Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana kara gode wa Allah a ransa, hakika duk wanda yake da cikakkiyar lafiya ya dinga godewa Allah kullum, komai Taulacin sa kuwa, domin gashi Yana da Arziki da dukkanin ababen more rayuwa, Amma baya Jin dadin su saboda tafiyar da baya iyawa.

" Thank you lord, Thank you jesus!" Abraham yace a hankali.

Idanun sa ne ya sauka kan abincin da Aysha ta shirya masa, dan yamutsa fuska yayi, cikin sa dake lafe masu dauke da manya-manyan six packs ya shiga shafawa a hankali, k'watak'wata baya Jin yunwa, domin farinciki daya cika zuciyar sa.



Kallon ledojin daya shigo dasu yayi, ganin bata shigo ba yasa shi kwashe siyayyar daya Yi mata ya nufi dakin ta, ƙwanƙwansawa yayi ba tare da kuma ya Jira ta bashi izinin shigowa ba ya tura kofar ciki...


Zaune ya hangon ta kan sallaya, hannun ta a sama tana addu'a, yayin fuskar ta ya nuna farinciki, ta burge shi kwarai, musamman kwayar idanunta fare kal da suke kallon sama, sannan yanda ta bawa addnin ta muhimmanci ya burge shi ainun, domin ko kallon inda take Bai yi ba, bare ta damu da wanda ya shigo, addu'ar ta ta cigaba da yi, duk da cewa taji shigowar shi, janye idanun sa yayi kana ya ajiye ledojin ya fita...




*30Minutes later*
A hankali Aysha ta shiga cire hijab dinta, tana sakin murmurshi, Dadi sosai take ji ganin Abraham ya warke, so take ta kira Inna ta mata albishir sai ta kuma ta Yi tunanin sun yi bacci, haka ta hakura da tunanin gobe zata kira ta.



Ledojin ta bude ta fito da abubuwan ciki, duk da bata furta ba, Amma tayi farinciki da siyayyar da ya Yi mata, kifin da Ice cream ta ajiye a gabanta ta shiga ci, domin dama ita Mai son kifi ce, sosai taci har ya rage dan kadan, sannan ta Sha ice cream kwatan roban.
Bayan ta gama ta shiga toilet ta wanke hannunta, sannan ta sake Yin brush saboda Karnin kifin, rogowar Ice cream da kifin ta dauka ta sauka kasa ta ajiye ice cream a fridge, ragowar kifin kuma ta ajiye a kitchen, sannan ta koma dakin ta ta yi Shirin kwanciya ranta fari kal, tana Jin farincikin da ta jima ba tayi irin shi ba.




*** *** ***



*BANGAREN ANTY SARAH*

Zaune take a madaidaicin dakin ta, ta Kara lalacewa yayin da tsufa ya bayyana karara a fuska da jikin ta, musamman da babu gyara da ingantaccen abinci, muskutawa tayi sannan ta zabga tagumi, mafarkin da ta Yi kan Nonye yau ya kara firgitata, burinta ta hada yan kudin mota da zai ishe ta domin taje Imo state, Abraham kadai zata nema, domin ta tono asirin dake boye sannan su nufi gombe gidan da ta ajiye yaran ta gudu, domin shi kadai ne hanyar dazai sa ta samu dan kwanciyar hankali, ta sani cewa ita da samun kwanciyar hankali Mai dorewa sai Wani iKon Allah domin kashe rai ba abun wasa bane.



*Bayan kwana biyu*
_2:30am_

A yanda take kwance da kuma yanda take shura kafafun ta zai tabattar Maka da cewa, mafarki mara dadi take...

A firgice ta farka, gumi sai tsatsafo mata yake, gaba Daya ta jika yar T-shirt din jikinta daya gama tsufa saboda dadewa, "zan tona asirin da muka dade da binnewa, Dan Allah kiyi hakuri Nonye, Wayyo Allah ka taimake ni na tuba" Anty Sarah ta fada da yaren Igbo cikin fitar hayyaci...



**********

Da safe a sanyayye take komai domin mafarkin da ta yi Yana makale a ranta, gashi kudin bai taru bare ta tafi yau, Yan kayan abincin da take samu a gona ta dauka, sannan ta nufi makotan su, ta siyar musu a raha, musamman da suka ga tana da bukatar kudi, hakan yasa suka mata tayin wulakanci, Amma bata da zabi Daya wuce ta siyar din, domin a gobe take son tafiya.
Amma abin daya bata mamaki a yau shine lami lafiya ta kwanta bata yi mafarki ba.



