Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bai fi 7seconds ba...
da kallo mai tattare da zallan tsana hadi da muradin cika mugun nufin ta a kanshi ta bishi, kana ta dawo da kallon ta ga plate dinta mai shake da chips with fried eggs, a hankali tace "shege mai taurin rai, dama kayi accident a hanya ka mutu idan ka fita, kaga ka sauk'ak'e min aiki, na rasa me yasa har yanzu na kasa cika burina akan ka, tabbas nayi kuskuren barin Dan zaki ya girma" ta fada cikin yaren igbo hadi da cizon yatsan ta mai dauke da artificial nails...


*ABRAHAM*
Har ya murda handle da niyyar shiga part dinsa, sai kuma ya tsaya cak! Sak'amak'on brain din sa daya tariyo masa lokacin da fasashen plate din nan ya caki kafar ta da karan da ta saki, Lumshe ido yayi a hankali ya furta "is it still in her leg? “(ko har yanzu yana tafin kafar ta).


Tamkar wanda ake ja, haka ya nufi hanyar dakin ta, a hankali ya tura kofar ciki...

Kwance ya hangota, jin bata motsa ba yasa shi fahimtar bacci take, wanda hakan ya bashi kwarin guiwan zuwa gareta duk da bugawar da kirjin sa ke yi...




Tafin kafar ta da yayi jaa ya kurawa ido, a hankali ya dire guiwar sa kasa, kasancewar rub da ciki tayi ya bashi daman ganin kafar da kyau, a hankali yasa karfaffan hannun sa mai laushi ya kamo kafar ta, sannan ya a hankali ya fara zare fasashen plate din...
motsa kafar tayi wanda yasa shi dakatawa, hadi da fatan kad'a ta farka har ya gama...



Sai daya bari baccin ta ya kara nisa kana ya cigaba, inda yayi nasaran cirewa, ajiyar zuciya amma boyayye ya saki, kana ya cilla fasashen plate din cikin wani karamin dust bin dake dakin, da haka ya Mike ya bar dakin zuwa nasa, inda cikin mintuna arba'in ya shirya cikin wani Turkish suit ya bar gida zuwa ginin company dinsa daya kammala, inda a cikin satin nan za a yi bikin bude shi....




*AYSHA*
Awa biyu ta d'auka cikin baccin da bata jin dadin sa ba Sam, kana ta farka...

mikewa tayi zaune tana marairaice fuska saboda zogin da ta ji daga kafar ta, a hankali ta kamo kafar, yayin da kwalla ta cika idanun ta, sai dai rashin ganin alamun fasashen plate din ya bata mamaki kwarai, a hankali ta kai hannu ta shafi daidai wajen ciwon, taji wayam babu alamun plate din a tafin kafar ta, sosai hakan ya tsaya a ranta domin iya tunanin ta bata cire da kanta ba, toh waye? ganin kanta ya fara tsarawa sak'amak'on tunanin da ta fara yasa ta mike tana Jan kafar ta har zuwa toilet....



*Bayan kwana biyar*

Zuwa yanzu Aysha taji sauki sosai a kafarta, domin tana yawan dannawa da ruwan zafi,, kuma tun daga lokacin da Abin nan ya faru bata sake ganin Abraham ba, wanda hakan yayi mata dadi, domin idan ta ganshi rasa nutsuwar ta take yi, ko gyaran dakinsa sai ta tabbatar baya nan take shiga ta gyara masa....




*madam Gloria*

Zaune take kan gadon ta, tana k'ark'ad'a kafa hadi da sakin murmushin zallan nasara, Bud'e tafin hannun ta tayi, inda wani karamin roba mai dauke da guba, wanda wanna gobar ke da hadari sosai, domin daga India tayi order din sa, inda ta hanyar sirri tayi har ya iso gareta, domin hadarin da gubar ke da shi, saboda idan aka yi kuskuren kamata tata ta kare, hakan yasa tayi taka tsantsan k'warai wurin ganin cewa ba a samu matsala ba har poison din ya iso gareta...


Duba agogo tayi ta ga karfe 5:30pm inda a yanzu ta San cewa Aysha ta gama dinner, ko tana daf da gamawa, mikewa tayi ta fito zuwa kitchen, inda maganin na tamk'e cikin tafin hannun ta....




Share fisabillah

Comment for more typing...



