Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

••••


*BAYAN WATA BIYAR DA KWANA GOMA*

Cikin wadannan watannin abubuwa da dama sun faru, ciki har da zuwan Anty Sarah Gombe gidan su Aysha, ko Allah yasa mutanen su taimaka mata wajen tayata neman Abraham, domin cikin watannin nan ta sha wahala gaba-daya ta sake fita a hayyacin ta, sak'amak'on yawan mafarke-mafarken ma rasa kyau da take yi, har abun ya fara mata gizo, gaba-daya ta rasa nutsuwar ta, hakan yasa ta zo Gombe, sai dai abin mamaki duk bulayinta ta kasa gane gidan, unguwar ya sanja mata, komai ya kwance mata, amma bata hakura ba...

Kullum daddadare sai ta je kasan gada in da mahaukata da masu Bara ke kwanciya, nan take shiga Cikin su ta kwanta, washegari ta kuma cigaba da neman gidan amma bata samu ba, amma still bata hakura ba.



***. ***. ***.


*KADUNA*

"Aysha! Aysha!!"

A hankali Aysha ta waiwayo da murmushi saman fuskar ta domin ta san mai kiran ta.

Ta kara kyau, girma, da wani wayewa daya bayyana ƙarara a tare da ita, komai yanzu cikin aji da wayewar addini take yin sa, saboda mu'amala da mutane musamman yammata iri daban-daban hakan yasa komai tayi tana burge mutane, gashi yanzu ta kara ilimi sosai, turanci daidai gwargwado tana yi, tana kuma ji, kana tana tana iya rubutawa, tsakanin ta da Abraham yanzu babu musayar rubuta da takarda, ta kan yi mai magana da turanci shima idan yana bukatar abu zai fada mata da turanci.

hakika MM HARUNA ENGLISH ACADEMY sun yi kokari matuƙa wurin koya wa Aysha turanci, musamman da suka ga Abraham ya sake musu kudi...


"Aysha! Why are you so In hurry, Ina zaki haka?"

Bola da ta kasance yar ajin su ta fada. Ta su ta zo daya da Aysha sosai, duk da kasancewar Bola bayerabiya amma musulma ce, tana amfanin da sunan Yaren ta ne a makaranta, kasancewar tun tana karama da sunan aka fi kiran ta.



"Bola! my boss is coming back from Dubai today, i have to rush home so that I can made him some meals"




"Oh yeah i remember, that's nice, shall well?" Bola ta fada tana mata nuni da hanya alamun su cigaba da tafiya...

Yanda Bola tayi da hannu sai ya bawa Aysha dariya...


Nan suka cigaba da hira har suka zo wajen driver, suka yi sallama da Bola, Aysha kuwa ta shiga Mota suka nufi gida.



Tana zuwa gidan jakar makarantar ta kawai ta ajiye ta shiga kitchen, tunani tayi tunda yaje dubai kusan wata ɗaya tasan ba lallai ya samu abinci irin na nan Nigeria ba, hakan yasa tayi tunanin dafa masa abinda zai rike cikin sa sosai, had'add'en miyar efforiro tayi masa daya sha namomi da ganda, sákwárá take son Yi Amma Allah ya gani bata da karfin dakawa, hakan yasa ta tuka masa *pando yam* na leda, ai kuwa sak sákwárá haka yayi danko ya kuma yi kyau, bayan nan tayi masa pepper chicken, ta zuba komai ta jera a dining table sannan ta gyara kitchen.

Dakinta ta nufa domin yin wanka saboda har an fara kiraye-kirayen Sallah....


A gurguje tayi wanka ta shower gel wanda Abraham ya siyo mata, har yanzu bai kare ba domin bata fiye amfani da shi ba, gashi 2.5L ne gashi da kumfa sosai, ita kam bata fiye son shower gel ba, sai mita take a ranta wai sabulun nan bata son shi sai ya yi ta sa jikin mutum sulbi kamar tayi wanka da klin ko da ruwan sama.



Bayan ta iddar da sallar ta sauko falo ta zauna shiru, so take ta kira Inna amma kuma bata son damun su, saboda kafin ta tafi makaranta sun yi waya.




Har aka fara kiraye-kirayen sallar Ishaq bai zo ba, har ta kosa da zaman sannan ta damu da rashin karasowar sa har yanzu, fatan ta Allah yasa lafiya.