Da misalin karfe shida na safe ta dau hanyar Imo state, sun yi tafiya mai tsayin zango sannan ta sauka a tasha, taxi ta tara ta shiga sannan tace ya kai ta wordbank estate...


Bayan sun iso, ta biya shi kudin sa sannan ta sauka, kallon gidan ta shiga yi, har abada bazata taba Manta gidan nan ba, yana nan yanda
Yake sai Dan abinda ba a rasa ba aka Sanja, sosai abubuwa da dama suka shiga dawowa brain din ta, musamman mugayen Abubuwan da suka aikata, hawaye ta share na nadama, sannan ta karasa jikin kofar gidan ta shiga k'wank'wansa wa a hankali, mintuna biyu kacal Wani katon mutum Mai sanye da blue da black uniform ya Bude kofar Yana muzurai...


"Madam how may i help you?" Ya fada da k'akk'auran muryan sa mai amon sauti.

Cikin rawar baki Anty Sarah ta ce....





Share fisabilillah☑️
Comment ☑️




NoorEemaan
07082281566



I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851


🍇🍇ABRAHAM 🍓🍓


*WATTPAD*
@NoorEemaan



https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din



Page 53-54


"'ple.... p...le...ase can i see your boss, i mean Abraham"

Cikin rashin fahimta mai gadi ke kallon ta, domin iya sanin sa ba sunan uban gidan sa Abraham ba, ita kuma Anty sarah ta gane shi tsaf domin shi ne dai mai gadin Abraham na da, amma bata nuna ta gane shi ba.

Shiru mai gadi yayi kamar yace batan gida tayi, sai kuma yayi saurin cewa "oh! Oh!! Oh!!!" Alamun ya tuna Abraham tsohon mai gidan sa, nan ya shiga bawa Anty Sarah labarin tashin sa daga garin ba kuma ya san ina suka koma ba, yana gama bata labari ya rufe gate din ya ruga cikin gidan da gudu sak'amak'on kiran da matar gidan ke masa.


Anty Sarah sulalewa kasa tayi ta ɗora hannun ta akai ta sa kuka mara sauti yayinda hawaye ke sulalowa daga idanun ta, gwanin tausayi, ita kam ina zata je? Ta ina zata fara neman su a fadin duniyar nan?
Ta jima zaune a wajen cikin rashin sanin abin yi, ga duk wanda zan wuce sai ya dinga kallon ta, hakan yasa a sanyayye ta mike ta shiga tafiya domin komawa garin su....



••• ••• •••


Zaune yake a had'add'en office din sa dake cikin ma'aikatar sa, yau kwanasa uku da dawowa aiki, inda sosai ma'aikatan sa suka yi murna da dawowar sa.

A shirye yake cikin suit baƙi, sosai hakan ya fito da kwarjinin sa hadi da haibar sa, Google ya shiga yayi searching wani abu sannan lambar dake karshen rubutun ya dauka, wayar sa yasa ya danna kiran lambar, magana biyu zuwa uku ya ajiye wayar, sannan ya mike ya dauki key din mota da waya, sake gyara zaman rigar sa yayi, murya kasa-kasa yace "yeah! I guess this is the only solution" ya karasa fada yana bude kofar office din ya fita, parking space dake company ya nufa ya shiga Mota, security da masu gadi na masa a dawo lafiya, hannu kawai ya daga musu kana ya fice...


Tafiyar mintuna arba'in ya kawo shi babban ginin mai dake da rubutun *MM HARUNA ENGLISH ACADEMY* kallo daya yayi wa ginin kana ya dauke kansa, lambar dazu yayi dialling, bayan anyi picking ya fada musu yana wajen ginin...

Mintuna uku kacal wani matashi ya fito, cikin girmamawa ya gaishe da Abraham, fuska a sake Abraham ya bashi hannu ya suka yi musabaha, sannan suka jera cikin wajen, office din shugaban su matashin nan ya nuna masa kana ya koma...

