Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kalli anty Sarah tace "gashi"

Amsar butar tayi, duk da a yawan lokuta idan fitsari zasu yi basu fiye amfani da ruwa ba, shiga bandaki tayi da jariran inda babu wanda ya lura cikin su Baffa cewar yarane sabuwar haihuwa a hannunta


Ta kai mintuna biyar a ciki kana ta leko ta kofar langa-langan inda ya huje ta ga baffa da Inna(matar baffa) sun shige daki, ya rage saura k'yakyawar bafulatanar yarinyar nan mai suna Aysha, ita ma daga karshe mikewa tayi zuwa nata dakin, duk anty Sarah na kallon su...


Ganin babu kowa a tsakar gidan ya Sanya ta ajiye jakar hannunta hadi da jariran a kasa cikin bandakin, kana a hankalin ta Bud'e kofar cikin sanda ta fito, sai da ta je soron gidan ta fara sauri-sauri gudu-gudu domin barin Layin.....







Ga wacce take bukatar ayi adding dinta a group chat this num👇
07082281566


NoorEemaan 🦋




I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851



🍇🍇ABRAHAM🍓🍓




WATTPAD
@NoorEemaan






https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.




Chapter 5-6


Sai da anty Sarah ta fito babban titi kana hankalin ta ya kwanta, ba tare da ta bata lokaci ba ta nufi tasha domin hawa mota da zai sadata da asalin kauyan su, Sam bata damu yamma tayi ba, haka zalika bata damu ko jin tsoron tafiyar dare ba, duk da yanda ta kai ga tsanar zaman kauye amma shine waje da zai sa hankalinta ya kwanta, domin bata son abinda zai sake hada ta da madam Gloria, ta kuma sani cewa har abada zasu da sauran kwannciyar hankali, domin kashe rai ba abun wasa bane.





Fatan ta daya mutanen nan su rike yaran amana, kuma in sha Allah zata yi kokarin sada Abraham da y'ay'ansa a lokacin daya dace matuk'ar tana raye, hawayen nadama ne ya saukar mata tuno cewa sune silan mutuwar Nonye, yanzu meye ribar su?





*GOMBE*

Baffa ne ya fito daga daki inna na biye dashi, "indo! Indon Baffa!!" baffan ya kira ta yana lekan Dan karamin dakin ta



"na'am baffana" ta fada cikin murya kasa-kasa wanda ke nuni da bacci ke shirin daukar ta.



Fitowar ta yayi daidai da dariyar da Baffa ya saki, kana cikin tarin kaunar tilon 'yarsa yace" shalelena ba dai bacci kike shirin yi ba ga magriba ta gabato"


"wallahi baffana bacci nake ji sosai" tafada a shagwabe tana dago lumsasun fararren idanunta da ya dan rine kadan sak'amak'on baccin da take ji.



"kinga ki danyi hakuri kiyi sallah idan yaso sai ki kwanta, zo mu zauna a tabarma kafin ayi kiran"

"toh Baffa bari nayi fitsari Ina zuwa" tafada tana daukar buta domin shiga bandakin.



Inna dake garken dabobbi tana tasar nonon shanu ta saki murmushi hadi da girgiza kai, domin sosai indo da Baffa ke kaunar juna wani zubin 'yar kallo take zama...



Kafar hagu indo ta saka a bandakin bakinta dauke da addu'ar shiga bandaki, sai dai addu'ar makalewa yayi sak'amak'on abinda tayi tozali dashi a kasan bandakin, shin mafarki take ko gaske? Ko ko shin aljanu ke kokarin bud'e mata ido?



Sanin cewa bata da mai bata amsa ya sanya ta kwala ihu daya yi matukar gigita su Baffa, hankali tashe suke nufi bandakin dan ganin abinda ke faruwa, ya kuma saka Indon su ihu...



*IMO STATE *
Zaune madam Gloria take sanye da bakaken kaya kamar yadda yake al'adarsu idan anyi musu rasuwa, idanunta sunyi luhu² sakamakon kukan karyan da take yi ba dare ba rana matukar a idon jama'a ne, sosai mutane ke tausaya mata, domin har tafi iyayen Nonye nuna mutuwar ta girgiza ta...



