Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya nuna min cewa tabbas akwai muradi da fatan cigaba da rayuwar sa domin ya cimma wani babban buri nashi"





Gaban madam Gloria ya yi wata mahaukaciyar bugawa, she can't believe that Abraham yana raye, despite the fact that yaci gubar nan...

"This is unbelievable" ta fada a ranta yayinda gumi na tashin hankali ya tsatsafo a goshin ta.


Ba tare da ta San maganar ya fito fili ba tace "doctor kana nufin bai mutu ba, yana raye?"



Murmurshi doctor yayi ba tare da ya lura da yanayin kuncin da take ciki yace "kinyi mamaki ko? Ni kaina da abokan aikina munyi mamakin hakan qwarai, domin Bamu taba haduwa da patient hero(jarumi) irin wanna ba, yanzu dai yana dakin hutu, kuma karfin gubar ya tsinka masa y'ay'an hanji hudu, a cikin sa, wanda hakan yasa bazai iya tsaye kan kafafunsa yanzu ba, amma hopefully zai iya tashi in sha Allah matukar an dage da yi masa magani da kula da lafiyar sa"




Wani dunkulallen abu madam Gloria ta hadiya, hakika mutuwar sa kawai taso ji, "na rasa wani irin taurin rai ne da wannan yaron, ace duk karfin gubar nan bai mutu" ta fada a ranta kana ta maida kallon ta ga doctor, ta ga hankalin sa na kan cike wani file, cikin sauri ta fice daga asibitin gabadaya...



Sai washegari madam Gloria ta dawo asibitin, amma ba a bata damar ganin Abraham din ba, a takaice dai sai bayan sati hudu aka fito dashi daga dakin hutu, inda aka turo Abraham kan keken guragu zuwa waje, saboda baya iya tsaye kan kafafun sa, gashi ya dawo so cool baya fiye da baya, ko yin magana baya yi, domin babu yanda doctors basu yi ba, amma baya cewa komai, kullum kanshi na duke.



Da taimakon driver aka saka shi cikin motar da wasu doctors, kana suka fice daga asibitin.



AYSHA
Zaune take a dakin ta tayi zuru-zuru kullum cikin tunanin halin da Abraham ke ciki take, burinta kada wani abu ya same shi, bata San yanda zatayi ba, kullum raba dare take tana tunanin halin da yake ciki hadi da sa shi cikin addu'oi'nta, gashi ko ganin madam Gloria ta daina yi tun daga ranar da Abin nan ya faru.



A karo na ba adadi ta shara hawaye, dama ita mai rauni ce da Sanyi, amma yanzu raunin ta da sanyin ta sun karu fiye dana baya, tana cikin haka taji an danna horn, a zabure ta Mike tsaye hadi da dafe kirjin ta daya tsananta bugu, cikin sauri ta sauko kasa, wanda yayi daidai da turo Abraham da madam Gloria tayi zuwa cikin falon, a hankali aysha ta sulale kasa hadi da furta "Innalillahi wa innah ilaihi raju'un" ta kasa yarda cewa lafiyayyen Abraham data sani ne aka dawo turo shi kan keken guragu?

Wani mugun kallo madam Gloria ta jefawa aysha daya sa hantar cikin kad'awa, amma bata ce komai ba, domin burin ganin bayan Abraham ne a ranta yanzu, bata da lokacin bata wa, saman part din Abraham ta nufa dashi, kasancewar kuma benen ba mai tudu bane yasa ta hau saman da shi da kyar zuwa dakinsa kana ta sauko...



Aysha ta jima sosai tana kuka a wajen kana ta nufi dakin ta yayin da ta dafe kanta dake Sara mata sosai, kwanciya tayi tana sakin sheshek'a har wani wahalallen bacci yayi gaba da ita.



*BANGAREN ANTY SARAH*

Tana zaune har yanzu a asalin kauyenta, ta sanja sosai, domin Sam jin dadi da take a birni babu shi a kauyen, tayi duhu kamar ba ita ba, domin Matar yayanta take bi gona suna aiki tare, daga nan take samun yan chanji na kashe wa, kullum cikin damuwa da neman tuba take wurin Allah saboda zunuban data aikata, lokaci kawai take jira domin ta bayyana gaskiya....





*MADAM GLORIA*

Safa da marwa take a dakin ta yayinda take naushin iska da k'aurarran hannunta, irin na jin haushin nan, duk da cewa ta samu tayi nasara wanna karon a kan Abraham amma ba haka taso ba, so tayi ya mutu gabadaya...


