Join Our WhatsApp Group

HAKA ALLAH YASO S4 Complete Hausa Novel Document by HAKA ALLAH YASO S4


HAKA ALLAH YASO S4

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 60169



HAKA ALLAH YASO S4

Reading Time: 5 Hours

Added On: 11, Sep 2023

Author: Jameela Jameey ƴar mutan Kankia ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Manazarta Writers Association

Author Phone : +234 816 050 8316

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 342.9 kb

File Type: txt

Views: 690+

Download: 327+

Last download: 18 hours ago

Description/Story: HAKA ALLAH YASO S4 Yar Mutan Kankia

_*HAKA ALLAH YASO❤‍🔥*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_



*Godiya ta tabbata ga Allah mai kowa mai komai daya bamu aron lokaci mai matukar tsada da muka sake haduwa daku a karo na hudu cikin littafin nan mai farin jini mai taken HAKA ALLAH YASO labarin Amina Caranci,inafatan Allah yasadamu da alkhairan dake cikin wannan labari ya karemu da duk wani sharri,yakarama annabi Muhammad SAW daraja da ahlilbaiti da dukkan sahabansa baki daya har zuwa tabi'ai da wa'anda suka bada gaskia har zuwa ranar saka mako,ameen*


S4/E1&2


Bankasance mai rakiba ko yawan butulci akan abinda Allah ya tabbatar da sai ya wanzu a gareni kuma nasan ita Jarabawar Allah ga mai imani kawai take tabbatuwa saidai cin Jarabawar abune mai matukar wahala sai ga wanda Allah yaso kuma ya saukakama hanyoyin da zaici Jarabawar da yaima bawan shi,nasan duk abinda ke faruwa dani *Haka Allah Yaso* kuma shi kadai zai kawo mani ɗauki a duk halin dana tsinci kaina yana sane dani,na dadi ko akasin haka,wannan dalilin kesawa ko ina cikin ƙunci nakanyi dariya duk da halin da nike ciki ya girmi jindadi ko nishadi amma na mikama Allah wahidilkahhar Sarki buwayi gagara misali kukana nasan shi zai kawo mani ɗauki a duk inda na tsinci kaina,bani da wata dubara sai abinda Allah ya tsara mani domin shikeyin komai yanda so ga ɗan Adam a lokacin dayaga dama nasan,a yanzun ma bai manta dani ba saboda *HAKA ALLAH YASO!*


_Rayuwa kenan ba yanda Allah bai Jarabtar bawa dan yaga girman imanin shi Ya Allah idan katashi Jarabamu kaimana wadda zamu iya dauka ka tsare mana imanin mu a duk inda muke,ameen_


*_AMINA CHARANCI kenan da rayuwa taima ƙunci a ciki Prison,Ya Allah ga baiwar ka nan ka kawo mata dauki👏🏻_*


************

Tunda aka shigo dani Kurmawa Prison hankalina yai matukar tashi musamman dana ga anbani uniform wani karamin ɗaki aka nuna mani na shiga na sauya kayana zuwa dark blue mai number ajikin su, saidai 22 shine last digit number kayan da aka bani.

Ina gama sawa Gandiroba ta tisani gaba zuwa wani ɗaki dake dauke da mutun ukku,nice cikon ta hudun su,ana budewa akasa na duka nakurɗa cikin shi gabana na duka fat fat fat,ban taba tunani rayuwata zata sauya zuwa irin wannan rayuwar ba da nike kallo yawanci a film din kasashen waje yau gani ni Amina Yusuf Caranci a cikin Prison na ƙwaryalwaryar birnin Kano babban Prison din su.

Fadin tashin hankalin da nike ciki bai misaltuwa saidai tashin hankalin rasa HUSNA danayi ya girmi musibar da nike ciki.

