Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a fuskar sa.


"Can You tell us why actually you want to convert to Islam, and is any one dragging or forcing you into Islam?"



Cikin husky voice dinsa dake a dake yace "i just love Islam, i mean I love everything about it, and no one is dragging me into Islam, am doing it for the seek of Allah, i love Allah, and I love everything concerning Islam too".




Liman yace "Attak-bir ya jama'a"


Jama'a suka ce "Allahu Akbar!"

Domin duk suna jin abinda Abraham yace kasancewar akwai manyan speaker da Mic🎤 dake gaban inda Abraham ke zaune.


Kallon sa liman yayi yace "repeat after me"


Jinjina kai Abraham yayi, liman ya kara cewa "say! Ash-hadu Allah ilaaha illallaahu, wa Ash'hadu anna Muhammadan rasulullah"

Ta cikin loudspeaker Muryar Abraham ya kara de ko ina, ya fara fadin kalimatul-shahada kenan ya kasa karasa wa saboda kalmomin sun yi masa girma domin bai saba jin irin su ba, hakan yasa liman ya dinga faɗa masa kalma bayan kalma, tsaf kuwa ya fada, yana gama faɗa wasu hawayen dadi masu sanyi suka zubo masa.

Nan mutane suka saka kabbara.


Liman ya kara cewa wani suna yake so, nan yace "i have no choice" domin bai san sunan muslumai ba, bare ya zaba.


Liman yace "if you permit me, i will make a choice of better name for you"



"Okay, i will really appreciate it sir" Abraham ya fada.



Murmushi liman yayi yace "As from today your name is Abubakar Assadik"


"Abubakar Assadik" Abraham ya maimaita sunan domin sunan ya kwanta masa a rai.


Nan liman yace " Masha Allah, Alhamdulillah, You re now a Muslim. Congratulations Abubakar assadiq, welcome to the religion of peace"



Nan mutane suka shiga yi masa murna, hadi da fatan alkhairi, Abraham tsakayau yake jin sa tamkar an cire masa wani abu mai nauyin gaske a kan sa, wani iska na ni'imar Allah ke ratsa shi...



Bayan duk mutanen sun
watse, ya rage daga liman, Abraham da Alhaji Umaru, nan dai liman ya koya masa yan kananan abubuwa irin su alwala, wankan tsarki da sauran abubuwa masu sauƙin fahimta, tsaf kuwa Abraham ya rike, ya kuma ja Abraham sallar azahar sallar domin ya fara ganewa, daga nan ya bashi wasu littattafai na addini masu fassara da turanci, sannan ya karbi numbern Abraham din kan ya ware lokaci ya dinga zuwa suna karatu, da haka suka yi kyakkyawar sallama zuciyar kowa fal farin ciki...



Bayan sun iso gida, Alhaji Umaru kwangila ya kara mai yan wa'azi, sannan ya roki Abraham alfarman kan yazo yaci dinner yau a gidan sa, mutuncin Alhaji Umaru kwangila da Abraham ke gani yasa shi kasa musu masa, da haka suka yi sallama kowa ya shiga gidan sa...



Aysha dake tsaye tana jera warmers a dining table ta dago kanta ganin an turo Kofar general falo, Abraham ta ga ya shigo, abin da ya bata mamaki jin yace

"Assalamualaikum"

Kasa amsawa tayi, sai bin fuskar sa tayi da kallo, saboda wani haske mai ban sha'awa ɗaya mamaye tun daga kafar sa har izuwa fuskar sa, wanda ba komai bane face hasken Musulunci.


Murmushi Abraham yayi sannan ya kara cewa "Assalamualaikum" Hadi da nufo inda take tsaye...




Share fisabilillah.


Comment for more typing...





NoorEemaan
07082281566




I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851


🍇🍇ABRAHAM🍓🍓


*First edition*



*WATTPAD*
@NoorEemaan





https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din



Chapter 59-60


Daf da ita ya matso ya hura mata iskan bakin sa, sannan ya kara cewa "Assalamualaikum" a karo na uku.


Dan firgigit tayi daga tunanin da ta faɗa kana cikin cracking voice tace "wa...wa...'alaikum Sa...salam"

sai tayi kasa da kanta, bambarakwai haka taji a lokacin da yayi sallama,
domin abu ne wanda bai taba yi ba.



