Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta kalle ta, tayi mamakin meya hada su Indo da wanna matar amma bata furta ba.


"baiwar Allah zauna mana" ba musu Ta zauna, domin dan zaman data yi a Gombe, ta na dan jin Hausa kadan-kadan.



Aysha ce ta muskuta hadi da kallon Inna tace "Inna kin gane wanna matar?"


Aysha ta faɗa tana nuna Anty Sarah da ta tsunkuyar da kanta.


Dan kankance ido Inna tayi tana kallon Anty Sarah, saboda dan tsufan daya fara kamata, kana ta girgiza kai alamun bata gane ta ba.


"Hmmm! Inna ita ce fa matar nan da ta ajiye su Ammar a banɗakin shekarun baya da suka wuce ta gudu"



Zabura Inna tayi, ta dafe kirjin ta kana ta saka salati. "Indo da gaske kike? Ta yaya kika gane ita ce"



Nan Aysha ta labartawa Inna yanda ta dauki sarkan wuyan ta da photo Album a dakin baffa, da haduwar da suka yi da da Anty Sarah yanzu, sannan ta sanar da Inna cewa ita kam bata manta fuskar ta ba.



Kuka mai dauke da abubuwa da dama Anty Sarah ta saki saboda taji wasu abubuwan da Aysha ta fada, nadama da kunya mai tsanani na sake lullube ta.


Fuskantar Abraham tayi cikin turanci tace "Waɗannan yaran da na ajiye a banɗaki gidan nan....."

wani abu mai daci ta hadiya, sannan cikin kunya mai tsanani hadi da sabon nadama ta ɗora da cewa "yaran ka ne daka haifa tare da Nonye!. Sannan ban ajiye su da mugun nufi ba, illa saboda na tseratar da rayuwar su daga hannun kishiyar mahaifiyar ka Gloria!"


A haukace Abraham ya kafe ta ido, yayin da bugun zuciyar sa ke ta karuwa yana bada sautin fat! fat!! fat!!! har yana nuna wa ta saman rigar sa, ya haɗa uban gumi, yayinda ya kasa ko da motsa yatsa ne, saboda dumbin al'ajabi daya tsinci kansa a ciki, ƙwaƙwalwar sa ta tsaya cak da aiki, bangaren Inna da Aysha ma suna cikin shock jin abinda ya fito daga bakin anty Sarah, Aysha mai raunin zuciya tuni ta fara kuka, infact dukkaninsu su shiga wani hali da damuwa mai tsanani bare ma Abraham da al'amarin ba mai sauke bane a gareshi.




Tsahon mintuna goma babu wanda ya sake magana, ko wa da abinda zuciyar sa ke saka masa, Abraham kuwa har yanzu bai dawo dai-dai ba, sai da anty Sarah ta ɗora da cewa "na san labarin da zan baka yanzu zai iya tarwatsa zuciyar ka, amma kayi hakuri ka yafe Ni, tun bayan da muka aikata mugun nufin Mu da Gloria na nemi salamar zuciya na rasa, burina na ganka na nemi yafiyar ka...."

Kamar yadda Kuka sani reader's tiryan-tiryan haka Anty Sarah ta shiga gayawa Abraham abinda ya faru....

Tun daga lokacin da Gloria ta hadu da mahaifin Abraham, da asirin da tayi masa, da yanda ta kashe mahaifiyar Sa, da yanda ta cigaba da farautar rayuwar Abraham domin malleki dukiyar sa, da yanda ta kashe Nonye, amma su Ammar na motsi a cikin ta duk da ta mutu, da yanda ta tseratar da su Yan biyu tun daga asibiti a imo har izuwan Gombe gudun kada Gloria ta gano komai, da hoton album hadi da sarkan Nonye data dauko a dakin ita Nonye a lokacin da zasu tafi asibiti cikin dare, da kiran Madam GLORIA data yi ta Sanja murya tayi karyan ta mu saboda duk kada Madam GLORIA ta gano komai ta biyo ta .


