Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kin tashi lafiya?"
mai gadi ya fada yana washe hakoran sa da suka sanja kala zuwa brown.

"lafiya lau, dama yallabai zaka taya ni dorawa kan keken sa" ta fada cikin marairaicewa.





"yanzu kuwa indo do, Allah sarki yallabai mai kirki, gashi waccen uwar tasa ta fita, yaro ba lafiya amma taci wata uwar Kwalliya sai kace yarinya ta fita, babu abinda ta iya sai masifa da iya daga hanci" ya fada yana k'waik'wayon yanda madam Gloria ke daga hanci.



Aysha kuwa duk da kalaman sa na karshe ya bata dariya amma Bata yi ba, sai ma gaba da ta yi, domin tana daya daga cikin Wacce bata so ayi maganar wani, ko aibata wani da ita.

Mai gadi kuwa take mata baya yake, ya ja bakin sa ya tsuke ganin Aysha bata bashi fuskar cigaba da kowa mata wata maganar ba.



Sabanin dazu da yake kokarin mik'ewa, yanzu kawai ya kwanta ne ya Lumshe ido cikin kunar rai, yaji shigowar mutane amma bai Bude idanun sa ba bare ya ga ko su waye , karasa jikin gadon mai gadi yayi yana cewa "sorry sir, how Body? your body go soon better you hear, sorry oga na" mai gadi ya fada cikin pidgin English daya koya a nan kaduna, duk da tune din hausa ya fito sosai a harshen sa wanda hakan zai sa mutum ya fahimci cewa shi din bahaushe ne.



Abraham kuwa shiru yayi still bai Bude idanun sa ba, da k'yar mai gadi ya fara kokarin daga shi, jajayen idanun sa sun firfito waje, kasa hakuri yayi yace "jar uba! Wallahi Indo oga ya shiga gasar dambe dole ya kad'a maza, karfi ne dashi sosai Al-k'uranin ubangiji"



Kasa d'aurewa Aysha tayi har sai da ta fashe da dariya cikin siririyar muryar ta da amon sautinsa ya fito, wanda hakan yasa Abraham Bude sexy eyes dinsa ya watsa mata su, saurin gimtse dariyar ta tayi, tana mai yin kasa da kanta.


Mai gadi kuwa bayan ya dora Abraham a keken sa da k'yar yace "Allah ya kara lafiya oga, Indo sai anjima" ya fada yana fita daga dakin cikin tafiyar sa ta sauri.




Shiru dakin ya dauka, can ta Kara sa wajen shi ta tura shi izuwa toilet, maclean ta matsa masa a brush, sabulu da soso ta ajiye masa a inda hannun sa zai kai, kana ta bar bandakin tana rufe masa kofa, gyara masa dakin ta shiga yi, ta goge masa komai, Airfreshna ta fesa a ko wani kusurwa na dakin, sannan ta shiga kitchen da gymimg room din sa ta goge hadi da gyara masa, domin babu wani datti sai kura kawai suka yi....



Bayan ta gama taji shiru bai fito ba, hakan yasa ta kara sauka ta dauka masa breakfast ta dawo, sai a lokacin ta fara jin alamun an Bude kofa, idanun ta takai wajen kofar inda yake fitowa, tozalin da ta yi dashi Yasa ta juya da sauri tace "Innalillahi wa innah ilaihi raju'un" sak'amak'on ganin shi data yi da short nicker kadai, domin ya cire rigar da dogon wandon jikin sa, domin sun ishe shi.



Da fari ya zata wani abu ta gani, sai daga baya ya fahimci abinda take nufi, sai ma ta bashi dariya, murmushi da iyakar sa labb'a yayi kana ya dawo da fuskar sa yanda take a had'e har girar sa na tattarewa...



Aysha kuwa ba tare da kara juyowa ba ta nufi wardrobe din shi, wani riga ta gani hadi da 3 quarter wando ta miko masa idanun ta a gefe, bai kalle ta ba ya karba hadi da sanya rigar, sai wandon daya sa da k'yar shi ma bai zauna da kyau a waist din shi ba, kasancewar a zaune yake wanda kuma bashi da ikon tashi domin hakan na daga cikin kaddarar sa a yanzu....




