Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

๐Ÿ‡๐Ÿ‡ABRAHAM ๐Ÿ“๐Ÿ“


*First edition*


#NoorEemaan





*WATTPAD*
@NoorEemaan



Am back again๐Ÿšดโ™€๏ธ it has been a while now....


All characters and lifestyle in this story are all drawn from my imagination, any resemblance of story should be considered as a coincidence!


โš Caution โš ๏ธ
Wanna liittafin Hakkin mallakan NoorEemaan ne! Ban yarda a juya min novel ta kowacce siga ba, idan kunne yaji...



The writer of
Rayuwar faheemah
Mijin ammina ne sila
Kyautar koda
Papi ne and now ๐Ÿ‘‡
ABRAHAM...



*Wanna book din na so yin shi a matsayin paid book, amma saboda yanda masoyana suke ta tambayar :Noor yaushe zaki fara mana sabon novel ya sanya zan sakar muku shi a free domin Jin dadinku my fans, comment dinku kadai nake bukata, sannan wattpad fans dina kada ku manta da following dina sannan voting nagode...


*( bari na Baku wani takaitaccen labari game da book din ABRAHAM dazan fara in sha Allah...*

*Few days back ina cikin keke napep zuwa gidan mu, kwatsam naji labarin yazo brain dina, it's funny RIGHT? Yeah it's! Ni kadaina murmushi na saki domin abin yazo min a bazata, buh trust me guys zaku ji dadin shi fiye da zaton ku, ku dai ku rikitani da comments dinku kana kuyi following dina a wattpad.)*


_In sha Allah daga yanzu har zuwa lokacin dazan ajiye alkalamina wanna emojis din grapes da strawberry (๐Ÿ‡๐Ÿ“) zan dinga amfani dashi a dukkanin novel dina kamar yadda kuka gani a sama, Dan haka masoya matukar kuka gan wanna emojis din ๐Ÿ‡๐Ÿ“ toh tambarin novel dina ne_

*Note*
_Wanna shine second to the last novel dina Dana Yi, so ina ฦ™ara reposting ne, ba sabo bane_

https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din



In the name of Allah, most gracious most merciful


Chapter 1-2


IMO OWEERI STATE NIGERIA

_WORDBANK ESTATE_


Unguwar wordbank na daya daga cikin unguwanin masu hannu da shuni a jihar imo. Wani Had'add'en gidane mai sassa daban-daban na hango, Ana wa gidan lakabi da ABRAHAM MANSION, sannan shine gida mafi kyau, haduwa, hadi da girma a Unguwar wordbank din gabadaya, cikin wani sashe na gidan na nufa....

Wata farar matashiya ce tallafe da katon cikin ta wanda yayi girma sosai, fridge ta nufa domin dauko Eva table water sakamakon kishirwan da take ji, balle murfin ruwan tayi ta fara sha, lumshe ido tayi kewar Mijin ta na nukurkusanta, Sosai take bukatar ya dawo, sai da ta shanye duka ruwan kana ta cilla Goran cikin dustbin, hanyar part din su ta nufa domin dauko wayar ta saboda ta yi Kiran mijinta, mutum mafi soyuwa a duniyar ta gabadaya baya ga iyayen ta, miskilancin sa kadai da ta tuno ya sata sakin murmurshi, she loves everything about him...

Har ta gifta sitting room ta dawo da baya sakamakon muryar mummy(madam Gloria) dake tashi, wani mugun murdawa dan cikinta yayi sakamakon abinda kunnuwanta suka jiyo mata...

"Sarah (babbar aminiyar madam Gloria) bazan taba bari wanna damar ta wuce ni ba, dole ne na salwantar da Nonye da Abinda ke cikinta, wanna aikin kuma zamu yi shi cikin daren yau kafin dan taurin ran ya dawo, domin matukar ya dawo komai ya lalace min , kin san cewa yana da wayo sosai basai na gayamiki ba, Dan haka ki shirya karfen biyun dare zamu aikata lahira, sannan na fasa ihun kukan mutuwar ta da safe, bayan na gama da ita, sannan a hankali zan aika Abraham lahira shi ma, daga nan dukiyar ABRAHAM ya dawo mallakina kaf, abinda na dade ina buri Kenan" madam Gloria ta fada da yaran igbo tana sakin dariyar zallan mugunta.