Haka dai ta cigaba da gaya masa komai tana kuka mai ban tausayi.


Jikin Abraham rawa yake kamar wanda zafaffan zazzaɓi ya kamasa, ya kai mintuna goma a haka, sannan ya ja guiwar sa har gaban Aysha ya dora kansa kan cinyarta, ya saka karfafan hannunwan sa ya zagaye waist (kugu) dinta dashi, ya matse ta sosai, mafaka yake nema, mafakan da zai samu ko da dan sanyin ne a zuciyar sa, cikin tausayi Aysha ta nausa hannun ta cikin gashin sa, tama manta Inna na zaune a wajen, sai a lokacin Abraham ya samu wani kuka mai sauti ya kufce masa, kukan da amon sa duk ya taba zuciyoyin su bare ma Aysha, hakika duk wanda ya ga Abraham a wanna halin dole ya tausaya masa ainun.


Inna kuwa kauda kanta gefe tayi, saboda kara, tunda Aysha na matsayin yarta ta fari kamar yadda aka san Fulanin Usul da kunya, amma ta tausaya wa Abraham sosai duk da bata gane komai da anty Sarah ta fada ba, amma ta tausaya masa matuk'a.



Ba tare da ta kalli Aysha ba saboda har yanzu Abraham yana runkumkume da ita, tace "Indo wai menene, duk ban fahimci abinda matar nan take fada ba" Cikin kuka Aysha ta shiga gayawa Inna komai, amma a takaice kamar yadda anty Sarah ta faɗa.



Girgiza kai Inna ta shiga yi, har kwalla ta zubar saboda tausayi, sannan ta jinjina rashin imani irin ta Madam Gloria cikin dumbin al'ajabin yadda mutanen yanzu suka fifita duniyar su fiye da lahirar su, bayan duka wanna abin duniyar mutum bazai tafi da su lahira ba, kana mutuwa shikenan, wasu ne zasu cinye abin duniyar, amma saboda imani da tausayi yayi karanci yanzu sai ka kashe rai Saboda kwadayin mata'ul hayat (kyale-kyalen rayuwa).


Anty Sarah ta ja hanci saboda mugun muran daya kamata a dalilin kukan da ta sha, kana ta hade hannayenta waje daya alamun roka, ta ɗora guiwarta a ƙasa tace "dan Allah kayi hakuri ka yafe Ni, kullum cikin tashin hankali nake da mugayen mafarke, matuƙar baka yafe Ni ba bazan taba ganin haske ko da kadan ne a rayuwata ba, ban kuma ajiye yaran nan a toilet din gidanan saboda wata manufa ba, a lokacin ina cikin wani hali ne, burina a lokacin kawai na nisantar da su daga GLORIA, sannan a ganina gwara na barsu na gudu ba tare da bayin Allah nan sun sani ba(, tana nufin su Inna) a ganina hakan zai sa su karbi yaran, sannan zasu yi nisan gaske daga wajen GLORIA, duk da an sanar mata cewa yaran sun mutu, amma nasan Gloria, shu'uma ce, zata iya gano komai, hakan yasa na iya takuna wurin ganin ba ta gane cewa yaran na raye ba, kullum tunanina a wani hali yaran suke, amma idan na tuno karamcin bayin Allah nan a zuwana gidan nan na farko sai hankalina ya ɗan kwanta, domin na ga suna da zuciya mai kyau, dan Allah ka nemi waje ko yaya ne a zuciyarka ka yafe min, na tuba, ka yafe min dan Allah!" ta karasa tana buga hannunta a kasa, alamun tayi nadamar abubuwan data aikata a baya, Sannan tana jin ciwon su.



Ido duk suka zuba mata, babu mai kuzarin sake magana ma a cikin su, domin Abraham har yanzu bai gama dawowa hayyacin sa.




