Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dakin ya sha gyara sosai, ya kuwa same ta zaune a tsakiyar gado ta rufe fuskar ta da veil.

Wata dariya ce ta zo masa ganin ta a lullube, saboda abu ne wanda bai taba gani ba, kasancewar baya daga cikin al'adar su, sai ya ga abin ya mai wani iri.


Aysha kuwa da ta ji dariyar sai ta yaye mayafin a hankali tana cuno baki, gimtse dariyar sa yayi, sannan ya dawo kusa da gadon ya zauna.

Cikin turanci yace
"Meyasa kike rufe fuskar ki haka?"

"Hakan al'adar mu ce, ko wacce amarya idan aka kai ta gidan miji sai an rufe fuskar ta, shi kuma ango ya zo ya bude" ta karasa tana turo bakin shagwaba.





Jinjina kansa yayi alamun gamsuwa sannan yace "is like na ji wanna kalmar a wajen Alhaji Umaru, he was like Ango, where is your amaraya"

Fashewa Aysha tayi da dariya saboda yadda yayi magana da harshen sa na Igbo gashi ba Hausa yake ji ba.

"Why Are You laughing?"

Ya tambaye ta yana taya ta dariyar.

"It's called amarya, not amaraya"

"Ohh!" Yace yana dafe kansa.


Sannan yace "Meye ma'anar hakan"

Tace "amarya means bride, while Ango means groom"


"Wow! I will like to speak Hausa too" ya fada.

"That's nice, and i'm sure you will love it" Aysha tace tana murmushi.



Haka dai suka cigaba da hirar su ta masoya har karfe tara sannan Abraham ya kalle ta, cikin so mai tsanani yace

"Get up let's perform abulution"
(tashi muyi alwala)

Kasancewar Alhaji Umaru ya fada masa komai da sabbin aure ke yi.


Ta ɗan yi mamaki jin abinda yace domin bata taɓa tunanin ya san da hakan ba, ba ta ce komai ba taje tayi alwala, ta fito ta tarar ya shimfida sallaya, hijab dinta ta saka ya shiga jansu sallah.


Hakika Abraham yayi matuƙar kokari wurin ganin cewa ya yi sallar yadda ya kamata, duk da cewa bai dade a Muslunci ba, amma ya yi kokari, har Aysha ta yaba masa a ranta.


Yaso yi mata tambayoyi kan abinda ya shafi addini Kamar yadda Alhaji ya fada masa angwaye nayi, amma ya kasa, domin bai san me zai ce ba, saboda yasan cewa Aysha ta yi masa nesan zango a karatun Addini.


AYSHA ta fahimci hakan, saboda ta kara masa karfin guiwa sai ta ce
"yi min tambaya kaza"

Shi kuma sai ya maimaita abinda tace matsayin tambaya yake mata, ita kuwa a ladabce ta shiga bashi amsa, abin yayi matuƙar kayatar dashi.


Bayan nan ya mike ya shiga toilet ya sakar wa kansa ruwa mai sanyi, nishadi na ratsa zuciyar sa domin ya mallaki abar kaunar sa, ya dauki mintinan ashirin sannan ya fito sanye da bathrobe, kallon Aysha yayi ya watsa mata dan ruwan wankan hannun sa yace "it's your turn now, go and take your bath".


Murmushi tayi, Jiki a sabule ta mike, haka kawai take jin faduwar gaba da mutuwar jiki, tana daf da shiga banɗaki ta ji yace

"Ụmammmm!"

Juyowa tayi tana Fuskantar shi, cikin kulawa yace "why Are You so cold?"

Murmushi ta k'ak'aro hadi da girgiza kanta sannan ta shige toilet din.



Abraham kuwa numfashin ya furzar sannan ya cire bathrobe din ya daura towel a kugun sa, baya ra'ayin shafa mai, hakan yasa ya fesa body spray masu k'amshi da oil perfume.


