Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

maimaita rubutun cikin ranta, a hankali ta dago tana masa kallon zallan mamaki wanda hakan ya kasa buya a saman fuskar sa "Dama ya iya hausa?" ta fada a ranta.

Ya karanci hakan ta fuskar ta , hakan yasa shi dago mata wayar, yana mata alamun daga nan ya rubuta, murmushi tayi tana sunkuyar da kan ta.


A memon ita ma ta rubuta
"Bakomai, kar ka damu."

Ta mika masa, karba yayi ya shiga typing abinda da ta rubuta, dama already ya sauke App din translation daga hausa i zuwa turanci tun ranar da Aysha ta tafi gombe...

ya shiga typing, bayan ta gama app din ya fito masa da amsa kamar haka...

"it's nothing, never mind"

Hakan nan yaji baya so ta tafi, so yake hirar kuraman ta su ta cigaba, a hankali ya rubuta da turanci

"is it true that you gave birth to twins as small as you re?"

Bayan fassaran ya fito ya rubuta ya mika mata, murmushin daya Bayyana siririyar wushiryarta tayi, saboda tuno lovely twins dinta, ga kuma kalaman sa da suka bata dariya wai ita karama, a hankali ta kara karanta abinda ya rubuta,


"da gaske ne cewa kin haifi yan biyu duk kankantar ki?"


Amsa ta bashi da "Eh! da gaske ne, ina da yara maza biyu, suna wajen mahaifiyata"

Bayan yayi typing fassarar ta fito da masa da amsa kamar haka "yes! It's true I have kids, two boys, they are with my mother"



Jinjina kai yayi, yana mamaki wanna abun, kamar ta ace tana da yara, sai yaji wani iri ba dadi, shi a ganin sa iyayen ta sun cutar da ita.



Aysha kuwa ta zabi boye wa ko ma waye gaskiyar lamarin domin ba ta so ko da wasa su Ammar su tashi su San cewa ba ita ce ta haife su ba har akan ya shafi rayuwar su, bata so suyi kukan maraici, ko a ina ne zata fada, idan ma aure zata yi sai ta fada wa Mijin da zata aura cewa tana da yara.


*ABRAHAM*
Sai after 11 yayi mata alamun taje ta kwanta, a hankali ta tashi ta fita, yabi bayan ta da kallo, numfashi pya sauke yana jin wani yanayi na musamman daga gareta, wanda har yanzu ya kasa gane ko na menene, domin Sam tunani da k'wak'walwar sa basu taba bashi cewa wata kalma ta SO zata shiga tsakanin su ba.




"amma meyasa na damu da rashin ta kusa dani?" ya tambayi kansa, sai kuma ya kau da tunanin daga ransa, kan wheelchair ya cigaba da zama har bacci ya dauke sa yana jin gab'obin jikin sa na masa ciwo, saboda zaman da ya jima yana yi a waje daya.


*(lafiya babban jari inji masu iya magana. Da Abraham na da lafiya yanzu zai tashi ya kuma kwanta a duk lokacin da yake so ko da babu mai taimaka masa, shiyasa komai da mutum zai yi maka ba zai taba zama yanda zaka yiwa karan kan ka ba, Allah ka wadata mu da lafiya)*



*BAYAN KWANA UKU*
Tsaye Aysha take a gaban sif dinta bayan ta fito daga wanka, Riga da skirt na wani lace din ta mai saukin kudi ja hadi da touches din fari a jiki ta sanya kana ta saka wani madaidaicin farin hijab mai roba, as usually fuskar ta fess babu ko digon make up, zata rufe sif din Kenan idanun ta suka sauka kan Ghana most go din ta mai dauke da photo album dinan, a hankali ta kai hannu da niyyar budewa domin ta ga abinda ke ciki, har ta fara zuge zip din taji horn daga bakin gate, mayar da zip din tayi ta rufe kana ta nufi window din dakin ta cikin sauri ta zuge, domin iya sanin ta dai babu bai shigowa babu kuma mai fita a mota tunda Abraham ba lafiya gare shi ba, Wacce ta gani ta fito daga mota ne ya sanya gaban ta fad'uwa fiye da ganin farkon da ta fara yi mata tun zuwan ta na farko gidan.




_Idan ina free gobe zaku iya ganin update_



Share fisabilillah
Comment
Vote



Thank you for reading my story #Abraham



NoorEemaan
07082281566





2:33pm
Saturday 12, 2022




I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851




🍇🍇ABRAHAM 🍓🍓

*First edition*



https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din




Chapter 43-44


"MADAM!"