Nonye dake tsaye a bakin kofa ta saka dukkanin hannayenta ta rufe bakinta, sakamakon kukan dake k'ok'arin kufce mata, sosai zallan al'ajabi ya kamata, da mutum ne ya gayamata cewa madam Gloria nada irin wanna mugun halin sai inda karfin ta ya kare, amma gashi da kunnuwanta taji, azahiri ba wai a duniyar mafarki ba...


Kokarin barin bakin kofar take domin wani mugun duhu ke kokarin ratsa idanun ta, burinta ta isa dakinta domin Kiran Abraham ko da ita da Dan cikin ta basu rayu ba, amma zata so Abraham ya san da wacce yake zama, sai dai tana daga kafa daya tayi luuuuu zata fadi, sak'amak'on haka kofar ta girgiza, a kuma daidai lokacin ne madam Gloria da aminiyar ta Sarah suka kai idanun sa ga kofar a firgice, domin basa son kowa ya San da nufin su har su aiwatar dashi

Ta bangaren Nonye kuwa zaro fararren madaidaitan idanun ta tayi cikin tsananin tsoro da rudewa, domin Sam bata so su san cewa tana labe, hakan yasa ta aro jarumtar ta tsaya kan kafafunta, maimakon ta nufi dakinta sai tayi hanyar waje domin yafi mata sauki bacewa ganinsu...
tana fita waje su madam Gloria na bud'e kofar sai dai wayam basu ga alamun mutum ba...

Kallon juna suka yi, kana suka sake janye idanun su, cikin rashin yarda madam Gloria tace" kawata Sarah anya babu wanda ya mana labe kuwaโ€œ ta tambayi Sarah da yaran igbo.

"abinda nake hasashe Kenan" Sarah ta amsawa madam Gloria


"tabbas akwai wanda ya mana labe, masu aiki basa shigowa nan sai idan za su yi aiki ko shirya dining table, shiyasa na zabi mu yi maganar a nan, amma zo muje in gani ..." madam Gloria ta fada tana nufar part dinsu Nonye....

Sai dai sama da kasa ta duba babu Nonye babu alamar ta, sosai hankalinta ya tashi kana zarginta ya tabatta.

A haukace ta nufi compound din gidan ta tambayi mai gadi ya sanar da ita cewa babu jimawa yaga ta fita...

Ai bata jira mai gadi ya karasa jawabin sa ba ta koma ciki ta dauko key din mota ta fito, kana ita da Anty Sarah suka fada ciki ta bawa motar wuta suka bar gidan a guje, shi dai mai gadi da kallo ya bisu kana ya tabe baki ya koma bakin aikin sa....

Bayan sun fito babban titi ta latsa wani number, bayan seconds biyar kacal aka daga... "hello Emma mu hadu a junction yanzu"


Daga dayan bangaren saurayin da aka kira da Emma ya amsa hadi da kashe wayar, wanda kallo daya mutum zai masa ya fahimci cewa shi din tantiri ne...

mintuna goma kadai suka kawo Emma Junction din, kasancewar ya San motar ta hakan yasa kai tsaye ya shige gidan Baya motar, yace "madam Gloria meye labari ne"? Ya tambaya cike da nuna shi din Jan wuya ne"

"babu labari mai dadi Emma, sanin kanka ne cewa duk sanda na kira ka aiki za ka min, ba kuma yau ka fara min aiki ba, in fact babu lokacin bayani" ta karasa tana fisgar motar da gudu, tayi driving mai nisa kana ta hango wata kamar Nonye tana sauri tamkar ba mai ciki ba, gudu ta kara har ta cimmata...