Kasancewar ta na da alwala ga Kuma hijab a jikin ta yasa ta mike ta koma gefe ta kalli gabas ta tada sallah, cikin sallah taji abu na dan kauri daga kitchen, amma bata motsa ba, haka ta cigaba da salla domin bazata iya katse sallar ta ba.



Daidai lokacin Abraham ya karaso gidan...
tun kafin ya shiga falon yaji kauri sosai, mamaki ne ya kama shi, yana murda kofar ya shiga yaga Aysha tsaye a gefe tana sallah a nutse, taku biyu kacal yayi Cikin falon yaji bumm!!!
Ƙaran ya fito daga kitchen, ga wuta daya fara ci bal-bal...

Cikin sauri da tashin hankali ya kalli AYSHA a tsawace yace "hey! Run, i said run outside my friend"

Amma Ina Aysha'n ka bata ko motsa ba sai sallar da ta cigaba da yi nutsuwa.

Cikin sauri ya nufi abin kashe wutar nan da ake manna wa a bangon ( fire extinguisher) ya zaro ta ya shiga fesawa cikin kitchen din, shima ya kare, wutan bai mutu ba ya sake zaro dayan ya cigaba da kashe wutan har ya mutu, sai mugun hayaki daya cika kitchen din har ma da falo, fitilar wayar sa ya kunna da kyar ya karasa shiga kitchen ɗin domin hayakin yasa baya gani sosai, murda gas din yayi zuwa off, inda ya tabbatar Aysha ta manta ne bata kashe ba, tukunyar mai dake kan gas ne yayi mugun zafi har ya kama da wuta, Allah yaso wutar bata ratsa pipe din silinder ba da tuni labari ya sha bambam.


Fitowa yayi falo ya zube kan kujerar yana sakin tari saboda hayaki daya shaka over, ya kuma gode wa Allah daya takaita.

Sai faman fadin "Thank you Jesus, Jesus is Lord yake". (Allah ya ganar da duk Wanda yake hanyar bata Ameen!)

Sai da tarin ya lafa ya d'ago kansa, a razane ya kai idanunsa inda Aysha take dazu, so his greatest surprise har yanzu tana nan hankali a kwance tana sallah...

Zaro ido yayi, "Jesus Christ" ya fada kana ya nufi wajen ta, yana zuwa daidai wajen ta tana sallame shaf'i da wutri.

Hannun ta ya ja da karfi ya mikar da ita, cikin fadan da bai san ya iya ba yace "Are You insane? Did you want to kill your self huun? da ban zo da wuri ba haka zaki bari wutar ta kama ta kona ki, bayan Kina da halin guduwa, ki tsaya all in the name of praying, wait! like are you for real?" Ya fada unbelievable yana jijjiga dan kafadar ta da karfi"



Kuka mara sauti Aysha ta sakar masa, cikin rawar murya tace "Am sorry! My religion, or i should say Islam is beyond your expectations, i have already started praying, i can't run, na yarda cewa idan yau kwanana zai rage ko na gudu ko na tsaya zan mutu, addinin Muslunci ba kamar sauran addinai bane, zan iya guduwa na katse sallar sannan na roki Allah yafiya, amma katse sallar is not Good ln Islam sai da wata Babbar hujja da zai iya fadawa Allah idan ya mutu, but na zabi na tsaya ne, domin Ina son gwada zama muslumar kwarai, jaruma kan addinin ta, zan iya sadaukar da rayuwa ta ga Muslunci and I will be happy idan na mutu ta silar hakan"



Jikin sa ne ya mutu, zubewa yayi kan cushion ya zuba mata ido kamar ya samu hoto, tabbas addini Muslunci ya girmama tunanin sa kamar yadda ta fada, suna kaunar addini su, sannan suna bada dukkanin nutsuwar su wurin yin ibada basa wasa, Musliman kwarai zasu iya sadaukar da rayuwa da dukiyarsu wurin kare addinin su.

A duk lokacin daya ji Aysha na karatun qur'anin ya kan ji tana burge shi har baya son ta daina, amma a yau saboda jarumtar ta, son addinin Muslunci ne ya mamaye ilairin zuciyar sa. (Allahu Akbar!)

Cikin mutuwar jiki ya mike bayan ya gama tunani, daf da ita yazo yace "Am sorry too for yelling at you" ya karasa cikin sanyin murya sannan ya ra6a ta gefen ta cikin sauri ya haura sama...