Bayan sun gaisa da shi, Abraham yayi gyaran murya yace "am.... I want to register a girl here, i don't mind to pay extra money if she can be fluent in speaking English" Ya karasa Yana dan bugu teburin office din da yatsun sa biyu a hankali, bai sani ba ko Aysha zata yi na'am da wannan makarantar ta koyan turanci da zai sa ta ba, kawai yana so ta iya ne domin ya saukaka musu wajen magana da juna, ya lura cewa bata yi karatun boko ba, matuƙar ta bashi hadin kai, tana kuma kaunar karatun zai bata dukkan wata gudunmawa domin ta cigaba, domin tana daya daga cikin halittun da bazai iya taɓa mantawa ba a rayuwarsa, shiyasa take da dubbin darajar a idanunsa.

Maganar shugaban makarantar ce ta sa shi daga kansa, sannan ya daina buga yatsun sa kan teburin, cikin turanci mutumin yace...
"In Sha Allah zaka yi mamaki yanda zata kware a fannin turanci, karka damu, sannan kamar yadda kace za ka iya ƙara kuɗi domin ta fi saurin kwarewa. Toh zan yi making arrangement a saka ta a special class domin a koya mata komai yanda ya kamata, sannan yace zata iya farawa ranar juma'a, tunda yau Laraba, domin dama kwana uku kaɗai ake karatun juma'a, asabar, da Lahadi"

Hannu Abraham ya bashi suka yi musabaha, sannan ya biya dukkanin kuɗin da ake bukata, sannan aka bashi Form ya cike mata sannan a yi attaching passport din ta da filling foam din, karba Abraham yayi, domin bai san sunan ta ba, bare ya cike mata, baya ga haka ma babu passport din ta a wajen sa, hakan yasa ya karbi Form din yace zai je gida ya cike gobe zai dawo dashi, da haka ya bar wajen

Bayan ya koma office, babu jimawa P.A dinan na shi ya shigo bayan ya bashi izinin shigowa, a sake suke tattauna da Abraham kan abinda ya shafi business din su musamman da bayan nan, yana masa bayanin komai da komai, bayan sun gama maganar business din yace "boss!"
Abraham ya dage girar sa alamun amsawa.
"Wallahi matar ka tana da kirki sosai"...
Dan waro ido Abraham yayi saboda mamakin kiran kalmar *mata* da personal assistance din sa yayi, shi kuwa P.A bai lura da yanayin fuskar Abraham ba, nan ya shiga bawa shi labari tun daga zuwan sa gidan da karramawar da Aysha tayi masa, sannan maganar da suka tattauna kan yana k'asar waje, komai dai bai boye ba...

*Some minutes later*
Bayan fitar P.A "What!" Abraham yace Yana sakin murmushin gefen baki, "so this Hausa girl is smart as this, oh my goodness" sosai ta burge shi, musamman karkashin ta, dakewar ta, hadi da boye rashin lafiyar sa da ta yi, ya jima yana tunanin a kanta da irin hallacin data yi masa...




••••••• ••••••• ••••••



Da misalin ƙarfe hudu ya bar company'n sa zuwa gida. Biyar saura mintuna k'alilan ya iso gida saboda dan hold up dake hanya, a parking space ya faka motar sa, kana ya fito rike da brief case din sa, har ya fara tafiya ya tuna da Form din, ya kuwa ya d'auka sannan ya nufi cikin gidan.....


Kamar kullum fakon shiru sai plasma dake aiki she kad'ai, kamshi yaji ya bugi hancinsa wanda ya tabbatar masa da cewa tana kitchen kenan, bai ce komai ba, ya haura sama, bayan ya ajiye Form dinan a dining table ya ɗora remote control akan takardan.


_7:55pm_
A daidai lokacin Abraham ke saukowa sanye da fararen kaya na shan iska da suka yi matukar karban chocolate skin din sa, kan dining table ya zauna, yana jiran Aysha tazo tayi serving din sa, domin sosai ya fara jin yunwa tun abincin safe, a hankali ya daga kansa ya kalli sama, a ransa cewa kila sallah take yi.

Bayan mintuna goma ya ji takun tafiyar ta, sanye take da hijab ja har kasa, yayi matukar karban farar fatar ta, tamkar wata zinariya haka ta yi kyau.

Kallon ta Abraham ke yi, maganganun da P.A yayi masa ke dawowa ƙwaƙwalwar sa, innocent face dinta ya ke kallo, ba tare da sanin sa ba, murmushi ya subuce masa, tana da sanyi sosai, yayi mamaki kwarai data samu kwarin gwiwa har haka.