Sai da ta daina jin motsin saka kayan, ta shiga bude idanun ta a hankali ta kalleshi, take idanun ta suka fada cikin nashi, saurin dauke idanun ta tayi kunyar sa mai yawa na ratsa ta, hakan nan take ji a ranta cewa tana huce gona da iri wurin bashi kulawa, domin da bata yawan zuwa dakin sa bazata ganshi a haka ba, duk da cewa wanna ba shine karon farko ba, amma akwai bambamci da ganin data fara masa ba riga, sai dai bata da zabi daya huce kula dashi din, tunda babu mai kula dashi din baya ga ita, domin ko kafar mahaifiyar sa bata gani a dakin sa, wanda hakan ke daure mata kai sosai, kawar da tunanin tayi ta fara serving din shi Abinci, ta dora masa a cinya, Bayan ta caka fork kan Irish potato omelet din, sai tea data zuba masa a cup, dakin ya gauraya da kamashin mai shiga zuciya...

Idanun sa ta ga ya rufe ya dora hannun sa saman abincin ya fara addu'a irin na chiristian a lokacin da zasu ci abincin...



Kura masa ido Aysha tayi ganin abinda yake yi, domin ita kam bata da ilimi kan abinda yake yi, garin kallon nasa ne idanunta suka sauka kan cross(+) din wuyar sa dake rito, a ranta tace "Dama maza na sa sarka, oh ni Aysha Indo" ta fada a ranta tana cigaba da kallon sa, sai da ta ga yana k'ok'arin d'agowa tayi saurin dauke kanta zuwa wani bangare daban...





Da yamma Lubabatu ta samu Aysha a kitchen tana girkin dare, gaisawa sukayi, kana ta mikawa Aysha kudin albashin ta, inda Lubabatu ke sanar mata cewa tun jiya madam Gloria ta mata transfer na albashin su, amma iya su mata masu aikin gidan, domin yau tafiya zata yi ba kuma zata dawo yau ba, duk da Aysha tayi mamakin jin cewa madam tayi tafiya, amma ta 6oye mamakin ta hadi da yiwa Lubabatu godiya ta fita, domin bata taba bari hira mai tsayi ya hada ta da ma'aikatan gidan ba, domin daga nan kananun maganganun ke fara tashi har ta kai ga gulma, hakan yasa take tsaye kan Lane(iyaka)dinta.



Allah yaso ruwa kadai ta dora a gas din, sai kawai ta tafasa musu spaghetti, Bayan ta gama tayi musu egg sauce daya hadu sosai sai tashi k'amshi yake, daga nan tayi mango juice da zallan fresh mango sai flavour data saka, hadi da sugar kadan, sai da ta tabbatar komai yayi daidai, ta dauki warmers biyun da jug din mango juice din ta nufi up stairs dasu....


Dakinsa ta ajiye warmers din, kana ta nufi dakin ta tayi wanka, domin ya zame mata sabo matukar tayi girki sai tayi wanka take jin dadin jikinta, tana cikin wanka taji Kiran magriba hakan yasa ta d'aura alwala kana ta fito daure da towel a jikinta, mai ta shafa a jikinta sama-sama sannan ta saka inners hadi da riga da skirt na atamfar ta mai saukin kudi, dama ita ba gwanar Kwalliya bace, hakan yasa ta saka hijab dinta ta tayar da sallah...



*8:01pm*
Tana iddar da sallah'n isha ta fito domin zuwa dakin sa, ko ina shiru ba motsin kowa, a hankali ta nufi dakinsa, ta kama handle din ta shiga,
hango shi tayi a zaune idaunsa a Lumshe, girgiza kai tayi irin na tausayin nan ta shiga serving dinsa, sannan ta mika masa, karba yayi kamar dazu yayi addu'a sannan ya fara ci, lomar farko ya Lumshe idaunsa, saboda wani mugun dadi daya ratsa kwanyar sa, sosai yaci fiye da rabi kana ya ajiye, mango juice din ta siyaya ta bashi ya shanye, yana tand'e baki daya sa Aysha murmusawa a 6oye, Abraham kuwa a ransa yana yaba iya girkin ta, domin tun daga lokacin daya fara dandana girkin ta yaji cewa bana biyun ta a iya girki.



Aysha kuwa sai daya gama ta dauki plate mai dauke da ragowar abincin sa ta cinye ta kora da juice, a ranta tana jinjina karfin halin ta na yau, domin ko giyar wake ta sha bata isa cin Abinci a waje daya da Abraham ba, bare daga kwanon daya ci, matuk'ar madam gloria na nan, tana zaune a dakin shiru, sai goman dare ta koma dakinta ta kwanta...