Yana shiga dakinsa ya cire kayan jikin sa, Sannan ya nufi toilet, shower ya sakar wa kansa, ya shiga dukan kansa zuwa murd'add'en jikinsa

sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke, fuskar Aysha ke masa gizo, murmushi tattausa ya saki, domin hakan ba bakon sa bane cikin kwanakin nan, musamman da yayi tafiyar nan, tunanin ta yaki barin zuciyar sa, da yayi tunanin ta sai ya dinga sakin murmushi shi kaɗai, tun yana ƙaryata cewa baya kaunar ta, basu dace da juna ba, addinin su da Yaren su ba daya, ta yaya zasu so juna har ya saduda, domin har lau abubuwa uku zuwa huɗu ke hana mu cigaba a ƙasar mu, nuna kabilanci, addinin, hadi da son kai.


Bai damu da kome mutane zasu ce ba, domin abinda mutane zasu ce bazai cuce kan sa ba, tunda ba abu mara kyau yake kokarin aikatawa ba.


Cikin wata murya mai cike da shauki yace "Yes!i can't deny or hide it any more, i love her, and I'm saying this from the bottom of my heart"
ya karasa faɗa yana shafa kirjin sa..



A gurguje ya gama wankan ya shirya cikin wasu pyajams masu taushi farare masu touches din green, ya fesa body spray din NIVEA DEEP FOR MEN.


Tun kafin ya karasa sauko wa ya hango ta zaune shiru tayi tagumi, sai ta bashi tausayi, bayan ya sauko direct dining table ya nufa, domin yayi missing abincin ta sosai, gyaran murya yayi, Cikin sauri Aysha ta taso ta fara serving din sa, Bayan nan ta nufi hanyar kitchen domin hayaƙin ya gama washewa, so take ta gyara.



"Where are you going to?"

" I want to clear up the kitchen" ta fada a sanyayye


"No come back, you can't do that alone" ya fada yana kai abincin bakin sa, bayan ya gama ci sannan ya ciro wayarsa dake aljihun wandon sa ya kira wani number inda ya ce gobe da safe yana so a zo a gyara kitchen din, sannan abubuwa da suka lalace a cire a saka sababbi...


Aysha dake jin duk wayar da yake taji ya bata tausayi, domin yayi tafiya mai tsayi ya kamata ace ya huta amma gashi daga dawowarsa ba hutu zai fara kashe-kashen Kudi.



Kasa shiru tayi, tace "Am so sorry please, it was a mist...."



"Shhhh! You don't have to apologize, you did absolutely nothing, and that's how God want it, so cheers ok?"

"Ok" tace tana jinjina kan ta, Sanyi taji a ranta ganin bai yi fushi da ita ba, hakika kyawawan halayen sa na burge ta, duk da kasancewar sa ba Muslimi ba, amma yana da zuciyar musulmai kwarai masu yarda da ƙaddara.



Mikewa yayi daga dining table, ya dawo falo ya zauna yace

"come with me"

"Okay" tace tana nufar kitchen, domin ajiye kayayyakin daya ci abinci dasu, sakin baki tayi tana kallon barnan da wutar tayi a kitchen, a sanyayye ta dawo falon ta zauna.



Gyaran murya yayi yace "so tell me about religion, i mean Islam"







Share
Comment



Noor Eemaan
07082281566




I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851




🍇🍇ABRAHAM 🍓🍓


*WATTPAD*
@NoorEemaan



https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din




Chapter 57-58

Cikin zallan mamaki ta kafe dashi da ido, yayin da shi ma Abraham ita ya ke kallon hadi da gyada mata kai cikin tabbaci.


Zaro beautiful eyes din ta tayi cikin mamaki, domin bata taɓa tunanin abinda zai ce kenan ba, "amma shi da ba Muslimi ba, meyasa yake son sanin abinda ya shafi addini Muslunci?"
ta fada a ranta, amma ko ba komai taji daɗi duk da bata san dalilin sa ba, amma tana son hira ko magana kan abinda ya shafi addinin Musulunci.


"You...you... mean i should tell you about my religion?" Aysha ta tambaye shi domin ta kara tabbatar wa.




"Exactly that's what I want, tell me come on" ya fada cikin k'aguwa da son ta fara gaya masa.


"Okay" Aysha tace tana dan murmushi.

Gyara zama tayi, ta saki, jikin ta tama manta cewa gaban yallabai Abraham take zaune, nan ta shiga gaya masa Meye Muslunci, abubuwa da Muslunci ya koyar, da yanda Muslimi zai tafiyar da rayuwar sa, da yanda annabawa suka bauta wa Allah, sannan da yanda Mala'iku suka bauta wa Allah, da kuma yanda yan zamanin da suka shude suka yi rayuwar su, sannan ta bashi labarin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama.

