Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai da yamma zan zo mu gaisa da Inna"




Ba dan taso ba ta tsaya tana shagwab'e fuska, driver ne ya fito ya fara fito da kayan Aysha yayinda Anty bintu ke fada masa kayan dake na iya Aysha, kafin kace me yaran layin har sun zagaye motar tare da fara dauk'ar kayan suna shigar wa shi cikin gidan, gabadaya hayaniyar su ta cika wajen
"Indon baffa liman ce ta zo" ...


Sai da Aysha ta ga an shigar da kayan ciki duka kana ta mara musu baya, tozali ta fara yi da Inna dake tsaye rike hab'a ganin yara nata shigo da kaya, murmushi mai taushi Aysha ta sakar wa Inna kana ta mayar da kallon ta ga yaran, dubu daya ta bawa babban cikin su tace "harisu gashi ku raba dari biyu-biyu" ta fadi hakan ne kasancewar dama su biyar ne.



Ihu na zallan murna yaran suka fara yi kana suka bar gidan a guje, da gudu ita ma Aysha ta fada jikin Inna da fuskar ta ke bayyana farinciki ganin tilon yarta a lokacin da bata zata ba, ita ma Inna hannu tasa ta rungume yarta "Inna ta nayi...." kasa karasa maganar tayi saboda hango twins da ta yi sun tsaya hadi da zuba mata ido, duk da cewa sun shaida ta, amma rashin ganinta na watanin biyun da basu yi ba yasa suke jin wani yanayi kamar bakunta a tare da su.




"y'ay'a na!" ta fada cikin zakin murya tana ware musu hannuwan ta, fuskar ta dauke da murmurshi tana yaba yanda suka girma a ranta, ai kuwa kamar jira suke suka nufe ta, hadi da Kiran "Ammuh!" dire guiwarta tayi a kasa tana jiran isowar su gareta, hannayenta ta rufe a lokacin da suka shiga jikin ta...


Aysha ta Lumshe idanun ta a lokacin data ji dumin su a jikinta, dago fuskar su tayi tace "nayi kewar ku yan biyu na sosai, ku fa kunyi kewar Ammuh?"


washe bakunan su yaran suka yi suna kallon ta, domin ba wai sun iya magana bane sosai.





"toh tashi ku zauna kan tabarma ko mai y'ay'a" Inna ta fada tana kallon su da burgewa.



Dariya Aysha tayi ta Mike, yayin da yaran suka mara mata baya, kowannen su ya kama rigarta ta gefe da gefe har suka zauna, domin a ganin su zata kara tafiya ta barsu ne.






Sai kallon su Aysha take, ta tallafi fuskar su hagu da dama tana kallon su, masha Allah kuma sunyi kyau Abin su kuma fess suke alamun Inna na matukar basu kulawa, fadin dadin da ta ji a ran ta ba zai misaltu ba.




Mikewa tayi ta dauro Alwala ta yi sallah a nutse, Bayan ta iddar Inna da kanta ta kawo mata dambun shinkafa daya ji gyada, zogale, hadi da man kuli na asali, babu abinda ke tashi sai k'amshi, lomar farkon da Aysha tayi ta Lumshe ido saboda wani mugun dadi daya ziyarci harshen ta, hak'ik'a ta yi kewar dad'add'an girkin Innar ta, hakan yasa ta mai yawa, ci bana wasa ba, wanda ta manta rabon da ta ci irin shi, su Ammar ma na taya ta ci.






Sai bayan la'asar suka kunce kayan da Aysha ta kawo ta bawa kowa nasa, su twins sai murna suke sunyi sabon kaya, Albarka kuwa ta sha shi cikin k'wando a wajen Inna...


Inna har kukan farinciki tayi saboda ni'imar da Allah yayi musu na sanjin rayuwar da suka samu.



*ABRAHAM*
Sai karfe goman safe ya fark'a daga bacci, a hankali ya Bude sleepy eyes dinsa, tarr ya ga rana ya shiga ta window'n dakin hakan ya tabbatar masa da cewa gari ya waye sosai, ya kuma yi mamakin dadewar da yayi a baccin, turo kofar dakin da aka yi, a tunanin sa itace, tsabanin haka mai gadi ne ya shigo.