A hankali Abraham ya dire gwiwowin sa a kan tiles, kana ya kafe ta da kyawawan idanunsa, jikin Aysha ne ya fara rawa, ganin namiji babba a gaban ta kan guiwar sa, sannan ita da ta kasance yar aiki a gidan sa meyasa zai dinga yi mata haka?

Ta lura yanayin sa da komai nasa ya sauya, musamman a yan kwanakin nan.



"Ụwammmmm!" Abraham ya ja sunan da wani salo da bai san ya iya ba. (Ụwam yana nufin Duniya ta da Yaren igbo)


Aysha kuwa lumshe ido tayi, har wani bubud'ewa kofofin gashin jikin ta su ke yi saboda yadda sunan ya ratsa ko wani sassa na jikin ta, sannan taji sunan ya burge ta ainun ya kuma tsaru a kunnuwan ta duk da bata san ma'anar sa ba.




"Will you be my wife?" Ya tambaye ta kamar zai sakar mata kuka, domin ya kai gejin da bazai iya cigaba da boyewa ba.


Jin abinda yace ne yasa Aysha saurin ware idanun ta, ta kafe shi da kallo cikin rudu da daurewar kai.



Abraham kuwa kansa yake jinjina mata cikin tabbacin abinda ya fada, sannan ya ɗan ƙara motsa wa daf da ita sosai yace "will You marry me please, i love You. Since from the First day we meet in the tricycle my heart beat for you, don't say no please"
ya karasa yana kama kasan skirt din jikin ta ya damke, kamar ba Abraham ba, mamakin kansa yake.



Wani sabon mamakin mai tarin yawa ne ya sake lullube Aysha, murza idanun ta tayi, domin gani take kamar gizo idanunta ke mata, anya Abraham ne wanna, ko dai ya sha wani abu ne, ita Aysha indo yake so, yar aikin gidan sa, gaba-daya kanta ya kulle ta ma rasa wani tunani zata yi.


"Please say yes! i mean every single word i said to you, i have never sees you as a house girl or look down on you. I always sees you as a special human in my life, which my mouth can't explain or describe how special you are in my heart, please accept the love that i have for you"



Buɗe baki Aysha tayi tana kallon sa, ta zama so speechless, "yanzu wanna had'add'en guy ke Sona haka" ta fada a ranta yayinda wani hawaye Mai sanyi hadi da dariya suka zo mata a tare, sai tayi saurin rufe bakin ta cikin kunya ta ruga up stairs da gudu.



Da kallo Abraham ya bita yana sakin sanyayyar ajiyar zuciya, at least yaji sanyi a ransa, ko da bata son sa, amma kuma bata nuna tsanar sa ba, zai kuma yi iya kokarin sa Wurin ganin ya koya mata son sa, bazai kara mistake din da ya yi kan Nonye ba, a yanzu idan yana son abu zai fada, domin rashin fada zai iya sa ka rasa dama ko ka makara wurin fadawa wa wacce kake so ko wanda kake so.


Gashin sa ya shafa, sannan ya bi bayan ta cikin sauri.


*AYSHA*
Sam bata ji haushi da ya ce yana son ta ba, duk da bata san ko tana son shi ko a'a ba, amma taji wani sanyi a lokacin daya furta mata yana son ta.



"Ko hakan na nufin nima ina son sa?" Ta tambayi kanta a shagwabe.


Sai kuma ta ta6e baki kamar zata yi kuka, tuno suna da bambancin Addini.

"koda muna son juna bazamu iya auren ba saboda bambancin Addinin mu" ta fada a hankali cikin sanyin guiwa.


Dadai lokacin Abraham ya karaso bakin kofar dakin ya tsaya, yayi knocking har sau uku, jin shiru Bata ce komai ba, sai ya cije lips dinsa Yana kokarin yin dariya, domin abin na dan bashi dariya da mamaki a lokaci daya, ganin wai shi ke bin Aysha saboda ta bar shi ta tafi, ba kaɗan ba kuma yake jin daɗin yanayin da suke ciki.




Dan gyara murya yayi yace "Please come and serve me, am starving"

(Ki zo ki zuba min abinci, yunwa nake ji)

Yana fadin haka ya bar wajen, bai gama sauka daga step case din ba ya ga ta buɗe kofar ta fito, amma bai juyo ba, gudun kar ya kara mata kunya.

Aysha kuwa Sam bata so ta ji mutum na jin yunwa, duk da cewa ita din ba mai son abinci bace sosai.