Ta fada cikin cracking voice tana jin wani irin tashin hankalin sak'amak'on ganin ta, hakan nan taji rashin nutsuwa da ganin ta.


"ya Rahman!" ta furta a fili hadi da dafe kirjin ta dake bugu da sauri - sauri...


A sanayaye ta fito daga dakin ta, wani bangare na zuciyar ta na mata fad'an cewa "Aysha me kike yi haka ne? Mata da gidan ta amma kina jin rashin dadin ganin ta, bayan ita ce dalilin kawo ki wanna gidan"

Numfashi mai dumi ta furzar Kamar zautaciyya a fili tace "na sani, nima na san abinda nake ji a raina bai dace ba, amma na kasa sarrafa zuciya ta, ban San meya sa ba"

ta karasa kamar zata saki kuka, domin har ranta tana son daina jin wanna yanayin amma ta kasa.


Dakin madam Gloria ta nufa domin gaishe ta, saboda rashin zuwa gaishe'n ta kan iya janyo wata matsala da bata San abinda zai haifar ba...

A hankali ta shiga k'wank'wansa kofar tsahon mintuna hudu kana madam Gloria ta bud'e kofar, hadi da tsare hanya, kamar yadda zuciyar ta yake baka haka fuskar ta yake, Sam babu alamun fara'a bare Imani.


Cikin tsora da Aysha ke k'ok'arin boyewa ta dan russuna alamun girmamawa tace
"Madam ina kwana, Sannu da dawowa ya hanya?"


"Lafiya" Madam Gloria tace a dak'ile hadi da bango kofa, wanda hakan ya sanya Aysha firgita.


A sanyayye ta juya ta koma sama, tana jan Numfashi, saboda wani karni-karni da wari-wari da madam Gloria ke yi a lokacin da ta fito, inda har yanzu warin bai bace ba, sai ma yanzu ta tuno da maganin da Inna ta bata tace ta hada wa Abraham.


Madam Gloria kuwa lock ta saka wa kofar, domin a halin da take ciki bata kaunar ganin kowa har sai ta cimma ma burin ta, ga wani mahauk'acin tsanar Aysha da ta kara ji yanzu da ta ganta.

Wata bakar leda dake kan gado ta dauko a hankali, cire ledar tayi, inda wata madaidaiciyar k'warya ta bayyana, an zagaye k'waryan da Jan kyalle, murfin
K'waryan ta bude inda take wani hayaki ya fito, sai wani abu kamar kwallo karami mai tsakanin haske kamar an saka k'wan lantarki a ciki yana ta birgima cikin kwaryan.


Murmushin zallan mugun ta ta saki, tana mai rufe murfin, kasan gado ta mayar da k'waryan, kana ta nufi bathroom domin yin wanka, saboda ita kanta tana shak'an warin dake fita a jikin ta, wanda baya rasa nasaba da jimawar ta a garin kwara da kuma aikin da bokan ya gudanar a kanta, domin wasu abubuwa da bata San ko meye ba yake ta watsa mata a jiki...



AYSHA
Bayan ta dauko duk abinda Inna ta bata inda yake cikin Wata leda ta hado da qur'ani kana ta nufa dakin sa, Bayan ta Bude kofar ta jingina kanta da kofar tana kallon sa, duk da shi ma ita yake kallo amma a yau ta kasa janye idanun ta domin wani mugun tausayin sa take ji a ranta wanda bata taba Jin kamar sa ba, ajiyar zuciya ta sauke bayan ta karasa shigowa cikin dakin, ajiye jakar bakon tayi kana ta nufi kitchen dinsa inda yaune karon farko da za a fara amfani dashi, ta kuma zabi hakan ne saboda bata son madam Gloria ta ganta.

Ta San kowacce uwa da danta ke fama da irin wanna lalurar zata yi farinciki idan aka ce yau ga wani magani a jarrraba masa, ko wata hanya ta samun lafiiyar sa, amma ita kam zuciyar ta yafi kwanciya kan ta boye mata, ba tare da ta San dalilin hakan ba.



*ABRAHAM*
Da kallo ya bi Aysha yana ganin yanda fuskar ta ke bayyana damuwa. "what's wrong with her?" ya tambayi kansa, sai kuma ya Lumshe idanun sa yana tsammanin fitowar ta domin ya tambayeta waya shigo ko ya fita kasancewar daga gidan, kasancewar yaji horn dazu.


