Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sa da ta sauya, wanda akan ta ne ya fara Jin hakan, mamaki yake kan meya kawo yarinyar cikin gidan su har dakinsa.




Jikin ta na bari, cikin rawar murya tace "ehm... Is your, is na mahaifiyar ka ta ce kazo kasan bene" ta fada cikin duburbucewa idanunta taf da k'walla...



Yamutsa fuska yayi domin ko kalma daya bai fahimta daga abinda tace ba, a hankali ya bud'e idanunsa da suka dan rine saboda jimawa da suka yi a rufe ya sauke su a kwanta, sai dai bayan ta kadai yake hangowa, ita kuwa jin bai sake magana ba yasa ta fita da gudu, ta nufi dakinta dake da dan nisa da nashi duk da saman bene ne.




ABRAHAM kuwa da kallo yabi bayanta, kana ya tabe bakin sa hadi da mikewa tsaye, toilet ya nufa domin yin wanka, shower ya kunna inda ruwan ya shiga dukan kansa zuwa jikinsa, a hankali muryata ya amsa kuwa a kunne sa "Ammarrr" ya maimaita kalmar can kasan makoshi, duk da bai san ma'anar sa ba, kawar da tunanin yayi ya cigaba da wankan sa inda mintuna ashirin ya dauka kana ya fito daure da farin towel.




Tsad'add'en lotion din sa ya shafa, kana yayi oiling kansa hadi da tajewa, gaban wardrobe din sa ya nufa, inda wayar sa ta fara ringing... Dubawa yayi ya ga MUM ce.

Amsawa yayi hadi da karawa a kunne sa,,
"Good morning Mummy"

"morning my son, I sent the house-maid to tell you breakfast is ready and.........."

"am coming mum" ya fada yana katse Kiran ba tare da ya bari ta karasa maganar ta ba, sai yanzu da mummy ta fada ya san dalilin shigowar Yarinyar nan dakin shi, wardrobe din ya bude ya fito da wani crazy Jean trouser white, sai bakin riga mai botira hadi da dogon hannu, cikin mintuna biyar ya shirya cikin su, gaban inda tarin takalman sa suke ya nufa ya dauki wani black palm sandals na company dolce and gabbana ya sanya, agogon zallan sliver ya manna a hannun sa, ba karamin kyau mai tsayawa a rai yayi ba , Bud'e kofar yayi ya sauko kasa...




Aysha da ta kasa kunne, jin motsin ya fito ya sanya ta fitowa da sauri, duk da faduwar gaba da Tsoron da take ji amma dole ta gyara masa dakin tunda aikin ta ne, baya ga haka bata ma so abinda zai hada ta da madam Gloria, dakin sa ta koma ta fara gyara falon da sauri² inda ba wani datti yayi sosai ba, bedroom dinshi ta nufa shima ta gyara kana ta yi mopping a ranta tana mamakin yanda ya iya kwanciya kan uban sanyin da tiles din ke da shi, domin ita kafar ta kadai dake taka shi yanzu ya sa ta jin Sanyi.



Bayan ta gama, ta wanke toilet ta fito, wani kofa ta gani by the left, Bude kofar tayi ta ga kitchen ne, a gyare yake babu wani datti, wani kofa ta sake gani ta cikin kitchen din ta bi, take ta bayyana a gyming room dinshi wanda ke gyare tsaf, "Dama makeri ne shi" ta fada tana kallon karafunan da abubuwan motsa jikinsa, wanda ita bata San amfanin su ba.





Sosai ta shagala ta kallon dakin motsa jikin, can ta tuno cewa zai iya shigowa yasa ta fita cikin sauri, dakinta ta koma tana sauke ajiyar zuciya, yayin da har yanzu tana mamakin wannan kammanin, daga kashe dai ta basar, tasa a ranta cewa kawai kama ce....




ABRAHAM kuwa tea kawai ya sha, dama shi ba ma'abocin cin abinci bane sosai, madam Gloria tayi-tayi yaki ci, dole ta hakura, fita yayi zuwa unguwar rimi, domin so yake ya je su yi magana da wani attajiri mai harkan filaye wanda ya ga ya dora wani fili mai girman gaske a Instagram din shi wanda na siyarwa ne, wanda tun yana dubai yaga tallan, luckily kuma yaga kaduna state ne , so yake ya siya domin ya gina company a nan kaduna, wanda hakan zai yi keeping dinsa busy...