Kamar mara gaskiya haka ta sauko sum sum ta nufi dining table inda yake zaune ta fara serving din shi, kanta a kasa sai jin idanun sa take yana yawo a kanta, hakan yasa hannun ta ke rawa.


Abraham kuwa kunya ba abu bane Mai burge shi a da, amma yana fara gani a fuskar AYSHA sai hakan ya zama ado dake kara masa son ta.



***. ***. ***.


Da misalin ƙarfe uku da da Mintuna arba'in Aysha ta iddar da Sallar la'asar ta fito, domin fara hada girkin dare, saboda girki mai dan ɗaukan lokaci take son yi yau.



Har ta fara taka matatakalar bene domin saukowa, but to her greatest surprise bayan Abraham ta hango tsaye ya fuskanci gabas yana sallah.


"Mahammadur Rasulullah! Kamar sallah na ga yana yi" Tace cikin zunzurutun mamaki.

Murza idanun ta, saboda gani take gizo yake mata, ga wani mugun kwarjinin daya yi mata gaba-daya ya cika idanun ta, duk da bata ga fuskar sa ba.



Da biyu, uku haka ta dinga tsallake matatakalar benen har ta sauko, tama manta babu kyau tsayawa gaban mai sallah, haka ta masa kuri da ido bata kuma motsa ba na tsawon seconds...

Can kuma kamar wacce aka mitsila ta fasa wani uban ihu, sannan kamar da a sigar waka ta fara cewa "wallahi shi ne, sallah yake, sallah yake, wayyo dad'i, ya zama Muslimi, maza idar da sallar ka bani labari, yaushe hakan ta faru bani da labari, alhamdulillah ya Allah"

sai ta dire gwiwowin ta a kasa ta yi sujjada tana godewa Allah, a gaba-dayan Rayuwar ta zata iya cewa babu ranar da yayi mata sugar kamar wannan, gefe ta koma ta dinga kallon yadda yake sallar a nutse kamar wanda ya jima a musulunci, ita kadai sai murmushi take na zallan farinciki.




Bayan Abraham ya idar da sallah, yayi addu'o'in sa da Yaren igbo da kuma turanci tunda bai fara koyan addu'ar Larabci ba, ya kuma yi imanin babu Yaren da Allah baya ji, sannan zai amsa in sha Allah.



Bayan ya shafa, ya juyo gare ta suka hada ido, ya ga fuskar ta dauke da murmushi, ya mayar mata da martani.

Sannan ya fada a ransa cewa har abada bazai taba manta wanna kyakkyawar murmushi da ya gani a fuskar ta yau ba sakamakon sallar da ta ga yana yi.



"Ụwammmmm! Nayi kuskure a sallar ko? I knew kina kallona, Please gayamin in gyara" ya fada yana kallon ta.



Wani abu mai girma gaske ta ji ya shiga zuciyar ta game da shi, wani tausayin sa taji musamman da tune din da ya yi magana.


"You did everything perfect, but when, how comes you didn't tell me? Ooh my God am so so happy for you gaskiya..." ta fada tana kallon sa



Mikewa yayi yana murmushi, sannan yace " Thanks you! is a long story, i will explain to you"


Shiru tayi, sai yanzu kunyar ihun da zu ya kamata, ya fahimci hakan sai kawai yayi murmushi dama yasan murna ne yasa ta dinga ihu daya kusan fasa dodon kunne sa.


Nan ya shiga gaya mata komai da komai, dadi sosai taji a ranta, ta kuma yi masa murna fiye da zaton mai zato hadi da addu'ar fatan alkhairi.




Dago kansa yayi ya kalle hadi da cewa
"tell me more about Islam, it make me feels happy" domin Yasan ta hakan ne kaɗai zata saki jikin ta su yi hira, saboda ya fahimci duk wata magana daya shafi addini tana son sa.




Aysha kuwa ta samu abinda take so, nan ta shiga gaya masa yadda zai yi ibadar sa tsarkake, saboda ta kara masa son addinin Musulunci sai ta ɗora da
cewa

"There's something you need to know, Christian always said Jesus which Isa Alaihissalam is the son of God, or they even called him God subhanallah! Which is prohibited.
Allah is alone, he has no son, no mother, no father not even a sibling.
(Akwai abinda ya kamata ka sani, kiristoci na yawan cewa Annabi Isa dan Allah ne, har ma su ce Allah, subhanallah!
Hakan haramun ne.