Aysha kuwa electric cooker dake kitchen din ta jona, tukunya ta dauko ta dauraye, kana ta tari ruwa a ciki, ta sink din dake kitchen ta dora a wuta.

Kara fitowa tayi, ba tare da ta kalle shi ba ta dauki wasu magunguna kana ta koma kitchen...

Abraham kuwa ya bita da kallo yana mamakin meya sanja mood dinta haka.


*AYSHA*
Ta bata wasu mintuna kana ta fito da maganin cikin jug sai ta dora karamin cup a saman sa, gaban sa ta zauna ta zuba maganin daya d'an huci a cup ta mika masa, k'urawa maganin dake da kalar ruwan hanta yayi, yana mamaki ko meye wanna.


Idanun ta dake cike taf da ruwan hawaye da bata san ko na menene ba ta kura masa, ba tare da ta damu da ya ji, ko kar yaji ma'anar abinda zata fadi ba tace "ka sha Dan Allah! magani ne, Inna ce tace na baka domin samun lafiyar ka in sha Allah, ka yarda dani, bazan cutar da kai ba, bazan taba cutar da kai ba, ka sha Dan Allah kaji"

ta karasa cikin zubar hawaye hannun ta har k'ak'arwa yake wanda yasa maganin cikin cup din ya shiga rawa kamar zai zube, bata san meyasa yau raunin ta ya fito fili ba, ji take kamar tayi kuka sosai.


Tunda ta fara magana ya kurawa cute lips din ta ido, ko kalma daya bai fahimta daga maganganun ta ba, dadin amon muryata dake fita daki-daki hadi da dark pink lips din ta sune suka ja hankalin sa har ya kasa d'auke idanun sa daga kanta, amma abu daya ne, abu daya ne ya sosa masa zuciya ganin hawayen ta...


Bai kara bari zuciyar sa ta yi wani tunani ba ya zagaye hannun sa kan hannun ta dake jikin cup din, hakan yasa hannun ta ke kasa, yayin da nasa k'arfaffan hannun yayi wa na ta rumfa.

Numfashi mai tafe da shesheka Aysha ta saki, sakamakon taushi da dan Sanyi da tafin hannunsa ke dashi wanda ya ratsa har tafin kafar ta, hakan bai taba faruwa da ita ba, baya ga baffan ta, Abraham shine mutum na farko daya fara taba mata hannu.


Abraham kuwa a hankali ya zare hannun sa, sannan ya zari cup din daga hannun ta, without even a second thought ya kai cup din bakin sa, ya sani cewa bazata cutar da shi ba, yayi yarda da ita hundred percent, zargin da yayi mata a baya na tunanin cewa ko itace tayi poisoning din sa kuskure ne, zama waje daya da yake yawan yi da ita ya fahimci wacece ita da kuma dabi'unta, dan haka baya shakku a kanta ko kad'an, a hankali ya shiga sha yana yamutsa fuska saboda baurin maganin, amma haka ya daure ya cigaba da sha saboda da ita, domin a ganin sa idan bai sha ba kuka zata cigaba da yi.



Aysha kuwa ganin cewa ya karba ya sanya ta sauke Numfashi kana ta fito da wani madaidaicin Allo hadi da tawadda Ledan, wasu surori cikin Alqur'anin mai girma da Inna ta fada mata ta shiga rubutawa cikin k'warewa, Bayan ta gama ta ajiye qur'anin kan dayan drawer, tashi tayi ta shiga kitchen ta dauko wani bowl ta dawo ta zauna, zama tayi ta dauko ruwan zam-zam dake cikin ledan kana ta shiga wanke rubutun cikin bowl din bayan tayi bismillah.


Duk abinda take Abraham yana kallon ta, sosai rubutun ya burge shi, bama kamar saurin daya ga hannun ta nayi alamun ta k'ware sosai, bai ankara ba yaga ta miko masa ruwan rubutun, kurawa ruwan ido yayi, musamman bakin daya ga yayi, a tunanin sa wani abu ne daban.

"Ka sha kajiiiii" ta karasa tana mai Jan karshen maganar.


Kawai kallon rubutun yake cikin wani yanayi, Aysha kuwa Dama tayi sammanin hakan, ta San Mawuyaci ne ya karba kai tsaye, Numfashi ta furzar tana kara matsowa kusa dashi, ta mika masa kawar da kan yayi domin scent Din tawaddar daya bugi hancin sa, kara mayar da kallon sa ga Aysha yayi, cikin marairaita tace masa

"Dan Allah!"