Nonye dake a rude ta waigo Jin karan mota a bayanta saidai wadanda ta hango ya sanya hantar ta kadawa, hakan kuma yasa Dan cikin ta wani tsalle

"get in the car" madam Gloria ta fada a kausashe hakan kuma shine karon farko data fara bayyana wa Nonye asalin kalar ta da tarin tsanar da take mata, domin dukkanin abinda ya shafi ABRAHAM tana adawa dashi

Sosai hankalin Nonye ya tashi, gashi shida na yamma ta kusa, ba tare da ta tsaya wani tunani ba ta fada dajin dake gefenta ta fara hudu, tana fatan ta tsira daga kaid'in madam Gloria.


Da gudu Emma da madam Gloria suka rufa mata yayinda anty Sarah ta shige motar, hakan nan take Jin wani yanayi a tare da ita mai kama da tausayi...

Sosai Nonye ke gudu tana kuka, yayinda su madam Gloria ke bin ta a baya a kokarin su na kamota, sun yi gudu mai nisan gaske har karfin Nonye ya fara karewa hakan yasa ta fadi ruf da ciki yayinda ta buge kafar ta a katon dutsen dake gefen ta, zafin daya ishe ta ne ya sanya ta saki karan azaba, kokarin mikewa take amma ta kasa sakamakon nauyin da cikin ta yayi, gashi ya dunkule waje daya, tana cikin wanna halin ne su madam Gloria suka cimmata...

Cikin kuka mai matuk'ar ban tausayi tace "please don't kill me" (na roke ku Karku kashe ni)

Daf da fuskar ta madam Gloria ta karasa kana cikin tsantsar mugunta tace "don't worry Nonye darling bazan kashe ki a nan, saboda haka relax ok" ta karasa tana shafa gefen fuskar ta cikin mugunta kana ta fashe da dariya, can ta dinke fuskar ta ta kalli Emma tace "daukota mu bar nan kafin duhun ya kara yawa" tamkar kayan wanki haka Emma ya sabe ta a kafada ko tausayi babu, Nonye kuwa shiru tayi sai hawayen dake zuba a fuskar ta, karfin ta ya Kare gabadaya, a halin yanzu tafi tausayin dan cikinta....



Bayan sun fito titi Emma ya wurga ta a bayan mota , madam Gloria kuwa ta mika mishi bandir din yan dubu daya ya tafi cike da mata kirari....



*2:00am*

Ko ina da haske a gidan tamkar rana,
tsaye madam Gloria take a kan Nonye, macece mai matsakaicin tsaho hadi da kiba, fara ce irin farin inyamurai nan (igbo). Ta sha kitson twisting kananu, tana sanye da short skirt hadi da farar singlet Wanda hakan ya taimaka kwarai wurin bayyana katon tumbin ta. Ido ta Kurawa Nonye da a shekaru bazata wuce shekara ashirin da shida zuwa da bakwai ba, sosai Nonye ke cikin mayuwancin hali da katon cikinta dan wata Tara da kwana biyar, juyi take tana zub da kwalla masu zafin gaske saboda azaban da take fama dashi, magana takeson yi amma ta kasa furta ko da kalma daya ce, sai bakin ta dake motsi, ga cikin sai wani motsi hadi da juyi yake sosai, wanda hakan ke nuni da cewa dan cikin ya galabaita yana bukatar shakar iskar duniyar mu.


Murmushin mugunta madam Gloria ta saki, ganin hakkan ta yana daf da cimma ruwa, Anty sarah dake gefenta ta share kwallar tausayin Nonye, ta sani cewa duk muguntar ta, bazata iya kallon mace mai tsahon ciki a halin nakuda ba tare da ta taimaka ko sausauta mata ba, kusan awa goma Kenan da Nonye ta soma nakuda saboda tsananin tsoron da firgici, Sannan bata isa ta hana madam Gloria aikata komai ba, duk da kasancewar Anty Sarah kawa ga Madam Gloria, amma a gidan take zama permanent, tana kuma a matsayin kukun su ce, wanda madam Gloria ta tsara hakan ne gudun kada ABRAHAM ya fahimci wani Abu a tsakaninsu, sosai Anty Sarah ke Rayuwa a gidan tamkar a gidan su. sannan ta San cewa idan ta nuna wani yanayi na tausayi ga Nonye dake kwance, ba shakka madam Gloria xata iya mata komai, domin tasan cewa anty Sarah ta gama sanin dukkanin sirrin ta....