Ajiyar zuciya ya yi, yana tunanin yadda kaddara ta haɗa shi da Aysha, da irin kalubale kala-kala daya fuskanta, da musuluntar da yayi, da auren su da Aysha, komai dai ya dinga dawowa brain din sa tamkar Film, sai gani yake kamar ba a kansa duk wadannan abubuwa Ya faru ba, ya dawo wani sabon mutum, domin tabbas Abraham din da ba shi bane na yanzu.


A hankali Aysha ta buɗe kofar banɗakin, kasancewar bathrobe ne a jikin ta baby pink, shaf ta manta bata dauki hijab ba, ga kayan jikin ta sun fada a ruwan toilet, hakan yasa bata da wani zabi daya wuce ta sa bathrobe, amma ta rasa yadda zata yi ta fito gaban Abraham a haka...

Ta bude kofar ta ga idanun sa a lumshe, sai ta ɗauka yana bacci ne, hakan yasa sadaf-sadaf Kamar mara gaskiya ta nufi inda ta ajiye hijab dinta dake gefen Abraham da niyyar ta ɗauka.

Ta sa hannu ta dauka kenan ta ji ya rike hannun ta hadi da janyota, ta kuwa fado a jikin sa, zazzaro idanu Aysha ta shiga yi, yayin da bugun zuciyar ta ya karu.

Cikin ƙoƙarin danne dariyar sa yace
"zaki mun wayo ko?"

K'ala ta gaza cewa, Abraham kuwa ya sake holding dinta so tight ta yadda bazata iya kwace kanta ba, ajiyar zuciya mai karfe ya sauke, wani dadi da bazai misaltu ba ya dinga ji, ganin Aysha a shimfide a kirjin sa, is the most sweetest thing he has ever came across with, ga wani kamshi mai sanyin dad'i da ke fita daga jikin ta yana ratsa hancin sa, gashin kanta irin na fulanin usul ya shafa, bai yarda cewa wannan uban gashin na ta bane, ya zata kari tayi, hakan yasa cikin shakakiyyar murya yace
"is this your natural hair?"

Jinjina masa kai tayi domin magana ma bata jin zata iya, bayanta ya shiga shafawa a hankali daya sa jikin Aysha daukan rawa, tausayi da dariya ta bashi a lokaci ɗaya, bai yi expecting wanna tsoro daga gareta ba, domin ita din ba budurwa bace a tunanin sa, sannan hakan ta sanar dashi.


Da zai iya, daya barta ba tare da yayi mata komai ba, amma ya kai gejin da ba zai iya hakura ba, kusan shekara biyu yayi hakuri.



cikin kunne ta ya sa harshen shi ya latsa sannan ya ce
"relax babe, i will be gentle ok"

Kamar mai shirin kuka ta gyada masa kai, tana ƙoƙarin danne tsoron ta, sai dai hakan na neman gagarar ta.

Lallaba ta ya shiga yi, domin a tunanin sa ya dauka ko tsahon mijin ta baya bi da ita a hankali ne yasa take a tsorace haka, kashe wutar dakin yayi, sai dim light daya bari, Sannan ya zare towel din jikin sa ya cillar, bathrobe din jikin ta ya cire mata, sannan cikin so da kauna mai tsanani ya haɗe bakinsu waje ɗaya...


Tun yana yi a hankali har ya dawo kissing dinta a zafafe kamar zai cire mata baki, Aysha kuwa numfashin ta ne ya dauke na wucin gadi kana ya dawo.


Ganin yana ƙoƙarin cire mata dan bakin ta yasa ta sa dan ragowar karfinta ta fisge bakin ta Hadi da fashe masa da kuka.


Sam Abraham baya jin ta, kara janyota yayi ya shiga bata wasu zafaffan romance Daya kusan haukata Aysha, domin ƙwaƙwalwar ta ya gagara dauka.




