikin tsananin tsoro da rudewa, domin Sam bata so su san cewa tana labe, hakan yasa ta aro jarumtar ta tsaya kan kafafunta, maimakon ta nufi dakinta sai tayi hanyar waje domin yafi mata sauki bacewa ganinsu...
tana fita waje su madam Gloria na bud'e kofar sai dai wayam basu ga alamun mutum ba...

Kallon juna suka yi, kana suka sake janye idanun su, cikin rashin yarda madam Gloria tace" kawata Sarah anya babu wanda ya mana labe kuwa“ ta tambayi Sarah da yaran igbo.

"abinda nake hasashe Kenan" Sarah ta amsawa madam Gloria


"tabbas akwai wanda ya mana labe, masu aiki basa shigowa nan sai idan za su yi aiki ko shirya dining table, shiyasa na zabi mu yi maganar a nan, amma zo muje in gani ..." madam Gloria ta fada tana nufar part dinsu Nonye....

Sai dai sama da kasa ta duba babu Nonye babu alamar ta, sosai hankalinta ya tashi kana zarginta ya tabatta.

A haukace ta nufi compound din gidan ta tambayi mai gadi ya sanar da ita cewa babu jimawa yaga ta fita...

Ai bata jira mai gadi ya karasa jawabin sa ba ta koma ciki ta dauko key din mota ta fito, kana ita da Anty Sarah suka fada ciki ta bawa motar wuta suka bar gidan a guje, shi dai mai gadi da kallo ya bisu kana ya tabe baki ya koma bakin aikin sa....

Bayan sun fito babban titi ta latsa wani number, bayan seconds biyar kacal aka daga... "hello Emma mu hadu a junction yanzu"


Daga dayan bangaren saurayin da aka kira da Emma ya amsa hadi da kashe wayar, wanda kallo daya mutum zai masa ya fahimci cewa shi din tantiri ne...

mintuna goma kadai suka kawo Emma Junction din, kasancewar ya San motar ta hakan yasa kai tsaye ya shige gidan Baya motar, yace "madam Gloria meye labari ne"? Ya tambaya cike da nuna shi din Jan wuya ne"

"babu labari mai dadi Emma, sanin kanka ne cewa duk sanda na kira ka aiki za ka min, ba kuma yau ka fara min aiki ba, in fact babu lokacin bayani" ta karasa tana fisgar motar da gudu, tayi driving mai nisa kana ta hango wata kamar Nonye tana sauri tamkar ba mai ciki ba, gudu ta kara har ta cimmata...

Nonye dake a rude ta waigo Jin karan mota a bayanta saidai wadanda ta hango ya sanya hantar ta kadawa, hakan kuma yasa Dan cikin ta wani tsalle

"get in the car" madam Gloria ta fada a kausashe hakan kuma shine karon farko data fara bayyana wa Nonye asalin kalar ta da tarin tsanar da take mata, domin dukkanin abinda ya shafi ABRAHAM tana adawa dashi

Sosai hankalin Nonye ya tashi, gashi shida na yamma ta kusa, ba tare da ta tsaya wani tunani ba ta fada dajin dake gefenta ta fara hudu, tana fatan ta tsira daga kaid'in madam Gloria.


Da gudu Emma da madam Gloria suka rufa mata yayinda anty Sarah ta shige motar, hakan nan take Jin wani yanayi a tare da ita mai kama da tausayi...

Sosai Nonye ke gudu tana kuka, yayinda su madam Gloria ke bin ta a baya a kokarin su na kamota, sun yi gudu mai nisan gaske har karfin Nonye ya fara karewa hakan yasa ta fadi ruf da ciki yayinda ta buge kafar ta a katon dutsen dake gefen ta, zafin daya ishe ta ne ya sanya ta saki karan azaba, kokarin mikewa take amma ta kasa sakamakon nauyin da cikin ta yayi, gashi ya dunkule waje daya, tana cikin wanna halin ne su madam Gloria suka cimmata...

Cikin kuka mai matuk'ar ban tausayi tace "please don't kill me" (na roke ku Karku kashe ni)

Daf da fuskar ta madam Gloria ta karasa kana cikin tsantsar mugunta tace "don't worry Nonye darling bazan kashe ki a nan, saboda haka relax ok" ta karasa tana shafa gefen fuskar ta cikin mugunta kana ta fashe da dariya, can ta dinke fuskar ta ta kalli Emma tace "daukota mu bar nan kafin duhun ya kara yawa" tamkar kayan wanki haka Emma ya sabe ta a kafada ko tausayi babu, Nonye kuwa shiru tayi sai hawayen dake zuba a fuskar ta, karfin ta ya Kare gabadaya, a halin yanzu tafi tausayin dan cikinta....



Bayan sun fito titi Emma ya wurga ta a bayan mota , madam Gloria kuwa ta mika mishi bandir din yan dubu daya ya tafi cike da mata kirari....



*2:00am*

Ko ina da haske a gidan tamkar rana,
tsaye madam Gloria take a kan Nonye, macece mai matsakaicin tsaho hadi da kiba, fara ce irin farin inyamurai nan (igbo). Ta sha kitson twisting kananu, tana sanye da short skirt hadi da farar singlet Wanda hakan ya taimaka kwarai wurin bayyana katon tumbin ta. Ido ta Kurawa Nonye da a shekaru bazata wuce shekara ashirin da shida zuwa da bakwai ba, sosai Nonye ke cikin mayuwancin hali da katon cikinta dan wata Tara da kwana biyar, juyi take tana zub da kwalla masu zafin gaske saboda azaban da take fama dashi, magana takeson yi amma ta kasa furta ko da kalma daya ce, sai bakin ta dake motsi, ga cikin sai wani motsi hadi da juyi yake sosai, wanda hakan ke nuni da cewa dan cikin ya galabaita yana bukatar shakar iskar duniyar mu.