Babu jimawa da fitarsa professional chef din da zata fara koyawa indo girki-girki tazo mai suna miss Zaynab Akindele yar jahar ogun ce, ba bata lokaci madam Gloria tayi Kiran Indo ta sauko suka shiga kitchen....



____________________




*Gombe State*

Bangaren su innah kuwa sosai suke fama da tsananin kewar Aysha indo, bare ma su Anwar, ranar farkon da basu kwana da Ammuh din su ba, cikin dare Inna ta ga ta kanta, domin zazzabi ne ya rufe su, babu abinda suke kira sai Ammuh! Ammuh! Suna kuka, innah bata taba sanin cewa haka suke da Wayo ba, domin ta yi iya yinta sun ki hakura...




Washegari da asuba zazzabin ya sauka, suka fara dan wasan su, amma abu kadan sun kira sunan Indo ko su je dakinta, lallaba su innah ta dinga yi tana musu Wayo da haka ta samu dan sauki.




★★★







*KADUNA STATE*

Kiamanin sati daya Kenan da miss Zaynab Akindele ta fara koyawa Indo girki, kuma ba laifi tana fahimta sosai wanda hakan ke sa miss zaynab kara himma wurin koya mata, domin ita macece mai son ta koyawa mutum abu ya dauka da wuri, ta bangaren Aysha kuwa tana jin nishadi a duk lokacin da ake koya mata girkin, karin dadi kuma miss Zaynab na jin hausa sosai duk da kasancewar ta yare, wanda hakan ke sa Indo saurin fahimta.




Ta bangaren Abraham kuwa yayi nasaran siyan filin nan, inda babu bata lokaci aka fara gini, abinka da kudi, sosai ya zama busy baya samun zama...




Ta bangaren madam Gloria kuwa tana nan tana shirya yanda zata kashe Abraham, sai dai kwatsam wani tunani ya zo ranta yasa ta dan dakata, domin tabbas Abraham ya wuce duk tunanin ta, shi din ta kasa kashewa har yanzu saboda taurin ransa, da asirin ta ya tono a idon duniya bata more dukiyar da ta dade da burin mallaka ba gwara ta sanja salo, sai kawai ta yanke shawarar amfani da AYSHA Wacce tasan yar gidan talakawa ce, domin kashe shi, ko da bincike yayi bincike aysha za a kama...





KO TA YAYA MADAM GLORIA ZA TA YI AMFANI DA AYSHA WURIN KASHE ABRAHAM??? KU BIYO ALKALAMIN NOOR...✍️😊




Share✅
Comment ✅
Vote ✅




Editing is not allowed❎





NoorEemaan🦋
07082281566



Thanks for reading my novel 🤝
🍇🍓ABRAHAM 🍇🍓




I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851



🍇🍇ABRAHAM🍓🍓


*First edition*


https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din


*WATTPAD*
@NoorEemaan


*NOTE*
*_dan Allah masu tura Abraham Daga page 30 zuwa gaba ku daina, kuna rudar min da reader's, ina ta samun tsakonnin a yau saboda kun fitar fiye da page din dana tsaya, Ni a page 23-24 na tsaya, baku fini son Ganin na kamalla posting din ba, mun sani cewa Abraham ba sabon typing bane, idan kin san kin karanta complete Fyn, ba sai kun turawa mutane ba, alhalin Ni ban zo wajen ba, saboda irin wanna issues din yasa ban mayar da complete ba tun da Yawan mutanen da suka bukaci hakan, saboda Wani dole Sai ya fitar, ina da both pages da document complete Amma ban mayar ba Saboda kada a rude, Ina bada pages biyu kullum still hakan bai isa ba har sai an tura daga Page 30 zuwa karshe, wasu ma pages din a hargitse, Dan Allah ku bari nayi reposting din yadda na tsara abu na, da sannu zamu gama Kamar yau, na san kauna ce tasa kuka yi haka, amma wasu na shiga rudani, ɗan Allah in dai ba daga farko zuwa inda Ni na tsaya aka nema ba, karku fitar, duk wanda baxai Iya jira ba, ya je Wattpad akwai complete a can, ngd habibte's_*🫶💖



Chapter 23-24

(Not edited)



Kimanin wata daya da kwana biyu Kenan da zuwan Aysha gidan su Abraham, inda yanzu ta iya kalolin girki² da Dama, domin miss Zaynab akindele na matukar Kokarin wurin koya mata musamman da ta ga Aysha na da interest akai.