Gefen sa ta tsaya tace " sannu da zuwa! Ina wuni"

Daga maka kai kawai yayi, domin bai ji abinda tace ba, kwara ina kwana yafi gane mai, Aysha bata kara cewa komai ba shiga serving din sa, bayan ta gama ta fara kokarin barin wajen.

"Hey! Sit" yace Yana nuna mata kujeran dining table, a sanyayye ta dawo ta zauna, alamu yayi mata kan taji abinci, girgiza masa tayi sannan ta motsa kananan lips dinta tace "Na koshi"

Bai kara magana ba ganin har ta fara raurau da idanu, sai da ya ci fiye da rabi sannan ya mika mata wata takarda, Domin kafin ya sauko ya shiga app dinnan, yayi typing da turanci kan bayanai abinda za a cike Form da shi, abun ya fito da amsa da turanci, ya yi coping a paper, idan ta rubuta masa, she kuma sai ya cike mata Form din da kansa.

Duk da tayi mamakin mezai yi da sunan ta, shekaran ta, da sauran personal details dinta, amma bata tambaya ba ta shiga rubuta komai a inda ya bar space gashi rubutun da Hausa wanda Hakan yayi mata sauki kwarai...

Bayan ta gama rubutuwa ta lura da wasu rubutu still da Hausa a kasan takardan "Ban san yanda zaki dauki abun ba, amma na saki a wata makaranta ta koyan turanci, inda zaki dinga zuwa juma'a asabar da Lahadi, gobe zamu je ayi miki passport idan na dawo, amma idan bakya so zaki iya fadamin"


A hankali ta dago kanta fuskar ta dauke da murmushi, kasancewar ita yake kallo yasa shi ganin murmushin, wani sanyi yaji a ransa, hannayenta ta dage alamun godiya kana tace
"Nagode sosai, Allah ya saka...."

Hannun ya ɗora a lips din sa alamun tayi shiru, saboda ya fahimci godiya take kokarin masa.

Bayan ya gama ya sha lemo sannan ya janyo Form din da abinda ta rubuta ya shiga cike mata.
Aysha kuma ta mike ta gyara dining table, sannan ta kai plate da cups da yayi amfani dasu ta wanke kana ta fito...
"sai da safe" tace tana hayewa sama, bai je komai, domin bai fahimta ba, sai bin ta da ido yayi har ta bacewa ganin sa...

Numfashi ya furzar, kana ya kai idanun sa kan dakin Madam Gloria, wani abu ya daki zuciyarsa tuno wacce mummy, domin sai Yanzu ainihin hallayen ta suka bayyana, ashe duk zaman da suke fuska biyu ce! Bai sani ba, bata kuma taɓa nuna wata alama ba, ganin ransa zai fara ɓaci yasa shi daina tunanin Madam Gloria, sannan ya raya a ransa cewa da safe kafin yaje office zai biya bank ya sanja pin account din sa, saboda a ranar data kwashe ATM din duk yana jin ta, dama pretending baccin karya yayi...

Yana jima a zaune yana sake-sake kana ya kashe duka kayan wutan dakin da plasma ya nufi dakin sa domin bacci...


*WASHEGARI*
Hudu saura mintuna takwas Abraham ya dawo, domin ya yi alƙawarin cewa yau zasu je tayi passport, cikin dan sauri-sauri yake tafiya.
Dakin sa ya shiga dake a kimtse gwanin burgewa sai kamshi ke tashi, kayan jikin sa ya cire, daura towel, sannan ya jefa wanda ya cire a laundary basket kana ya shiga wanka, mintuna goma kacal yayi ya fito ya shiga shiryawa...

Bayan ya gama ya fito, har zai leka dakin ta ya kira ta, sai kuma ya hango ta zaune a downstairs, da alama shi take jira, bayan ya gama saukowa ba tare da ya kalle ta ba yace "let's go"

Duk da bata gane abinda yace ba, amma haka ta bi bayan sa ganin ya nufi waje, sai Yanzu take jin son turanci a ranta, musamman da Abraham ke yi, domin sosai take dad'i a bakin sa...


Har zata shiga baya, taga ya buɗe mata gaban motar, ba musu ta shiga ta zauna. Wani babban gidan hoto Mai suna *INFINITY* ya kawo su, Bayan yayi parking, kusan a tare suka fito daga motar, cikin wajen suka nufa, cikin girmamawa ake karɓe su, nan mai yin passport din ya sanar dasu cewa passport takwas 3,500 hake yake yin sa...