Sannan ta ɗora da bashi labarai kan rayuwar iyalan gidan sa, kissoshi dai kala-kala ta dinga bashi, a takaice komai dai wanda ya shafi addini da ta sani ta fada masa, tsikar jikin Abraham sai tashi take saboda abubuwan da take fada duk suna shiga kwakwalwar sa, suna ratsa jijiya da tsokar jikin sa, sannan sun samu muhallin zama a zuciyar sa.




Aysha kuwa sosai tayi kokarin wurin hada turancin ta domin yi masa bayanin yadda zai fahimta, domin wasu manyan kalmomi dake cikin abinda take fada masa, fassara su da turanci wuya zai yi mata, amma tayi ƙoƙarin fassara masa da sauk'ak'ak'iyyar turanci, kuma Thank God ya fahimta.



Shiru falon ya dauka, babu mai magana, domin ita Aysha har bakin ta ciwo yake mata saboda dadewar da ta yi tana Magana, idan bata yi karya ba, zata iya cewa tun da aka haife ta bata taɓa magana mai tsayi irin wannan ba, kallon agogo Abraham yayi ya ga karfe biyu saura Mintuna biyar, kenan haka suka jima suna magana bai sani ba ya fada a ransa.



Duk da yasan dare yayi, amma bazai iya yin shiru bai yi mata tambayar da ta fi makalewa a ransa ba, dan gyara murya yayi wanda hakan ya zame masa dabi'a, hakan yasa Aysha dago kanta, domin ta fahimci matuƙar yayi hakan toh akwai magana a bakin sa.



" Am.....You said every child was born as a Muslim, expect lf his parents changes his religion, how sure are you. (Kin ce ko wani d'a ko y'a a Muslim ake haifan sa sai dai iyayen sa su sanja masa addini, taya kika tabbatar da hakan)".


Murmushi mai sauti Aysha tayi tace
"Am not the one who say it, Allah subhana wata'ala said so in the Qur'an(bani na fada ba, Allah subhanahu wata'ala ne ya fada acikin kur'ani)"



Jinjina kai Abraham yayi cikin gamsuwa da amsar ta, sannan yace "one more question, you said earlier that i was born as a Muslim right, but my parents changes my religion, does that mean am a sinner, and will i go to hell? (Tambaya ta karshe, kince dazu an haife Ni a Musulmi sannan iyayena sun sanja min addini, hakan yana nufin Ni mai zunubi ne, sannan wuta zan shiga?)" Ya tambaye ta cikin iyakar gaskiyar sa, domin har ga Allah yana son sanin komai...



Gyaran wuyan hijab dinta Aysha tayi, tace "of course yes! Allah will asked you when you died, because you are no longer a kid, you re now an adult, you know what's right, so you can determine the best for yourself if Allah's will, and about you asking if you re going to hell, i can't say, because no one enters in between God and his servant, so Allah alone knows the best. (kwarai da gaske, Allah zai tambaye ka idan ka mutu, saboda yanzu kai ba karamin yaro bane, kai Babba ne, kasan abinda yake daidai, zaka iya zabar abinda yafi maka alkhairi idan Allah ya amince, sannan game ta tambayar ka ta cewa shin wuta zaka shiga idan ka mutu? Bazan ce ba, domin babu mai shiga tsakanin Ubangiji da bawan sa )"



***. ***. ***.


*SOME MINUTES LATER*

Tun bayan lokacin da Aysha ta bashi amsar karshe basu ƙara wata magana ba, sai yanzu daya dago ya kalle ta, yaga har ta zube kan kujera bacci ya dauke ta, sannan daga yanda take baccin Zai tabbatar wa mutum cewa bata shirya ba, baccin ya ɗauke ta.




Mikewa yayi ya nufi inda take, sosai baccin ya kara mata kyau murmushi yayi cikin shaukin so, a hankali yasa hannu da niyyar daukar ta zuwa dakin ta, sai kuma ya tsaya da hannun sa cak! sak'amak'on tuno maganar da suka yi, domin ya tuna Aysha tace haramun ne namiji ya taba jikin mace matuƙar babu aure a tsakanin su"


Duk da yana ganin addinin Musulunci is somehow difficult to him, domin ba a ciki ya taso ba, shiyasa yake ganin haka, but Yana son yadda komai na addinin ke da tsari gwanin sha'awa.