Ajiyar zuciya Abraham ya sauke, domin kwata-kwata baya jin dadin jikinsa da ma bakinsa, ganin mai gadin yasa yaji dadi a ransa, kamar kullum gaishe da Abraham mai gadi Yayi, Abraham ya amsa da kai, da k'yar ya dora Abraham kan keken sa ya tura shi zuwa toilet, kana ya fito, mintuna goma kacal ya gama abinda yake, mai gadi ya kara turo shi waje yace zuwa yamma zai zo kwantar da shi kana ya koma bakin aikin sa da gudu, domin dabi'ar sace baya abu a hankali...






Bayan fitar sa Abraham ya Bude idanun sa, ya fesa numfashi mai dumi daga bakinsa, inda ya shaki k'amashin toothpaste din daya wanke baki dashi a hancin sa.





Rashin ganin ta yasa shi jin wani iri ba dadi a ransa, wanda shi kan sa bai fahimci hakan ba, a hankali ya kai kallon sa inda ya ga drinks da wani tray a rufe, a hankali ya tura kansa ya bude tray din, kana ya sake rufewa.



Idanun sa ne suka sauka kan farar takarda, a hankali ya kai hannu ya dauka, ganin yanda rubutun ta yayi wani iri a wargaje kamar na yara masu koyon rubutu ya bashi nishadi, for the first time murmushi ya subuce masa, a ransa yace


"what on earth did this hausa girl wrote?"


ya fada a ransa domin shi dai bai fahimci ko da kalma daya ba, amma hakan nan yake son sanin abinda da ta rubuta, sai a lokacin wayoyin sa suka fado masa, tun bayan da aka sallamo shi daga asibiti bai gan su ba, bai kuma damu ba.


Akwai wata karamar wayar android dinsa da bai fiye abinda da ita ba, a hankali ya turo keken ya zuwa inda yake ajiye ta, tare da fatan ya ga wayar, kasancewar drawer bai da tsayi ya kai hannun sa ya ja shi, ya kuwa hango wayar, a hankali ya ciro shi, ya kunna, 30 percent ya gani, numfashi ya sauka ganin akwai 600mb, goggle ya shiga , ya yi searching Abin translation daga hausa zuwa turanci domin ta hakan ne zai fahimci abinda ke jikin takardan, ya fara typing a wayar, da k'yar yake gane rubutun.


"Assalama alaykum ina kwana, kayi hakuri ban sanar mana ba, na je gidan mu garin gombe domin ganin mahaifiyata da yan biyuna, kwana biyu kacal zan yi in dawo, nazo gayamaka jiya amma kayi bacci, yallabai Allah ya kara maka lafiya, sai na dawo"



A hankali yake murza takardan cikin hannunsa bayan goggle ta fito masa da translation din, duk da har ransa yaji ba dadi na rashin ta a gidan, amma kalaman ta na karshe ya bashi dariya matuka

"she has twins, really? β€œ

ya tambayi kansa unbelievable yana murmushi da iyakar lips dinsa ne suka nuna, sosai Aysha ta bashi dariya daga short note din data ajiye masa...





Gabadaya baya jin dadin gidan, sai misalin karfe Daya yaci cake din yanka daya da lemo domin gabadaya baya da apatite, Abu kadan ya kai idon sa ga kofar, har gizon shigowar ta yake gani a idanun sa.




Bai tashi sanin cewa ya shaku da Aysha ba duk da ba magana ke hada su ba sai yau, hakika ko wani Dan Adam komai kankantar sa yana da amfani, ko da dabba ne, bare mutum mai daraja, a yau ya yarda da wanna maganar, haka ya wuni suk'uk'u gwanin tausayi.








*MADAM GLORIA*
Kwara State

Zaune take a wani kusurmin daji kan wani dutse da bai kai kasa ba, sannan shi ba a sama yake ba, ta saka wasu jajayen kaya yayinda aka zama mata wasu abubuwa a ciki da farin alli, duk da cewa ba wanna bane karon farko da take zuwa wurin bokaye amma tabbas ta tsorata da wanna bokan, domin hatsabibi ne sosai, kwanan ta biyu kan wanna dutsen ba tare da ta sauka ba, ko ta motsa ba, tamkar Wacce aka datsa, jajayen kayan jikin ta sai ji tayi an saka mata su ba tare da ta ga kowa ba, haka zalika abubuwa da aka zana mata a jiki, duk da cewa ta jigata da zaman amma kudurin da take da shi wurin son aiwatar da mugun nufin ta kan bawan Allah Abraham ke kara mata karfin guiwar cewa zaman ta a nan na dan lokaci ne...




