Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a sanyayye...

gaishe su tayi, duk suka amsa, amma Banda Abraham, dake wasa da yaran sa kamar bai ji ta ba.

Ko da yaji bai ma san mezai ce ba, baya so ya dinga ganin ta, saboda yana tuno masa da abubuwan da suka aikata a gareshi, ana haka wayar Abraham yayi ringing ya duba ya ga mai gadi ne, ya picking call din inda mai gadi ke sanar masa cewa ga fa Madam Gloria ta zo, amma yaki barin ta ta shiga domin yaga kamar ta haukace, zuciyar Abraham na suyo, ransa ya ɓaci amma ya danne yace a barta ta shiga amma Kada su bari ta wuce farfajiyar gidan
gasu nan zuwa yana fadin haka ya kashe wayar sa.


Ya kalli Aysha da jajayen idanun sa yace ta shirya su wuce, Inna ta ce ya bari suyi karin kumallo, bai musu ba, duk bai iya cin komai ba, sai ruwa kadan daya sha, wanda ma ya kara kulle masa ciki amma bai damu ba, saboda halin da yake ciki.

Bayan ta shirya suka mike domin tafiya, Cikin turanci ya shiga yiwa Inna godiya sosai da yaba karamcin su, da ƙoƙarin su wurin kula da yaransa, ya kara da cewa bazai iya biyan su ba, Allah kadai ne zai biya su, ya kuma yi wa baffan addu'a sosai.

Inna bata ji duk abubuwan da ya ce ba, Aysha ce mai fassara mata, cikin jindadi addu'ar Inna ta shiga amsawa da Ameen.


Sai ya ajiye wa Inna bandir hudu na dubu ɗaya-daya, taki karba, da kyar da roko Inna ta karba daga hannun shi, da haka suka fito har bakin mota...

Su Ammar sai tsalle suke zasu shiga mota, basu wani damu da Inna ba tunda suna tare da Ammuh'n su.


Har zai ta da mota Suka tsinci Muryar Anty Sarah Cikin turanci tace "Abraham please zan bi ku, ba dan komai ba saboda na nuna wa Gloria cewa duk zakaran da Allah ya nufa da cara sai yayi, sannan ta gane cewa babu wanda ya isa ya kashe mutum sai lokacin da Allah ya dibar masa yayi" .

Shiru yayi ya ma kasa magana, Inna ce tasa baki kan ya tafi da ita, tana da gaskiya, jinjina kan sa yayi alamun amincewa.

Ta shiga bayan mota da su Ammar, kana ya ja motar, su Ammar suka fito da kansu ta window suna dagawa Inna hannu dake tsaye cike da kewar su itama tana daga musu hannu.




***********


Awannin ƙalilan ne ya kawo su Kaduna, saboda gudun da Abraham ya dinga yi a hanya.

Bayan sun shigo farfajiyar gidan tun kafin ya gyara parking yake jin hayaniyar Madam GLORIA da mai gadi daya toshe hancinsa saboda wari, amma hakan bai hana shi zazzaga mata rashin mutunci ba, domin yanzu haka kawai baya ganin girman ta bare tsoron ta.

Ta mirror motar sa ya hango yanda ta lalace, ta koma wata mahaukaciya girgiza kansa yayi sannan ya fito daga cikin motar, Aysha ta biyo bayan sa, Anty Sarah ta biyo bayan Aysha, sannan su Ammar ne karshen fitowa...



A zabure Madam Gloria ta nufo su, tana tafiya kamar barauniya dake tsoron aji takun tafiyar ta haka ta nufo su, cikin shock tana soshe-soshen.