Allah shi kadai ne, ba shi da ɗa, ba shi da uwa, bashi da uba, ballantana kanne ko yayye)



Jesus is the servant of Allah, and if any Muslim doesn't believe in Jesus as the prophet of Allah there fore he's not a good Muslim.

(Annabi Isa annabin Allah ne, sannan duk wani Muslimi da bai yarda da Annabi Isa a matsayin annabi Allah ba, toh bai cika Muslimin kwarai ba)


What christians don't understand about Muslims is...
They thought we don't love Jesus, but the fact is we love him and we believe in Jesus as the prophet of God subhana wata'ala, not his son or God.

(Abinda kiristoci basu gane game da Muslimai ba shine, sun ɗauka bamu son annabi isa, amma gaskiyar maganar shi ne, muna son annabin isa, mun yarda cewa Annabi Isa Alaihissalam annabin Allah ne, amma bamu yarda cewa shi Allah ne ko dan Allah ba).


We also have four books Allah send to his prophet's which is
TAURAH
INJI
ZABUR
QUR'AN

(Sannan akwai litattafai guda hudu da Allah ya saukar ga Annabawan sa, sune...
INJILAH
ATTAURAH
ZABURA
ALQUR'ANI).




You see taurah was revealed by Musa Alaihissalam.
(Kaga an saukar da attaurah ga Musa Alaihi salam)


Inji, which Is the bible was revealed by Isa Alaihissalam who christian Called Jesus.


(An saukar da injila ga Isa Alaihissalam, wanda kiristoci ke kira Yesu)



Zabur was revealed by Dawood Alaihissalam.

(An saukar da zaburah ga Dauda Alaihissalam)


Qur'an was revealed by Muhammadur Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama.

(An saukar da Alkur'ani ga Muhammadur Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama).



Did you know among these four books, the christian has changes the inji which is the bible, if you go into the old statements there's a huge difference with the new statement now, they change almost everything, there's a chapter in the bible which i actually can't remember in the old statements, they describe how Jesus perform ablution and also faced the Qibla to pray, buh if you go through the new statement now it has totally changed, they edit those part which is also prohibited.

(Ko kasan cewa cikin littafan nan guda hudu, kiristoci sun sanja wurare da dama a injila, wanda suke kira da bible, idan ka duba ainihin injila da sabon da kiristoci suka yi akwai bambamce-bambamce masu yawa, sun sanja kusan komai.

Akwai wata surah a injila na ainihi wanda bazan iya tuna surar ba, an kwatanta yadda Annabi Isa yayi alwala sannan ya fuskanci alkibla yayi Sallah, amma idan ka duba sabon bible din yanzu an cire wanna wajen, wanda hakan haramun ne).


Numfashi Aysha ta ja Sannan ta sauke ajiyar zuciya, murmushi dauke a fuskarta ta cigaba da cewa

"i don't know how to say it, but am deeply happy you are now a Muslims, but there is one thing am afraid of..."

(Basan yadda zan fada ba, but ina matukar farin ciki daka dawo Muslimi yanzu, amma akwai abu guda da nake tsoro....)



"what's that?" Abraham yace yana dage girar sa daya.

(Menene shi?")



"How about your mum, ain't you afraid if she hears you re a Muslims now?"
(akan mahaifiyar ka ce, baka tsoro idan taji ka zama Muslimi yanzu).



Murmushi Mai ciwo Abraham yayi, sannan ya ce "shhhh!" You no nothing about Abraham's life, when the right time comes i will tell you ok"

("Shhhh! Baki san komai game da rayuwar Abraham ba, idan lokacin yayi zan gaya Miki kinji)


"Okay" tace tana jinjina kanta a sanyayye, yayin da kanta ke sake daure wa, ta ma rasa gane wanna wani irin uwa da da ne haka, domin bata taɓa gani ba Irin su ba...



*ƁAYAN KWANA ƊAYA*

Bayan Abraham ya gama breakfast ya kalli Aysha dake gefen sa a zaune, domin har ta saba matuƙar ta zuba masa abinci sai yasa ta zauna har ya gama, tun tana mita a ranta kullum yasa ta zauna kamar matar sa har ta daina.

As usually gyaran murya yayi yace "Ụwammm!"

Dagowa tayi ta kalle shi ba tare da tace komai ba.