Kwarab kake ji ta zube a gadon ta kana ta kada kai da harshe irin na zallan muguntar nan tace "a Sannu zaka karasa mutuwa matuk'ar ni Gloria ina raye"



Sai bayan la'asar ta tashi daga bacci, inda ta ji ciwon kan ya dan lafa kadan, tuno cewa bata yi azahar ba ga la'asar yasa ta Mike a hankali ta shiga toilet, alwala ta dora kana ta fito ta shiga yin sallah, Bayan ta iddar ta zauna tayi addu'ointa sosai kana ta Mike bayan ta dan yi tilawa kadan.


Kitchen ta nufa inda tayi musu abinci cikin kasa da awa biyu, gyara kitchen din tayi ta mayar da komai muhallin sa, abinci ta jera a dinning table kana ta bar wajen zuwa sama, har ta wuce taji cewa ya kamata ta leka dakin Abraham, duk da faduwa da gaban ta keyi amma haka ta shanye tsoro da fargaban da take ji ta murda kofar dakin, bakin ta dauke da sallama....



Zaune ta ganshi kan wheelchair kanshi na duke, tausayin sa mai yawa take ji na ratsa zuciyar ta, a hankali ta fara takawa zuwa gareshi, yayinda ko wani taku da zata yi yana tafiya da bugun zuciyar ta...




Bangaren Abraham ma kamar ko yaushe idan ta samu kusanci dashi ya kan ji bugun zuciya da wani yanayi da baya ji ga kowa sai ita...


Gaban shi ta tsugunna ta kama hannun wheelchair din, kanta a kasa yayinda ta kurawa kafar sa ido...



K'walla ta share, cikin rawar baki tace "ina wuni, ya jikin ka? dan Allah kayi hakuri ni kaina ban San abinda ya faru ba, k'wak'walwata ta toshe" ta karasa tana sakin kuka gwanin tausayi....


A hankali ya dago kansa yana jin kukan ta har kasan rashi, be San me yasa yake jin ta special ba a ransa, amma tuno poison din daya ci daga Abincin data serving din shi sai yake jin wani Abu mai kama da rashin yarda da ita, duk da babu wanda yafi bashi zunzurutun mamaki kamar madam Gloria, amma so yake zuciyar sa da kunne sa su karyata masa abinda yaji madam Gloria ta fada kafin ya suma, ya kasa yarda cewa mummyn sa mai matuk'ar kaunar sa ce ke son ganin bayan sa, daya takurawa kanshi da tunani sai yaji brain dinsa kamar zai tashi daga aiki, sosai yake cikin pain mai tsananin gaske, komai ma baya masa dadi, yanzu ne kewar mahaifiyarsa, mahaifinsa, hadi da Nonyen sa mai tsananin gaske ke kara lullubeshi, baya manta tarin son da iyayen sa ke masa, haka zalika baya manta kulawar Nonye gareshi...





Shiru dakin ya d'auka, sai kukan Aysha dake tashi kadan-kadan, a hankali ta dago da niyyar kallon shi jin bai amsa gaisuwar ta ba, ta ma manta cewa shi din ko digon hausa baya ji, ita burinta kawai ya amsa mata domin ta samu salama a ranta, karaf idanunsu suka fada cikin na juna, cikin sauri tayi kasa da kanta, gaban ta na kara fad'uwa Sam ta kasa fassara kallon da yake mata, a hankali ta Mike ta fice daga dakin cikin sanyin jiki...



Da kallo yabi bayan ta yana sauke numfashi a boye, ji yayi zuciyar sa ta kuntata, dama zai iya tashi kan kafafun sa, domin ya San ta yanda zai gano wace makiyar sa? sannan meye laifin sa? domin har yanzu he is totally confused.



*7:55pm*
A daidai lokacin Aysha ta iddar da sallah isha, Bayan ta gama addu'oi'nta, ta yamutsa fuska kamar mai son yin shagwaba tace "ko ya ji abinci?β€œ domin bata ga madam Gloria ta hauro saman ba balle ta ce ta bashi abinci, mikewa tayi da hijab dinta zuwa down stairs, Bude duka warmers din tayi taga alamun an dibi abincicikan kuma ta San madam Gloria ce, amma still tana tsoro hakan yasa ta dauki wani spoon tayi loma daya na ko wani abinci, idan ma akwai Abin cutarwa a cikin abinci ita zai fara cutarwa, domin har ga ranta yanzu tsoron gidan nan take...