Abraham ta fara gani tsaye kan kafafunsa, murza idanun ta tayi domin ta tabbatar, ta ga dai shi ne tsaye kan kafafunsa, sannan ga Aysha ta fito daga bayan sa, wani sabon mamakin ne ya sake rufe ta, tana mamakin Meye hadin Abraham da Aysha, bata gama shan mamaki ba sai lokacin da ta ga Anty Sarah ta fito daga bayan Aysha, wannan karon ta kasa rikewa.
Ihu tayi irin na rashin hankalin nan tace

"Wannan ba Sarah kawata bace? ba kin mutu ba, ta yaya kika dawo duniyar nan" sai ta sa dariya tana tafa hannu, da alama kwakwalwar ta ya soma tabuwa.


"Ni ba kawar ki bace, domin nayi nadama kulla ƙawance da mara imani irin ki, tabbas ina raye, ban mutu ba, sannan ina so ki sani cewa yaran da kike so kashewa tun bayan da kike kashe uwar su Nonye basu mutu ba, ga sunan da ran su cikin koshin Lafiya"

S daidai lokacin da Anty Sarah ta fadi haka, a lokaci su Ammar suka fito daga bayan ta suka manne a jikin Aysha.


Ƙwaƙwalwar Madam Gloria zai tarwatse, a kafatanin rayuwar ta bata taɓa ganin rana mai munin gaske irin wannan ba, ashe duk aikin da take yi da zuwa wurin bokaye a banza ne, tana ganin kamar Abraham kadai ya rage mata ashe ba haka bane? Kitson attachment din ta da kusan rabi ya warware saboda dadewa, hakan ya bawa cinyayen gashin kanta damar fitowa, ta shiga sosawa da karfi, kana ta saka ihu, kuka, hadi da dariya a lokaci daya.


Tana fadin "oh! No no this is not truth, i must be dreaming"
Sai ta matso daf da Abraham ya kauda kansa saboda wani bad odour Daya bugi hancinsa, cikin fitar zarewa tace "Kai kuma yaushe ka warke? Kana so kace bazan ci Nasara a kan ka ba? Toh karyar ka, Ni nan sai na kashe ka, sai na kashe ka, kuma na kashe banza, bari ma kaji ni ce nan na kashe uwar ka, na kashe Nonye, eh nice na kashe su Hhhhhhhhh" sai ta sa dariya tana rawa kamar yadda mahaukata ke yi.


Jikin Abraham ya shiga rawa, saboda ɓacin rai, Aysha ta rike hannun sa gam tana kokarin calming din sa down, Domin zai iya karya kasusuwan ta a halin da yake ciki yanzu, domin idan akwai kalmar daya fi TSANA ita yake wa Madam Gloria, ta kashe masa uwa, da mata, still hakan bai ishe ta, ina zata kai tarin zunuban nan?


Allah ne tsare su shi da ya'y'an sa, baya jin zai bari wata kalma ta hadu su da ita, domin a yanzu bata da mutunci, kima, da darajan da zai mata magana, ta gama ficewa a ransa tun lokacin da ya fahimci tana farautar rayuwar sa bare daya ji ta kashe masa mutane na musamman a garesa. Abu daya ya sani shine bazata kara rayuwa cikin gidan sa ba, ko ina zata je he don't bloody care, shi kam baya bukatar ta cikin rayuwar su.




Bayan ta gama haukar ta, ta kalli Aysha tace "ke kuma meya daku dashi, ta ina kuka hadu da har kika zama ta musamman a gareshi har kuka fito daga cikin mota daya, ai ni na kawo ki Kaduna ko? Toh maza koma kauyen ku, bana bukatar ki cikin gidan nan Kuma yar kau..."

Kafin ma ta karasa cikin son abin ya kona mata rai anty Sarah tace "ina kike so ta je? bayan nan gidan ta ne, ita din matar sa ce"

kasancewar Inna ta bata labarin auren su har da Musluncin da Abraham ya shiga.



Ai fa kamar an sake birkita ƙwaƙwalwar Madam Gloria nan ta ce "oho! dama son shi kike siyasa na zuba masa guba mai hadarin gaske domin yaci ya mutu, kika yi yadda kika yi bai ci dayawa bako" nan dai ta shiga surutai kala kala tana tona wa kanta asiri duk abubuwan data aikata, domin sauran notikan kanta masu amfani sun ƙarasa kuncewa.