Thank you all for reading my novel 🍇Abraham 🍓





#Noor🦋



I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851



🍇🍇ABRAHAM🍓🍓

*First edition*


*WATTPAD*
@NoorEemaan



https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.




Chapter 27-28


Tamk'ar barauniya haka ta fito cikin sanda, jin shiru babu motsin kowa a falon ya sanya ta sakin ajiyar zuciya, kana ta ci mur ta nufi kitchen kai tsaye, nan ma shiru babu kowa, hakan yasa cikin sauri ta shiga bud'e poison din, amma ta kasa, dogon tsaki ta saki, saboda ba karamin dauri aka masa ba, karshe dai wuka tasa ta yanke saman robar da k'yar, atishawa ta jera sau biyar, saboda karfin gubar da ta shak'a, gumi ta share, kana ta mayar da kallonta ga tukunyar dake ta tashin k'amshi mai dadin gaske...



Leka waje tayi ta ga babu alamun tahowar kowa, hakan yasa ta bud'e tukunyar, inda porridge yam din ke ta tafasa, murmushi ta saki, domin hakan yayi mata daidai, juye robar guban gabadaya cikin tukunyar mai dauk'e da porridge yam din tayi, inda dama ta cewa Indo ayi wa Abraham shi kadai, dama ka'idar gidan ne mai girki bata d'and'ana abincin da za ta yi wa masu gidan, idan ma ka yi tasting a bakin aikin ka.



Babban spoon ta saka ta jujjuya, rufe tukunyar tayi ta fita da sauri, inda taje toilet din dakinta ta yi flushing robar hadi da wanke hannun ta da hand-wash sosai saboda karfin gubar, fadawa tayi flat kan gadon ta, yayinda katon cikin ta da kamar ana kara masa girma kullum yayi tsalle, dariya zallan mugun ta ta saki tace "you re dead already Abraham hhhhhhhhh"



★★★

Aysha da ta fito daga toilet kuwa, cikin sauri ta sauko tuno abinda ta dora kad'a ya kone...

Shigar ta kitchen ya haddasa mata wata fad'uwar gaba da har yasa ta dafe kirjin ta, "Ya Rahman" ta furta saman labb'anta masu taushi da kyalli.



Idanunta ne ya kai kan saman murfin robar guban da madam Gloria ta yanke, wanda ta manta bata dauka ba, a hankali ta tsugunna hadi da dauko shi, while kirjinta ke cigaba da bugu kallon robar tayi ta ga anyi rubutun, amma ko harafi daya bazata iya pronouncing ba, cilli tayi dashi cikin dan kwand'on shara dake kitchen din, ganin wuka cikin sink ya bata mamaki, domin ita dai ta wanke komai ta mayar muhallin sa, ganin spoon again gefen sink ya kara bata mamaki....


"waya shigo kicin (kitchen) din nan?“ ta fada cikin karyewar zuciya..


Bude tukunyar girkin tayi, kana ta mayar ta rufe tana sauke numfashi, ganin kuma ya dahu ne yasa ta yi turning off gas hadi da dauko had'add'en warmer ta juye ciki...




Wanke komai tayi ta kara kyar kitchen din, dama ta gama girkawa madam Gloria abinda take so, fito da komai tayi kan dinning table, sannan ta koma dakin ta saboda lokacin magriba ya kusa...





*6:55pm*

Cikin sassarfa ya shigo cikin falon, idaunsa har lumshewa suke, ga wata azababben yunwa da yake ji, domin tun safe ruwan Black tea ne kawai a cikin sa, a matuk'ar gajiye yake sosai, sak'amak'on gajiyar daya kwaso, domin bai taba zirga-zirga irin na yau ba...

Cikin kulawa madam Gloria ta tare shi hadi da bashi side hug, "welcome back my son, my son has suffered today, Undu nwamu nkwo (Sannu yarona kaji) " ta karasa da yaren igbo.



Murmushi saman labb'a kwai yayi, yayin da idaunsa na kara lumshewa, kamar wanda aka tilasta wa yin magana yace "mum am badly hungry"


Wani irin sanyayyar dadi ne ya ratsa zuciyar madam Gloria, kansa ta shafa tace "toh son bari na kira Aysha tayi serving dinka"


A hankali ya bud'e idanunsa kana ya lashe labb'ansa da suka dan bushe kadan yace "lemme fresh up first"


"OK son, zan sa ta kawo maka dakin ka"

Ta fada tana bin bayan shi da wani mugun kallo hadi da murmushin samun nasara, sai daya bacewa ganin ta sannan ta saki wata katuwar dariya amma kasa² har da buga cinyar ta, duk da bai kai ga cin abincin ba, amma wani dadi ne ke ratsa ta, domin ta hango alamun NASARA a yau, domin abu ne mai wuya Abraham ya nemi Abinci a k'aran kansa...