A lokacin da Abraham ke ƙoƙarin su zama abu ɗaya, sai dai bai iya addu'ar saduwa da iyali ba, abin mamaki, duk da halin da Aysha ke ciki bai hanata karanta addu'ar a ranta ba, domin koyi ga Annabi (S.A.W)




•••••••••••

A karo na uku Abraham ke ƙoƙarin neman hanyar sa, amma ya rasa, hakan ya yi matuƙar daure masa kai, Aysha kuwa har ta gaji da kuka saboda wuya.



Cikin fitar hayyaci Abraham ya rike kafadunta, yace "why are you so tight? Why?
meyasa kike a matsayin budurwa har yanzu, Bayan kina da ya'y'a biyu, what are you hiding from me, ki gayamin, gayamin nace" ya faɗa a tsawace.



Kasa magana tayi, sai kuka take tana girgiza masa kai.

"I said..." Kasa karasa maganar yayi saboda hango sakar nan mai dauke da sunan NONYE a wuyan ta yana kyalli, wayar sa dake gefen bed ya mika hannu da sauri ya kunna fitilar sannan ya haska wuyan ta domin ya tabbatar da abinda ya gani, gaban sa ne yayi wata mahaukaciyar bugawa, tunanin kala-kala ne suka zo brain din sa a lokacin daya.

Hannu yasa ya damki Sarkan ya kura mai ido tsahon Mintuna kamar yana neman wani abu a jikin sarkan, tabbas bazai taba mantawa ba, bazai taɓa manta wanna sarkan ba, domin shi da kansa ya sa aka ƙera wa NONYE Sarkan nan a Dubai.


" How comes Sarkan nan yazo wajen ta?" tunanin dake ta yawo a brain din sa kenan.



Dago kanta yayi da hannun sa, sannan ya kafe ta da jajayen idanunsa, a tsawace yace "now tell me, ta yaya kika samu wanna Sarkan, kina so na cire yarda da nake dashi a kanki ko? ki gayamin nace, wacece ke!"




"ki gayamin, who are you?"

saboda tsawar da yayi gashi kuma dare ne, hakan yasa sau uku Muryar sa ta amsa kuwwa a dakin.

Kuka mai sauti Aysha ta saka ga wani mugun tsoran sa daya shige ta yanzu, gaba-daya ya firgice, ya sanja mata, gashin kansa hadi da na jikin sa duk sun mimmik'e ga jijiyoyin kansa da suka fito rudu-rudu, cikin rawar baki gwanin tausayi tace...





Share fisabilillah



Comment




Noor Eemaan
07082281566



I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851




🍇🍇ABRAHAM🍓🍓

*First edition*


*WATTPAD*
NoorEemaan


https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din




Chapter 63-64


Cikin in-in na Aysha tace "Ni..ni...ni... Ba kowa bace, sannan bana boye maka komai, ba san komai ba ga me da sarkan nan ba" ta karasa cikin kuka mai ban tausayi.


"Tell me, ta yaya sarkan nan ya zo wuyan ki?" Abraham ya kara tambayar ta cikin tsawa domin ya fara loosing control.


"A dakin Baffana na dauka kafin ya rasu, dan Allah ka sakar min wuya, You re hotting me, wayyo baffana da na ji maganar ka da hakan bata faru ba" Aysha ta fada tana kuka sosai, domin bata manta lokacin da baffa yace Kada ta ɗauki sarkan nan ba.



Cikin daurewa kai ya maimaita kalmar "Baffa!' sannan yace "Who's baffa?"



"My father, but he's dead!" ta karasa cikin kuka sosai har wani shidewa take, musamman daya sanja mata lokaci ɗaya, ka kallon idanun sa bata son yi saboda tsoro, domin yanayin sa ya fi kama da na mai gushewar hankali.


Doga ta zaune yayi yana sakin wuyan ta, Sannan ya haɗe jikin su wajen daya ya matse ta cikin faffad'ar kirjin sa, dumin fatar jikin su na ratsa ta juna.