Anty Sarah kuka tasa, domin HAKKIN RAI ke gara rayuwar Gloria.
Gashi duk abinda suka aikata babu riba.
Dama duk wani mai mugun hali baya cigaba ga misali nan a kansu ita da Madam Gloria, me ye ribar su? sun dawo kamar wasu halitta marasa cikakkun lafiya da hankali, gwara ita ma akan Madam Gloria data fara hauka tuburan...



Suna kallo haka madam Gloria tasa mugun gudu ta bar gidan tana faɗin zan kashe ka, ka jira Ni, yanzu zan dawo, yau zaka dawo gawa a Abraham!"
Da surutai kala kala dai wadanda suke binne a ranta take amayo su a yau.


Ko kallon gabanta bata yi, tafiya take tana fadin "zan kashe ka Abraham Patrick yau, Hhhhhhhhh" yau har da kiran sunan tsohon sa, tana fadin haka kuma sai tasa dariya.


Tana fitowa babban titi kamar wacce aka tura haƙa ta shige tsakiyar titi, babban mota ya kade ta, ya markade ta, babu mai iya gane kamanin ta abun babu kyawun gani, mai mota kuwa bai tsaya ba ya arce, haka madam Gloria tayi mutuwar wulakanci da Burin ganin bayan Abraham a zuciya da bakin ta.


(Ya rabb!!! Ka barmu da imanin mu, ka tsare mu da tsare war ka, ka kiyaye mu da kiyayewar ka, ka mana katangar karfe da mugayen mutane ya tawwabul Raheem)




Ta bangaren Anty Sarah kuwa sallama tayi musu ta nufin komawa garin su, ta kara neman tafiyar Abraham amma still abinda ya fada mata a Gombe ya maimaita mata, abu daya ya duba karamcin ta wurin tseratar da ya'y'an sa da ta yi, har ta fara tafiya ya biyo ta ya bata bandir biyu na dari biyar-biyar yace "Nagode da tseratar da rayuwar y'ay'a na da kika yi daga hannun kawar ki "


Da fari taki karba ya bar mata, domin ka'idar sa ce, idan ya yi niyyar bawa Mutum abu baya sake karba, Aysha da har yanzu suke tsaye ta ji dadin abinda yayi, bai jira godiyar ta ba ya goma wajen iyalan sa ya kama hannun su suka shige ciki.


Anty Sarah kuwa kuka tasa mai sauti tana waiwayon su, tabbas zuciyar Abraham mai kyau ce kamar iyayensa, har kalmar GODIYA ya furta a gare ta, bayan duk tarin laifukan ta.




Share share share Please



NoorEemaan
07082281566



I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851



🍇🍇ABRAHAM🍓🍓


*First edition*




https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din



*WATTPAD*
@NoorEemaan




Chapter 69-70



A sanyayye Abraham da Aysha suka yi wa kan su mazauni a kan kujerar general falo, domin al'ajabin Madam Gloria bai gama sakin su ba, yayinda su twins ke ta wasan su cike da farinciki hadi da yarinta da kananan throw pillow da suke kan had'add'un kujeru.



Abraham ya fito da wayar sa da bai fiye girma ba, amma sai mugun tsada ya latsa wata number ya kara a kunnen sa.


Bayan an daga, ya bada umarnin wa kamfanin masu decorations da hada daki su zo su hada masa dakin yara da dukkani abun bukatar su na wasa.


Ai kuwa mintuna arba'in na cika suka zo da motar company'n su, dakin Madam Gloria ya nuna musu, sannan yace komai na dakin a fitar su zubar, hatta fentin dakin sai daya sa aka Sanja, sannan suka shiga hada wa su twins daki.