*ABRAHAM*

Yana shiga dakin sa ya shiga toilet hadi da cika ruwan dumi a bathtub ya fada ciki, ya dauki tsahon mintuna goma a ciki, yayin da yake jin gajiyar na warware wa yana barin jikinsa a hankali...


Madam Gloria kuwa sawa ta yi lubabatu Kiran mata Aysha, inda babu bata lokaci suka sauka tare da ita, a yatsine ta kalli Aysha tace "ki dauki Abunshin (Abinci) yarona ki kai masa part din sa"



Cikin ladabi Aysha ta amsa da "toh" duk da fad'uwar gaban da take fama dashi, wanda sai kara tsananta yake...



Kitchen ta shiga, ta d'auko wani k'yak'yawan tray, dinning area ta d'awo ta saka warmer din cikin tray hadi da plate da spoon, sai roban ruwa, sama ta hau dashi, madam Gloria dake binta da kallo ta saki dariya kasa² cikin farinciki.





Knocking tayi har sau uku shiru, hakan yasa bakinta d'auke da sallama d'aya zame mata sabo ta tura kanta ciki, Lumshe ido tayi, domin kamar kullum dakin na wani irin kamshin na musamman, ware idanunta tayi, daram! Kirjinta ya buga da k'arfi sak'amak'on hango faffad'an bayansa da tayi, wanda babu riga, domin tsaye yake da towel a gaban dressing mirror yana shafa lotion, duk da yaji shigowar mutum, sannan kirjin sa ya buga domin ta, amma ko juyowa bai yi ba....




Aysha kuwa kamar Wacce aka dasa, kasa dago kanta tayi, tun kallon farkon da ta yi masa, domin sosai ya cika mata ido, controlling kanta tayi sak'amak'on hannun ta dake rawa, gashi ta kasa ajiye tray din, kamar yanda ko motsi k'wak'wara bata yi.



ABRAHAM kuwa hankali kwance ya shirya abinshi duk da tana dakin amma ko a jikin shi...

Cikin dagon wandon fari kal, hadi da black singlet ya shirya, roll on mai suna *Old spices* ya Murza a hammatan sa hadi da taje kansa sama² ya dawo bakin gado ya zauna tsahon mintuna biyar ba tare da yace komai ba....


A hankali ya sauke ganinsa kan ta, inda baya ganin fusk'ar ta sak'amak'on kanta dak'e tsunkuye, dan cizan labb'ansa yayi ba tare da kuma ya sake kallon ta ba, yace

"Am hungry, serve me!"



Rud'u ta shiga saboda jin amon husky voice dinsa, da kuma turancin sa da bata fahimci ko kalma daya daga ciki ba.
Amma sai tunanin ta ya bata cewa abinci yake nufin ta tabatar masa...

Dan haka tamk'ar mai tausayin taka saman tiles din ta nufi inda yake zaune, a hankali ta dire tray din kan Wani tum-tum dake gabansa, plate ta dauka ta fara serving din shi...


Sirarran hannun ta dake ta faman rawa ya shiga rarraba idanun sa a kansu, yana mamakin meke haddasa mata wanna rawan jikin...



Aysha kuwa abubuwa da dama sun dame ta, na farko kusancin su dake haddasa mata shiga wani yanayi na loosing control, na biyu kuma haka kawai kallon Abinci ke sata fad'uwar wanda bata taba Jin hakan ba, hakan nan bata yarda da abincin ba, duk da kyau, hadi da haduwar abincin...




Bayan ta zuba masa ta ajiye gabansa, gefe tayi ta shiga murza hannun ta, domin ta kasa barin dakin, a hankali ta Lumshe idanunta hawaye suka gangaro kuncin ta, hak'ik'a abinda take ji a zuciyar ta ba karami bane a yau, saboda bata taba faduwar gaba irin wanna ranar ba.




Share hawayen ta tayi, ta Bude idanunta inda ta sauke su kan doyar daya raba biyu da spoon, maimakon taga cikin doyar fari sai ta ganshi yellow shaar, ga wani kyalli da cikin doyar keyi kamar maiko-maiko...

kanta ne ya kara d'aurewa domin lok'acin da take fere doyar fari kal sosai yake, ba wanna ba, iya Sanin ta dai ko an dafa doya cikin shi baya wanna yellow'n ko da faten sa ne kuwa...