Wata yar'uwar su ce ta kalli madam Gloria hadi da cewa "Gloria kiyi hakuri hakan nan, sannan ya kamata zuwa yanzu ki kira ABRAHAM domin ya sani, saboda babu amfanin cigaba da boye masa"



Wani kuka madam Gloria ta saki har da majina tace "tayaya zanyi in sanar da dana wanna mummunan labarin? Banason hankalin shi ya tashi" ta karasa cikin kuka tana bubbuga kafafunta a kasa, riketa duk sukayi suna bata hakuri hadi da karfafa mata guiwan ta kira shi kan cewa ya dawo gida amma kada ta sanar dashi mutuwar Nonye sai idan ya dawo kasar.


Tana Jan majina ta fara dialing number'n shi kana ta daidaita muryar ta...


*KOREA*
Kwance yake gefen beach a wani had'add'en kujera sanye da boxer, sai sunglass dake manne a idanun sa, haka zalika sauran mazan sanye suke da boxer musamman masu shiga ruwan yayinda matan ke sanye da bikini wanda daga kirjinsu sai al'auransu ya rufe. Kyakyawane, chocolate color mai haske, yana da kirar nan da akewa lakabi da *giant* sai had'add'en six-packs dinsa idaunsa bai fiye girma ba, amma suna da matukar jan hankali, hancinsa dogo ne mai dan kauri, yana madaidaicin lips daya kara fuskar tasa kyau ainun, akwai wani karamin dankunne a kunnensa yayinda ya rataya cross + a wuyansa wanda hakan ke nuni da cewa shi din mabiyin addinin chirista(Christian) ne.




Burinsa yanzu ya gama abinda ya kawo shi kasar nan ya tafi domin yayi kewar gida sosai, kasancewar agajiye yake dawowa ko damar Kiran nonye da mummy baya yi, dan karamin tsaki yaja wanda sautinsa bai fito ba sai labb'an bakin sa ne suka motsa.


Haka kawai yake jin ranshi ba dadi, latsa wayarsa yake kokarin yi Kiran madam Gloria ya shigo, yaji dadi sai dai Sam babu alamar hakan a fuskar sa, domin shi mutum ne miskili da zurfin ciki wanda kai tsaye mutum bazai iya karantar abinda ke fuskar sa ba.

Latsa kore yayi hadi da kara wayar a kunnensa "good evening mummy, I was trying to call you guys now" ya fada da turanci.


Daga bangaren madam Gloria kuwa sosai ta daidaita muryar ta kana tace " yes son! Ya kamata ka zo kawo gida hakan gobe, idan yaso ka koma daga baya" ta fada masa da yaren igbo


"mummy is everything alright? How's Nonye and my baby doing?" kit madam Gloria ta kashe wayar ta, domin batasan sauran amsar bashi ba.




Haka nan yake Jin cewa there's something wrong Dan haka babu bata lokaci ya shirya kana yayi booking flight Inda yaci sa a samun jirgin da zai je Nigeria, amma sai karfen taran dare.




Dan haka gida ya dawo ya shirya cikin wasu had'add'un kaya da ganinsu kadai zai tabbatar maka da tsadar su, wayoyin sa hadi da system dinsa kadai ya dauka kana ya tura sakon Gmail ga company daya zo takanas domin su cewa akwai dalili mai karfi daya sanyashi komawa kasar sa, amma zai dawo as soon as possible, daga nan filin jirgi ya koma domin zuwa lokacin takwas ta wuce, ba kuma yaso yayi missing flight.




*NIGERIA*
IMO STATE
Bayan ya sauka a airport ya kira lambar driver gidan hadi da sanar dashi yana Airport, babu Jimawa yazo amma wanna karon driver'n bai yi masa surutunsa irin yanda ya saba ba, hakan ya dan bawa Abraham mamaki domin yasan driver akwai surutu sosai, amma Sam bai nuna ba


Tafiyar mintuna ashirin ya sada su da Abraham mansion, sauka yayi, bai jira driver ya Bude masa ba, direct ya shige general parlour sai dai abinda ya gani ya sanya gabansa fad'uwa sosai domin a iya saninsa a kuma al'adar su ta igbo sai idan mutum ya mutu ake sanya bakakken kaya irin haka, toh me yasa duk suka sanya bakin kaya? Waye ya mutu? Yayi duka tambayar a ransa yana bin fuskar kowa da kallo


Da sauri madam Gloria ta taso, ta isa gareshi kana ta fashe da kuka sosai tace....