Tana a haka wani mumunan halitta da tsayin sa bazai misaltu ba ya bayyana a gaban ta, har hakan ya firgita ta.

Hakoran sa, idanun sa da faratan sa sun fi komai muni a hallitan jikin sa, a hankali ya shiga zagaye madam Gloria yana mata wani kallo shi ba harara ba gashi nan dai, sosai jikin ta ke rawa, kamar Wacce aka warware mata jiki, ta budi baki da niyyar magana amma ya daga mata katoton hannunsa masu dauke da yatsu takwas, kana cikin Murya mara dadin amo yace "na San meke tafe dake, kuma kin zo wurin da za a share miki hawaye, matukar kike bi umarnin da zan gindaya miki, akasin haka kuma zan jefa rayuwar ki a mumunan yanayi da zaki gwanmaci mutuwar ki da Rayuwar ki a doron kasa"


ya karasa a tsawace, wanda hakan ya girgiza bishiyoyin wajen kana amon muryar sa ta amsa kuwwa.



Cikin rawar murya madam tace

"z...zan...bi duk umarnin da ka bani"


Dariya ya shiga k'yak'yatawa har na tsawon mintuna goma, yana yi wa kan sa kirari da wasu manya-manyan kalmomi, sai kuma ta ga ya bace bat, sai sautin dariyar sa dake cigaba da tashi duk da cewa baya nan, sai jin Murya tayi yana cewa "kamar yadda na fada miki, zamu kashe shi kamar yadda kike bukata, sai dai ki wayi gari ki ga gawar sa, babu Mai zargin ki matukar kika yi amfani da abinda zamu baki hhhhhhhhhhhhhhhh" dariya mara dadin sautin ya cigaba da tashi babu k'ak'autawa.


AYSHA
Dare ya tsala amma bacci ya kasa ziyartar idanun ta, Kwance take kan gado yayin da twins ke jikin ta a manne, kura wa fuskar Ammar ido tayi ta cikin hasken farin watan daya shigo ta window, tana gani kamar Abraham take kallo, musamman yanzu da ta dawo taga sun kara girma sai taga kamanin su ya dada fitowa, numfashi ta sauke hannunta kan gashin Ammar tana shafawa tana mamakin wanna kamanin nasu, Lumshe kyakyawa idanun ta tayi hoton fuskar Abraham kawai take gani, tabbas tayi kewar sa ba kad'an ba, tuno lalurar sa yasa hawaye suka cika idanun ta har suna biyo gefe da gefen kunnen ta...

"WAYESHI"

tayi wa kanta tambayar a karon farko, sosai kuma zuciyarta ta kwadaitu da son sanin waye shi, me yasa baya farinciki kamar kowani dan Adam, wacece madam Gloria a garesa domin ta kasa yarda cewa ita ta haife shi amma ace babu tausayi da jin kan uwa ga yayanta.

"ZAN TAMBAYESHI"

ta fada a saman labb'anta, sai dai rashin jin yaren juna da basa yi yasa jikin ta yin Sanyi har akan ya nuna kan fuskar ta, ta jima cikin tunani kana bacci ya dauke ta.




WASHEGARI
Bayan ta tashi da sassafe ta taya Inna aikin gida, sannan tayi musu abincin yan gayu kamar yanda tayi musu alkawari.


Bayan ta gama ta zubawa kowa, Inna da su twins sai santi girkin suke, Anwar da ya fi surutu cikin gwarancin sa yace "Inna! Ammuh ta fi ki iya giyiki(girki)"


Dariya suka yi kawai, sai da Aysha ta yi wanka ta zubo abincin, ta dibi loma daya zata ji sai maganar sa da hoton fuskar sa ta fado mata a rai, "ko ya ci abinci" zuciyar ta ta nemi sanin amsar da babu wanda zai bata"a sanyaye ta mayar da Abincin kwano cikin damuwa, ganin inna na kallon ta yasa ta daure taji spoon biyar ta ajiye, domin kwatata bata jin yunwa yanzu...

Bayan ta ajiye Abincin inna tace "zo nan Indo"

A sanyaye ta zauna zusa da inna, su twins kuwa na ta aikin jagwalgwala wayoyin inna da aysha.