Take k'wak'walwarta ta kara hasko mata yanda ta ga kitchen dazu, so take ta furta wani Abu amma ta kasa ganin ya kai lomar farko bakinsa...


Wanda ya kara hadd'asa mata wata faduwar gaba mai tsanani, ganin yana kokarin kai loma ta biyu bakinsa yasa da gudu ta nufe shi, ta ture hannun shi, inda Abincin ya zube har kan farin wandonsa...


AYSHA
duk da tsananin tsoron da take ji a dalilin abinda ta yi masa, amma bata da zabi, sannan bata damu da hukuncin da zai biyo baya ba matuk'ar ta samu ta hanasa cigaba da cin Abincin...



"ka... ka... ka... yi hakuri dan Allah da Annabi, wallahi hankalina bai kwanta da Abincin nan ba, duk da ni na dafa, kayi hakuri yanzu zan je in dafa maka wani Abu mai sauri kaji" ta karasa cikin yanayi na rud'ewa da zubar hawaye masu zafi...



*ABRAHAM*

Zuba mata ido yayi, yana kallon kananan labb'anta masu moving very fast, ba dan ya fahimci ko kalma daya daga maganganun ta ba, illa yana mamakin dalilin barar da lomar Abincin da yake kokarin kai bakinsa...
Me hakan yake nufi?




Aysha kuwa cikin sassarfa ta nufi hanyar fita daga dakin, har ta dora hannun ta a handle ta ji ihun sa...
"Arrrrrrrh!!!“

A razane ta juyo, inda ta gan shi har ya sauko kasa kan guiwar sa hannun sa biyu dafe da cikin sa, yayin da ya zuba mata idanun sa da suka yi wani irin jaa tashi daya hadi da tara ruwan hawaye cikin su...


(Not edited) 🤒



What's your opinion on this episode reader's???




Share✅
Comment✅



NoorEemaan🦋
07082281566




I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851




🍇🍇ABRAHAM🍓🍓

*First edition*



*WATTPAD*
@NoorEemaan



https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.



_kuyi hakuri Na san page din yayi kad'an sosai am sorry, dan nayi alkawari ne shiyasa na cika, at least da babu gwara ba dadi , ba haka na so ba wlh, amma banda zabi daya huce haka, domin babu lokaci, kuyi manage da wanna in sha Allah ranar lahadi zan Baku update, karku yi korafi please_🤒





Chapter 29-30

(Not Edited)


Sandarewa tayi a tsaye sak'amak'on abinda take gani, "mike shirin faruwa ne yau ya Allah " ta aiyana a ranta yayinda hawaye wani na bin wani a fuskar ta, jin ya kara sakin wani karan hadi da sulalewa kasa dafe da cikinsa da yake jin wasu azaba a cikin su.




Cikin firgicewa hadi da tsantsar tsoro daya bayyana a fuskar ta karara ta nufi wajen shi da gudu, cikin rud'ewa ta tallafi kansa da ke kansa tiles ta rike a tafin hannun ta, fashewa tayi da kuka tace "Dan Allah yallabai ka tashi, ka rufa min asiri, ni Dama ban yarda da wanna abincin ba, duk da ni na dafa, dan Allah ka tashi wayyo Inna ta!!!" ta karasa cikin amon sauti mai matuk'ar taɓa zuciya, Abraham kuwa wata mahaukaciyar yamutsa cikin sa ke yi, yayinda yake jin kamar ana saka wuka mai kaifi Ana dasa ko wani jijiya dake cikinsa, kasan maransa kuwa ji yake kamar ana diga masa narkakiyyar ruwan dalma a kai...





Still idanunsa na kan Aysha da yake bin ta da wani irin kallo dashi kan shi bai San ma'anar sa ba, ruwan hawaye ne suka taro a cikin kwarmin idanunsa, amma basu zubo ba, duk da sanyin air conditioner dake dakin, hakan bai hana jikinsa hadi da singlet din jikin sa sun jike da gumi daya karyo masa all of a sudden ba, saboda tashin hankali mara misaltuwa da yake ciki.