Da safe ita ke preparing musu breakfast, haka zalika dinner, inda na rana ne kawai suke yi tare da miss zaynab, domin madam gloria ta kara cika miss zaynab da kudi kan ta kara koyawa Aysha har na tsawon wata uku gabadaya Kenan domin ta kara zama expact.





Ta bangaren Abraham kuwa ginin company'sa yayi nisa sosai saura kadan, kasancewar k'wararrun ma'aikata ya dauka masu sanin
makamin aiki...




____________________




Misalin karfe biyar na yamma Aysha na zaune saman bed dinta, ta kara kyau kana jikinta ya murje, duk da cewa har yanzu mai gurguwa take shafawa amma skin color dinta ya fito tarr yana shining sak'amak'on Air conditioner da take kwana tana wuni da shi.



Albashin ta da madam Gloria ta bata, ta kurawa ido... hawaye suka zubo a kuncin ta, a lokacin da madam Gloria ta bata kudin to tsorata, domin bata taba ganin kudi masu yawa haka ba balle ta rike, Wai yau ita ce ke da wanna tarin kudin...

"Alhamdulilahil-lazee tatimus solihat" ta fada a hankali hadi da mikewa, kudin ta mayar cikin farin envelope din da aka rubuta sunan ta da biro b'aro,-b'aro a kai, hijab dinta ta sanya kana ta sauka kasa, babu kowa a falo sai plasma dake ta yi shi kadai, waje ta fita inda tun zuwanta gidan bata taba fitowa ba, gaisawa suka yi da mai gadi ta fita da sauri domin so take ta yi ta dawo domin ta dora dinner.



Gidan da bintu take aiki ta nufa, k'wank'wasa Dan karamin kofar tayi, Bayan minti biyu mai gadi ya leko hadi da tambayar ta wa take nema, ta sanar da shi, ya Bude mata ta shigo hadi da nuna mata hanyar da zata bi domin yaga bakuwar fuska ce, bata San kan gidan ba.





Bakin kofa ta tsaya hadi da yin knocking, jim kadan wata yarinya ta bude Wacce aysha ta tabbatar itama yar aiki ce, bakinta dauke da sallama cikin siririyar murya ta shigo inda kamilar dattijuwar mata mai sanye da medicated glass ta amsa hadi da binta da kallo irin ban gane wanna fuskar ba, fahimtar hakan yasa Aysha kara so gabanta, durkusawa tayi ta gaishe ta hadi da sanar mata cewa tazo wajen Adda bintu ne.



Murmushi Matar tayi daya bayyana hakoran makkah ta biyu sliver da golden dake gefe da gefen hakorin ta kana tace "ke kanwar tace ko?"


"Eh" Aysha ta amsa mata kawai tana mayar mata da martanin Murmushi.


"masha Allah, bari na kira ta a waya domin suna can suna kiciniyar hada dinner" ta fada tana latsa tsad'ad'iyyar wayar hannun ta....


Mintuna biyar kacal bintu ta fito, ganin Aysha yasa ta kara fad'ad'a Murmushin ta...


"yau Indon baffa ce ta fito da kanta" bintu ta fada cikin zolaya.



Murmushi Aysha tayi tace "wallahi Addah, an biya Albashi ne, kin ganshi nan" ta dora mata a cinyar bintu kana ta cigaba
"ina so kudin su isa ga Innata basan ya zan yi ba"


Jinjina kaifin tunanin Aysha, bintu tayi a ranta, a fili tace "kinyi tunani mai kyau Indo, hakika kin cika y'a ta gari, abinda za a yi shine zan karbi cash din hannun ki, sai na yi wa jauro (kanin bintu) transfer yaje bankin cikin gari ya cira gobe ya bata tunda ya iya, dama gobe ina son zuwa bankin na ciri kudi, Kinga na huta, yanzu nawa kike so a tura mata? “


"duka Addah"

Dariya bintu tayi tace "A'a² ba za a yi haka ba, kin San fa kin girma yanzu, dole zaki kula da kanki, siyan pad, man shafawa, man gyaran gashi, da Dan kayan sawa haka Kinga duk kina da bukatar su, abinda za a yi shine za a tura wa Innah wuro dubu hamsi, saura dubu ashirin din sai a yi miki siyayyar dashi ko, gobe zanzo na yi wa madam magana kan zamu je kasuwa dake"



"toh Addah, Kema ki cire kudi a ciki kiyi amfani dashi"


"a'a² Allah ya kiyaye indo, tamkar kanwata ta jini na dauke ki, duk abinda na yi miki saboda Allah ne, dan haka ki bar kudin ki Nagode kinji"



"toh Addah Nagode Allah ya biya ki, amma nayi kewar Innah ta sosai da su y'ay'ana" ta fada hawaye na ciko idanunta.