"Ke."
Wata matashiyar mace ta kwada mani kara bisa kaina ta kirani da Ke

Kallo ɗaya nai mata na sauke kaina kasa dan alokacin zuciya ta ke ƙuna hoton Asma'u ke mani yawo cikin zuciya ta,musamman dana isketa kwance cikin jini lallai wannan abune mai matukar tashin hankali a gareni inama hukunci da aka yanke mani ta hanyar ratayane dana huta da ƙuncin rayuwa irin wannan.

"Ke dan gyatumar ki,baki zuwa kikawo gaisuwa wajen shugaba shine zakizo ki samu waje ki zauna sai kace ta Allah."

Jin kalaman matar da naji sun kira da Mairo su sukasa hawayen da suka ƙafe a idanuna suka ziraro mani masu ɗumi.

"Ku kamo mani ita nan,muyi mata wellcome to gidan Yari gidan Ɗan Kande duk wanda yazo nan saida ya shirya."
Cewar wadda suke kira da Sarauniya,kafin in ankara sun kinkimoni hannuna da kafata sukai mani sharga sharga zuwa gabanta niko sai wullewulle nike suna ajeni gaban ta na kifama Mairo mari raina a bace.

"Kai dan gyatumin Yarinyar nan dole yau mukoya mata hankali tasan tarabu da duk wasu masoyanta dole taima *Cankwai* biyayya ko adauki buzunta Mairo kama mani kafarta,ke kuma Salame rike hannun ta ku ɗage mani ita."
aiko haka akahau kiciniya dani aka ɗagani sama,a kalkashi gadon su,na karfe ta zaro bulalar geza ta dinga shauɗa mani ita bisa gadon bayana zuwa mazaunai na,sai wullina nike tabbas inajin zafin saidai tension din da nike ciki ya girmi kagane bala'in dukan da Cankwai ke mani aikin wulle wulle nike kwalla na zirara bisa kuncina hakan yasa tace a barni nafara kuka suka sakeni da kyal na zauna duk mazaunaina sai zugi suke mani.

"Maza kiba shugaba hakuri ko asake maki na jaki kuma sai mun tubeki zamu zaneki."

Dago idanuna nayi kamar garwashi nace yi hakuri.

Abinda ya isheni ya isheni kuma na fahimci ita rayuwar nan daga inda akace ga mutun gidan Yari tabbas kwanan Alkiyamar shice ta tsaya domin kamar rayuwar kace,aka datse ka rabu da iyayen ka Yan uwanka dangin ka da duk wani masoyan ka na gaskia dole rayuwa taima Yan gidan Yari kunci.

"Ke miye sunanki.?"
"Aminatu."
nace muryata na rarrabewa.

"DA'GO zakice Malama daga yau sunan ki kenan kinajina.?"
"Eh naji."

"Laifin uban mi kikayi kikazo gidan Kaso."?

"Aminiyata na kashe."
Nasamu kaina da furtawa duk da saida na faɗa naji abinda nafada din.

"Kai amman anyi matsiyaciya marar imani duk kin fimu rashin imani tunda har kika iya kashe masoyiyar ki,gaskia Dago kinci amana,kusa ke ɗaga mani ita inci Ubanta."

Ban musa masuba haka takara zaneni sannan suka sakeni daman ance Sarkin yawa yafi Sarkin karfi dole na mika wuya inaji ina gani.

"Azzaluma to koni da nike shugabar mata ban wannan rashin imanin irin nakiba,domin zuwana gidan yari na farko kishiyata na datsema harshe saboda na gindaya mata sharaɗi kada ta kwanta da mijina amman na iske tana mashi kiss shine na yanke harshen ja'ira.

Zuwana na biyu kuwa Uwar mijina naima dukan mutuwa saboda katsalandan a cikin al'amuran mijina aurena na biyu kenan.

Zuwana na ukku kuwa Kanwar Baba na zane dan ta zageni danni ba mahalukin da zai zageni in kyale shi koda kuwa gyatumi ne.