*MADAM GLORIA*

Tun daga lokacin da ta je wajen boko Nandera kullum da irin aikin tsafin da yake yi a kanta, Burinta a kullum watanin daya diba hadi da kwanakin su cika domin ta bar wannan dajin, domin ta gaji sosai, sannan hankalin ta ba a kwance yake ba, saboda macizan nan dake ko wani kusurwa na fadar Boka Nandera, a haka ta cigaba da lallabawa tana jurewa har watanin da kwanakin daya diba suka cika...



Sai dai me, a ranar boka Nandera ya fito da abinda ya dade a ransa muraran.
Ma'ana dai yana bukatar ya kusance ta, a ranar Madam Gloria ta ga tashin hankali, ya Kada ya raya taki yarda, ita kam iskanci baya damunta, sam bata damuwa da shi ba, ita matsalar ta son kai, rashin imani, hadi da son abin duniya ne ya dame ta, ya kuma rufe mata ido.
Sannan kuma tana k'yank'yamin wanna bokan, ta ina ma zata fara kwana dashi.

Cikin tsoro da fushi ta bar fadar a kokarin ta na barin dajin, wanna karon kuwa zuciyarta ta k'ek'ashe ta Kuma gaji da aikin bokayen nan, sam basu da gaskiya, gwara ta nemi tantirai ta biya su, a kashe mata Abraham ta huta kawai.



Amma abin mamaki ta kasa gane hanyar barin dajin, da ta dau hanya sai taga babu hanya, sai munanan halitta da take ta gani suna bata tsoro, abin dai ba sauki domin har duhun dare ya gabato tana neman hanyar barin dajin... da ta ga ba wata mafita, haka ta dawo guiwa a sanyayye wajen bokan domin bata da wani waje daya fi nan din a yanzu.


Dariya boka Nandera ya shiga k'yak'yatawa cikin Muryar sa mara dadin amo a lokacin da ta dawo, dama yana kallonta ta cikin allon tsafin sa.



A takaice dai a wannan daren ya danne ta ta ƙarfi ya kusanci ta, kusan kwana yayi yana abu ɗaya, wuya iya wuya Madam Gloria ta sha shi.



Washegari again ta sake gwada barin dajin, amma ta kasa, saboda da ta fito sai komai ya Sanja ta rasa hanya, haka boka Nandera ya mayar da Madam Gloria kamar matar sa, kullum babu fashi, duniyar tayi wa Madam Gloria zafi, gashi irin warin da boka Nandera ke yi ya kama jikin ta tun daga lokacin da ya fara kusantar ta, haka ta cigaba da fama cikin mayuwancin hali.



*Bayan wasu kwanaki*

Da misalin ƙarfe takwas na safe madam Gloria ta tashi, kasancewar boka bai bari ta huta cikin dare ba sai kusan shida saura Bacci ya dauke ta...
Da fari wani mugun wari ta ji ya fara ziyartan hancin ta, ta kai kallonta ga inda ta ji warin...

Gabanta ne ya yi wata bugawa, Domin boka Nandera ta gani kwance flat a kasa babu numfashi a tare da shi, majizan nan sun kanannad'e jikin sa, da kyar ma ake iya ganin fuskar sa saboda Yawan macizan nashi, gashi ko wannen su na kai mai cizo ta ko ina a jikin sa, abin babu kyawun gani...



Ihu Madam Gloria ta shiga yi, yayin da tsigar jikin ta har tashi ya dinga yi, sai take jin kamar majizan nan na ya dawo a jikin ta itama, haka ta dawo zautaciyya, sai faman soshe-soshe take, duk wanda zai ganta a halin yanzu zai dauka mai tabin hankali ce da ta shafe shekaru talatin a cikin hauka.

Banda kananun surutai babu abinda take da alama ƙwaƙwalwar ta ya fara tabuwa...