"me ke damun ki ne?β€œ

Cikin raunin murya tace
"babu komai Inna"

"ban gane babu komai ba, kar dai ki manta ni mahaifiyar ki ce, shin akwai damuwar da zaki boye min, amma idan kina ganin ban isa ba shikenan, tunda kina ganin kin girma da gaya min matsalolin ki" ta fada da yanayi fushi, domin ta San logon yarta bata kaunar fushin ta.

Ai kuwa cikin sauri Aysha ta kama hannu Inna tace "wallahi Inna kin isa dani, kiyi hakuri, kawai na damu da....."

Sai kuma tayi shiru ta tsunkuyar da kanta tana tunanin yanda zata sanar da Inna cewa damuwar ta Abraham ne, ta yaya zata dauki abun, me hadin su, anya bata tsawwala da yawa ba kuwa?

Boyayyen ajiyar zuciya ta sauke tace, Inna ta kalli yarta tsaf tace" uhmm gaya min menene,
waye shi? β€œ


"Inna....dan Matar da nake wa aiki ne, kwanaki Dana kai masa abinci wanda ni na dafa da kaina...." daga nan dai ta shiga bawa Inna labarin daya faru da Abraham, shiru Inna tayi tana nazarin maganganun cikin hikima.

Labarin ya bata Inna sosai, kallon Aysha tayi tace" anya babu wanda ya saka guba cikin Abincin da kika girka masa kuwa? "


"Guba!" Aysha ta maimaita cikin zaro ido.


"kwarai, daga labarin da Kika bani na fahimci hakan, ina tsoran wanna Mahaifiyar tasa, akwai wani Boyayyen almari a tare da ita, ki iya takun ki da ita Dama kowa na cikin gidan, ki dage da addu'oi' sannan ki rike azkhar din safe da maraici, in sha Allah zai tsare ki da sharrin masu sharri har ma da mugaye, akwai wasu magunguna da baffan ki ya taba yiwa wani mutum mai shigen irin lalurar shi wanna mutumin, zan Baki shi, sai ki jika ki bashi ya dinga sha, zan miki bayanin yanda zaki yi amfani dashi, in sha Allah za a dace"

Numfashi mai fita da relief Aysha ta saki cikin jin dadi, har hakan yasa ta ware suka cigaba da hirar su da Inna, sannan sun sha wasun su da twins har take ji kamar kada gobe yayi...

Washegari da sassafe anty bintu ta shigo gidan inda ta tarar da Aysha a shirye tsaf, zaune take kusa da inna tana kukan rabuwar da zata yi dasu, Allah yaso su twins na bacci da abubuwan sun kara kacamewa.
Da kuka tana komai Allah suka dau hanya, Inna ta bi su da adduar sauka lafiya.


*12:40pm*
Daidai na rana suka shigo garin kaduna, kasancewar kayan aysha ba yawa kamar lokacin da za su tafi yasa a bakin gate ta sauka da kayan hannun ta, inda kuma su anty bintu suka shiga nasu gidan da suke aiki...


A mutunce suka gaisa da mai gadi, kana ta shiga gidan, falon shiru kamar ko yaushe, sai k'amashin air freshener na lavender da ke tashi...

A hankali ta nufi upstairs da kayan ta ta ajiye, kana ta cire kayanta ta daura towel daya tsaya iya cinyar ta, ya kuma bayyana madaidaicin hips dinta mai kyau da tsari, bata hims ba ta fito bayan ta daura alwala, ko mai bata shafa ba saboda zafi ta zira doguwar Riga bayan ta saka inner wears, sallah tayi hadi da addu'a, sannan ta Mike ba tare da ta cire hijab din ba ta nufi dakin sa, domin zuciyar ta sai azazalar ta take da son ganin sa.






_ban nutsu nayi editing ba, kila kuga typing error, sannan meye ra'ayinku kan wanna page din_?









Share fisabilillah

Comment for more typing...


NoorEemaan
07082281566



Thanks for reading my story πŸ‡ABRAHAM πŸ“




I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851




πŸ‡πŸ‡ABRAHAMπŸ“πŸ“
*First edition*


Written by
NoorEemaan



WATTPAD @NoorEemaan




https://facebook.com /groups/943534712916776/
Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din




Chapter 41-42



A hankali ta tura kofar dakin sa ta shiga, idanun ta a Lumshe tana fatan ganin sa cikin kyakyawar yanayi.

cikin yanayi mai kama da fargaba ta shiga bud'e idanun ta...