A hankali yasa hannu ya karba, toshe hancin sa yayi kana cikin sauri-sauri ya shiga shan rubutun, murmushi Aysha tayi ta kuma San kamshin tawaddar ne baya so shiyasa ya toshe hancin sa, ruwa ta bashi ya dan sha, sannan ya Lumshe idanun sa, Numfashi ya shiga saukewa kamar wanda yayi tseren gudu...



Aysha ta kai Ledan kitchen ta ajiye sannan ta wanke bowl da cup din hadi da tukunyar dafa maganin daya dan sanja wa tukunyar launi, Bayan ta gama ta fito, hanyar barin dakin ta nufa, kamar daga sama taji yace

"hey!"

cikin sauri ta juyo, hannu yayi mata alamun ta zo, ba musu ta dawo.
Da littafin hirar su ya rubuta mata tambayar da yake so bayan App din ta fito masa da amsa.

Karba tayi ta karanta sannan ta dan yi Jim kana ta masa reply da cewa

"MADAM ce ta dawo"

Bayan yayi typing fassarar ya karanta sai ya dafe kan sa kawai, yana jin wani daci a ransa sosai, har yau yana ganin kamar mafarki yake, kamar ba mummyn sa bace wanna.



*AYSHA*
ganin yanayin sa ya sanja ya sanya ta kasa tafiya, kasan tiles din ta zauna duk suka yi zaman kurame na tsahon mintuna goma, sannan tunanin Kiran Inna yazo zuciyar ta, contact list ta shiga inda lambobin mutane biyu gareta, daga na lnna sai na Anty Bintu, number'n Inna ta shiga sannan ta danna dialing hadi da sakawa a loudspeaker, domin taji da kyau Idan an bawa su twins waya.


Ringing uku kacal tayi taji kamilaliyyar murya Innar tayi sallama, amsawa Aysha tayi cikin farincikin jin muryar Innar ta, Bayan sun gaisa tace a bawa su Ammar taji muryoyin su, tana jin Inna tace

"karbi kai Anwar kuyi magana sai ka bawa Ammar, Ammuh dinku ce"

A rude yaran suka shiga Kiran "Ammuh! Ammuh!!“ babu k'ak'autawa tamk'ar zasu fasa wayar su shigo ciki...

Aysha kuwa dariya ta shiga yi, da k'yar tace " yarana ku nutsu, daya bayan daya zamu sha hira kun ji"

A tare da suka ce "toh" yayinda daga can bangaren Ammar yayi nasaran warcen wayar a hannun Anwar yace "Ammuh nah! Ammar ne"
Abraham da idanun sa ke a Lumshe yayi saurin bude ta, saboda muryar yaron daya tsaya masa a rai kwarai.

Ga kuma k'wak'walwar sa da ta tuno masa shigowar Aysha dakin sa na farko, idan bai manta ba wanna sunan ya ji ta fada.

"Ammar! what does that means?" ya fada kasan mak'oshin sa sannan ya kurawa fuskar ta ido, yana kallo yanda take waya cikin annushuwa "da alama tana matukar son yaranta" zuciyar sa ta raya masa hakan.



Aysha kuwa biye wa Ammar ta yi suka sha hirar su sannan tace a bawa Anwar da har ya fara fushi an ki bashi waya da sauri suka sha hira sosai, har kudin wayar ya kare ba tare da ta shirya wa hakan ba, wanda har rashin jin dadin hakan ya bayyana a fuskar ta.


Ajiye wayar tayi a gefen ta ta dago kanta, idanun ta suka fada cikin nashi, sauke kanta tayi kasa tana wasa da yatsun hannun ta, tsahon mintuna biyar ta ga ya miko mata littafin hirar su mai dauke da tambaya kamar haka...



"kina da hoton yaran ki, ki nuna min ina son ganin su, I just want to see them" daga yanayin rubutun mutum zai fahimci wanda ya rubuta daga kasan zuciyar sa maganar ta fito, Bayan mintunan da ta dauka bata ce komai ba, sannan ta shiga rubuta masa reply, bayan ta gama ta mika masa.






*Afuwan my ppl ba nan naso tsayawa ba, buh I just have to*...





Share to others please.