A takaice dai madam Gloria ta ga tashin hankali, wanda tsaya fayyace wa makaranta bata lokaci ne, da kyar ta iya jan kafafunta ta bar cikin fadar da gudun ta...

Kuma abin mamaki hanyar lafiya lou take yau, kamar ranar data fara zuwa dajin.



Gudu sosai ta shiga yi, domin har gizo macizan nan ke mata, saboda gani tayi suna bin ta a baya.



Tafiya mai nisan gaske tayi, amma kamar bata yi, saboda ko alamar titi da gidajen mutane bata fara gani ba, da haka ta dauki kwanaki uku cur sannan ta fara ganin titi daga nesa sosai, shi ma sai da ta kara wasu awanni kafin ta fito aihinin babban titi.




Duk abin hawan da ta tsayar tsoron daukar ta ma suke, da kyar da sidin goshi ta samu wani taxi, dama akwai kudi a aljihun wandon dake jikin ta, nan ya chaje ta sosai, a hakan ma wai bazata zauna a sit ba, sai dai booth saboda wari take, sam Madam GLORIA bata damu ba.
Booth din ta hau, ita yanzu Burinta ta isa Kaduna, domin ganin bayan Abraham, saboda wata muguwar tsanar sa ne ya sake kamata, saboda a ganin ta duk wahalar nan da take sha saboda taurin ran sa ne.




**********************


*ABRAHAM*

A hankali ya d'ago kansa daga cinyar Aysha, ya dafe kansa dake sara masa, ya cije labban'sa da suka tashi daga pink izuwa red, komai da anty Sarah ta fada na yawo a brain dinsa one after another.


Sai da ciwon kan ya lafa masa sannan ya kalli Aysha cikin turanci hadi da raunin murya yace "dama ina da yara? Ina yara a doran duniyar nan ban sani ba, yaya suke Please, i want to see my kids, Ina yarana suke, please tell me"

Ya karasa yana rike hannun Aysha ga wani hawaye mai zafi daya biyo kuncin sa daya.

Komai gani yake kamar al'mara, cikin kankanin lokaci ya ji abinda ya kusan tarwatsa zuciyar sa, da ba dan yayi namijin kokari wurin danne zuciyar sa ba, da yanzu baya a zaune haka, da yana gadon asibiti a kwance.
Tabbas irin wannan abun yafi komai ciwo domin wanda baka taɓa expecting ba, kana ka bashi yarda da matsayin uwa ya ci amanar ka, ya fi ciwo sosai.




Aysha zata tambayi Inna ina su Ammar suka je kenan taji sallamar su cikin Muryar su ta yara, sun shigo gidan...

Gidan iyayen anty Bintu suka je wasa da yaran anty Bintu.
Dama wani zubin har sai Inna taje ta kanta ta dauko su, saboda sun saba da gidan sosai.




Cikin muryar kuka da Aysha ta sha ta kalli Abraham tace

"Oh! they are here already"


Cikin sauri Abraham ya mike ya leko su, sosai ya kura wa gudan jinin sa eyes dinsa da suka yi matukar yin ja, tun kafin su karaso...



duk takun dayan da su Ammar zasu yi, gaban Abraham ke cigaba da faduwa saboda tsantsar kamanin su, shi da Nonye da yaran suka dauko, ya kasa yarda cewa wadannan k'yawawan yaran na sa ne, amma bai san da su ba, babu zato ya ga hawaye na zubo masa, cikin sauri yasa hannu ya share, wani mugun soyayya irin ta ɗa da uba ta caki zuciyar sa, fiye da zaton mai karatu.

Hannayen sa ya ware musu, ya dire guiwowin sa a kasa... muradi, fata, hadi da burin sa yanzu yaran su zo gareshi domin yaji dumin su....










Share
Share
Share fisabilillah ☑️🙏



Comment for more typing.