Aikin da ya dauke su awa biyar kana suka gama.
Ya rabb! fadin kyau da haduwar dakin bata lokaci ne, tamkar babu halittar daya taba rayuwa cikin dakin saboda yanda komai ya dawo sabo fil gwanin kyau.

Bayan Abraham ya sallami mutanen da huge amount of money da suka chaje shi kana suka tafi.


A lokacin da su twins suka shiga dakin, Abraham ya sanar dasu cewa dakin su ne, suka dinga murna, wanda ya sanyayya ran mahaifin su.



********


Abraham da kanshi yaje nearest boutique ya siyo musu kaya masu kyau duk iri ɗaya, hadi dana bacci, sai kayan shafan su dangin su lotion, hair cream, shampoo da perfume duka na yara.

Aysha ce ta jere musu kayan a wardrobe dinsu, yayin da kayan shafar su kuwa ta jera musu kan dressing mirror.
Daga nan ta wuce kitchen domin ɗora musu girki, saboda yamma tayi sosai.

Amma hakan bai hana ta tuka musu lafiyayyen tuwo semovita da miyar ogbono daya sha ụgu,
stock fish, kayan ciki, jan nama da kpomo, tun kafin ta gama k'amshin girkin ya cika falon kasa gaba daya...


Tana cikin gyaran kitchen kenan bayan ta gama abinci, ba zato bare tsammani taji an zagaye hannu a kugun ta, saurin juyowa tayi ta ga Abraham ne.
Ajiyar zuciya ta sauke domin ta tsorata, sumba ya manna mata a gefen wuyan ta, sannan yace


"my Life"



"Uhmmmm!"

Aysha ta amsa domin ta kasa magana sakamakon hannun sa dake yawo a wasu sassa na jikin ta.



"i love You"

ya fada yana sake riƙe ta da kyau a jikin sa, hadi da birkita mata lissafi, wani yarrrrrrrrrr Aysha taji a jikin ta, duk da bata san me take ji ba, but tana karban sakonnin da yake aika mata.



Ganin yanayin sa ya fara sanjawa, ba kuma ya son ya ya katse mata aikin ta, sai kawai ya barta ya fice, ya koma dakin su Ammar domin suyi wasa. Yana so yaran su shaku da shi sosai, hakan kuma bazai faru ba matuƙar baya jan su a jiki.



*9:21pm*

A daidai lokacin Aysha ta fito daga dakin su Ammar da suka riga suka yi bacci, dama addu'a ta shiga ta tofa musu.



Sama ta hau ta shiga dakin ta.
Bayan nan ta tube kayan jikinta ta daura medium towel, ta saka shower cap, sannan ta shige bathroom ta sakar wa kanta shower, fuskar ta dauke da murmushi...
Farkon haduwar su da Abraham har izuwa yau da suke a matsayin mata da miji ne ke yawo a brain din ta. Ikon Allah da girma yake, komai daya faru yazo karshe kamar bai taba faruwa ba, sai dai labari kuma.


Bayan ta fito, oil perfume ta shafe jikin ta da shi kana ta saka riga da wando na bacci masu dan kauri, saboda yanayin sanyin da ake a daren yau.


Tana cikin jera pillow daya dan hargitse ta ji shigowar Abraham, bata juyo ba, ta cigaba da abinda take.


"Ụwammm!" Ya kira sunan ta.


A hankali ta juyo gareshi, zaro beautiful eyes din ta masu haske tayi sakamakon ganin sa a tsugunne a gabanta.


"Please stop! What are you doing?"
Ta fada cikin mamaki.

Bai bata amsa ba, bai kuma tashi ba sai ma hannun ta daya riƙe cikin nasa yana murza tafin hannun ta mai laushi.