_A GASKIYA COMMENT DINKU YANA KADAN HAKAN KE SANI RASA KARFIN GUIWAN TYPING DAN ALLAH IDAN KUN KARA YAWAN COMMENT ZAN DINGA YI MUKU KODA BAYAN KWANA DAYA NE, IF POSSIBLE KULLUM, DOMIN INA DA AIKI SOSAI NAKE DAUREWA NAYI MUKU DAN HAKA KUMA KU FARANTA MIN DA COMMENT DINKU_





Noor🦋


26/12/2021
9:41am



I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851


🍇🍇ABRAHAM🍓🍓

*First edition*



*WATTPAD*
@NoorEemaan




https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din


_note wanna ba sabon typing bane, reposting nake, so duk mai so ya fara bi yanzu ba sai nayi nisa ace daga farko ba_




Chapter 7-8

Yana shirin yin magana Kenan yaji muryar madam Gloria na fadin

"son munyi rashi, munyi rashi babba, Nonye ta tafi ta barmu, tafiya ta har abada, Nonye is gone for ever son" ta karasa tana fadawa jikinsa hadi da rungumeshi, yayinda sautin kukan ta ya karade gabadayan falon.



Tamkar wanda aka watsawa barkono haka ya runtse idanunsa, ji yayi gabadaya dakin na juya masa, sosai gabansa ke faduwa tamkar zata Faso kirjin sa ta fito



Nonyen sa ta mutu, ta tafi, tafiya ta har abada? abinda madam Gloria ta fada ya Shiga dawowa kunnuwansa , a karo na biyu madam Gloria ta kara cewa "ta haifi yan biyu wanda suma a take suka mutu, wayyo ni Gloria ya zanyi da raina" wanna karon k'wak'walwar Abraham ce ta daina gane komai sak'amak'on abinda madam Gloria ta kara fada, wanda ya sanya guiwowin sa yin Sanyi har ya gaza daukar gangar jikinsa, tilas ya sulale kasa, gabadaya jikinsa ya dauki rawa tamkar wanda yake cikin kankara, sabanin hakan gumi ne ke keto masa, na zallan tashin hankali, ga gashin kansa sun mimmike, duk da cewa babu ko digon hawaye a jajayen idanunsa, amma dole dukkanin wani mai tausayi da imani ya tausayawa halin da Abraham yake ciki a yanzu.




Rikeshi madam Gloria tayi tana kuka hadi da bashi hakuri, ko kala ya gaza furtawa domin nauyi da labb'ansa suka yi, hannu biyu ya sa ya rike kanshi dake barazanar fashewa, haka ya kasance cikin wanna halin fiye da awa uku kuma ko motsi bai yi ba, banda zuciyarsa dake bugawa da sauri² mutum zai yi tunanin matacce ne....




*GOMBE STATE*

Ba tare da su baffa sun lura da jariran dake kasa ba suka riketa hadi da cewa "aysha lafiya meya same ki, yi magana meya same ki aysha? " suka fada a tare suka duba jikinta...




Idanunta ta runtsa, sakamakon hakan hawaye ya zubo kan kyakyawar fuskar ta, hannu ta mika ta yiwa su baffa nuni izuwa ga kasan bandakin inda babies din ke kwance wanda zuwa yanzu sun fara mutsu² sak'amak'on sanyin ruwan bandakin daya fara ratsa ta cikin towel din zuwa fatar jikinsu, a tare suka zaro idanun su ganin abin al'ajabi, da ba dan kada su kara firgita tilon diyar su ba, da ihun suma zasu zunduma, a take kuma k'wak'walwarsu ya tariyo musu sanda anty Sarah ta shigo da farin towel din nan, amma basu taba tunanin cewa abu mai rai ne a ciki ba, a tunanin su ko wani kayan ta ne bata son ajiyewa a waje shiyasa ta shigar dashi bandakin.




Sosai mamaki da al'ajabi ya rufe su, babban tambayar su anan shine menene dalilin ajiye yaran da anty Sarah tayi? Domin basu ga alamun tabin hankali ga anty Sarah ba, bare su ce rashin cikakken hankali ne ya sanya ta manta yaranta a Bandakin, shakka babu wanna babban al'amari ne ya shigo cikin Rayuwar su...





Baffa da tausayin yaran ya gama rufe shi ya tsunkuya, amma gabansa na faduwa, amma ya dake, domin abu ne wanda bai taba ji ko gani ba ne ya ratsa gidan sa, sosai ya dake gudun kada ya kara firgita su Inna, addu'a dauke a bakinsa ya hade yaran a jikinsa, kana ya kalli su Inna yace "ki dauko jakar nan ku fito daga bandakin hakan nan" ya fada yana barin bandakin, sai a lokacin indo ta Bude idanunta dake ziraro da hawayen zallan tsoro, cikin tsoro Inna ta sanya hannu ta dauki jakar hadi da riko hannun indo suka fito daga bandakin....