"I...i....i... Oh Allah! am confused, i don't know what to say, Please gayamin komai, i mean everything concerning ta yadda sarkan nan ya zo wajen ki"


Kara shigewa jikin sa tayi ba tare da ta san tana hakan ba, cikin sheshekar kuka tace
"ranar da bazan taba mantawa ba itace sha biyar ga watan Oktoba (October) shekarar dubu biyu, muna zaune da yamma Ni, Baffana, da Inna ta.
Sai muka ga wata mata ta shigo cikin gidan mu, daga ganin matar yare ce, cikin turanci tace tana son yin fitsari, duk cikin mu babu mai jin turanci, sai baffana dake ji kaɗan-kadan, ya kalle ni yace na zuba mata ruwa a buta tayi tsarki, bayan na zuba na mika mata, ta karba, Sannan ta shiga banɗakin...
Ta ɗauki wasu Mintuna bata fito ba, amma bamu kawo komai a ran mu ba, domin ko wani dan adam Akwai uzuri da yake yi a banɗaki, sai muka dauka cewa kila kunya take ji shiyasa tace fitsari ne, baffan ne ya mike, sannan Inna ta mike itama da alama wani abun take son dauko masa, ya rage Ni kaɗai a tsakar gida, nima mikewa nayi domin zaman ya ishe Ni, dakin na na shiga na kwanta, kuma abun mamaki sai muka manta da babin matar, domin mun ɗauka har ta tafi".


Wata ajiyar zuciya mai tafe da sheshek'a Aysha ta kara saki, sannan ta ɗora da cewa "bayan wasu Mintuna na fito daga dakina domin shi ga banɗaki nayi fitsari... kafata daya na saka cikin banɗakin mu, sai na tsaya cak! Ka san me na gani?"



Girgiza kai Abraham yayi, domin a halin da yake ciki yanzu sam baya jin zai iya magana,domin harshen sa ta yi masa nauyi.


"Yara yan biyu jarirai da ko Cibiyar su ba a yanke ba na gani kwance cikin farin towel a kasan banɗakin mu, sai wata jaka a gefen su, ihu na kwala daya fito da su Inna a guje, kasa magana nayi sai nuni da na musu da jariran da suke kwance a kasan jikina na matuƙar rawa kamar an jona min electric shock mamaki sosai ya kama iyayena domin duk cikin mu bamu lura da cewa da akwai jarirai hannunta a lokacin da zata shiga banɗaki ba, mun ɗauka cewa kila wani kaya ne nata da bata son ajiye wa a waje ne, domin ta lullube su ta yanda babu mai tunanin jarirai ne a ciki...." Nan dai Aysha ta cigaba da gaya masa komai daki-daki kamar yadda abin ya faru...



*Abraham*

Zufa ce ke karyo masa mai yawa har tana diga kan gado, abu ya ji yana biyo kuncin sa ya shafa yaji ashe hawaye ne, saurin goge idanun sa yayi Domin dai bai san ko kukan me yake ba, har yanzu akwai abubuwan da yake son sani, amma ganin jikin ta na rawa da alama zazzaɓi ne ya rufe ta saboda tsoro hakan yasa ya mike, ya nufi sif dinta daya sanja mata zuwa mai six doors ya buɗe ya dauko bargo, zai rufe kenan idanun sa suka sauka kan Ghana most din ta nan, cak ya tsaya yana kallon ghana most din, domin lokacin da ake hada mata sif dinnan ya ga jakar ghanan, ya so ya buɗe domin dubawa idan ba abu bane Mai muhimmanci ya fitar waje, har ya kai hannu da niyyar dauka, kira da ga kamfanin sa ya shigo wayar sa, hakan yasa ya manta gaba-daya...


Bargon ya rufa mata sannan ya dauko ghanan most go din, haka kawai yaji zuciyar sa na azalzalar sa ya buɗe, ya kuwa zuge zip din hadi da zazzage ta a kasa, abin ciki ya fado kasa...