✨NoorEemaan✨
07082281566




I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851

🍇🍇ABRAHAM🍓🍓

*First edition*



*WATTPAD*
@NoorEemaan



https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din



Chapter 67-68

Maimakon su je wajen Abraham ɗa ya ware musu hannu, sai suka fada jikin Aysha bayan su karaso saboda basa san shi ba...



Cikin Muryar su ta yara suka shiga kiran "Ammuh Oyoyo" rungumesu sosai Aysha tayi a jikin ta, wani mugun son su da kaunar su fiye dana baya na sake ratsa zuciyar ta.


Abraham kuwa sauke hannun sa cikin rashin jin dadi da basu Wajen shi ba, ya kuma san rashin sabo ne yasa su hakan.

Sai ya kafe su Aysha da ido cikin burgewa ganin yadda yaran suka saba da ita, sai faman murmushi.


Aysha ta shafa kansu tace "na yi kewar ku sosai my twin" hakoran su suka washe mata suna dariya, juyo da su tayi ya zamana suna fuskantar Abraham sannan tayi musu nuni da shi tace "ga Daddyn ku, ku je ku gaishe shi"


Tsaye yaran suka yi suna kallon mahaifin su Abubakar Assadik cikin rashin sabo, sai da Aysha ta sake magana sannan suka tafi wajen shi a hankali, kana a tare suka shige jikin sa.


Wasu hawaye masu sanyi ne suka zubo kuncin sa, hakika yau ya dawo mai rauni, saboda abubuwa mabambamta masu cike da al'ajabi da ya ji cikin rayuwar sa a yau, ashe all this year's cikin duhu yake, sai yanzu haske ya bayyana, duhun ya yaye...

Kara rungume ya'yan sa yana basu sumbatar ta ko ina, abin so heart touching and lovely. Aysha ma sai ta data share hawayen tausayin su.


Muryar Anty Sarah ya ji tana sake bashi hakuri da neman yafe, su Ammar da suka lafe a jikinsa ya sake riƙe su da kyau sannan yace " bani da abinda zan ce miki, wadanda kuka zalunta basa duniyar, dan haka ki koma ga Allah kawai" yana gama fadin haka ya mike, sannan ya riko hannun yaran sa suka bar gidan izuwa masallaci domin ya ji kiran sallah.



Kuka mai suna kuka Anty Sarah ta fashe dashi, ina ma ina ma hannun agogo zai dawo baya da ta gyara kuskuren ta.

sai ta dawo bawa su Inna tausayi, domin duk da tarin laifukan ta, amma duk wanda ya ganta a halin yanzu zai matukar tausaya mata.

Baki suka shiga bata kan ta daina kuka, ta cigaba da neman yafiyar Allah, domin Ubangijin talikai gaffurul Raheem ne.



Nan Inna tace mata ta je tayi wanka, saboda maganar gaskiya wari take, bata Musa ba, saboda ita ma ba jin dadin jikin ta take ba, bayan ta yi wanka Inna ta bata wata doguwar rigarta ta atamfa ta saka, sannan aka zubar dana jikin ta a shara.



Abraham kuwa suna fita ya hango masallaci, nan suka karasa suka yi alwala a bakin masallacin domin akwai ruwa da butoci, a gurguje ya karasa alwalar domin har liman ya tayar, su Ammar ma suka yi alwalar su yanda yara suka yi ya rike hannun su suka shige masallacin.


Bayan sun iddar sun fito, yara da manya sai kiran Ammar da Anwar suke, yaran kuwa su dinga amsawa da na'am, yayin da wasu kuma mamakin kamanin yaran da Abraham suke.


Abraham kuwa abin yayi matuƙar kayatar da shi, ya kuma ji dad'i saboda yanda jama'a ke son yaran sa.

Yana so suyi hira amma basa jin wani turanci, shi kuma baya jin Hausa, sai yanzu rashin iya Hausar sa ke damun sa.