*30 minutes later*
Sai yanzu hankalin ta ya kwanta da Abincin hakan yasa ta dibar masa komai ta jera a tray ta nufi upstairs...




_Jiya nayi alkawarin posting, amma wani bacci mai dadi ya dauke ni da ban shirya zuwan sa ba, am so sorry for the inconvenience_.




Share and comment please πŸ€’


Noor πŸ¦‹
07082281566





Thank you for reading πŸ‡AbrahamπŸ“



I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851





πŸ‡πŸ‡ABRAHAMπŸ“πŸ“


*First edition*




*WATTPAD*
@NoorEemaan



https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din



_Making Dua for the others without knowing them is one of the exceptional beauties of Islam and in return, the angels would recommend to Allah for you. Keep praying. May this valuable day bring satisfaction in your heart and fill your life with the endowments of Allah_.

Happy New week my lovely fans




Chapter 33-34


Sanin cewa ba bata izinin shigowa zai yi ba yasa kai tsaye ta shiga dakin bakinta dauke da sallama as usually.


Gabansa ta ajiye tray din, kana cikin yanayin ta na Sanyi da nutsuwa ta fara serving dinshi cikin wani karamin bowl, Bayan ta gama ta dauke tray din ta ajiye a gefe, sannan ta kara matsowa daf dashi, spoon tasa ta dibi abincin ta kai bakinsa....



*ABRAHAM*
Kura mata ido yayi, yayin da wani yanayi mai kama da rashin yarda ya shiga ratsa zuciyar sa, amma gangan jikina sa taki yarda da hakan, Aysha kuwa ganin cewa har yanzu bai karba ba, yasa ta dago idanunta da suka cika taf da kwalla ta zuba masa, wanda ya sanya ruwan hawaye daya taru a idanunta suka diga kan abincin dake cikin spoon din hannun ta, tabbas ta fahimci yanayin sa kuma duk wanda yayi passing through irin abinda ya faru dashi hakan zai yi, saboda haka bata ga laifin sa ba, juyar da spoon din zuwa bakinta tayi, a nutse ta shiga tauna abincin har ta hadiye, cokali uku tayi, sannan ta kara diba ta kai bakin shi, Abraham daya kurawa kyawawan labb'anta ido tun daga lokacin data fara tauna abincin ya Bude bakinsa kamar wani karamin yaro ta zuba masa a baki ya shiga taunan abincin, hak'ik'a idan yace baya jin yunwa yayi karya, damuwa ce tayi masa yawa...


Aysha kuwa sosai taji dadi wanda har hakan yasa taji wani zallan dadi a ranta, hakan yasa ta cigaba da bashi har ya koshi, da ta kara debo na karshe ta nufi bakin sa dashi ya yi kasa da spoon din hannunta wanda yasa ta fahimci cewa ya koshi, ajiye cokalin tayi ta siyayi ruwa a cup ta dora masa a lips dinsa, ya Bude baki ya sha kadan kana ya cire bakin sa, tattara wajen tayi ta fitar da tray din kitchen, ta wanke komai, duk da cewa baya daga cikin aiyukan ta na gidan wanke-wanke.



Bayan ta haura sama, dakinta ta nufa kai tsaye, domin gajiya take ji a ko wani sassan na jikin ta, direct toilet ta shiga tayi wanka kana ta fito daure da towel a k'irjin ta, sosai skin d'inta ke shining, ga girma da ta d'an kara wanda hakan ya kara bayyana kyawun ta.




Hannunta ta daura a k'irjin ta-ta kurawa kanta ido ta mirror, sarkan nan mai dauke da sunan NONYE ta saka hannun ta daya ta shiga shafawa, sarkan na shinning tamk'ar yanda ta dauko a dakin baffa tuno baffan kuma yasa ta ji wani iri ba dadi ranta, sai dai tayi k'oka'rin k'awar da tunanin sa, inda ta shiga shafa lotion a sanyayye kan lallausar farar skin dinta, Bayan nan ta zira doguwar rigar roba ba tare da ta sa bra ba domin bata iya bacci da bra, wani farin hijab dinta medium size ta sanya kan kayan, kasancewar hijab din bai da hula hakan ya taimaka wurin bayyana gashin gaban kanta kwantaccen kamar na jarirai, kan gado ta hau ta kwanta tana nannade jikin ta tamk'ar mai jin Sanyi...