Direct dakinsa baffa ya nufa da yaran, hakan yasa cikin muryar tsoro indo ta ce "wayyo baffa nah! kada ka shigar dasu dakin ka, Kar su cutar da mu, kila ba mutane bane, ni gaskiya bazan iya kwana a gidan nan ba, Dan Allah baffa ka fitar dasu daga gidan nan, muje mu nemi matar mu bata yaran ta " ta karasa cikin zallan tsoro mai hade da kuruciya hadi da sakalci....



Itama Inna irin tunanin Indo ne a ranta na cewa
Yaran ba mutane bane, amma bata furta ba, sai sai tsaf baffan ya karance ta, hakan ya sanya shi sakin murmushi, ya kuma girgiza kansa, tabbas duk shekarun mace da kaifin tunanin ta namiji ya fita koda bai kai ta yawan shekaru ba, ba tare da kuma yayi magana ba ya ida shigewa dan karamin dakin sa, ya kuma san cewa zasu biyo bayan sa domin basu taba ketare umarnin sa...





Wata jibgegiyyar kodaddiyyar malum-malum baffa ya janyo cikin kayansa ya saka yaran a ciki ya lullube su kana ya kwantar dasu kan gado irin dai na kauyen nan, towel din ya fitar waje ya saka cikin roban wanki ya saka kilin da ruwa ya jika shi, kana ya saka kilin ya wanke hannunsa sosai sannan ya koma dakin....





Gyaran murya yayi hadi da mai da duban sa ga Aysha Indo yace "shalelen baffa ina so kwantar da hankalin ki, ta ina kike tsamanin zamu ga matar? Wacce hanya tabi? Ba mu sani ba, Allahu masani.
Sannan ba fa manta yaran tayi ba, ko mai tabin hankali ta san kaunar abinda ta haifa, Allah ka dai yasan dalilin daya sa ta ajiye mana yaran, wadannan yaran mutane ne kamar mu, ki cire tsoro a ranki kinji, Allah kadai yasan dalilin daya sanya wadannan bayin Allah shigowa cikin Rayuwar mu, ko nace kaddarar mu" ya fada yana nuna yaran kana ya cigaba "domin akwai gidaje bila adadin a unguwar nan, amma nan gidan yaran suka fado, Dan haka nayi alkawarin kula da yaran nan har sanda zan daina numfashi, ina fatan zan samu goyan baya daga gareku"




Jinjina kai inna ta yi, wanda tsoron ya dan ragu sak'amak'on maganganun da baffan yayi, zai kara magana yaji an kwala Kiran sallar magriba a wani masallaci hakan ya sanya shi barin dakin da sauri yana gayawa su inna suma su hanzarta yin alwala kada su rasa jam'i domin su kan bi jam'i domin masallacin yana kusa da gidan su, wanda baffa shine Limamun masallacin....




Bayan an iddar da sallah da kamar mintuna talatin baffa ya shigo hannun sa dauke da bakar leda, kallon inna dake kokarin yin tarke/talke yayi, Cikin sauri yace "da kin fara yi wa yaran wanka da ruwan zafin nan, idan yaso sai a sake dora na tuwon" ba musu ta ajiye kayan tuwon, wani tsaftataccen bokiti ta dauko ta juye ruwan, kana ta zuba wani, hadi da gyara wutan, dakin baffa ta nufa da bokitin, kana ta fito ta nufi dakin ta domin dauko roban wanka wanda tun na indo ne amma yana nan da sauran kyansa da sabunta(kun San fulani akwai iya ajiya🤩)



Sai da ta wanke roban wankan kana ta dan sirka ruwan zafin kadan, kan gado baffa ya zauna, jariran na hannunsa yayinda indo ke gefe tana raba idanu wanda zai tabbatar wa mutum cewa har yanzu tsoron bai barta ba.




Ledar da baffa ya kawo inna ta zazzage, kayan jarirai da na Sanyi, sabulun yara da so so, man shafawar su, mataji(comb) hadi da hular Sanyi. Ba laifi siyayyar tayi daidai talaka...




Sosai inna ta wanke yaran ta kuma gasa musu jiki sosai, sai a lokacin jariran suka canyara kuka tun lokacin da suka shaki iskar duniya....