Fuskar ta ya kurawa ido cikin wata murya mai dauke da abubuwa da dama ya fara cewa

"You re a gift from God to me, shigowar ki cikin rayuwata yayi sanadin haskaka min duhu dana jima a ciki, kin so yarana tun kafin kisan ni ne mahaifin su, kin basu tarbiyya kamar y'a'yan ki duk da karancin shekarun ki, Nagode sosai da wannan taimako da kike min, Allah yasa aljanna ya zama makoma gareki, da Inna, da baffa, sannan ki yafemin abinda nayi miki kafin mu tafi Gombe, I was not my self, sannan ina rokon alfarma, dan Allah ki so ni Ko da kaɗan ne, ki so mahaifin su Ammar please ụwammmmmmm!"



Kallon shi Aysha ke yi da burgewa, ita kam idan bata so mahaifin su Ammar ba wa zata so a wannan duniyar? gaban sa itama ta durkusa, ta ɗora dayan hannun ta kan na shi hannun dake rike da hannun ta ɗayan tace "baka min laifin komai ba, na fahimce ka, sannan bazan taɓa kin ka ba, nayi alkawarin rayuwa da kai komai rintsi komai wuya"


Ajiyar zuciya mai sauti ya saki, ko bata furta tana son shi amma yaji dad'i a ransa tunda zata iya rayuwa da shi.


Hannun sa ya zare daga cikin na ta, kana ya buɗe hannun sa yace

"come, come here"


Da sauri Aysha ta fada jikin sa domin wani shauki sosai take ji a wannan daren mai cike da iska mai dadi daga ni'imar Allah.



Daga runguma, salo ya fara sanjawa, Abraham ya birkice mata, yana ƙoƙarin birkita Aysha da ita ma ta fara karban sakonnin shi, da abu ya girmama cak ya daga ta sai kan gado yayi mata rumfa da fafadd'ar kirjin sa...


Ya jima sosai yana abu ɗaya sannan ya fara kokarin su zama abu ɗaya, nan Aysha ta dawo hayyacin ta, ta fara kuka tana roko, hadi sa ture shi amma ina gogan bai ma san tana yi ba....



*12:30*

Tana kwance a saman kirjin sa yana bubbuga bayanta, murmushi dauke a fuskar sa, a yau wani yanayi na nishadi sosai yake ji, yana kara gode wa Allah daya samu Aysha a cikakkiyar mace, wanda hakan yafi komai yi masa dadi domin bai taba Experiencing hakan ba.
A yanzu samun mace da mutuncin ta na matukar wahala a wannan zamanin na yanzu, wasu sukan siyar da mutuncin su domin abin duniya or wani dalili mara tushe.



Gashin ta daya rufe fuskar ta ya tattare mata zuwa baya, sannan ya leka fuskar ta, sai faman kananun koke-koken ta take a hankali, wanda har da zallan shagwaba domin Abraham ya bi da ita a hankali kasancewar yasan ita din yarinya ce kuma budurwa.




Shafa bayan ta yayi yace "Am sorry my heroine"
(kiyi hakuri jaruma ta)



Ai fa kamar kara tunzurata yayi sai ta fara didire kafafun ta a jikin sa cikin sakalci da shagwaban da bata san ta iya ba.


Danne dariyar sa yayi yana bata hakuri hadi da yi mata wata waka ta soyayya da Yaren Igbo, cikin abun da bai fi mintuna ashirin ba wani bacci mai daɗin gaske ya ɗauke ta.....



*(Kafin na cigaba bari nayi wata yar sanarwa, masoyan littafin NoorEemaan ina mai farin cikin sanar daku cewa in Sha Allah cikin satin nan sabon book dina zai fara sauka, wanna karon bazan tafi hutu mai yawa ba Saboda yanda hannun na ke k'aik'ayin fara rubuta wannan novel mai dauke da abubuwan mabambamta ba, ku san dai akodayaushe Noor da sabon salon nake zuwar muku dashi. Wannan karon tafiyar mai zafi ce, ina mai tabbatar muku da cewa zai yi sugar fiye da Rayuwar Faheemah, mijin Ammina ne sila, papi Ne, kyautar koda, da ma Abraham. Amma paid book ne kan dari uku kacal saboda tanadin dana yiwa book din yasa bazan iya sakin sa free ba, amma ina kaunar baku dukkanin wani book nawa a matsayin free, fatan zasu yi patronazing dina, much luv habibte's)*❤️



***************


Da asuba da kansa yayi mata wanka duk da tace zata iya amma bai bar ta ba, bayan ya gama yi mata wanka shima yayi, sannan suka daura alwala ya dauke ta suka fito.