Ajiyar zuciya ya sauke, kana yace "my life" cikin shaukin so mai tsanani.
komawa kan kujerar ɗaya tashi a kai yayi kana ya kafe ta da ido kamar ya samu plasma.



Mintuna talatin ya dauka yana kallon ta, kana ya sauke sanyayyar ajiyar zuciya hadi da lumshe sexy eyes din sa.


Bai san yadda Zata dauka ba, bai san ko zata amince ba, but he just have to spell it out ko zai samu sassauci a zuciyar sa, bai taɓa sanin cewa ya kamu da son ta ba sai tafiyar nan da yayi Dubai domin duba hark'ok'in kasuwanci sa.

Haka ya dinga tunane-tunane har bacci mai daɗin gaske ya dauke shi kan kujerar...




*5:20am*

Tarrr ya bude idanun sa da suka bata awannin a rufe, idanun sa ya kai kan kujerar da Aysha ke kwance tana bacci, kiran sallar ya ji a masallacin dake unguwar, lumshe ido yayi, sannan ya kara buɗe wa, mikewa yayi tsaye, inda take kwance ya nufa, ya tsugunna gaban kujerar da take kai, har ya mika hannu da niyyar taɓa ta domin ta tashi sai kuma ya fasa.

Kujerar da take kwance ya shiga dan bugawa a hankali, a dan firgice ta farka tana yamutsa fuskar ta, saboda wuyan ta daya k'age sakamakon irin kwanciyar da ta yi.

"Wake up! It's time for your prayer" ya fada cikin whisper.


Idanun ta a rufe cikin baccin da bai gama sakin ta ba ta gyada masa kai, ganin ta farka yasa Abraham mikewa ya hau sama domin zuwa dakin sa.




A hankali ita ma Aysha ta mike ta hau saman, cikin sauri ta watsa ruwa sannan ta daura alwala ta fito ta sanja kaya, hijab ta saka Sannan ta tada kabbara..


Bayan ta iddar ta yi addu'o'in ta, daga nan ta dauki qur'anin ta.

Ta bude Surah Al-mu'minun (The believers) kenan zata yi Bismillah taji an turo Kofar...



Dago kanta tayi taga Abraham ne, sai hakan ya ɗan bata mamaki amma bata nuna ba, jikin kofa ya jingina bayan sa, sannan ya hard'e hannun sa a kirji yace "sorry for distracting you, i just wanna listen to the recitation of the Quran if you don't mind "



Mamaki sosai Abraham ke bata tun jiya, duk da tana farinciki da kulawar sa ga addinin musulunci, amma bata san dalilin sa na son Sanin abinda ya shafi Musulunci ba, murmushi ta k'ak'aro tace "okay"

Sannan ta yi Bismillah ta fara karatu cikin sanyayya kuma zazzak'ar Muryar ta mai daɗin amo.



Mutumin kuwa wani dad'i sosai ya shiga ratsa shi, yayin da nishadi ya mamaye zuciyar sa, sai faman Kada kai yake, domin daɗin da yake ji daga karatun qur'anin nan ya fiye masa dadin busar sarewa.



Bayan Mintuna arba'in Aysha ta rufe qur'anin ta sannan tayi addu'a kamar kullum ta shafa, ta dago kenan ta hango shi tsaye kamar dai dazu, ita zuciyar ta naga karatun har ga Allah ta manta yana dakin har yanzu.




Kanta a kasa tace "good morning sir"

"Morning!" Yace, bai kara cewa komai ba ya bar dakin...



Da kallo Aysha ta bishi sannan ta mike ta ajiye qur'anin ta, dakinta ta shiga gyarawa kafin gari ya karasa wayewa ta shiga kitchen...




*WASHEGARI*
FRIDAY MORNING


# Unforgettable day


Abraham ke tsaye a kofar gidan Alhaji Umaru kwangila yana k'wank'wansawa...


Mai gadi ya leko,
ya kuwa shaida Abraham hakan yasa shi washe baki sannan ya gaishe shi, hannu Abraham ya bawa mai gadi suka gaisa sannan yace yayi wa mai gidan magana.



Da sauri mai gadi ya tafi domin iskar da sakon Abraham, ya kuwa tari Sa'a ya samu Alhajin zaune a general falo Yana breakfast da Hajiyar sa, nan mai gadi ya sanar masa cikin girmamawa, duk da Alhaji yayi mamakin dalilin zuwan Abraham wajen shi domin ya ga baya shiga harkan kowa a unguwar, amma yace mai gadi ya shigo dashi setting room kafin ya gama breakfast, cikin sauri mai gadi ya fita, can ya shigo da Abraham kamar yadda Alhaji ya bada umarni.