Washegari da misalin karfe goma anty Bintu ta zo gidan, inda take sanar wa Aysha cewa gobe zata je gombe, amma kwana biyu zata yi ta dawo, tafiyar gaggawa ce ta taso mata, idan
Aysha nada sako ta kawo a kai wa Inna, domin yanzu haka kasuwa ta nufa...




Ai magiya Aysha ta fara yi cewa zata bi ta, dama tayi kewar su Inna, Anty bintu tace Sam bazata bi ta ba...

"waye zai dinga yiwa su madam girki? Indo kin San cewa aiki na wahala a wanna zamanin yanzu ko? Karki yi wasa da aikin ki fa"



Cikin sauri tace "wallahi Anty bintu madam bata gida, tayi tafiya kuma bata fadi ranar dawowar ta ba, dan Allah Adda muje zan biki, ai kwana biyu zaki yi, har mu dawo ma nasan bata dawo ba" Indo ta fada cikin marairaicewa ba tare da tunanin cewa akwai wanda yake matukar bukatar kulawar ta a yanzu ba, saboda zumudin ganin su Inna da twins din ta....





Ban wani yi editing sosai ba, idan kun ga typing error kuyi ๐Ÿ™



*ko ina madam gloria ta je Readers?*
Muje zuwa...




Share fisabilillah

Comment for more typing




NoorEemaan
07082281566




Thursday, 3 March
7:36pm




I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851



๐Ÿ‡๐Ÿ‡ABRAHAM๐Ÿ“๐Ÿ“

*First edition*


*WATTPAD*
@NoorEemaan


https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din



Chapter 37-38


Ganin tarin damuwa da hawayen da suka cika idanun ta yasa Anty Bintu ta sauke ajiyar zuciya hadi da cewa "toh ya isa, zamu tafi tare, amma Karki manta kwana biyu kacal zamu yi, kar mu tashi dawowa ki ce min baki San zance ba" anty bintu ta karasa tana mata hararan wasa.




Ihun murna Aysha tayi ta rungumi Anty Bintu kana cikin farinciki da wani kwarin guiwa ta mike da gudu hadi da fadin cewa "anty Bintu ki jirani bari na dauko kudi muje kasuwar tare"




Murmushi hadi da girgiza kai Anty bintu tayi tana bin bayan ta da kallo.


Aysha tana shiga dakin kuwa ta d'auko kudin albashin ta, rabawa tayi biyu duk da bata San ko nawa bane, kana ta zuro hijab dinta ta kara saukowa da gudu, anty Bintu ta Mike ganin ta taho , da haka suka nufi kasuwa inda a motar gidan da Bintu ke aiki suka tafi, hakan kuma umarni ne daga hajiyar gidan....



******

Sosai Aysha tayi siyaya, ta siyi kayan sawa wa su Anwar kala uku masu saukin kudi kuma iri daya, ta siyawa Inna atamfa da hijab hadi da takalmi flat, sai kayan Abinci hadi man shafawa na yara, da nata da na Innah duk ta Siya, sai man goge baki(toothpaste) da sabulu, har da spices sa veges ta siya wanda tace zata musu had'add'en girki da zaran ta isa gombe kamar yadda tayi wa Innah Alkawari, anty Bintu dai sai dariya take mata domin zallan zumudi yasa Aysha ke siyan ko me ta gani, sai da kudin hannuna ta suka dawo saura dubu uku sannan idanunta suka washe ta hakura hakan nan...




Kallon Anty Bintu tayi cikin marairaicewa tace "Anty Kinga Wai kudin hannuna har sun k'are, ni dana ce zan siya mana kananun wayoyi ni da Inna ta" ta fada, ta na zumburo baki kamar wani ne ya sata siyayyar dole.



Dariya Anty Bintu ta saki, "ho ho hoo Indo ba dai sakalci da yarinta ba, yanzu nawa kudin ki suka rage?"


Dan d'aga kanta sama tayi hadi da juya manyan fararren idanunta alamun tunani sannan tace "ina ji kamar dubu talatin ne, domin nayi siyayyar dubu talatin da bakwai"


"Na gane yanzu, a takaice dai kudin hannun ki saura 33 thousand ko?" anty Bintu ta fada.


"33! Menene 33 anty Bintu?"