Riga mara nauyi da iyakar sa cinye red color ya sanya mata, ganin ba a tayar da sallah ba sai ya jona hand-dryer a socket ya busar mata da sumar ta yana jin dadi a ransa, domin shi din mai kaunar gashi ne.


Yana gama wa yaji ana ƙoƙarin tayar da sallah, a gurguje ya saka kaya, sannan ya shimfida mata sallaya kana ya bata sumbata a lips mai tsayawa a rai ya fice da sauri.



Da murmushi Aysha ta bi bayan shi, kana cikin shauki ta rufe idanun ta da har yanzu basu gama sacewa daga kumburin da suka yi ba, Sakamakon kukan data yi a jiya, ta yi nisa a duniyar tunanin Abraham ba tare da ita kanta ta san tana hakan ba, sai ji tayi liman ya tafi ruku'u kana ta dawo hayyacin ta, cikin sauri ta mike ta tada kabbara...



Shida saura Abraham ya dawo ya ganta zaune tana karatun Alqur'ani, gabanta ya zo ya zauna hadi da tankwashe kafafunsa yana kallon ta cike da burgewa.



Sai da Aysha ta kai aya, ta dago ta ganshi ya kura mata ido, girgiza kanta tayi tana murmushi sannan ta daga hannu tayi addu'oi'n ta, a tare suka shafa.



Qur'anin ya karba ya ajiye a muhallin sa kana ya taya ta zare hijab din jikin ta, kanannad'ewa tayi a jikin sa tana boye fuskar ta.



Dariya sosai ta bashi, yana ƙoƙarin dagota tana sake shige masa jiki.
Abin dariya ma, wanda take jin kunyar sa kuma take kara shiga jikin sa, cikin muryar dariya yace

"Hey stop! Why are you doing this"


ai kamar kara tunzurata yake domin sake shiga jikin sa take, sai kawai ya gyale ta yana murmushi, can da dan jimawa ya ga tana kokarin barin jikin shi, kara riƙe ta yayi bai bata damar tashi ba ya tambaye ta ina zata.



Tace zata je duba ƴaƴan ta sannan ta ɗora musu breakfast.

Yaki yarda yace ta kwanta ta huta, zai je yayi duk abinda ya dace ta yi.

Ba dan ta so ba ta amince, ya kwantar da ita ya fita, bayan ya sake kissing dinta... tun idanun ta biyu har bacci ya dauke ta dama akwai sauran gajiya a jikin ta.


Abraham yana sauka ya ga mai aiki na gyara falo, cikin girmamawa ta gaishe shi ya amsa, kana ya shige dakin su Ammar.

A nutse ya tarar suna bacci, Anwar har da ɗora wa Ammar kafa a baki amma haka suke manne da juna, dariya yayi mara sauti yana girgiza kansa kana ya karasa a hankali ya gyara musu kwanciya hadi da basu sumbata a goshi sannan ya fita.



Kitchen ya shiga, hannu ya dora a kugu, shi kam idan akwai abinda bai iya ba ko yake bashi wahala toh girki ne.


Dankalin turawa ya fara ferewa, ferewar ma abin dariya domin sai ya haɗa dankali da bawo mai yawa ya fere ya zubar, bayan ya gama ko gishiri bai barbada ba ya shiga suya.
Bayan ya gama da dankali, ya fasa kwai goma ya saka albasa, attaruhu, da maggi da sauran kadan ya yi yawa a cikin kwan, kana ya hau suya, bai bari kwan ya soyu ba ya juya shi hakan yasa ya hargitse, dan bata fuska yayi irin ba haka na so ba.