Murmushin mugunta madam Gloria ta saki, ganin hakkan ta yana daf da cimma ruwa, Anty sarah dake gefenta ta share kwallar tausayin Nonye, ta sani cewa duk muguntar ta, bazata iya kallon mace mai tsahon ciki a halin nakuda ba tare da ta taimaka ko sausauta mata ba, kusan awa goma Kenan da Nonye ta soma nakuda saboda tsananin tsoron da firgici, Sannan bata isa ta hana madam Gloria aikata komai ba, duk da kasancewar Anty Sarah kawa ga Madam Gloria, amma a gidan take zama permanent, tana kuma a matsayin kukun su ce, wanda madam Gloria ta tsara hakan ne gudun kada ABRAHAM ya fahimci wani Abu a tsakaninsu, sosai Anty Sarah ke Rayuwa a gidan tamkar a gidan su. sannan ta San cewa idan ta nuna wani yanayi na tausayi ga Nonye dake kwance, ba shakka madam Gloria xata iya mata komai, domin tasan cewa anty Sarah ta gama sanin dukkanin sirrin ta....


Da murnushi mugunta kan fuskar madam Gloria ta juyo ga anty Sarah, k'ank'ance ido tayi, kana cikin son gasgata abinda take karantowa a fuskar anty Sarah tace " SARAH! ba dai tausayi nake gani shimfud'e a fuskaar ki ba, yau she kika fara Tausayi? Domin tun zamanin yarintar mu ke din ba mai Tausayi bace"(ta tambayeta da yaran igbo)

Saurin sanja fuska Anty Sarah tayi, wanda da a ce madam Gloria ta lura da ta gano abinda takeson gani din. "ko daya bana tausaya mata, ranar da muka dade muna jira ce fa tazo, haba kawata sai kace baki sanin ba " Anty sarah ta fada tana sauke boyayyen ajiyar zuciya, tana fatan kada madam gloria ta gano ta...

Murmushin jin dadin madam gloria ta saki, mayar da kallon ta tayi ga Nonye, ta kara galabaita sosai gwanin tausayi ga cikin daya tsananta motsin da yake, gashi tana son magana amma ta kasa...

Babu zato, babu tsammani madam gloria ta dauki pillow ta shiga dannawa a fuskar Nonye da dukkanin karfin ta, shure_shure Nonye ta dinga yi da kafafun ta saboda sosai madam gloria ke cigaba da danna pillow a kokarinta na kashe Nonye, Anty sarah ta dauke fuskarta, karon farko da ta ji wani mugun tausayin Nonye, sannan tayi nadaman biyewa kawarta...

A yau taji tana tsanar halayenta, domin har da gurbataciyyar shawarar ta a kisan da madam gloria ke kokarin yi wa Nonye

miye laifin nonye? yarinya mai kirki da faram faram da jama'a....

Sai da Nonye ta daina motsi kana madam Gloria ta d'auke pillow'n daga fuskar ta, sai dai me duk da cewa Nonye ta mutu, numfashi ya bar gangan jikin ta, amma sosai dan cikinta ke motsi....




Salon na daban ne,
Comment dinku kadai zai sa na cigaba da ABRAHAM...


Noor Eemaan🦋



I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
But
Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851



Sunday 19 December

8:46pm



🍇🍇ABRAHAM🍓🍓

*First edition*



*WATTPAD*
@NoorEemaan




https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din




Chapter 3-4

(Not Edited)

Sosai tsoro ya bayyana a fuskar madam Gloria, domin abu ne wanda bata taba gani ko ji ba, ta yaya dan cikin Nonye ke motsi bayan ta mutu? Sosai murnan cikar burinta ya ragu
Mai da kallon ta tayi ga Anty Sarah data yi mutuwar tsaye, sosai nadama da tsoron Allah ya rufe ta, domin abinda ke faruwa yanzu ikon Allah ne mai yin yanda yaso.



"Sarah kina ganin abinda nake gani kuwa ko mafarki nake yi?" madam Gloria ta fada a rude, tana jijiga anty Sarah


"ba mafarki kike yi ba kawata, da gaske ne, amma ga shawara daya" ta fada tana satar kallon madam Gloria, fatan ta ta amince da tunanin daya zo zuciyar ta yanzu, domin ta hakan ne kadai zata samu sasaucin tsantsar mugunta da suka yiwa Nonye.

"meye shawarar ki Sarah fadi ina jinki" madam Gloria ta fada a kage.

"mezai hana mu fita da ita ta kofar baya inda ba security sai ki kira Emma ya hayo mota daga nan mu kai ta asibiti ayi operation kana a ciro dan cikin kafin gari ya waye mun dawo, idan ba haka ba matukar mutane suka Lura da dan cikin Nonye na motsi za a samu matsala domin abinda bakya so ne zai faru, ma'ana Dan Abraham zai rayu" anty Sarah ta fada tana fatan kawarta ta amince.


Jinjina kai madam Gloria ke yi cikin gamsuwa domin ta yarda da shawaran Kawarta dari bisa dari, babu bata lokaci ta kira Emma ta sanar dashi abinda take bukata, mintuna ashirin kacal ya kawo Emma unguwar wordbank, Kiran madam Gloria yayi yace ya iso, ta fada masa cewa ta Bude kofar baya ya shigo domin su biyu baza su iya daukar Nonye...


Read / Download ABRAHAM

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album