A kuma daidai lokacin ne Indo taji wani mugu_mugun tausayin yaran ya ratsa jikinta, wani Sanyi ya fara ratsa ko wani huda na gashin jikin ta, sak'amak'on hakan tsikar jikinta ya fara tashi, haka nan ta ke Jin wani yanayin na mussaman kan yaran Wanda bakinta bazai iya furtawa ba...

Ajiyar zuciya ta sauke, kana ta mai da duban ta ga yaran Inda zuwa Yanzu Inna ta shirya su cikin kayan da baffa ya kawo, sunyi kyau sosai gwanin sha'awa, karon farko da Indo taji tana son daukan yaran ta rungume su, hakan yasa ta fara takawa domin isa garesu....





*yanzu Abraham ya soma, yawan comment dinku shi zai bani kwarin guiwar cigaba da typing, idan ba comment nima bazan yi update ba*

*Sannan mai son nayi adding dinta a group ta yi chatting dina up ta lambar nan*👇

NoorEemaan🦋
07082281566







Share fisabilillah

Comment

Vote




I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851



🍇🍇ABRAHAM🍓🍓



*WATTPAD*
@NoorEemaan






https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din





Chapter 9-10

Daidai ta gefen baffa ta dire gwiwowinta, kura wa yan biyun ido tayi, hakan nan taji gabanta ya bada ras! Amma sai tayi saurin aro jarumta domin so take wanna tsoron da bata san na menene ba ya barta, sosai yaran suke da kyau mai shiga rai, hannu tasa a nutse ta karbi daya, dayan kuma ta riko dan mitsilan hannunshi, kallon baffa tayi tace "baffana ina son su sosai , daga yau na dauke su y'ay'ana bama kanne ba, sannan kai da inna sun zama jikokin ku" ta fada Cikin iyakar gaskiyar ta kamar ba aysha indo mai kananun shekaru ba, domin duka shekarun ta bai wuce sha biyar ba.




Murmurshin farinciki ne ya bayyana a fuskar baffa, yasan cewa dama haka zata faru, tsoro ne dama ya sanya bata zo garesu ba, domin Indo na da son yara sosai, Allah ne ya nufa bazata samu kanne ba, domin baya mantawa Indai sunyi baki masu kananun yara ta dinga murna Kenan, amma da zaran sun zo tafiya zata fara kuka.



"toh Indon baffale Allah ya tayaki riko" dariya tayi har ya bayyana jerarrun fararren hakoranta, kana ta sanya hannu ta karbi dayan ta hada dukkansu ta rungume....



Ta dauki mintuna biyar a haka, yaran na manne da jikinta tana shakar d'adadd'an k'amshin jikinsu irin na jarirai...



Inna dake kallon su da murmushi a saman fuskar ta ta Mike domin zubar da ruwan da ta yi musu wanka hadi da wanke towel din da baffa ya jika, Bayan ta gama komai ta dawo dakin, baffa ya kalle ta yace "ina ga nonon shanu ya za a tasa a fara bawa yaran kafin mu ga yanda Allah zai yi, domin ragowar kudina nayi musu siyayyar nan dashi, naso dai siya musu madaran yaran"





"toh malam, bari na tasar musu, in sha Allah ma zasu karba, karka damu" ta fadi hakan domin kwantar wa da baffan hankali.



"Allah yasa" ya fada yana maida kallonsa da indo hadi da tsokanar ta, ganin yadda ta rike yan biyu gam bata da alamar kwantar dasu....



Bayan Inna ta kawo madarar shanun da ta dumama, ta wanke feeder ta zuba a ciki, cikin sauri indo ta karba ta fara sawa daya a baki, wani ikon Allah kuma ya karba ya fara tsotsa wanda hakan ya faranta ran baffa, yana fatan dayan ma ya karba.




Bayan dayan ya koshi, ta fara bawa dayan, shima ba laifi ya sha amma bai kai na farko ba, Bayan ya gama sha Inna tace indo ta kwantar da yaran hakan nan, basu da kwarin da za a yi ta daukar su sosai....


Ai fa nan indo tace bata San zance ba, ita haka zata rike su har gari ya waye, dariya su Inna suka saka mata kana da kyar aka lallaba ta kan cewa tare dasu za ta kwana, ganin lokacin isha ya karato ya sanya baffa ficewa zuwa masallaci, inda bayan sun iddar da sallar ne ya yi sanarwa abinda ya faru a yau na ajiye jariran da anty Sarah tayi, bai boye komai ba, ya kuma bayyana din ne saboda sanin halin jama'a, ya kuma yi hakan ne ko dan nan gaba, domin wasu zasu iya tunani, ko yin sharri ga tilon yarsa...