NoorEemaan
07082281566


Thank you for reading my story #Abraham



I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851



🍇🍇ABRAHAM🍓🍓

*First edition*



WATTPAD
@NoorEemaan



🌙EID MUBARAK TO ALL MY FANS, MAY ALLAH ACCEPT OUR IBADAT, AND GRANT US JANNATUL FIRDAUS🌙



https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din



chapter 45-46


"I don't have their pictures (bani da hoton su)" ta amsa masa a takaice.

numfashi Mai zafi ya furzar a lokacin Daya karanta fassarar abin da ta rubuta kasancewar da Hausa ta rubuta masa.

Hakan Nan yaji ba Dadi, sai kuma ya dafe Kansa domin sai yanzu ya tuna cewa karamar keypad ce a hannun ta, ba kuma zai dauki Wani hoton kirki ya zama clear ba, but aleast ya so ganin hoton ko da yayi dishi-dishi kuwa daya fi farinciki fiye da amsar da ta bashi, domin sosai maganar yaran ya tsaya a ransa.


Dan satar kallon Aysha da kanta ke kasa yayi, sannan ya ja numfashi a ransa yace "mother of two, I really can't believe this" ya fada a ransa da mamakin wai yar yarinyar nan (Aysha) tana da y'ay'a har biyu.


Sha biyu ya wuce da kad'an Aysha ta bar dakin ta sauka izuwa kitchen Domin daura girki, saboda Sam bata son yin kuskure ko laifi ga Madam Gloria, domin bata ga alamun sauki a gare ta ba.


Tsaye take a kitchen ta dafa kitchen cabinets tana tunanin abinda zata dafa, can tunanin dafa alale ya fado mata domin tunda ta fara yi musu girki bata taba dafa alale ba, wake ta debo ta wanke domin already Mai kyau ne Babu bukatar sinta, sannan ta cire duka wannan baki-bakin na Saman wake, bayan ta gama ta debo albasa da attaruhu Hadi da crayfish ta gyara sannan ta zuba cikin blender ta mark'ada su duka har da waken.
Kana ta zuba a Wani babban bowl, Man kuli da manja ta zuba kan markadadiyyar kullin, domin bata so yayi ja sosai, sannan ta zuba maggi seasoning da spices masu Dadin kamshi ta sa cokali babba ta juya ingredients din da kyau sannan ta dauko dafaffen kwai da kifi wanda ta gyara ta yanyanka cikin kullin, sai ta dauko wasu mazubi masu kyau da shape kala-kala ta shiga zuba kullin alalen.
Dama already ruwan da ta daura a gas kan babban tukunya ya Soma tafasa Nan ta shiga jera alalen ciki tun kafin ya karasa dahuwa har k'amshi ya cika kitchen din zuwa falo...

Daga nan ta shiga hada cucumber juice Daya Sha kayan Hadi.

bayan ta gama ta zuba komai a warmer, juice din dama ta zuba a jug ta saka a fridge, sannan ta gyara kitchen din, ya dawo fess.

Warmer daya ta ajiye a dinner da cucumber juice, sannan ta dauki na Abraham da juice din shi ta nufi sama ta ajiye masa.

bata Jin cin komai, Hakan yasa ta sauko kasa ta hada quaker oat ta koma sama, har zata wuce dakin ta sai ta dawo da baya ta shiga dakin sa.


Zaune yake ya kurawa tray din abincin ido ba Tare da ya taba ba, tausayin sa taji Mai tsanani a ranta, ajiye cup din quarter oat akan centre table tayi kana ta shiga serving din shi, bayan ta gama ta ajiye masa a gaban sa sannan ta dauki quaker oat din ta daya Sha Madara ta koma gefe ta zauna ta shiga Sha a hankali, duk da cewa bata fiye son quaker oat ba saboda dan yaukin sa, amma hakan ta daure ta shiga Sha kadan-kadan.



Abraham kuwa kallon ta kawai yake, sai kuma ya dauke Kansa yayi gyaran murya, saurin dago kan ta tayi ta kalle shi, ba tare da ya kalle ta ba yace

"come and join me"

shiru tayi tana tunanin abinda yace, sai dai nuni da abincin da yayi ya sa ta fahimci abinda yake nufi, cikin sauri ta girgiza kanta, hawayen da ba ta San ko na menene ba ya cika idanun ta.