Amma yasa a ransa cewa yaran su iya turanci hadi da Yaren sa na Igbo, numfashi ya sauke, duk da bai san akwai su a doran duniyar nan ba, amma yaji dadi ganin su cikin koshin lafiya da kulawa.




Bayan sun iso kofar gidan, ya buɗe musu mota suka shige hadi da kunna musu Ac yaran suka hau murna, suka kalle shi suka ce "wannan motar ka ce?" Be ji abinda suka ce ba, amma haka ya daga musu kai alamun eh yana murmushi.


Su Twins suka hau murna wanda hakan ya sa zuciyar Abraham yin sanyi.
Kurawa Ammar ido yayi yana tuno ranar farkon da Aysha ta fara shiga dakin sa, tabbas wannan sunan ta faɗa, kenan ta ga kamanin su shi yasa cikin rashin sani ta kira shi da sunan Ammar....

Ya sake mai da duban sa ga Anwar, sak Nonye kamar an tsaga kara, nan fa Abraham ya maida su tv ya dinga kallon su, labarin komai da Anty Sarah ta bashi na dawo masa daki-daki.



Inna data ji shiru bai dawo ba, sai tace Aysha ta leka waje ko yana nan, su zo su ci abinci, ba musu Aysha ta mike, domin ita ma ta damu da rashin shigowar su, kawai ta maze ne kar Inna ta ga rashin kunyar ta.

Tana fitowa ta hango shi zaune ya kurawa yaran sa ido a mota, hannu ta ɗora a kugu tana kallon su murmushi dauke a fuskar ta, domin su burge ta, kai kace sun dade da sanin juna.



Jikin Abraham ne ya bashi ana kallon shi hakan yasa shi dago kan sa ya kalli direction din da take, murmushi yayi kana ya kira ta da hannu.

A nutse ta shiga takawa har tazo bakin motar, su Ammar na ganin ta suka shiga kiran "Ammuh!" Sannan suka fito daga motar suka rungume ta.

So take ya saki ransa, hakan yasa cikin tsokana tace "kazo kaci abinci inji Inna"


"What!" Yace yana kafe ta da ido.
Dariya ta sa, dama so take ta tsokane shi, kasancewar ba Hausa yake ji ba.




Ya fahimci tsokanar sa take, sai ya girgiza kansa yana murmushi.

Sai ta dawo serious ta fada masa abinda Inna tace da turanci, baya jin zai iya yin musu ga surukar tasa, saboda girman da take da shi a idanun sa, amma maganar gaskiya sam baya jin yunwa, amma bazai iya cewa a'a ba, fitowa yayi daga cikin motar ya sa key sannan suka jera zuwa cikin gidan.



Dakin ta dake a gyara suka shiga, domin duk da bata nan Inna na gyara mata.
suna shiga kuwa suka tarar Inna ta jere musu wainar shinkafa da miyar taushe da ya sha tantakwashi da nama, sai had'add'en fura da nonon kindirmo zallan sai ruwan randa mai sanyi.


Aysha ta zuba musu komai, tayi wa Abraham Bismillah, Dan yamutsa fuska yayi alamun baya ci, domin duka cimmar bai taba gani ba bare ya ci, nan Aysha ta shiga mai daɗin baki kan ya dandana akwai dad'i Sosai.

Domin ya faranta mata yanka daya ya ci na wainar bai kara ba, domin bai yi masa ba, ko dan bai taba ci bane.

ya sha fura ludayi biyu, sannan ya sha ruwan randa mai yawa bai yi k'yamk'yami ba.



Aysha dasu Ammar kuwa suka ci, duk da ita Aysha Bata wani ci da yawa ba, saboda ganin har yanzu da damuwa a tare da Abraham, wanda hakan kuma dole ne domin rasa uwa, da mata sannan kashe su akayi ba abu bane mai sauki da kuma saukin mantawa a gare shi bane.