Nan fa mutane suka fara fadin albarkacin bakinsu, wasu ma har cewa suke sun ga shigowar anty Sarah Layin a firgice da farin towel , wasu kuma sun ce sun ga fitar ta cikin rashin gaskiya amma basu kawo komai a ransu ba, maganganu dai kala² kowa na fadin albarkacin bakinsa.






*IMO STATE*
Kwance yake flat kan had'add'en kuma yalwataccen gadon sa, azahiri idan mutum ganshi a yanda yake zai yi tunanin kallon pop'n daya k'awata saman dakin yake, sai dai sam ba haka bane, domin sosai ya zurfafa a tunani, Nonyen sa ta mutu? Abin ya yi matuk'ar tabashi fiye da zaton mutum, ganin abun yake kamar a mafarki, ji yake kamar yanzu zata shigo dauke da cikin sa ta zo gareshi, yanzu ta tabbata bashi da kowa sai mummy(madam Gloria) daddynsa ya mutu, mummy'nsa ma haka, tun daga lokacin daya rasa su ya rasa dukkanin farinciki kana walwalar sa ta ragu, shigowar Nonye cikin Rayuwar sa ba tare da ya shirya ba ya rage masa wasu abubuwan, duk da a lokacin babu soyaaya a gaban sa, ya kuma ki sauraran ko wacce mace, amma haka Nonye ta d'aure ta jure duk Wata shariya da yayi mata, ta kuma cire kunya ta furta tarin kaunar da take masa a matsayin ta na 'ya mace...



Hak'ik'a bai taba kawo wa ransa cewa zai rasa ta yanzu ba, ya kuma kasa yafe wa kansa kan me yasa bai nuna mata zallan soyaaya ko da rabin wanda take masa ba, gashi yanzu ta tafi tafiya ta har abada, ya tabbata bashi da kowa sai step mummy'nsa(kishiyar mahaifiyarsa wato madam Gloria)

Kasa rike kukan daya taho masa yayi, sosai ya saki kukan da sautinsa ke fidda zallan kunci, maraici, hadi da kewar da yake ciki, dole Abraham ya bawa mutum tausayi, domin cikakken namiji kamar sa na kuka tamkar karamin yaro.


Ya jima sosai yana kuka kana ya yi shiru yana sauk'e tagwayen ajiyar zuciya, k'amk'ame jikin sa yayi hadi da takurewa kan gadon yayi, duk da Sanyin da yake ji, amma ya kasa tashi ya kashe Ac ko kuma ya rufe jikinsa...




*Bayan Kwana Biyu*

Garin enugu a kauyen Nusukka anty Sarah ce ke zaune a asalin jahar ta, dakin karami ne ginin Jan kasa, duk da Rayuwar kauyen na matuk'ar bata wahala, domin ta jima rabonta da kauye, Rayuwar birni yagama ratsa ta, amma duk da haka ta fi Jin kwanciyar hankalin zaman nan din, Abu na karshe take son aiwatar wa kafin ta yanke duk Wata alaka dake tsakaninta da madam Gloria, hakan yasa ta fara latsa wayar ta, ta saka magic voice muryar namiji kana ta kara wayar a kunne ta mai dauke da barima guda shida....





Bangaren Madam Gloria kuwa zaune take a gadon ta da plate din kaza tana ci, key ta saka wa kofar domin bata so kowa yasan tana cin abinci, domin nuna wa take a gaban mutane cewa bata iya cin komai saboda tsananin damuwa da alhinin mutuwar Nonye, sosai take yagar kazar ta tana korawa da sanyayyar juice, Kiran daya shigo wayar ta ya sanya ta ajiye juice din hannunta, daukar wayar tayi, dam taji gabanta ya buga, ita kam har ta manta da anty Sarah, saboda yawan jama'a dake zuwa kullum yasa ta sha'afa.....





Latsa kore tayi ta kara a kunne ta, "Sarah ina...." kasa karasa maganar tayi a dalilin muryar namiji data ji, kara kallon number'n tayi taga dai number anty Sarah ce, tana cikin wanna tunanin taji muryar ta ce da yaren igbo "ba Sarah bace, Sarah ta mutu, ni yayan ta ne, Ina ta Kiran lambobin wayar ta ne ina sanar musu, hatsari tayi, Sarah ta tafi ta barmu, jiya aka yi burial din ta" muryar anty Sarah da ta rikide ta dawo

Please Login or Register in order to submit comment