Dan zaro mata ido yayi Hadi da Kara hade fuskar sa yayi mata nuni da abincin, Wata shakkar sa ce ya shige ta, a sanyayye ta shiga can guiwa har ta iso gefen sa, da kallo ya shiga bin ta cikin admiration, domin yanda take Jan guiwar ta ya fito da yarintar ta kwarai.


Addu'ar su irin na christian a yayin cin abinci yayi kana ya sa spoon ya yanki alalen ya Kai bakin sa, lumshe ido yayi saboda zallan Dadin daya ziyarci harshen sa, sosai yake yaba kwarewar ta a ransa, domin Babu girkin wacce ke masa dadi kamar na Aysha yanzu.

A hankali ya Bude idanun sa da tun sanda ya fara tauna abinci suke a rufe, ganin kanta a kasa bama ta da alamar cin abincin yasa a hankali ya debo alalen a spoon ya mika mata, a hankali Aysha ta dago ta kalle shi, sai kuma tasa hannu kan spoon din ta dauki alalen, a hankali tasa a baki ta fara tauna, bai kara kallon ta ba ya cigaba da cin abincin sa.


Aysha kuwa ta cigaba da shan quaker oat din ta domin bata so ya kara bata alalen domin bata Jin cin abincin yanzu...



Bayan ya gama ci ya sha cucumber juice dinsa ta tattara wajen ta fita da kwanukan, tana sauka ta hango Madam Gloria hakimce kan dinning table tana cin abincin, gabanta ne ya fadi, amma ta dake....



"ke! wa kika kai wa abinci?"

Madam ta tambaya cikin muryan ta Mai kama da fada-fada.

cikin rudu Aysha tace
"hm.....hmmm yallabai na...na kai wa"


"Hmmmm... ya ci iya cin sa a yanzu, domin daga rana irin ta yau zai bar wanna duniyar yabi iyayen sa, idan yana bukatar kari ma ki kara masa, bai dame ni ba"

ta fada a bayyana, amma cikin yaren Igbo wanda hakan yasa Aysha dake zaro ido kasa gane me ta ce.


Madam Gloria kuwa hannu tayi wa Aysha alamun ta bar gaban ta, cikin sauri Aysha ta nufi kitchen har tana tuntube.

Da gayya ta shiga wanke-wanke a hankali gudun kada ta fito ta tarar da madam Gloria, aikuwa sai bayan mintuna talatin ta fito, ajiyar zuciya ta sauke ganin babu Madam a dining table, hakan yasa ta nufi upstairs da gudu kamar wacce taga abin tsoro.



*********

6:00pm
Bayan Aysha ta gama dinner Mai sauki, ta ajiye na madam a dining table, sannan shima ta kai masa na sa dakin sa...

Dakin ta ta fada tayi wanka, bayan ta gama ta daura alwalan magriba ta fito, tana cikin shiryawa aka kira magriba.


Bayan tayi sallah ta kishingida da jikin gadon ta, ba tare da ta shiryawa Hakan ba Wani bacci Mai Dadi ya dauke ta.



*1:45pm*
AYSHA

A firgice ta farka cikin tsoro, sak'amak'on baccin da ta Yi Mai tsayi, cikin sauri ta mike salati dauke a bakinta, dafe gefen kanta daya tsara mata tayi, sannan ta nufi toilet domin daura alwalan Isha da bata Yi ba.


*********

Mintuna goma Sha biyar ya dauke ta yin sallah'n Isha Hadi da sha'afi da wutiri.

Bayan ta iddar ta zauna shiru, tunanin Abraham ya shiga yawo cikin brain din ta, kasa zama tayi Hakan yasa ta mike domin ta je gareshi, duk da cewa dare ne Amma ta San cewa matuk'ar bata je ba hankalin ta bazai taba kwanciya ba.


A hankali ta tura kofar dakin ta shiga, gabanta ne ya bada ras sak'amak'on ganin sa zaune ya kura wa hanyar shigowa ido, tamk'ar Yana jiran isowar ta ne.


Kallon gefen da ta ajiye masa abinci tayi, taga ko taba wa bai yi ba, sosai taji ba Dadi a ranta...


"Kila yunwa yake ji shiyasa ya kasa bacci"

Ta fada a ranta yayin da fuskar ta ke k'wabe kamar zata saki kuka...

A hankali ta karasa Wajen abincin domin zuba masa sai dai...

Karfaffan hannun sa Mai tsayi ya daga mata alamun ta barshi, mamaki Hakan taji, a sanyayye ta dago tace



Please Login or Register in order to submit comment