A nutse cikin turanci ya fara cewa"ya kamata ki fadawa mummyn ki magana ta, ina so ayi bikin mu cikin satin nan, na gaji da zama cikin kaɗaici, ina so na gina sabuwar rayuwa mai cike da farin ciki, kuyi magana da ita Please, Ni Kuma zan sanar da Alhaji Umaru kwangila ya shige min gaba, domin bazan sanar da dangin iyayena yanzu ba saboda hakan zai iya bani matsala, ba kuma na son a samu jinkirta wurin mallakar ki, Please kuyi waya ki sanar mata komai game dani matukar kina son rayuwa Dani, zan ji amsa daga gareki idan na dawo, ki kula da kanki, i love You" Yana fadin haka ya bar dinner area zuwa waje domin tafiya aiki.


A sanyayye Aysha ke kallon sa har ya bace mata, gaba-daya tsoro ya kamata, bata san me Inna zata ce ba, har tsoron sanar mata take, tunanin zuwa wajen Anty bintu tayi hakan yasa ta mike da hanzari ta yi clearing dining table din, ta kai plates da cups daya yi amfani kitchen ta wanke, duk da Akwai mai wanke-wanke amma bata saba ayi amfani da abu ta dinga kallon sa ba tare da ta tsaftace shi ba .

Sama ta hau ta Sanja hijab dinta sannan ta nufi gidan Alhaji Umaru kwangila.


Bayan ta shiga gidan ta tarar da Hajiyar gidan ta fito da alama unguwa zata je, har kasa Aysha ta tsugunna ta gaida ta, a sake Hajiyar ta amsa sannan tace "tashi ki shiga, yar'uwar taki tana ciki"

"Toh, a dawo lafiya" Aysha tace, sannan ta nufi cikin gidan.


Tana shiga ta tarar da Anty bintu tana ƙoƙarin shiga dakin ta.

Dakin na ta suka shiga, suka zauna.
Cikin sanyin murya ta gaishe da Anty bintu, daga yanayin gaisuwar Anty bintu ta fahimci akwai abinda ke damun Aysha.


Bata yi kasa a guiwa ba, cikin kulawa ta tambaye ta mene ne ke damun ta.

Nan Aysha ta shiga sanar wa anty Bintu da komai har da auren ta da Abraham ke son yi.


Bayan ta gama mata bayani, anty bintu ta yi murmushi hadi da girgiza kanta tace "Indoooooo!!! Shine kike tada hankalin ki har haka, na zata wani abun ne, duk da akwai tarin kalubale, amma ki kwantar da hankali ki, yanzu ki kira Inna anan kiyi mata bayani mu ji me zata ce"
.

A razane Aysha ta kalli Anty Bintu, cikin Muryar wacce kuka ke son kwace Mata tace"wallahi tsoro nake ji Addah Bintu, bana son fushin Inna, ke kiyi mata magana Please"


Girgiza kai anty Bintu tayi, cikin son karfafa Aysha tace "karki ji tsoro, zan iya yin magana da Inna, amma ba zan yi hakan ba, zan fi so taji komai daga bakin ki, ki saka wa zuciyar ki jarumta, in Sha Allah alkhairi zamu je, amma kafin nan bari na tambayi ki, kina son shi"

Tambayar tayi matuƙar ba wa Aysha kunya, sai ta fada jikin Anty bintu tana cuwuikuye ta...



"Ke me haka? Oya tashi ki gayamin" Anty bintu tace tana danne dariyar ta.


Cikin shagwaba da sakalci tace"toh Ni ban san ko ina son shi, amma kuma Ban tsane shi ba"


Dariya anty Bintu tayi, ta lura Aysha na son Abraham, Amma yarinta bai bari ta fahimci hakan ba.


"Maza kira Inna toh" anty Bintu ta fada.


A sanyayye Aysha ta yi dialing number gabanta na bugawa, ringing hudu tayi sannan taji Inna ta daga, saboda tsoro ta ma rasa me zata yi sai ta fashe da kuka...


Salati Inna ta sa, cikin tashin hankali jin tilon yarta na kuka ta shiga tambayar ta damuwar ta.



Ganin haka yasa anty bintu ta bar dakin domin ta basu damar yin magana yanda ya kamata...



"Inna! kiyi hakuri, basan yadda zaki dauki maganar ba, ban zubar da ko ƙwayar tarbiyyar da kika bani ba, wanda nake aiki a gidan su, wannan da bai da Lafiya kwanaki"....

Katse ta Inna tayi da cewa "eh na gane shi, Meya faru?"

Nan Aysha ta shiga gayamata komai tiryen-tiryen har karshen, sannan ta ɗora da cewa auren ta yake son yi cikin satin nan.