Murmushi Bintu tayi tace " Toh dubu talatin da uku nake nufi"



"oho! Eh haka suka rage" Aysha ta amsa mata .


"toh bari na ara miki dubu tara anan, sai ki kara da dubu uku ki siya muku wayar ko yar dubu shida-shida ce, idan munje gida sai ki bani ko" anty Bintu ta karasa tana dafa shoulder dinta.





"yawwa Addah Nagode sosai"

Aysha tace cikin farinciki daya gagara buya a saman k'yak'yawar fuskar ta.



Da suka je wajen masu waya aka fito musu da kala uku, daya kirar techno, daya airtel, daya kuma bontel, aka fada musu price din, akwai ta 5,500 sai ta 7000 har da na 10k ma, anty bintu tace a basu airtel din dan 5,500 guda biyu, inda a nan suka siyi simcard a wani shagon register'n layi dake kusa da shagon wayar, sai da komai ya yi normal suka bar kasuwar Aysha sai murna take tayi keypad...




*****

Bayan sun iso Gate din gidan Aysha ta sauka, inda kayan da suka siya yake booth ba kuma za a fito dasu ba, tunda a ciki zasu tafi gombe, wanda hajiyar gidan ta ce a kai Anty Bintu a motar gidan ba sai taje tasha ba, hak'ik'a karamci da mutumcin hajiyar ya wuce misali.





Tunda suka dawo Aysha ta yi sallah ta sauka kitchen da wuri, inda ta dafa wa Abraham indomie da ya sha veges, hadi da kwai domin shi zai yi saurin dahuwa, ita gabadaya ta manta bai ci komai ba tun karin safe, Bayan ta gama ta zuba a plate ta rufe saman da wani plate din ta hau sama tana fatan kada yayi fushi duk da ba magana yake ba, har tana tunani a ranta cewa ko dai wanna cutar da yayi ya sa muryar sa samun matsala ne, domin Abin da matukar mamaki ace mutum kusan watanin Kenan baya ko gyaran murya bare ya kai ga furta wata kalma...




Zaro idanunta tayi sak'amak'on abinda ta gani, zaune yake kan gado ya jingina bayan sa bed din, a yanda yake zaune ba wanda zai taba tunanin cewa bazai iya tsaye kan kafafun sa ba, inda tunanin ta yafi bata cewa kila mai gadi ko wani daga cikin ma'aikatan gidan ne ya dora shi kan gadon...



Hada idanu suka yi tayi saurin yin kasa da kanta gabanta na tsananta bugu, saboda mugun jaa da kwayar idanun sa suka yi, ga jijiyoyin kansa da suka fito rudu-rudu.



A sanyaye da yanayi irin na tsoro ta ajiye abinci a gefen gadon, a hankali ta ciri murfin da ya rufe abinci inda k'amshin mai dadin gaske ya daki hancin sa, a hankali ya lumshe idanun sa, fork Aysha ta saka kan abinci ba tare da ta kalleshi ba tace "ga Abinci" duk da tasan cewa ba jin abinda tace yayi ba, amma bata da wani zabi daya fi tayi masa magana .


Sai dai ko motsi bai yi ba kusan mintuna biyar, a dame ta dago da idanunta masu kyalli ruwan hawaye ta kafe masa, a hankali ta kamo k'arfaffan hannayen sa a kokarin ta na bashi fork din, ya janye hannunsa da karfi, har hannun ta na buga fork din.




Mamaki tayi sosai, "me yasa yanayin sa ya sanja a yau, ko dan ban bashi abinci kan lokaci bane yasa shi fushi?" ta fada a ranta tana fashewa da kuka.



A fili tace "Dan Allah kayi......"

Katse ta ya yi ta hanyar daga mata hannu hadi da yi mata alamun ta fita ba tare da ya ko bude idanunsa ba...



Kamar Wacce kwai ya fashewa a ciki haka ta fice tana share hawaye.


Kan bed dinta ta fada tana kuka, daga nan ta fada duniyar tunani.