Kamar mai tsoron taba wani abu haƙa ya mika hannu ya ɗauka, gabansa na tsananta bugawa Saboda ganin hoton album din sa, tabbas baya mantawa farkon zuwan su Kaduna ya nemi hoton album din nan bai gani ba, har Madam GLORIA tana cewa kila garin
kwashe kaya ne suka manta a Imo State.


Shafin Farko ya buɗe ya fara tozali da hoton sa, cikin sauri sauri ya cigaba da buɗe hoto album din yana kallo, fadin tashin hankali da mamakin daya shiga bazai fadu ba.


Mayar da kallon sa ga Aysha dake kwance idanun ta a lumshe yayi, sai da ya ɗan daidaita nutsuwar sa, sannan yace "ụmammmm!" Ya kira ta Cikin murya dake bayyana halin tashin hankali da yake ciki.


A hankali ta bude kumburarun idanunta ta kalle shi, idanun ta na sake yin raurau kamar mai shirin kuka...
(Kamar yadda kuka sani dama Abraham da turanci yake magana, ina saka Hausa ne domin sauk'ak'awa makaranta na) cikin Yaren Ingilishi yace "wannan album din ma a tare kika gan su tare da sarkan nan dake wuyan ki?"


Cikin rawar murya tace "eh! Yana tare cikin jakar da Matar ta bari a banɗakin gidan mu"


"Oh God!"
Ya fada yana hargitsa gashin kansa, daf da Aysha ya matso sosai har yana juyo bugun zuciyar ta yace "You no what? First thing tomorrow morning we are living to Gombe, i just need to finalize some issues, am so confused ụmammmm, am confused" Yana gama fadin haka ya bar daki kamar zai tashi sama.

(Kin san me? Abu na farko gobe zamu je Gombe, ina so na tabbatar da wasu abubuwan, na rude rayuwata, ina cikin rudu)



Jinjina kai Aysha tayi, tana kallon shi ya bar dakin, ta sani cewa yana bukatar kaɗaici, sam bata ga laifin sa ba, lumshe ido tayi wasu hawaye Masu dumi suka zubo mata.



Idanunta ta kai kan photo album din, tun da ta dauko a dakin baffa bata taɓa budewa ba, a hankali ta sa hannu ta janyo shi daga gefen gado inda ya bar shi, dan mikewa zaune tayi tana cije lips dinta saboda kanta dake barazanar fashewa, majina ta ja sannan ta bude shafin Farko, zuciyar ta ne ya bada dam! Tsoro, firgice, hadi da dimbin al'ajabi ne suka kama ta Saboda hoton Abraham da ta gani, duk da a kananun shekaru aka yi hoton, amma still kamanin sa basu sauya ba.



Toh Meye haɗin sa da matar nan da ta bar su Anwar ta gudu? Ya akayi photo album din sa yaje har Gombe, kuma a lokacin basu san juna da Abraham ba, infact Bama ta yi mafarkin fara aiki a gidan nan ba...

Maganganun da suke ta yawo a ƙwaƙwalwar ta kenan, sosai zazzaɓi mai zafin gaske ya kara rufe ta, saboda damuwa da tashin hankali, har kad'awa hakoranta ke yi dana juna.

A takaice dai haka kowane su ya kwanta ba tare da bacci ya dauke su ba cikin damuwa, firgice, hadi zullumin abinda zasu tarar gobe...



Karfe shida na safe sun ɗauki hanyar Gombe, inda Abraham ke tuka su, Aysha na zaune a gefe shiru, duk wanda ya kalli su biyun a lokacin sai ka tausaya musu, domin sai ka rasa waya fi wani tashin hankali a cikin su.




***********


Bayan wasu awannin suka isa garin Gombe, sannan suka dauki hanyar unguwar su Aysha, duk da ya gaji da tukin, Amma still Abraham Bai huta ba, burin shi kawai su isa gidan, hakan yasa ma ya kara gudun Motar.