"shagwaba ko? Toh Karki damu zan fadawa jauro idan ya kai mata kudin ya kira wayata a wajen sai na hadu ku, ai shikenan ko? "

Da farinciki Indo ta koma gida, jin gobe za ta yi waya da Innar ta, a k'age take goben yayi, cikin kwarin jiki da bata taba irin sa ba tun zuwan ta gidan ta shiga dora musu dinner.



*WASHEGARI*

Kamar yadda bintu ta fada tazo wajen madam Gloria tare da rokon Alfarma kan ta bar Indo su Je kasuwa, bata hana su ba, sai dai cikin isar da ji da kai ta ce Indo ta dawo kan lokaci...



Basu jima da hawa keke-napep ba, sai ga Kiran jauro, danna answer bintu tayi hadi da sallama, amsawa jauro yayi suka gaisa kana yace ga Inna wuron, amsa Inna tayi ta fashe da kuka, kana ta shiga yi wa Allah godiya, sannan ta dora da yi wa bintu godiya sosai hadi da yi mata addu'oi'n fatan alkhairi...




"Bakomai Inna, ai yi wa kaine, ga Indon" abinda bintu tace Kenan tana kara wayar a kunnen Aysha....




Rike wayar gam Aysha tayi a kunnen ta, kana cikin murya mai nuna zallan kewa da son mahaifiyar ta tace "Innata... Nayi kewar ku sosai" ta karasa tana sakin kuka....



Itama Inna, hawaye ne masu Sanyi ne suka zubo mata sak'amak'on jin muryar tilon yarta, "munyi kewar ki sosai Indon baffale, yi shiru Karki tada min hankali, kina lafiya dai ko?"


"eh Innata" ta amsa.

"toh alhamdulillah,na ga abun arziki, Allah ya miki albarka ya tsare min ke, Sannu yar albarka kin ji ko? "


"Ameen Innata kin cancanci fiye da haka, albishirin ki Inna? Aradu na iya kalolin girke² irin na yan birni masu dadi, idan na dawo zan yi mana shi ki ci, ki ji dadi ke da yan biyu na" ta fada cikin sakalci da kuruciya.




Dariya Inna tayi tace "toh Allah ya kowa mana ke lafiya, gashi kin aiko mana da duka albashin ki, dame zaki yi amfani?"


"ai inna da ragowar dubu ashirin, albashina dubu saba'in ne fa"



"saba'in!!!" Inna ta maimaita cikin mamaki hadi da zaro duka idanun ta waje.




"aradu Inna, mun zama masu kudi" tilas Bintu dake gefe tasa dariya, indo ba dai sakalci ba.


Itama Inna Dariya tayi a ranta tana kara godewa Allah, a fili tace "ga y'ayy'an ki nan sun ishe ni da Kiran Ammuh"


"wayyo Ammar da Anwar dina, nayi kewar su Inna ki bani su naji muryoyin su"





Anwar aka fara bawa wayan, banda Kiran Ammuh da gwaracin sa babu abinda yake, Lumshe ido Aysha tayi, kewa hadi da tsananin son yaran ya kara shiga zuciyar ta..


bayan nan aka bawa Ammar shima sai Dariya yake saboda jin muryar Ammuh dinsu, kuma abun mamaki sun gane ita ce, itama Aysha take ta tuno tsananin kaman Abraham da Ammar din ta, ta so bawa Inna labari sai tayi shiru.



Zuciyar Indo fess saboda jin muryar su Inna da ta yi, ba dan ta so ba, bintu ta kashe wayar, Bayan ta cewa jauro zata turo masa kati...



Daga bangaren Inna kuwa Dubu Biyu ta bawa jauro daga cikin kudin inda da kyar ya karba, kana yayi godiya ya tafi, itama innah bashin da ta dan ci ta biya, kana tayi musu siyayyar kayan Abinci masu yawa, sabulun wanki, sabulun wanka, man shafawa, man goge baki, har sabbin kaya ta siya musu masu saukin kudi sosai, ranar har da namomi cikin Abincin da suka ci..... (ni Noor nace talauci Nesa da mu ooo, arziki zo nan ga😹💔)




Su Aysha kuwa sha biyu saura suka dawo gida, inda bintu ta taya ta zaban man shafawa da ta San zai karbe ta da sabulun man, sai toothbrush da tooth paste, kayan make up, turare, palm shoe guda daya, sai wasu roba² ready made gown guda biyu masu saukin kudi......