AYSHA

Kuka sosai take tana jijjiga kansa, fadi take ya rufe mata asiri ya tashi, ganin abin kara gaba yake yasa ta ajiye kansa a hankali ta fice da gudu zuwa downstairs....



Madam Gloria da ta yi pretending cewa tana kallo TV , amma azahiri Sam ba haka ne, ta kasa kunne ne taji kyakyawar labarin cewa Abraham is no more...


Jin takun sauk'owar Aysha yasa ta dago kanta da sauri, yayinda ta saki boyayyen murmushi, domin tsantsar tashin hankalin data hango a fusk'ar Aysha wanda ko tantama bata yi, alamun samun nasarar ta ne.



Gabanta Aysha ta zube, cikin shesheka take nuni da hanyar step din, kana ta fisgo maganar daya makale a makoshin ta... "zai mutu, ki taimaka min ki zo, yana kwance cikin mayuwancin hali"




"ke nutsu ki fadamin, me yana faruwa, waye zai mutu, me kika yi wa yarona, ki sani duk abinda ya samu yaron na bazan bar ki ba" madam Gloria ta fada hankali a tashe, kamar gaske.



Cak kukan Indo ya tsaya sak'amak'on jin abinda madam Gloria tace, wani sabon kukan ta kara sawa, kana cikin raunataciyyar murya tace "wallahi Allah na rantse ban yi masa komai ba"




Madam Gloria bata kara cewa komai ta nufi hanyar step da gudu, burinta ta kawai ta isa dakin, ba Wai dan ta damu da halin da yake ciki ba, a'a a k'age take ta je domin ganin halin da yake ciki, wanda take fatan ransa ya bar gangan jikinsa...




A tare ita da Aysha dake biye da ita suka sanya kansu dakin, sai dai shiru dakin, ba motsin komai, rarrabe ido madam Gloria tayi har ta hango shi kwance flat a can gefe idanunsa a Lumshe inda zuwa yanzu dishi-dishi yake gani.



Da gudu madam Gloria ta kara sa gareshi, kukan zallan tuggu da makirci ta fara yi tana fadin, "please son wake up! don't do this to me, somebody help me oo!" ta karasa tana jijjiga Abraham, amma daga ta cikin zuciyar ta farinciki ne fal cikinsa.




Cikin son juye komai ya dawo kan Aysha baiwar Allah tace " kin k'ade, kin shiga goma sha biyar bama uku ba, matuk'ar komai ya samu son, zaki gaya min me kika saka masa a abinci, ji ki kira min driver da mai gadi su tayani kai shi mota" ta karasa a tsawace mai hade da kuka.




Da gudu Aysha ta bar dakin gwanin tausayi, madam Gloria kuwa ta dire kan shi da karfi cikin halin ko in kula, wanda hakan yasa idanunsa dake Lumshe suka dan bud'e kad'an amma Sam mutum bazai lura ba ya bi madam Gloria dashi, cikin sauri ta Bude drawer din shi ta yi sa'ar samun wani kyakyawan farin leda, abincin cikin warmer hadi da na plate din ta juye cikin ledar, kana ta kulla da kyau ta jefar cikin karamin kwandon shara dake dakin, wanda tayi hakan ne domin koda za a yi bincike bata so ya tsananta, domin tasan dangin mahaifin Abraham basu da wasa, baya ga haka, matukar aka gano kalar guban, ba karamin matsala bace...




Dariya ta saka, wanda yasa Abraham mamaki kwarai, Sam baya son k'wak'walwa da zuciyar sa su yarda da abinda suke son bijiro masa, so yake ya furta wata kalma amma labb'ansa sun yi masa nauyi ainun, wani bakin duhu ne ya rufe idanunsa, sama² yaji tace "Dan banza mai tarin rai, dama ka mutu na huta" daga nan bai kara sanin inda kansa yake ba....




Jin takun haurowar su Aysha yasa da sauri ta koma kan Abraham tana jijjiga shi, sannan ta cigaba da kukan ta.



Hankali a tashe suka kama Abraham da kyar zuwa kasa, domin ginanen jikinsa yasa yake da weight, ba kuma dan yana da kiba ba, a'a kasancewar sa giant ne kuma mai gymming yasa haka.