Idanuwan su ne suka fada cikin na juna, tamk'ar dama jiran isowar ta Abraham yake, domin idanun sa na kallon kofar ne.



Kara Lumshe Idanun ta tayi, wani irin farinciki sosai take ji daga kasan zuciyar ta na ganin yana cikin koshin lafiya, a hankali kamar yadda ta saba tayi sallama kasa-kasa, duk da cewa tasan bai San ma'anar abinda ta fada ba bare ya amsa, amma ta saba yin sallama a duk inda ta shiga.


A hankali ta shiga takawa zuwa gare shi, zuciyoyin su na bugawa a tare, the more tana kara kusanta shi, the more zuciyar su ke kara bugawa a tare.

Kasa ta dire guiwowin ta tana jin yanda idanun sa ke yawo a jikin ta, sai ta kasa gaishe shi kamar yadda ta yi niyya, tattausan murmushi ya saki da har sautin sa ya fito saboda tuna cewa Wai tace tana da yan biyu, ta ya ya? Shi kam bai yarda ba, domin duk wanda yayi wa yarinya mace kamar ta aure a wanna kananun shekarun nata anyi mata child abuse a cewar sa, dauke idaunsa yayi daga kanta yana jin sanyin a ransa saboda ganin ta dawo.



Cikin sauri Aysha ta dago, jin sautin murmushin sa, tayi mamakin hakan domin abu ne wanda yake bako a gareta, "Dama yana murmushi?" ta fada a kasan mak'oshin ta.


Haka ta cigaba da zama a wajen tamk'ar Wacce aka dasa, ta ma kasa tashi, a hankali ta Mike ta shiga gyara dakin sa da ya d'an yi kura kadan, komai tana yi ne a tak'ure saboda idaunsa dake yawo a kanta, a ranta tana gulmar yaushe ya koyi kallo haka...


Bayan ta gama ta sauka kasa da tray din cake din da ba wani abun kirki yaci ba, tausayin sa ya kamata domin ta San ba karamin yunwa ya ji ba, yanka daya taci da lemo ta kai wa mai gadi ragowar, ya dinga godiya yana washe hakoran sa.

Kitchen din ta dawo, ta gyara, sannan ta kunna gas ta dora ruwa, duk da ba ta san actual abinda zata girka ba, dakin madam Gloria ta nufa da sauri domin ta gyara kafin ruwan ya tafasa, sai dai turin duniya tayi wa kofar taki budu wa, hakan ya tabbatar mata da madam Gloria ta rufe abin ta, kitchen ta dawo tana mamakin Wai wanna Wacce irin uwa ce, da bata tausayin danta, a hankali kalaman Inna suka Shiga dawowa kunnen ta, numfashi ta ja, abinda ya kamata ta girka take tunani, a hankali dad'add'an dambun Inna da ta ci ya dawo brain din ta, wani yawu ta hadiya saboda tuno dadin d'and'anon dambun.



Sai kuma ta bata fuska tace "gashi babu zogale da gyada, amma zan girka da su karas, Koren wake, da hanta" ta fada wa kanta a bayyane kana ta shiga hada dambun ta.


Sai daf da magriba ta gama domin har da cocktail drink ta hada masa, k'washe dambun a warmer tayi, kana ta dauki juice din dake cikin fridge ta nufi sama domin ta daina barin Abincin da zai ci a kasa saboda har yanzu bata San waye mai cutar da Abraham ba, gwara ta kiyaye ta kuma iya takun ta kamar yadda Inna ta fada mata.



Tana iddar da sallah'n isha ta nufi dakin sa domin serving dinsa.

Yana zaune idaunsa na kallon bakin kofar, ta shigowa suka hada ido, saurin dauke kanta tayi ta shiga serving dinsa, sai a lokacin tayi tunanin anya zai iya cin dambu? Tunda dai baya daga cikin cimmar su, musamman ma yaren su ta igbo, addu'ar ta daya Allah yasa ya yi masa dadi har ya iya ci da yawa.