Wani had'add'en dakin hoton aka shigar da Ita, mintuna biyar ta fito ta zauna gefen kujerar da aka tanadar wa Abraham two sitter.

Bayan an gama hada komai aka saka mata envelope, Ya mika mata, karba Aysha tayi ta ɗan buɗe ta ga yayi kyau sosai kamar dai hoto normal saboda haduwar sa.

Maimakon su koma gida sai ta ga ya nufi wani restaurant yayi musu takeaway, domin sam Yau baya son tayi girki, yana matukar ganin kokarin ta wajen iya girki da kula da gida tamkar babbar mace, at least once in the while ya kamata tana hutawa.



•••••. ••••••. •••••

MADAM GLORIA
Tafiya take cikin wani kusurmin daji mai matukar ban tsoro da abubuwan al'ajabi kala ² tun jiya take tafiya amma har yanzu bata kara so inda take so ba, ko wahala bare tsoro bata ji saboda mugun nufin daya cika zuciyar ta...

Tana cigaba da tafiya taji wata murya ta fara dariya cikin wata amo mai ban tsoro hadi da ruda ƙwaƙwalwar mutum, juye juye ta shiga yi ko zata ga mai dariya amma bata kowa ba, can kuma dif cikin wata murya da amon sa ke fidda zallan fushi taji an ce....






Share

Comment






NoorEemaan
07082281566




I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851



🍇🍇ABRAHAM🍓🍓

*First edition*


*WATTPAD*
@NoorEemaan






https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din




Chapter 55-56


Tana shiga cikin fadar bokan nan mai sunan Nandera, ta ga macizai iri daban-daban na ta shawagi a cikin fadar.

Wani sabon tsoro ne ya sake kamata, domin duk bakin halinta idan akwai halittar da take matuƙar tsoro toh bai wuce maciji ba.



Kasa gaba bare baya tayi, sai k'ak'arwa jikin ta ke yi kamar an jona electric shock, domin macizan har zagaye ta suke, ba tare da sun mata komai ba.



Wannan karon wani abu mai kama da danasanin zuwa wajen boka Nandera take, ba wai kuma saboda Allah tayi danasanin ba, sai dan tsoro.



Boka Nandera dake zaune kansa a kasa ya fara sakin wata mahaukaciyar dariya mara daɗin amo, wasu Surutai ya shiga yi tsahon Mintuna biyar sannan macizan nan suka koma wani gefe suka lafe, basu ƙara motsi ba.





Bakar fuskar sa mai dauke da kasumba abin k'yank'yami ya d'ago, sannan ya kalli Madam GLORIA da jajayen idanunsa yan ƙanana yace "karaso da baya ki shigo fada ta mai cike da abubuwa iri daban-daban, hhhhhh"



Jiki na rawa Madam GLORIA ta karaso da baya ta zauna a gaban boka Nandera kamar yadda yace.

Gaba-daya ta birkice, sai faman waiwayon macizan dake gefe take, domin gani take da ta daina kallon su zasu kawo mata sara.


"Ke nutsu! Babu abinda zasu miki sai na basu umarnin haka, hhhhhh" ya fada cikin ƙatuwar muryan sa.




Dan nutsuwa tayi, cikin dake wa ta shiga mai wasu kirari da manya- manyan kalamai. (a'uzubillah!)

Boka Nandera kuwa sai faman buɗe kafada yake cikin takama da isa hadi da jin dadi.


Bayan ta gama boka yace " hakika na jima ba a min kirari irin wannan ba, hakan yasa zan yi miki aiki mai zafin gaske, duk wahalar da kika sha shekara da shekaru wurin hallaka dan kishiyar ki yazo karshe"




"Toh ya...."

"Kada kice komai, nasan matsalar ki, na kuma san abinda kike so, saboda haka ki jira ki ga abin mamaki, ba a cika ni da tambayoyi, sannan zamu rike ki na tsawon wata Biyar da kwanaki a nan, haka ka'idar aikin yake, hhhhhh"




Azabure Madam GLORIA ta kalle shi, tana maimaita wata shidan a ranta, yayi mata mugun nisa, tamk'ar shekara dubu sittin haka take ganin su saboda muradin cika Burinta"

Dago kanta tayi domin yin magana ko zai rage watanni saboda a gaskiya wata shida yayi mata mugun nisa, sai dai tana dago kanta suka hada ido da boka ta kasa magana.