Da murnushi mugunta kan fuskar madam Gloria ta juyo ga anty Sarah, k'ank'ance ido tayi, kana cikin son gasgata abinda take karantowa a fuskar anty Sarah tace " SARAH! ba dai tausayi nake gani shimfud'e a fuskaar ki ba, yau she kika fara Tausayi? Domin tun zamanin yarintar mu ke din ba mai Tausayi bace"(ta tambayeta da yaran igbo)

Saurin sanja fuska Anty Sarah tayi, wanda da a ce madam Gloria ta lura da ta gano abinda takeson gani din. "ko daya bana tausaya mata, ranar da muka dade muna jira ce fa tazo, haba kawata sai kace baki sanin ba " Anty sarah ta fada tana sauke boyayyen ajiyar zuciya, tana fatan kada madam gloria ta gano ta...

Murmushin jin dadin madam gloria ta saki, mayar da kallon ta tayi ga Nonye, ta kara galabaita sosai gwanin tausayi ga cikin daya tsananta motsin da yake, gashi tana son magana amma ta kasa...

Babu zato, babu tsammani madam gloria ta dauki pillow ta shiga dannawa a fuskar Nonye da dukkanin karfin ta, shure_shure Nonye ta dinga yi da kafafun ta saboda sosai madam gloria ke cigaba da danna pillow a kokarinta na kashe Nonye, Anty sarah ta dauke fuskarta, karon farko da ta ji wani mugun tausayin Nonye, sannan tayi nadaman biyewa kawarta...

A yau taji tana tsanar halayenta, domin har da gurbataciyyar shawarar ta a kisan da madam gloria ke kokarin yi wa Nonye

miye laifin nonye? yarinya mai kirki da faram faram da jama'a....

Sai da Nonye ta daina motsi kana madam Gloria ta d'auke pillow'n daga fuskar ta, sai dai me duk da cewa Nonye ta mutu, numfashi ya bar gangan jikin ta, amma sosai dan cikinta ke motsi....




Salon na daban ne,
Comment dinku kadai zai sa na cigaba da ABRAHAM...


Noor Eemaan๐Ÿฆ‹



I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
But
Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851



Sunday 19 December

8:46pm



๐Ÿ‡๐Ÿ‡ABRAHAM๐Ÿ“๐Ÿ“

*First edition*



*WATTPAD*
@NoorEemaan




https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din




Chapter 3-4

(Not Edited)

Sosai tsoro ya bayyana a fuskar madam Gloria, domin abu ne wanda bata taba gani ko ji ba, ta yaya dan cikin Nonye ke motsi bayan ta mutu? Sosai murnan cikar burinta ya ragu
Mai da kallon ta tayi ga Anty Sarah data yi mutuwar tsaye, sosai nadama da tsoron Allah ya rufe ta, domin abinda ke faruwa yanzu ikon Allah ne mai yin yanda yaso.



"Sarah kina ganin abinda nake gani kuwa ko mafarki nake yi?" madam Gloria ta fada a rude, tana jijiga anty Sarah


"ba mafarki kike yi ba kawata, da gaske ne, amma ga shawara daya" ta fada tana satar kallon madam Gloria, fatan ta ta amince da tunanin daya zo zuciyar ta yanzu, domin ta hakan ne kadai zata samu sasaucin tsantsar mugunta da suka yiwa Nonye.

"meye shawarar ki Sarah fadi ina jinki" madam Gloria ta fada a kage.

"mezai hana mu fita da ita ta kofar baya inda ba security sai ki kira Emma ya hayo mota daga nan mu kai ta asibiti ayi operation kana a ciro dan cikin kafin gari ya waye mun dawo, idan ba haka ba matukar mutane suka Lura da dan cikin Nonye na motsi za a samu matsala domin abinda bakya so ne zai faru, ma'ana Dan Abraham zai rayu" anty Sarah ta fada tana fatan kawarta ta amince.