Babu bata lokaci suka bar gidan, yayinda Indo dake tsaye a compound din gidan ta bisu da kallo hadi da zubewa kan guiwar ta ta saki kuka mai tab'a zuciya, taso bin su asibitin amma madam Gloria ta ture ta cikin shammata a lokacin da take k'ok'arin shiga motar, ta jima sosai tana kukan, kana ta ja kafarta daya yi sanyin kalau zuwa cikin gidan, cike da fatan Allah yasa ya rayu, domin Sam bata son shiga tashin hankali har yaje ga kunnen Inna da ta dan samu farinciki, kuma ko da wasa bata son wanna farincikin ya gushe.





Ta bangaren su madam Gloria kuwa gudu sosai driver yake falfalawa yayinda madam Gloria ke kuka tana surutai cikin yaren igbo, wanda ba komai take fadi ba illa jifan Abraham da kalamai marasa kyau hadi da yi masa fatan mutuwa, driver dake tuki ya kalle ta hadi da girgiza kai cikin tausayin ta, tabbas a yanayin yanda take kuka tana maganganun dole ta baka tausayi, domin mutum zai yi tunanin abin arziki take fadi, sanin cewa driver baya jin yaren Igbo yasa ta fadi abinda take so babu ko sha yi




Tafiyar mintuna ashirin da biyar ta kawo su wani had'add'en private hospital, cikin sanin makamin aiki nurses din suka tura shi zuwa emergency ward ganin halin da yake ciki, kasa zama madam tayi, burinta kawai Doctor ya fito ya sanar mata mutuwar sa, da babu abinda zai hana ta fasa kukan murna...



_5 hours later_

Dare yayi sosai, kuma har zuwa wanna lokacin babu wani doctor ko nurse daya fito daga emergency ward din bare ta samu damar tambayar sa, safa da marwa kawai take a matukar kage, sai da aka sake dauk'ar wasu mintuna talatin din sannan doctor ya fito yana sharce gumi, kai kace ruwa ne a fusk'ar sa, cire medicated glass din idanunsa yayi ya kalli madam Gloria yace "madam follow me to my office"




*my wattpad fans keep the comment going and please don't forget to follow my account and also vote my stories thank you*



Share to other group's please 🙏

NoorEemaan
O7082281566


10:41pm
Friday, 18 February.





I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851




🍇🍇ABRAHAM🍓🍓

*First edition*



https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din



*WATTPAD*
@NoorEemaan


*Ku tayani da Addu'a my lovely fans🥺*




Chapter 31-32

Cikin zumudi ta bishi tana fata a ranta taji labarin mutuwar sa kawai...

"have a sit madam" doctor yace mata.

Da sauri madam Gloria ta zauna, numfashi ya sauk'e yace "am very Angry madam, ta ya ya za a yi poisoning din mutum da guba mai matuk'ar hadari irin wanna, taya ma gubar da babu a kasar nan ta shigo Nigeria? waya yayi masa wanna mummunar aikin, madam, lemme tell you idan baki dauki mataki ba, ni da kaina zan dauka, duk da ban hada dangi da ku ba, amma dole wanda yayi poisoning wanna saurayin a hukunta shi, domin ya zama izina ga duk wanda zai shigo mana da irin wanna abun mai hadarin gaske kasar mu" ya karasa cikin murya mai nuni da zallan bacin rai da kuma nuna hak'ink'anin abinda ke cikin zuciyar sa, wanda kai tsaye mutum zai fahimci cewa shi din ba iya likita bane mai duba mara lafiya, har kishin kasar sa da Al'ummar ƙasar sa yake yi.




Sosai cikin madam Gloria ya duri ruwa har wani dan motsi katon cikin ta yayi, domin bata ga alamun wasa a tare da shi ba, kuma yanayin sa kadai da ta gani ya nuna cewa shi din mai arziki ne sosai, cikin sauri ta fashe da kuka tace "makiya ne ke son ganin bayan tilon dana, ni kaina zan dauki mataki doctor, bazan bari ba, na kuma gode da kulawar ka ga Dana, yanzu a wani hali yake ciki doctor?" ta fada gwanin tausayi a fili, yayin da can kasan zuciyar ta take muradin jin cewa ya mutu...



Numfashi mai zafi likitan ya furzar domin haka kawai yaji maganar Abraham din har ranshi, wanda ba komai bane face haduwar jini da Allah kan hada mutum da mutum dashi, siririn farin medicated glass din shi ya cire, hadi da hade hannun shi waje daya kan teburi yace "hakika ban taba ganin JARUMI kamar dan ki ba, duk da hadarin da gubar nan ke da shi, amma har yanzu yana Numfashi wanda hakan

Please Login or Register in order to submit comment