Tun daga nesa yake danna horn ga wata mata dake tsaye a tsakiyar titin, inda Wannan matar tafi kama da mai tabin hankali, saboda yanayin shigar ta da kuma yanda kamanin ta suka sauya...
Kamar kurma haka matar nan ta tsaya, wasu mutane dake gefen titin har ihu suka dinga mata domin ta matsa amma inna, hakan bai yu ba domin bata tare da tunanin ta, ga gudun da Abraham ya keyi ya ma kasa taka birki, yana daf da buge ta Allah ya bashi nasara ya taka wani uban birki, amma duk da hakan sai daya buge matar a kafa, Allah ya takaita bai yi sama da ita ba, inda anan ne hankalin matar ya dawo jikin ta...


Ta kwala ihu saboda zafin da ta ji ya ratsa kafar ta, cikin sauri Abraham yace

"ya Allah!"

Sannan ya ɓalle murfin motar ya fito cikin sauri, Aysha ma ta fito, cikin kulawa Abraham yace "Am very sorry madam, please let's take you to the hosp...."


Sauri dago kanta matar tayi, wanda hakan yasa Abraham bai karasa maganar sa ba.

Cikin firgice, farinciki, hadi da mamaki tace

"Abraham!"


Cikin mamaki Abraham ya kalli matar jin ta kira sunan sa, ya kafe ta da ido, yana son tuno fuskar ta, amma hakan ya gagara.


Aysha dake ta zaro ido Saboda rudewa da tsoro, cikin Yaren Ingilishi tace itace! Itace ta ajiye su Ammar a banɗaki ta gudu, tabbas itace bazan taba manta fuskar ta ba" Aysha ta faɗa cikin tabbaci, nan aka shiga Kallon-kallo a tsakanin su uku.




_Manage pls, I'm damn tired, Kila ku ga typing error banyi editing ba_😩






*Guys new book Is loading next week, kuma paid ne #300*




Share fisabilillah


Comment for more typing



Noor Eemaan
07082281566




I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851




🍇🍇ABRAHAM🍓🍓



*First edition*



https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din




*WATTPAD*
@NoorEemaan



Chapter 65-66


Sun dauki mintuna biyar masu kyau suna kallon-kallo ba tare da sun ce wa juna komai ba, musamman Anty Sarah dake kallon Aysha saboda jin abinda tace. Abraham da komai ya fara girmama ƙwaƙwalwa da tunanin sa ya zuba wa anty Sarah idanu dake ta sharban kuka abin tausayi.



Cikin kuka tace"Abraham baka gane ni ba ko? i knew bazaka gane ni ba" numfashi ta sauke, yayinda ta hadiye Wani abu mai kama da tsoro sannan ta ɗora da cewa "nice Sarah, kawar Gloria dake a matsayin mahaifiya a gare ka, na jima ina neman ka, har imo naje gidan ka amma na samu labarin kun tashi, sai dai ban san ina kuka koma ba"


Runtse idanun sa yayi sannan ya bude saboda sunan mahaifiyar sa da aka kira Madam Gloria da shi, a yanzu kam baya so a danganta shi da ita.


Sauke idanun nasa yayi kan Anty Sarah, tabbas ya gane ta yanzu, ko lokacin da take matsayin yar aiki a gidan ba wani kallon ta yake ba bare ya wani gane ta, ya kuma yi mamaki da ta ce ita ɗin kawar Madam Gloria ce, domin a iya sanin sa yar aiki ce.
Domin madam Gloria ta sanar dashi cewa Sarah yar aiki ce.

Kawar da wanna tunanin yayi, saboda Akwai abinda ya sake daure masa kai, yana son yayi nazari da kyau ta yanda akayi ta je gidan su Aysha ta ajiye jarirai, sannan jariran na waye? kuma a wani dalili take neman shi? Sosai yake son samu amsar wandannan tambayoyin, amma ya ma kasa magana, saboda abubuwan da yawa ya rasa ta ina zai fara.