Jinjina kai madam Gloria ke yi cikin gamsuwa domin ta yarda da shawaran Kawarta dari bisa dari, babu bata lokaci ta kira Emma ta sanar dashi abinda take bukata, mintuna ashirin kacal ya kawo Emma unguwar wordbank, Kiran madam Gloria yayi yace ya iso, ta fada masa cewa ta Bude kofar baya ya shigo domin su biyu baza su iya daukar Nonye ba




Bayan su ukun sun fita da Nonye cikin sanda suka saka ta a mota Emma na mata kirarin har ta cika aiki ta masa banza domin yanzu damuwarta a cire dan cikin dake ta motsi, har Emma zai ta da mota anty Sarah ta fita tace ta manta Abu, cikin Sauri ta koma ta shiga dakin Nonye da Abraham wasu abubuwa wanda Allah kadai yasan me ta dauka, cikin wani Jakarta ta saka kana ta fito ta fada mota, ta tarar madam Gloria na mitar basu da lokaci fa, me taje dauko wa ne? Hakuri kadai ta bata domin bazata so ta San abinda ta dauko ba....

Bayan sun isa wani karamin asibiti inda da
farko likitan yace sai anyi bincike, hankalin madam Gloria ya tashi abinda tayi gudu Kenan shiyasa basu je babban asibiti ba, take ta siye likitan da makud'an kud'ad'e inda ya amince, aka shigar da ita aiki bayan sunyi gwaji ya tabbatar musu da Nonye ta mutu


Cikin awa daya aka ciro lafiyayyun kyawawan y'ay'an cikin Nonye maza biyu , dayan sak ubansa tamkar yayi kaki, dayan kuma sak Nonye.


Masu iya magana sun ce zakaran da Allah ya nufa da chara ko ana muzuru Ana shawo sai yayi...




Sun kansu likitocin Sun Jinjina ikon Allah, domin abu ne wanda bai taba faruwa a asibitin su ba, a cire rayayye daga matacce, gasu kuma yan biyu...



Su madam Gloria sun kansu sun girgiza da abinda ya fito a cikin Nonye, yayinda hankalin ta ya kara tashi, fatan ta kadai a fito da yaran ta shake su har lahira, yayinda anty Sarah ke tunanin hanyar tsiratar dasu....





Likitoci suka fara aikin dinka Nonye yayinda
Nurses suka yanka cibiyar su hadi da goge jikinsu da olive oil aka nade su a wani babban towel domin babu kayan saka musu, bayan komai ya kammala, anty Sarah ta saci jiki ta je wajen babban likitan tana kuka tace ya mata Alfarman tseratar da Rayuwar yayan, domin madam Gloria bazata bari su rayu ba, da fari likitan bai amince ba, amma ganin yadda take kuka bilhakki da gaske ya sanya shi amincewa, kana yace zai ajiye record din komai daya faru a yau din saboda ko da bincike ya taso watarana, take anty Sarah ta amince


Y'ay'an aka bata, likita yasa nurse ta bi da ita ta wata kofar inda ma'aikatan asibitin kadai ke bi har ya sadata da bakin gate, direct tasha ta nufa inda ta ji conductor's suna Kiran garuruwa masu yawa, ta rasa wanne zata shiga daga karshe taji anje GOMBE sauran mutum d'aya





Babu bata lokaci ta fada ciki, duk da bata San ko ina a arewancin Nigeria ba, amma ta San cewa yaran zasu yi nesa sosai da madam Gloria ta inda bazata taba kawowa ranta cewa suna arewa ba, duk da bata San abinda likitan zai fada mata game da yaran ba, bata kuma damu ba tunda burinta ya cika ta tseratar da Rayuwar yaran.....