Lumshe ido tayi tana jin kewar su Innah, so take abubuwa su daidaita ta siyawa Inna da ita kanta waya koda karama ce domin ta dinga jin muryar su a lokacin da take so, ta fi mintuna arba'in tana sake-sake, sai kuma tunanin ta ya sanja ya dawo na Abraham, "yanzu idan yana bukatar wani Abu cikin dare ko anjima fa, wa zai bashi?" tayi wa kanta tambayar yayinda fuskar ta ke bayyana tausayin sa mai yawa...





Kamar Wacce aka tsik'ara ta Mike, hanyar dakin, sa ta nufa ta tura a hankali ta shiga, kallon tausayi tayi masa wanda hakan yasa hawaye suka cika idanunta, kamar yadda ta barshi, bai motsa daga inda yake ba, tunani tayi ko zai yi amfani da toilet, tunda shima Dan Adam ne kamar kowa, hannun ta - ta shiga murzawa tana tunanin Abin yi, domin ba jin yaren juna suke ba, bare ta yara masa.






Bayan sake-saken da ta Dan tsaya yi, bisa umarnin zuciyar ta ta nufe shi, a hankali ta tura shiga tura keken da yake zaune sak'amak'on zuciyar ta da ta bata umarnin yin haka, Abraham kuwa ko gezau bai yi ba, duk da cewa fitsari ya matse sa sosai amma saboda damuwa da halin k'uncin da yake ciki ya sa hakan bai dame sa ba.





Rufe kofar toilet tayi ta jingina kanta da jikin kofar, duk da cewa bata tab'a samun kusance da ko wani d'a namiji haka ba, in aka dauke baffan ta, amma tana jin Abraham har jininta, duk da cewa zuciyar ta na tsananta gudu a duk sa'ilin data samu kusanci dashi amma zuciyar ta da gangar jikin ta sun yarda hundred percent cewa ba zai taba cutar da ita ba, Sam bata jin bakon yanayi a tare da hakan, jin karan flushing yasa taji wani tausayin sa har hawaye ya gangaro mata, wato a matse yake tun dazu, amma bai nemi taimakon kowa ba, sai da ta kara mintuna goma sha biyar sannan tayi knocking hadi da turawa a hankali kamar mai Tsoron ganin wani mugun Abu, ganin shi zaune normal yasa ta tura keken suka fito, daidai bakin gadon ta tsayar da keken nasa sannan ta koma gefe ta hada kanta da guiwar ta...



Tsawon mintuna 5 dakin ya dauki shiru ba motsin komai, a hankali ya dago idanunsa ya zuba mata, sosai yake Jin wani yanayi na musamman da take kusa dashi, bai San abinda zai ce yana ji a tare da ita ba, amma tabbas yanayin bazai misaltu ko ya fadu ba.





Aysha kuwa tun tana duniyar tunani har jikinta ya fara saki sak'amak'on baccin daya fara dibar ta, gyangyadi ta fara yi gwanin burgewa da dariya wanda hakan ya kara bayyana yarintar ta, babu jimawa ta sulale kasan tiles din, wani bacci mai dadin gaske yayi awon gaba da ita ba tare da ta shirya ba.




ABRAHAM
Kallon ta yake tamk'ar ya samu hoto, domin ko kyafta idanunsa baya yi, kyawawan labban ta da ta tsuk'e yafi komai Jan hankalin sa musaman da ta dan turo shi gaba kad'an, cigaba yayi da Kallon ta har ya dauke idanunsa a kanta, ya Lumshe su hadi da yamutsa fuska domin ya gaji da zaman wheelchair din.




_1:22am_

Sanyin tiles ne ya shiga ratsa ko wani sassa na jikina sosai, wanda hakan yasa ta motsa hadi da ware idanunta, cikin sauri ta Mike domin Sam bata San cewa baccin ya dauke ta ba, a hankali ta kai idanunta kan shi, inda taji wani mugun tausayin sa, ace mutum tun safe yana zaune waje daya bai motsa ba.



Mikewa tayi kusa dashi taga idanunsa a rufe yana bacci, tunanin taimaka masa wurin kwanciya tayi, sai dai ta rasa yanda zata fara, domin shi din ingarman namiji ne, duk da cewa yayi jinya amma bai yi loosing weight ba sai idanunsa kadai da suka fada ciki....




Hak'ik'a ko wani bawa da zaka gani yace abu kaza yafi karfin shi, ko ya dinga tunanin anya zai iya? Toh sai dai idan mutum bai sa kansa ba, amma matukar kasa kanka Allah zai taimaka maka, domin ubangiji baya taba dora wa bawa Abin da yafi karfin sa...