Wanna Kenan.




____________________


*1 WEEK LATER*
_5:56 am_


Zaune take kan sallaya, ta tankwashe kafafunta, yayin da take rike da Kur'ani tana rera karatu cikin suratul-tawbah, cikin sanin ya kamata take bawa ko wani harafi Hakkin sa.., kasancewar kuma gari bai waye ba, ko ina yayi shiru yasa amon zazzak'ar muryar ta ke fita....



A kuma daidai lokacin ne Abraham dake gyming room din shi yana daga karfe ya fara jin tashin muryar ta na shiga kunnen sa, cak ya tsaya da abinda yake yi, hakika zai iya rantsewa bai taba Jin dadin wani abu a kunne sa kamar karatun da Aysha'n ke yi ba, duk da bai San menene ba, bai San me take cewa ba, bai kuma fahimci ko harafi daya ba, amma yana matukar son abinda take fada, Lumshe ido yayi, yana jin yanda ko wani mahuda na gargasan jikin sa ke mikewa, yayin da wani Sanyi ya fara shigar shi slowly, duk da gumin daya hada saboda motsa jikin da yake yi....



A hankali ya dire karfen a kasa, kana ya Bude lumsassun idanun sa hadi da bude kofar ya fita, bai San me yake yi ba, kawai dai ya tsinci kan shi da bin hanyar da yake jin sautin muryar ta...., duk taku daya da yayi, yana kara jin sautin muryar ta na kusanto shi, kana bugun zuciyar sa na karuwa....✍️






_kuyi manage da wanna please, wallahi am so so tired today, meye ra'ayinku kan wanna episode din? Mu hade a next page_....





Share fisabillahi✅
Comment for more typing.✅



Noor🦋



Wednesday, 2 February 2022


I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851



🍇🍇ABRAHAM🍓🍓

*First edition*




*WATTPAD*
@NoorEemaan




https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.




_Am so sorry for keeping you guys waiting, na San ba dadi, kun jira ni da yawa, amma ba laifi na bane, ban ji dadi bane kwana biyu, ga ba lokaci, amma kuyi hakuri in sha Allah bazan kara jimawa irin wanna ba, har in gama Abraham, ngd sosai da kokarin jirana da kuka yi🙏 much luv masoyan NoorEemaan_😍




Chapter 25-26


Cak! ya tsaya a lokacin ya isa bakin k'ofar dakinta, inda a yanzu amon sautin zazzak'ar muryar ta ya fi tashi, hannu yasa kan handle din kofar a kokarin sa na son bud'e kofar, sai kuma yayi saurin d'auke hannun sa hadi da murza su cikin na juna, a hankali ya jingina bayan sa da kofar dakin ta, sannan ya Lumshe k'yawawan idanun sa yana cigaba da sauraron kira'ar ta mai dadi....


Sosai ko wani mahuda na gashin jikin sa suka kara bude wa, kasancewar yanzu yafi kusanci da ita, wani yanayi mai kama da zubar tsigan jiki, da Sanyi ya shiga ratsa shi...



*40 Minutes later*

Wanda yayi daidai da lok'acin da Aysha ta rufe qur'anin ta, kana ta shiga yin addu'oi'nta...

A kuma lokacin ne Abraham dake tsaye a bakin kofar ya sauk'e wata k'arfaffar ajiyar zuciya, kana a hankali ya bud'e lumsassun idanunsa da suka dan rine sak'amak'on jimawa da suka yi a rufe.



Cikin yanayi mai kama da rashin jin dadin ya yamutsa fuska tamk'ar yaro dake son wani abu daga mahaifiyar sa, haka nan yaji ba dadi a dalilin daina jin amon sautin muryar ta dake rera karatun qur'ani.
A karo na biyu ya kara sauk'e numfashi kana cikin tafiyar sa ta ingarman na miji mai ji da lafiya da kuruciya ya bar wajen...



Aysha kuwa bayan ta iddar da addu'o'in ta ta Mike, a gaggauce ta shirya kana ta sauko kasa ta fara shirya musu had'add'en breakfast mai rai da motsi tamkar ba Indon baffa ba.



*********



9:00am.