*ABRAHAM*

Sosai zuciyar sa ke suya, abubuwa da Dama sun cushe masa zuciya, yau kwana kusan uku bai ga Mummy ba, Matar da ke matukar bashi kulawa right from time amma Ashe fuska biyu ce da ita, Kenan maganganun daya ji tana fada rannan kafin hankalin sa ya gushe gaskiya ce, mummy tana so ya mutu, ya bar duniyar kan dalilin ta da bai sani ba, me yasa abubuwa suka taran masa lokaci daya haka, Aysha da yake jin motsin ta a kusa dashi amma yau tun safe bai sake ganin ta ba, ga kukan da ta fita tana yi yana taba sa matuka, Sam bai kamata yayi treating dinta haka ba, bai kamata dan zuciyar sa na zafi ya huce a kanta ta ba, ita din karamar yarinya ce mai tsananin kulawa da sanin ya kamata, basu hada dangi ba, basu hada addini, basu hada komai ba amma still tana kokarin kula dashi da dukkanin iyawar ta, "why did I make her cry" ya fada daga ta ciki yana cije lips dinsa, a hankali ya kai idanunsa kan noodles din, sannan ya kara kawar da kansa hadi da rufe rikitattun idanunsa, zallan damuwa, hadi da tsananin kewa ne suka yiwa zuciyar sa rubdugu...






_7:45pm_

AYSHA
A nutse ta iddar ta sallah isha kana ta Mike cikin sauri domin dauko Abinci ta bashi, saboda Sam bata so ya kara jin yunwa irin na dazu bare ya yi fushi da ita, domin tafi tunanin cewa barin sa da yunwa da ta yi ne yasa yake fushi da ita, Bayan ta isa kitchen ta dauko warmer mai dauke French fries hadi da chips sai wani had'add'en lemon k'wak'wa da madara da yayi Sanyi a jug kasancewar daga chest freezer ta jiro shi...



Bakinta dauke da sallama ta shiga dakin sa kamar yadda ta saba, gabanta na fad'uwa tana zullumin yanda zasu kwashe ta ajiye tray din kan gadon, inda idanunta suka sauka kan indomie daya sand'are, cikin rashin jin dadin ganin bai ci ko da loma daya ba, dauke indomie tayi daga kan gadon ta ajiye shi a kasan tiles.



"Ga...abin...cin...ka" ta fada cikin cracking voice da amon sa ke bayyana kukan dake son kwace mata...



Shiru babu Amsa bai kuma Bude idanun sa ba, a hankali ta sa dan knife ta yanki French fries din ta tura masa a bakin har yatsun ta na gogan miyau sa, a hankali ya shiga taunar French fries din

farinciki ya cika zuciyar Aysha, ware idaunsa da suka Dan fad'a ciki yayi ya watsa mata su, alama tayi masa da ido kan ga Abincin sa yaci, yayinda take langwabe kanta ba tare da San tana hakan ba.



Kamar karamin yaro mai jiran umarni ya dauki fork da knife ya shiga ci da sauri-sauri alamun ya jigata da yunwa, aysha kuwa zara-zaran yatsun ta masu dauke da ragowar Jan lalle a Farcen ta ta hade cikin na juna tana kallon sa da burgewa...




Yaci da yawa kana ya ajiye, lemon Aysha ta siyaya a tumbler ta mika Masa ya sha sosai har yana lashe baki, ajiyar zuciya mai tattare da farinciki ta saki ganin yaci Abincin.


Bayan ya gama tattara wajen tayi ta fita da kwanukan, ya bi bayanta da kallo kana ya Lumshe idanun sa...



Aysha kuwa ta cinye ragowar Abincin a kitchen ta wanke warmers din da plate hadi da jug ta mayar da komai a muhallin sa, har ta nufi kofar barin kitchen din ta tsaya cak! Saboda tunanin daya ziyarci k'wak'walwarta...

"tabbas ya kamata na yi masa wani abun kafin na tafi kafa yaji yunwa, domin ba lallai madam ta dawo da wuri ba" ta fada a sanyaye, tana ji kamar karta tafi saboda ta bashi kulawa, amma idan ta tuno twins dinta da Inna sai taji ba zata iya fasa tafiyar ba...




Ingredients din yin cake duk ta fito dasu, kasancewar zaynab akindele ta koya mata wasu abubuwan daya danganci baking, k'waba cake din tayi cikin kasa da 30min, sannan ta zuba a pan mai dan girma ta saka a oven, bayan mintuna arba'in kamshi ya gauraya kitchen din, fito da cake din tayi bayan ta saka hankici (handkerchief) wurin fito dashi, sinken sakace ta cak'a a ciki ta ga bai manne a jikin sinken ba, gyara kitchen din tayi sosai ya dawo hayyacin sa


Bayan ta gama ta dauko wani tray mai oval shape ta kife cake din a kai, sannan ta yanyanka madaidaita sannan ta rufe da wani tray din, wanke cake pan tayi shima ta mayar domin bata son barin ko da cokali mai datti ne, domin anty Bintu tace mata 6:00am daidai ta fito...