Misali Kamar Aysha Kenan ta kara matso da wheelchair din kusa da gadon sosai ya zamana babu wani sauran space tsakanin gadon da kujeran, sannan tayi kamar zata kife kujerar da dukanin karfin ta, sai ya fada kan gadon, kasancewar gadon bai da mugun tudu sai fadi hakan ya sa ta samu saukin kwantar dashi, sai dai yayi ruf da ciki, tsaye tayi tana sauke numfashin gajiya kamar wacce tayi tseren gudu, zaman wheelchair din ta gyara kana ta rufe shi da duvet bedsheets, a hankali ta shiga takawa cikin sanda domin barin dakin gudun kada ya farka....




*ABRAHAM*

Sai da daya daina jin motsin ta kana ya bud'e idanun sa, da suka bata hours a Lumshe ba kuma dan bacci yake ba, duk abinda tayi yana jin ta, daga kwantar dashi data yi har zuwa fitar ta daga dakin, dan cije labb'ansa yayi saboda wani zafi da yake ji daga cikinsa, ba kuma komai ya janyo hakan ba sai irin yanda Aysha ta kwantar da shi, wanda kuma ya jinjina k'ok'ari da jarumtar ta, haka ya cigaba da jurewa har bacci ya dauke shi...




Manage pls, kaina ya dauki chaji, ban da time wallahi, ina wajen aiki, gashi yau ina Azumi, may be kuga typing errors... πŸ€’






Share fisabilillah

Comment



NoorEemaan
07082281566



I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851

πŸ‡πŸ‡ABRAHAMπŸ“πŸ“

*First edition*



*WATTPAD*
@NoorEemaan



https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din.




Chapter 35-36


*WASHEGARI*
Da safe sai da Aysha ta leko dakin sa taga yana baccin kafin hankalin ta ya kwanta, downstairs ta sauk'a domin d'ora musu breakfast, ta rasa meyasa ta damu dashi har haka, sosai maganar sa da fatan ganin ya samu lafiya ya tsaya mata a rai kwarai.






Tana shiga kitchen din babu bata lokaci ta fara hada breakfast, cikin har da light food da ta San cewa zai yi daidai da condition din Abraham yanzu.



Tana cikin soya potato omelet taji knocking daga bakin kofar, cikin sauri ta kwashe omelet din, domin already ya riga ya soyu, kashe gas din tayi ta wanke hannun ta a sink ta gyara wuyar hijab dinta ta fita izuwa kofar falon da aka kara knocking yanzu.










Tsaye taga wani saurayi mai kimanin shekaru 35 sanye da bak'ak'en suit. Da kallo ta bishi na yan seconds kana ta dauke kanta hadi da cewa "ina kwana" duk da bata taba ganin fuskar sa ba.



Saurayin kuwa cikin girmamawa ya russunar da kan sa, domin a tunanin sa Aysha Matar Abraham ce, duk da yaga alamun cewa ita din Musluma ce, amma ba Abin mamaki bane tunda hakan na faruwa, ma'aurata masu mabambamtan addin, kawar da tunanin yayi yace
"ina kwana Hajiya, suna na Kabeer Usman dama nazo neman sir Abraham ne, tun sanda ya dibi ma'aikata da kwana biyar Bamu sake ganin sa ba, ni ne personal assistant dinsa shine naso na duba ko lafiya domin na kira wayoyinsa basa shiga, yanzu ma ma'aikatan zan wuce na biyo ta nan"




Shiru Aysha tayi tana tunanin Kiran madam Gloria domin ita kam wanna abun yafi karfin ta, amma kasa da sixty seconds k'wak'walwarta ya bata cewa tun baya da madam Gloria ta dawo da Abraham daga hospital bata kara zuwa duba shi ba, shin ita wace irin uwa ce a gareshi? ta aiyana a ranta.



Zuciyar ta ce ta kara sauya tunani, kamar yadda yayi tunanin ita din Matar Abraham ce, a hakan zata tafiyar dashi, cikin sauri ta dago kanta duk da gabanta na faduwa sannan tana addu'ar kada Allah yasa madam gloria ta tashi daga bacci yanzu...




murmurshi tayi tace "ohh! Mijina ya bani labarin ka, ka shigo daga ciki"
tace tana juyawa izuwa ciki yayin da gabanta ke tsananta fad'uwa domin gani take kamar ba Indon baffa bace ke wannan abun, amma ta kasa sarrafa kanta, kamar Wacce ake bawa umarnin yin komai daga ta ciki.