ABRAHAM tare da madam Gloria ke zaune a had'add'en dinning area suna jiran Aysha tayi serving din su, a hankali cikin takun nutsuwa Ayshan ta fito daga kitchen hannun ta dauke da plates na tangaran da zata yi serving dinsu dashi...




Jin kamar ana kallon ta yasa ta a hankali ta dago kanta idanunta suka fad'a cikin nashi, gaban ta ne ya bada dam! Domin tun lokacin da ta fara serving madam Gloria abinci yau ne karon farko data ganshi a dinning table, gabadaya ji tayi idanun sa na yawo a jikin ta wanda hakan yasa jikin ta fara rawa domin sosai yake ladabtar da ita da sexy eyes d'insa masu masakaicin girma, hannunta ne ya fara rawa, ba tare da zato ko tsammani ba plates din suka kufce daga hannunta suka tarwatse kan tiles din...


A zabure madam Gloria ta mike, hadi da daga lukutan hannunta da niyyar marin Aysha da ta k'amk'ame jikin ta sannan ta runtse idaunta...



Ganin yasa Abraham mikewa, taku biyu kacal yayi ya kamo hannun madam Gloria ya sauke, kana ya kalle ta, ba tare da yace komai ba ya koma kan kujerar sa ya zauna, yana k'ark'ad'e hannun sa saman dinning table din...




Da kallo ta bishi kana tace "why son? Meyasa zaka hana ni? Daka barni na nunawa wanna Bush Village girl din hankali"

Juyawa tayi ta ga Aysha tace "ke! Baki da hankali ko? what's your problem? Hannun ki ciwo yake? Kina abu kamar zararriya, bari in gaya miki, this should be the last time da zaki kara fasa min plate, kin San nawa each one?... “




" mummy plssssssssss" Abraham ya fada a dake, yana rike da kansa, haka nan yaji fad'an da take wa Aysha na bata masa rai, be San mai dalili ba, baya ga haka shi mutum ne mara son hayaniya...




Shiru madam Gloria tayi, ta zauna tana sauke hucin bacin rai, amma ba halin magana, domin ta San Abraham kaifi daya ne, sannan ta yi Controlling kanta ne domin kada tsanar da take wa Aysha ya fito b'aro-b'aro, saboda har ita kanta Ayshar bata so ta San cewa ta tsane ta, ta kuma tsara hakan ne domin plan din ta ya tafi daidai yanda ta tsara...





Indo kuwa runtse idanunta tayi tana jiran sauk'ar mari, jin shiru ne yasa ta Bud'e idanunta cikin mamakin rashin marin da madam Gloria bata mata ba, cikin sheshek'ar kuka ta dauko Abin shara da Abin kwashewa ta shiga tattare fasashen plates din, cikin rashin sani ta taka wani fasashen plate...

Kara ta saki, inda a tare ita da Abraham suka runtse idanun su, wanda shi kanshi bai San yayi hakan ba.....



Saboda d'auriya irin na Aysha, ta kuwa Mike ta karasa tattara wajen ba tare da ta damu da cire broken plate dake tafin kafar ta ba.



Cikin k'ok'arin shanye zafin da take ji ta koma kitchen din ta dauko wasu plates din, wanna karon Sam bata yarda sun hada ido ba, duk da yanda take jin idanun sa na yawo a kanta, a nutse ta fara serving dinsu, amma tayi kokari matuka wurin controlling kanta domin sosai hannun ta ke rawa....





Bayan ta gama, ta jaa kafar ta zuwa sama tana zub da hawayen da bata San koma menene ba, domin indai fada da zagin madam Gloria ne ta fara sabawa, har hakan bai fiye damun ta ba...



Kan mad'aid'aicin bed dinta ta zauna tana sauke nishi, kafar ta daya ta d'ora kan dayan da niyyar cire k'walban, amma ta kasa saboda zafin daya ziyarci k'wak'walwarta....



Kwanciya tayi a gadon ta cigaba kuka, har wani wahalallen bacci da bata shirya zuwan sa ba ya dauke ta....



Ta bangaren Abraham kuwa, hakan nan yaji ransa ba dadi a dalilin abinda ya faru, duk da dadin dandanon da abincin ke dashi akan bai sa yaci da yawa ba, ruwan black tea yayi sipping kana ya goge bakinsa da tissue, sannan ya mike...



"wait! Son don't tell me you re full?" ta fada cikin rashin jin dadi da kulawa kamar gaske.



"yes mum! Am going out"

ya amsa a takaice kana ya haura sama cikin abinda

Please Login or Register in order to submit comment