Boka kuwa ganin ya samu nasara ya shiga sakin dariya da ƙatuwar muryan sa mara daɗin ji.




*KADUNA*
Zaune Abraham yake cikin motar sa a daidai building din MM HARUNA ENGLISH ACADEMY yana jiran Aysha ta fito, haka kawai yau yaji shi ya cancanci yazo ya dauke ta, kasancewar driver ke zuwa kai ta ya kuma dauko ta, dalibai sai wucewa suke, amma bai ga Aysha ba, har ya fara kosawa da zaman, sannan ya hangota ta mirror tana tafiya Cikin nutsuwar ta.



Kasa ɗauke idanunsa daga kanta yayi, duk da cewa yau kimanin sati biyu da fara zuwa makarantar ta kenan, amma yana ganin improvment daga gare ta, musamman yanda take dagewa wurin tilawar abinda ake koya mata, duk da cewa har abubuwan yan primary one ana koya mata domin ta fi gane wa sosai, amma yana ganin kokarin ta kasancewar bata taɓa zama a ajin boko ba.


AYSHA
Sai faman kalle kalle take ta ina zata hango driver, Sam bata ma lura da motar Abraham ba, shima ya fahimci hakan, sai ya zuge glass din window ya leko da kan sa, karaf suka hada ido, zaro idanun ta tayi saboda mamaki ganin sa, domin bata taɓa kawowa a ranta cewa zai zo daukar ta ba.


Dayan bangaren ta zagaya ta shiga ba tare da tace komai ba, shima bai ce komai ba ya tada motar suka bar haraban wajen.


Bayan sun iso gida Aysha ta buɗe motar, ta saka santala-santala kafafunta kasa sannan ta waiwayo ta ɗan rusuna kanta tace

"welcome tank" (ita nufin ta so take tace weldone thanks)

Jinjina kan sa kawai yayi yana matse dariyar sa, sannan ta fita izuwa cikin gida.


Ajiyar zuciya kakarfa ya sauke a lokacin daya daina hango ta.

Wasu lokutan yakan ji wani iri musamman idan ta kama shi yana kallon ta, amma ya kasa daina kallon ta, ya sani cewa ba wani abu ke burge shi a jikin ta ba bare ace shi yake kallo, domin idan diri ne bata kamo Chinonyen sa ba, amma kuma baya kallon Nonye kamar yadda yake kallon Aysha, ya rasa dalili, sai dai a kullum idan yana tambayar kansa game da yawan kallon da yake mata, his heart always tells him that hallaci da kyawun zuciyar ta yake kallon deep inside her.

Amma abinda Abraham bai sani ba shine ya kamu da son Aysha tun daga ranar da suka fara haduwa a adaidaitasahu, a kuma ranar ne zuciyar sa ta fara bugawa domin ta.

Haka ya kwashe tsawon mintuna a motar sannan ya kashe motar ya fito, direct dakin sa ya wuce, ya fada kan gado yana tunanin rayuwar sa, kewa sosai yake ji yanzu musamman da babu wani nasa da zai gani ya ji dad'i, dan ma Aysha na gidan yana ganin Allah ne ya kawo ta cikin rayuwar sa, ta masa abubuwan da ko wani dangin sa bazai iya masa ita ba, duk da cewa yana biyan ta Albashi...



Numfashi ya furzar tuno cewa kusan wata daya rabon da mummy ta bar gidan nan kenan, "where is she?" ya tambayi kansa, sanin ba shida amsa yasa shi lumshe idanun sa yana fitar da numfashi daya-daya.



Har lau yana jin mummy a ransa, yana mata kallon uwa da bai da shi, duk da cewa bai san dalilin ta na son ganin ta kashe shi ba, amma yana kokarin matuka gurin ganin ya cire ta a matsayin uwa daya ɗora mata, domin babu wata uwa ta gari da zata zo kashe danta.


Aysha dake kitchen tana girki kuwa kusan tunani ɗaya suke yi, ita mamakin wannan abu take, ace uwa ki fita ba tare da kin damu da sanin halin da ɗan ki ke ciki ba, shi ma daya warke, bai nema ta ba, kanta ya kulle ta rasa gane kan abun nasu, ganin wannan abun bai shafe ta ba ne yasa ta ta6e baki ta cigaba da hada masa had'add'en fish pepper soup daya ji vegetable da spices, sai pure orange juice da zata hada masa.


Wanna kenan!


•••• ••••

Please Login or Register in order to submit comment