Maimakon taji Inna tayi magana, sai ta ji kit ta yanke wayar.


Sabon kuka Aysha ta saka, wani sabon tsoro ne ya sake lullube ta.

Bayan Anty Bintu ta shigo, cikin kuka ta gaya mata yanda suka yi da Inna, dan jim tayi cikin wani tunani sannan tace "Aysha karki ƙara kiran ta, ki bari Inna tayi tunani kin ji ko, in Sha Allah zaku mallaki juna" da haka ta rarrashe ta hadi da karfafa mata gwiwa sannan ta koma gida.


Sukuku haka ta wuni, ko girkin dare bata iya fitowa ta yi ba, daga ta yi sallah sai ta koma gado ta kwanta.



•••••••••••••••••••••••••


Bayan Abraham ya dawo da kusan awa daya, tana ji yana neman ta amma tayi lamo kan gado bata ko motsin kirki, yazo ya bubbuga kofar shiru bata amsa ba, hankalin shi ne bai kwanta ba, domin yasan bata fita ko ina, cikin sauri ya sauka ka kasa, wuri mai gadi domin tambayar shi ko Aysha ta fita ne.



A kuma daidai lokacin ne kiran Inna ya shigo wayar Aysha, gabanta yayi wata mahaukaciyar bugawa, ta kasa daukan wayar har ta katse, kira na biyu ya sake shigowa, idanunta ne ya tara ruwan hawaye yayin da hannun ta ke rawa, cikin sanyin jiki ta daga kiran hadi da ƙara wayar a kunnen ta...





_ban wani nutsu nayi editing ba, kila ku ga typing errors_🤒




Share fisabilillah🙏


Comments☑️




Noor Eemaan
07082281566




I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851


🍇🍇ABRAHAM🍓🍓

*First edition*




*WATTPAD*
@NoorEemaan



https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din



_idan na ga ruwan comments, zan sake baku sabon Page zuwa dare_





Chapter 61-62


*INNAH*

"Na amince miki auren sa matuƙar kina son sa, kin dauka nayi fushi dake ne?"
Sai tayi murmushi irin nasu manyan mutane ta cigaba da cewa "ko daya ban yi fushi ba diyata, illah ina bukatar nazari da kuma tunani mai zurfi, shiyasa kike na katse wayar ba tare da nace miki komai ba. Kasancewar ya Musulunta ba yana nufin bashi da damar auren mace muslima ba, dan mutum ya na sabon Musulmi ba shi ke nufin Wanda ya dade a Muslunci ya fishi ba, babu Wanda ya fi wani a wajen Allah sai wanda ya fishi tsoron sa, dan haka bazan hana ki ba, basan me Allah ke nufi da yayi haduwar ku ba, ba kuma zan shiga tsakani ba, na kuma san ko baffan ki na raye zai amince matuƙar shi yaron ya cika sharuddan zama miji a gareki, duk da basan halayen sa ba, na san bazaki zabi wanda bai dace ba matsayin abokin tarayyar ki ba, na yarda da tarbiyyar ki, ina kuma kyautatawa zaton ya zama miji abin alfahari agareki, ko yan'uwa baffan ki bazan gaya wa ba saboda tun lokacin da baffan ki ya mutu da suka kwashe abinda ya bari ban kara gani karfa kowa da niyyar zuwa duba mu ba, sannan zasu iya cewa basu amince da yaron ba, dan haka bazan aika musu ba, na amince Miki, Allah ya tabbatar da alkhairi"



Hawaye Masu sanyi ne suka zubo wa Aysha, tana matuƙar kaunar Innar ta, hawayenta ta share ta ce"Nagode Inna, Nagode sosai"


"Godewa Allah indon baffan ta, sannan ina so ki zo gobe, ki taho gida, bayan an Daura auren sai ki koma gidan sa, duk da abun yazo a kurarren lokaci, akwai bukata ayi miki kayan daki komai kankantar su"


"Toh Inna zan fada masa" Aysha ta fada. Sannan ta ɗora da cewa

"Inna ina y'a'yana suke?"

"Suna lafiya, na aike su nan makota gidan jauro su siyo min barkono"



"Inyeee! Yarana sun girma har sun fara zuwa aike" Aysha ta fada cikin farin ciki.



"Eh mana, kamar yadda maman su ta girma ba, ita ma zata yi aure " Inna ta fada a zolaye.


Cikin kunya Aysha ta katse wayar

Please Login or Register in order to submit comment