Mintuna takwas da zaman Abraham, Alhaji ya shigo, ya mika wa Abraham hannu suka gaisa sannan cikin zolaya yace Allah yasa ba laifi yayi ba Abraham yazo kamashi...



Murmushi Abraham yayi, sannan yayi gyaran murya cikin harshen Ingilishi yace " I don't know how to say it, buh I... i want to convert to Islam, basan ta yaya zan fara ba, ina son na shiga musulunci, shiyasa nazo domin ka fadamin yadda zan yi in shiga, domin ban san kowa a unguwar nan ba bayan kai"


"Allahu Akbar!"
"Allahu Akbar!!"
"Allahu akbar!!!"


Alhaji Umaru kwangila ya dinga fada cikin maɗaukakin farin ciki, siririn medicated glass din sa ya zare kana yace "come, come , come here" ya fada yana ware wa Abraham hannun sa...



Rungume shi Alhaji ya yi, farin cikin shi yaki boyuwa, nan ya dage ya shiga gaya wa Abraham wasu abubuwan cikin addinin Musulunci, sannan yace masa babban masallacin da yake zuwa sallar juma'a nan zasu je, da zarar an iddar da salla zai karbi shahada, da haka Abraham ya fito daga gidan, bayan Alhaji ya jadadda masa cewa kafin su tafi yayi wanka, sannan yayi niyya a zuciyar sa cewa wanna wakan shiga addinin Musulunci zai yi.



Alhaji na komawa cikin gidan ya shiga fadawa matar sa da y'ayy'en sa, farin ciki sosai suka yi, sannan suka yi masa murnar samun rahamar Allah.




***. ***. ***.



*2:pm*
Abraham ke zaune a farfajiya babban masallacin cikin motar Alhaji Umaru kwangila, kasancewar a motar sa suka zo, ko ina yayi shiru ga duban jama'a dake salla cikin jam'i gwanin burgewa.



Yana cikin motar yana kallon su tsigar jikin sa sai tashi take, musamman da yake jin muryan liman dake karanta Surah At-tin cikin raka'ar ƙarshe, abu yaji yana biyo kuncin sa, hannu yasa ya shafa, yaga hawaye ne, cikin sauri ya share, sannan ya cigaba da kallon su har suka idar da sallah'n.


Bayan liman ya gama addu'o'i an shafa, sannan yace "A saurara" hakan yasa wasu mutane dake shirin fita suka dakata da fitar da suke da niyyar yi.



"Alhamdulillah! Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki mai kowa mai komai, mai yin yadda yake so da kuma lokacin da ya so, a yau mun karu, eh mun karu kwarai, domin wani bawan Allah ne zai karbi Muslunci a yanzu haka, Kuma yana cikin masallacin nan"

kabbara aka saka bakunan mutane a washe saboda farin ciki, duk da Abraham yace kada a bari mutane su sani domin shi saboda Allah ya shiga musulunci, basai duniya ta sani ba, amma ina liman ya kasa hakuri saboda farin ciki, hakan yasa dole ya sanar wa jama'a.



"Nan liman ya shiga addu'a yace "ya Allah ka shiryar da wadanda suke hanyar bata kamar Yadda ka ganar da wannan bawan naka"


"Ameen!!!"


Jama'ar wajen suka hada baki Wurin fadin hakan, Alhaj Umaru kwangila yana kusa da liman yana ta faman sakin murmushi.


Nan liman yace aje mota a shigo dashi, ai fa nan jama'a suka yi zuga wurin zuwa dauko shi, bawan Allah Abraham na zaune cikin mota ya ga an bude kofar mota kowa so yake rike shi domin kai wa liman, da kallo Abraham ke bin su, ya ga fuskar su dauke da murmushi, son addinin Musulunci na kara ratsa zuciyar sa, ashe haƙa muslumai ke son mutane? Ya fada a ransa.



Har gaban liman suka kai shi sannan kowa ya zauna ana kallon shi wasu har video suke daukan shi ciki har da Alhaji Umaru.



"Sannu yaro dan albarka, welcome to Islam" liman ya faɗa fuska a sake.


"Thank you sir"
Abraham yace cikin girmamawa, da dan murmushi

Please Login or Register in order to submit comment