Numfashi Abraham ya furzar sannan ya kalli Anty Sarah yace "come with us" yana gama fadin haka ya juya cikin sauri ya fada mota, Aysha ta mara masa baya ta zauna a kujerar mai zaman banza, yayinda Anty Sarah ta shiga baya ta zauna shiru gwanin tausayi kamar kazar da ruwan sama yayi wa duka.



Nan Aysha ta cigaba da nuna masa hanya...
sun dauki mintuna sha biyar suna tafiya sannan suka iso kofar gidan tace ya tsaya sun iso.


Ba musu ya tsaya hadi da daura kansa kan sitiyarin motar, kallo shi Aysha tayi, cikin sanyin murya tace "lemme inform Inna we re together"
(bari na sanar da Inna tare muke)


Bata jira amsar sa ba ta
bude kofar motar ta fice hannun ta rike da jeka mai ɗauke da hoton Album din nan, dama already sarkan yana wuyan ta bata cire ba, Anty Sarah kuwa kurawa gidan ido tayi, tana jin ƙwaƙwalwar ta na tariyo mata zuwan ta na farko, duk da akwai yan sanjin gine-ginen a layin, hakan kuma yasa gidan ya bace mata tun zuwan ta Gombe, ta wani ɓangaren kuma taji dadi, domin wahalar ta bata tafi a banza ba, tunda gashi Allah ya haɗa ta da Abraham.



Da sallama ɗauke a bakin Aysha ta shiga gidan, tsakar gidan su a tsaftace ko tsinke babu a kasa, Inna na zaune fess da ita tana soya wainar masa da su Anwar suka ce ita suke so yau.



Salati Inna ta yi a lokacin da ta ga Aysha, ko sallamar ta kasa amsawa tayi
"Indoooooo lafiya, mezan gani haka? Amarya da fitowa a washegarin kai ta gidan miji"


Murmushi Yake Aysha tayi tace " kwantar da hankali ki Inna, muna tare da shi ne"


"Ya Salam! in ce ba wani abu kika yi ba, lafiya ko?" Inna ta tambaye ta a dame.



"Banyi komai ba Inna, sai dai ba lafiya"





"Innalillahi wa Inna illahi raju'un, ku shigo toh Allah ya yi mana magani"

Inna ta fada hankalin ta a tashe, dama suyar karshe take yi, hakan yasa ta kwashe bayan ya soyu ta saka a kula, sannan ta ɗora kular miyan taushe da ta jima ta gamawa a sama ta wainar ta kai daki...


Ta ɗan gyara inda ya bace garin suya kana ta shige dakin baffa ta zauna tana jiran su shigo... tana zama kenan ta sake jin anyi sallama.




Aysha ce ta fara shiga ta zauna kan babban sallayar dake shimfid'e a kasa, sannan Abraham ya shigo, cikin karfin hali ya tsunkuyar da kansa alamar girmamawa ga surukar sa yace

"Good afternoon ma"



Inna da bata san abinda ya ce ba, amma daga yanda yayi ta fahimci gaishe ta yayi, kuma duk da bai tsugunna ba, hakan bai sa ta damu ba, domin ta san cewa kila ba al'adar su bace, ko kuma bai saba da hakan ba.

Kuma abin da ya sanyaya ranta shine ganin Abraham mai hankali, domin yanayin sa ya nuna cewa shi din mai nutsuwa ne, ya kuma dace da mijin Indon baffan! hakan yasa hankalin ta kwanciya, ko ba komai ta san kalar mijin da diyarta ta aura.



"Yawwwa sannu ku da hanya, zauna ko" tace wa Abraham.


Bai ji abinda ta ce ba, Aysha ta kalli shi, a hankali tace masa"Inna said you should sit down" ba musu ya zauna, Anty Sarah dake gefe a tsaye Inna

Please Login or Register in order to submit comment