Bayan nan ya kwashe, ya haɗa da dankalin a warmer daya ya kai dining ya dawo, sannan ya tafasa ruwa a kettle ya juye a flask ya Kai dining domin shikam bai iya dafa irin shayin ta ba, ya kuwa haɗa duban gumi, kamar wanda ya tuka tuwon mutane talatin.



Ya fito daga kitchen kenan yaga mai aiki tana kokarin komawa bangaren su, dama aiki kadai ke shigo dasu ɓangaren nan, saboda hatta girki a bangaren su suke yi, domin akwai komai a wajen, Idan sun girka sai su zubawa mai gadi da mai gyara farfajiyar gida, kuma lafiyayyen abinci suke yi.

Yace mata "ɗan gyara kitchen dinan please"

Cikin girmamawa ta amsa kana ta nufi kitchen din, a ranta tana jinjina saukin kan shi.



Dakin su Ammar ya leka ya tarar da sun tashi, da gudu suka fada jikin sa wanda ya ji dad'in hakan, suka gaishe shi ya amsa cikin tsananin son su,
Kana ya cire musu kaya suka nufi banɗaki domin yi musu wanka.

Ta bangaren Aysha kuwa ita ma a daidai lokacin ta tashi, mikewa tayi ta kalli dakin babu ko datti sai gadon daya hargitse a hankali ta shiga gyarawa, domin Abraham ya sanja bedsheet tun jiyan, bayan ta gama ta cire rigar jikin ta, ta daura towel inda hannun ta ya taba sarkan wuyan ta, dan shiru tayi kana a hankali ta sa hannu ta cire sarkan, ta kuma yi hakan ne domin tasan ganin sarkan zai dinga yawan tuno wa Abraham da rayuwar sa ta baya...



Ruwa mai zafi ta haɗa wa kanta tayi wanka kana ta fito ta shirya cikin wata gown ta atamfa mai ruwan ja da dark blue daya yi matukar karban farar fatar ta.



Powder da kwalli kadai ta saka, sannan ta yi simple dauri daya fito da gashinta ta baya.

Flat shoe red color ta saka yayi matuƙar yi mata kyau, musamman da jan kunshi kafar ta da aka mata a lokacin biki mai sellotape ya sake maroon.



Turare ta fesa sama-sama kana ta bude kofar ta fita, hakan yayi daidai da fitowar Abraham daga dakin sa da alama shima wanka yayi sai zuba kamshi yake, ga su Twins da ta hango zaune daga falon kasa a shirye su ma.



Sakin baki Abraham yayi yana kallon Aysha, domin bata taɓa yi masa mugun kyau irin wanna ba, cikin sauri ya karaso gabanta ya daga ta cak ya shiga juyi da ita yana fadin
"You re so beautiful Ụwammmmmmmmm!"




*AYSHA*
Rike shi tayi da kyau tana dariya, wanda dariyarta ta ja hankalin su Ammar, da gudu suka hau saman suka yi tsaye suna dariya suma, sai da Abraham ya gaji dan kansa kana ya sauke ta, sannan suka sauka kasa gaba-daya.



Bayan duk sun zauna, Aysha ta bude warmer domin serving din su, sai dai yanda taga dankalin yayi wani iri yasa wata dariya da bata shirya zuwan sa ba yazo mata, Abraham kuwa bata rai yayi cikin wasa shi da yake jiran ta yaba masa.



"Sorry" tace tana rufe bakin ta, girgiza kansa yayi irin zan kama ki dinan.

Murmushi tayi kana ta shiga zubawa kowa, sannan ta haɗa tea mai kauri wa kowa

Please Login or Register in order to submit comment