Likita ke tsaye gaban madam Gloria yana sanar da ita cewa yaran sun mutu sakamakon ruwan haihuwa daya shiga kansu inda basu Lura da wuri ba, sosai murmurshi ya bayyana a fuskar madam Gloria wanda bata San cewa ya subuce mata ba, take Likita ya gasgata maganar anty Sarah ya kuma godewa Allah daya bata yaran ta tafi dasu, ganin duk ma'aikatan na kallon ta ya sanya ta ankara da abinda tayi, sai tayi saurin sanja fuskar ta zuwa ta zallan damuwa inda ta Riga ta makaro, tabbas madam Gloria ta cika shu'uma.


"Likita Allah ya jikan su, amma bazan iya kallon yaran ba, da wanne zan ji da mutuwar Nonye ko da rasa Y'ay'an dana saka ran zasu maye mun gurbin Nonye" sai ta saka kuka kana ta cigaba "a binne su kawai a makabartan asibitin nan, amma bazan juri ganin gawar su ba" ta karasa tana sakin sheshekan kuka...




Biyar saura na asuba aka basu gawar Nonye suka saka a mota, sai a lokacin madam Gloria ta Lura babu anty Sarah amma bata tsaya neman ta ba, domin bata so gari ya waye basu koma gida ba, a cewar ta Sarah zata zo gidan tunda ba bakuwar ta bane....

Wanna karan da kyar Emma da madam Gloria suka shigar da Nonye, suna yi suna hutawa har suka kaita dakin ta, hadi da rufe ta da bargo, falo suka fito ta sallami Emma ya tafi, kana ta koma dakin ta, tana fatan gari ya waye sosai domin yanzu karfe Biyar da mintuna ashirin ne.


*WASHEGARI*

Kamar yadda madam Gloria ta fada karfe shidan safiya ta gwala ihun mutuwar Nonye

sosai take kuka tana birgima a kasa tamkar gaske, hakan yasa ma'aikatan gidan suka shigo part din halin tashi, suma kuka suka saka sakamakon Jin abinda madam Gloria take fada, "ewooooo Nonye yata kin tafi kin barmu, tayaya zamu kasance cikin farinciki bayan babu ke, kin tafi kin barmu da son(ABRAHAM) ya zamu yi da rashin ki, bayan kece cikon farincikin mu, mutuwa kin min yankan kauna " sosai take maganganu cikin fitar hayyaci kai ka rantse da gaske take



Kowa na gidan yaji mutuwar Nonye matuka, domin macece mai son kowa, bata raina mutum komin kaskancin sa, haka zalika tana da son mutane sosai...


Kamar yadda yake a al'adar inyamurai idan mutum ya mutu basa binne shi a take, mortuary ake kai shi zuwa wasu lokuta kafin ayi bikin binne shi, hakan yasa madam Gloria da ta sanja shiga zuwa bakake tare da wasu yan'uwan su.

Haka al'adar su take idan anyi musu mutuwa komai na jikinsu yana kasancewa baki ne har izuwa wasu kwanaki.





*GOMBE STATE*

Bayan anty Sarah ta sauka a garin GOMBE ta shiga raba Idanu domin babu inda ta sani, ga yaran Allah ya basu wani mugun hakuri domin har yanzu basu yi kuka ba, daga karshe ta yanke hukuncin fara tafiya, tayi tafiya mai dan nisa kana ta shiga wani layi, gida na hudu idonta ya sauka a kai, haka kawai taji gidan ya kwanta mata a rai, shiga gidan tayi inda ta tarar da wata k'yakyawar yarinya fara sol hadi da iyayenta dake zaune a gefen ta suna hira cikin annushuwa





Da kallo duk suka bi anty Sarah ganin ta shigo musu babu sallama, "lafiya baiwar Allah" uban yarinyar ya tambaya a tausashe.




Jim anty Sarah tayi domin bata ji ko kalma daya daga abinda yace ba, dan haka tace "please can I use your toilet? Am really pressed"


Duk shiru suka yi domin babu mai Jin turanci cikinsu gwara-gwara baffa ya fahimci kalmar toilet din cikin abinda tace Dan haka yace "shalelen baffa zuba mata ruwa a buta"


Take yarinyar ta yi yanda yace kana ta

Please Login or Register in order to submit comment