Bayan ya zauna kan d'aya daga cikin had'add'un kujeran falon, kitchen ta shiga ta kawo masa shayi a kofin tangaran, kabeer Usman ya karba yana godiya hadi da yaba karamcin ta a ransa.


Aysha kuwa crossing legs dinta tayi tace "Am... kuyi hakuri bai sanar muku tafiyar sa ba, domin a gaggauce abubuwa suka zo masa, baya kasar shiyasa kuka ji shi shiru, tunda ya tafi nima jefi-jefi muke waya da lambar kasar domin baya da lokaci sosai, sakamakon Abinda ya kai shi kasar mai muhimmanci ne, sannan idan na samu lokaci zan zo duba kamfanin na ga yanda kuke gudanar da aikin, domin zai dauki watannin kafin ya dawo, duk da dama ya fada min cewa yana da mataimaki wanda zai iya kula da company's sa ko da baya nan wato kai, ina fatan zaki yi aiki tukuru wurin rike ragamar kamfanin da amana kamar yadda Mijina ya fada, ya kuma d'aura maka yarda"

Aysha ta karasa tana dan goge wani gumi daya karyo mata ya biyo ta gefen fuskar ta...



Shi kuwa Kabeer Usman murmurshin jin dadi yayi saboda kalaman ta na karshe, cikin kwarin guiwa yace "in sha Allah zan rike amanar company, har Allah ya dawo dashi, duk wani abu dake faruwa zan dinga tura masa ta gmail din sa".




"Na gode kwarai Malam kabeer Usman" Aysha ta fada, tana dan mazewa wanda hakan ya kara mata kwarjini, kai kace wata babbar mace ce.



Kabeer Usman kuwa kara sipping tea dinsa yayi, domin yayi masa dadi over, kana ya Mike yana goge bakinsa, sallama yayi wa Aysha ya nufi hanyar fita daga falon, inda Aysha ta take masa baya har izuwa bakin kofar falon kana ta dawo ta zube kan kujera tana sauke numfashi, sosai ta jinjina karfin hali irin nata, tuno cewa madam Gloria zata iya fitowa at any time yasa ta dauki kofin shayin data zuba wa P.A ta nufi kitchen, wanke wa tayi ta mayar muhallin sa kana ta shiga gyara kitchen din, tana kokarin jera warmers a tray taji takun takalmin madam gloria na tunkaro kitchen din...



Cikin sauri hadi da girmamawa ta shiga gaishe da madam Gloria, a yatsine ta amsa kamar yadda ta saba, Bude warmers din ta shiga yi, kana ta juya domin fita, har ta je bakin kofar kitchen din ta juyo cikin gurbataciyyar hausar ta tace "wa ya shigo gidan. nan dazu"



Waro ido Aysha tayi gabanta na fad'uwa, a hankali ta juyo tace "babu wanda ya shigo..." ta karasa cikin aro jarumta, ita kanta bata San dalilin boye mata ba, amma hakan zuciyar ta ke bata umarni.



"babu wanda ya shigo kika ce ?" madam Gloria ta fada tana bin fuskar Aysha da kallo a kokarin ta na son gano gaskiyar maganar ta.




"eh madam!" Aysha ta kara fada cikin dak'ewa fiye da dazu.

Kallon ta madam Gloria ta sake yi na mintuna biyu kacal kana ta jinjina kai tace "zo kiyi serving dina breakfast, zan fita yanzu"...



"toh" Aysha ta amsa tana cigaba da jera warmers din, a ranta tace

"na shiga uku ni Aysha, Mata da danta amma nafi zak'ewa akan al'amarin da ban San mafari ba" ta fada a hankali.



A sanyaye ta fita, ta serving madam Gloria kana ta haura sama domin yin wanka.


Tana cikin shiryawa taji fitar madam Gloria a mota, karasa shiryawa tayi a nutse kana ta leka dakin Abraham, kokarin mikewa taga yanayi amma ya kasa, instead sai ma zafi da yake ji, a sanyaye ta mayar da kofar ta rufe domin dama kadan ta bude shiyasa bai lura da ita, downstairs ta sauka, daga nan ta fita izuwa farfajiyar gidan, wajen mai gadi tace

"ina kwana"



"ah ah Indo ce,

Please Login or Register in order to submit comment