***
A matukar gajiye take taka matatak'alar bene hannun ta rike da cake din, burinta yanzu ta samu tayi wanka ta kwanta, a hankali ta tura dakin sa ta shiga.



Yana kwance flat kan gado, numfashin sa na sauka a hankali da alamun ya samu bacci, gajiyayyun idanun ta ta zuba masa tana kallon sa, yayi mata kyau fiye da yanda yake yin kyau idan idanunsa a Bude suke.... Sai kuma tayi saurin d'auke kanta tana gargadin kanta da yawan kallon shi da take yi....




Kan wani center table na zallan glass ta ajiye cake din, daidai yanda ta san hannun sa zai isa, sannan ta dauko lemon 5alive guda hudu na kwali, ta daukar masa Swan water guda biyu sai cup, komai ta jere kan table din, har ta kai kofa sai kuma ta tsaya saboda tuno cewa bai San zata yi tafiya ba.




"Gashi ni ba jin turanci, shi ba hausa, bare na tashe shi"
ta fada tana shagwabe fuska, da tunanin bai kyautu ta tafi hakan nan bai sani ba...




"ya ilaihi! Ya zanyi yanzu?"
ta dora hannun ta a kugu cikin nazari, can kawai ta nufi wajen bed side, ta dauko wani memo da biro da ta gani tayi rubutu a kai kana ta yagi daidai inda tayi rubutun, duk da ta San ba iya karanta wa zai yi domin mutumin da bai iya hausa ba tayaya zai iya karantawa, amma zuciyar ta tafi aminta data bar masa wasikan da haka ta fita, tana zuwa dakin ta ta fada kan gado sai bacci saboda tsananin gajiya ko wanka bata samu ta yi ba, ko mintuna goma bata yi ba bacci mai cike da gajiya ya dauke ta...




Washegari

Saura kiris ta mak'ara sallah'n asuba a kagauce tayi wanka hadi da brush, ta saka kaya hadi da tada sallah, Bayan ta iddar ne ta yi karatu kadan saboda karancin lokaci, ita da take cewa zata masa breakfast kafin shida tayi gashi ta makara...

Abubuwan amfanin ta- ta dauka daidai na kwana biyun ta sauko da sauri ganin shida har da mintuna biyar, duk da taso leka Abraham amma gani take da zaran ta kara bata wasu mintuna Anty Bintu zata tafi ta barta...


Tana fitowa mai gadi yace "ah! ah!! Ayshatu ina zuwa haka"


"barka da asuba, zan je gida ne amma kwana biyu kadai zanyi, anty Bintu na jirana sai na dawo"


Ta fada tana fita da gudu-gudu sauri-sauri...

"ai kuwa naji horn a waje, toh a dawo lafiya Allah ya tsare" mai gadi ya fada ba tare da ya samu amsa ba, domin Aysha ta riga ta fada mota, har driver ya ja motar suka harba kan kwalta....





*_mu hade a next page mah people, banyi editing ba, may be akwai typing error, bacci sosai nake ji shiyasa.. wallahi da k'yar na gama wanna episode din._*



Share fisabilillah

Comment




NoorEemaan๐Ÿฆ‹
07082281566



I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851





๐Ÿ‡๐Ÿ‡ABRAHAM๐Ÿ“๐Ÿ“

*First edition*


https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din



*WATTPAD*
@NoorEemaan




Chapter 39-40

(Not Edited)




Farinciki ya cika zuciyar Aysha, burin ta kawai ta ganta a garin su tayi tozali da twins hadi da Innar ta, ita gani take ma driver baya sauri saboda zumudi.


โ˜…โ˜…โ˜…

Da misalin karfe daya na rana suka isa kauyen su, inda ta kofar gidan su Aysha aka fara zuwa, cikin sauri ta balle murfin Motar ta fita, Anty bintu har ma da mai gadi suka fara dariya, cikin muryar dariya Anty bintu tace "Tsaya Indo! A ciro kayan nan, domin ni wucewa zanyi

Please Login or Register in order to submit comment