Haka dai suka kasance har dare.
Bayan sun yi sallar isha Abraham yace Aysha da su twins su raka shi ya ga gari, ya kuma yi hakan ne domin ya rage damuwa dake damun sa.



Aysha ta sanar da Inna, sannan ta rike hannun Ammar, Abraham kuwa ya rike hannun Anwar suka fice...

Sunyi yawo ba laifi, sun je dandali sunyi kallo, Daga nan suka dan zaga gari Aysha na masa bayanin duk inda suka wuce, daga nan suka je kasuwar dare, Abraham ya siya musu tsire da doya da kwai, da haka suka dago gida gwanin sha'awa, su twins sai surutu suke musu a hanya, Aysha na biye musu, Abraham kuwa sai dai yayi murmushi, domin zuciyar sa cike da farin ciki, ya kuma godewa Allah da ƴaƴan sa suka fada hannun na gari.



Bayan sun iso, Abraham yace zai kwanta a mota, su Aysha su shiga ciki...ya sumbace yaran sa, ya shige motar.


Bayan sun shiga ciki Inna tace "ina mijin ki yake?"

Cikin kunya tace "Inna wai a mota zai kwana"


"A'a A'a ba za a yi haka dani ba, Meye amfanin dakunan nan? Maza ce masa ya shigo dakin ki ya kwana, sai mu kuma mu kwana a daki na"



"Toh Inna"
ta ce tana fita, Abraham da har yayi nisa a tunani ya ji ana k'wank'wansa kofa, glass din motar ya zuge ƙasa, ya ga Aysha tsaye hannun ta rungume a kirjin ta "ụmammm! Hope all this well?"

"Nothing much, Inna said you should come inside"

Dan shiru yayi sai kuma ya bude kofar motar ya fito, ya saka lock sannan ya mara mata baya zuwa cikin gida.

Har baƙin kofar dakin ta Aysha ta kara shi, sannan yta juya zuwa dakin Inna, ba tare da tace komai ba, ta lura har yanzu bai gama sake wa ba, ba kuma ta so ta takura masa.


Da kallo ya bi bayan ta, tana dab da shige dakin Inna taji Muryar sa yace ta kawo masa su Ammar su kwana tare, ba musu ta ce masa toh.

iska ya furzar daga bakin sa, sannan ya shige dakin ya fada kan gadon yana rub da ciki...

Bayan ta kawo su Ammar ta sake fita tana mai sai da safe ya amsa...
haka yasa yaran a gaba yana kallon su cikin kauna har suka yi bacci.

Shi kam babu alamun bacci a idanun sa, haka dai ya dinga juye-juye baccin yaki zuwa har aka kira sallar asuba.




*WASHEGARI*

Bayan duk sunyi sallah, Abraham da ya je masallacin tun asuba bai dawo ba, Aysha kuwa ta fara ɗora musu abincin karin kumallo, bayan ta gama ta share tsakar gida ta gyara sannan tayi wanka hadi da brush.
kayan jikin ta na jiye ta mayar, domin bata dauko kaya ba, sam basu zo da niyyar kwana ba.

Su Ammar ta taso tayi musu wanka da brush, kana ta shimfida tabarma babba a waje, tace su zauna bari ta dauka kayansu da man shafawa...

Anwar ta fara shafawa mai, sannan ta saka masa kananan kaya riga da wando, ta taje masa gashi, ya koma ya zauna, kana ta fara shirya Ammar kenan taji sallamar Abraham.

Amsawa tayi tana satar kallon sa, gefen su yazo ya zauna Aysha ta gaishe shi ya amsa cikin kulawa, su Yan biyu ma suke ce Ina kwana ya shafa kan su yana murmushi.


Inna ta fito duk suka gaishe ta cikin girmamawa ta amsa, Anty Sarah da tun jiya bata bari sun sake haduwa da Abraham ba saboda kunya ta fito yanzu

Please Login or Register in order to submit comment