A hankali ta shiga serving din sa hannuta na dan rawa saboda kallo ta da yake yi, Bayan ta gama ta dora masa abincin kan cinyar sa, numfashi ya ja a boye ya mayar da idanun sa kan abincin, ya bi abincin da kallo a ransa yana mamakin meye wanna?

Ganin irin kallon da yake yiwa abincin yasa ta dauki wani spoon daga tray din ta dibi loma daya ta kai bakin ta, sannan ta Lumshe ido hadi da cigaba da tauna, sai da ta taune ta bude idanun ta hadi da yi masa alamar yaci akwai dadi, kamar karamin yaro mai jiran umarnin ya dauki spoon ya dibi kad'an ya d'and'ana, dadin da ya ji a harshen sa yasa shi fara ci bana wasa ba, tausayi ya bawa Aysha domin yanayin sa ya nuna cewa yana jin yunwa matuka, sai da ya ci rabi ta zuba masa cocktail juice din ya sha yana lashe lips din sa, kallon sa Aysha take da gefen ido ba tare da ta bari ya ganta ba.

Bayan ya gama ta fitar da plate din ta dawo, ta share inda ya dan bata kad'an.

Ta mike domin tafiya, har ta dora hannu a handle din kofa ta ji gyaran muryar sa, cak ta tsaya hadi da juyowa domin tun bayan da aka dawo dashi daga asibiti bata kara jin ko da tarin nan yayi ba banda da zu da yayi murmushi mai sauti, tsayawa tayi tana kallon sa, inda zuciyar ta ke bata cewa wani Abu yake bukata shiyasa yayi gyaran murya, hannu ya daga ya yafutota, cikin nutsuwa ta kara so ta tsaya a gaban sa.

"Sit"

Ta ji yace cikin karamin sauti yana dan buga kan gadon sa, ba musu ta zauna tana jin ta a takure, a hankali ABRAHAM ya juyo da keken sa, sai ya zamana suna facing din juna, ajiyar zuciya ya sauke, yana so yayi mata godiya bisa kokarin da take yi wurin kula dashi, domin samun kamar ta sai an tono, ya sha jin labari da ganin yadda wasu muslimai musamman hausawan mu da suke nuna bambamci ga chiristian ko nuna kyama, ko wariya a garesu, wanda hakan bai kamata ba, ko wani dan Adam yana da daraja, dan mutum ba Muslumi bane babu dace wa ka ce masa wai
WANNA ARNE NE, KO DUK ARNAYE WUTA ZASU SHIGA WUTA.


*(Subhanallah! Wane mutum da zai yanke wa bawa hukunci, Allah kadai ke da wanna ikon, sannan dukkanin mu Allah muke bautawa, addini ne ya bambamta mu, ba a shiga tsakanin bawa da ubangijin sa, kar mu yanke hukunci ga ko wani bawa, komai laifi da kuma tarin zunuban sa, dan haka matukar mun ga mutum chiristian ne Kar mu nuna kyama a garesu hakan zai sa su san cewa addinin musulucin addinin zaman lafiya ne da kaunar juna, wanda har hakan zai iya sawa su yi kwadayin shiga Muslunci Allah yasa mu dace)*


"Thank you for everything, i really appreciate your efforts, God bless you"

A hankali ta dago kanta dake maiko, sakamakon ruwan hawaye daya taru a ciki, domin ita kam bata fahimci abinda yace ba.

Fahimtar hakan yasa Abraham bud'e tafin hannu sa, take farar takardan da ta yi rubutu a kai ya bayyana, cikin rashin fahimta ta zuba wa soft palm din sa ido, furzar da numfashi yayi, domin zai sha ciwon kai saboda ba jin yaren juna suke ba, wani tunani ne ya fado ransa, hakan yasa shi tura keken sa zuwa gaban drawer ya dauko memo da biro hadi da wayar sa dake kan memon ya dawo.

Play store ya shiga ya yi searching App din translation daga turanci zuwa hausa, take aka fito masa da su da yawa ya zabi daya ya yi installing kana ya shiga typing turancin da yayi mata...

babu jimawa aka fito masa da fassarar, yayi copying a memon ya dora mata kan cinya, a hankali ta kai idanun ta kan kyakyawar rubutun sa mai kyau da tsari.

"Nagode sosai da komai, na yaba da kokarin ki, Allah yayi miki Albarka"

karo na uku kenan da ta

Please Login or Register in order to submit comment