Zuwa na hudu mijina na kusa kashewa zuba mashi guba nayi danma Allah yasa bai mutuba saboda nace yabani kudi yahanani,aurena na ukku kenan saida nayi shekara bakwi gidan Yari

sai wannan karan kuma wanda ba fita domin mijina na hudu yakawo mani budurwa abokin dandina har cikin gidana duk da kar tasan karce, ni kuma nagaza hakura duk na kashe su,kinga ko ai nafiki imani tunda ni kisan danayi amanata akaci amman ke kika kashe aminiyar ki da hannunki kin zama cikakkar butulu kinci amanar aminci."
Cewar Cankwai ta ida maganar tana dungurina,tace.

"Ke kuma Mairo gaya mata dalilin zuwanki gidan Dan Kande."
"Ba wani abu bane ya kawoni gidan nan ba, kishiyata na bankama wuta ta mutu dan kawai ta daukar mani magin miya alhali ba ranar girkin tabane,kuma bata nemi izinina ba minene laifina dan na rage mugun iri a cikin duniya aiko a lahira ban fatan sake zama da kishiya."

Nidai da idanu nike binsu naga tsantagoran yan bariki ni kuma haka rayuwa ta juyamani wannan shine tsakiyar rayuwar mai wahalar gaske.

"Kema Salame gaya mata naki labarin."

"Sanadin faɗa da kanwar kishiya har na tsige mata kunne jini yaita shatata daganan ta margaya barzahu shine fa nazo nan shekara ta goma kenan cif,dan haka kema ki shirya tsaf kinzo kenan ba fita mune uwarki mune ubanki mune dangin ki,ko biyayya kikai mana sai kinci na jaki. gidan nan ba wanda baisan Cankwai ba,da 'yan ukku bala'i gwarama ki daina kukan munafuncin da kikeyi tunda har kika iya kashe aminiyar ki wannan zaki iya komai su balama anyi asarar kunnuwa ga kyau kamar tsada saidai ba kyawun hali tir dake mugun halin ki Dago."
ta sake ran kwashina akai sai tsinata sukeyi,nidai kuka nike kamar raina zai fita ina ayyana girman aminci har waɗannan marassa imanin sunsan girman dake tattare da aminci ina gani,inalillahi wa'inna ilahirraji'un Allahma da kanshi daya halicci amana mala'iku da sauran halittu gaza daukar ta sukayi hatta kasa,sai mu yan adam muka dauka ina zankai girman amana,kauna da soyayya mai karfin gaske dake tsakanina da Husna ya mutanen garin mu dana duniya zasu kalleni in akaji da bakina na aminta ni na kashe Asma'u,taya zanyi da bakin mutane akaina gashi wadannan basu sanni ba basu san amincin dake tsakanina da Husna ba,amman sun tsinema halina inaga wadan da sukasan wacece Asma'u a wajena ya muke da junanmu lallai kam rayuwa inba Jarabawa bata cika cikakkkar rayuwa,Ya Allah kadauwamar dani nan Ya Allah kajikan Asma'u kayi gaggawar bi mata hakkin ta ka jibin rayuwar marayun data bari inalillahi ni Aminatu ya zanyi da rayuwata.

"Babu yanda zakiyi da ita ja'ira zoki danna mani kafafuna maciya amana kinbani dani ban kara ɗaga maki kafa tunda harkika iya kashe aminiyar ki,waima dan ubanki akan mi kika kasheta."?

Akan dukiya."
Nace atakaice kamar yanda aka rubuta a statement dina banda niyar canzawa nasan ta Allah itace daidai namu shine bi.

"Kutumar Uba akan dukiya kika kashe kawarki aminiyar ki gaskia Dago kedin kin cika mai busassar zuciya."

Kafa tasa ta halbani tace.
"Kikaimani wuƙi wuƙi da idanu kamar na mujiya dan uwarki cigaba da danna mani kafata kafin dare in sake daurayeki tas da bulalai tunda baki da imani kin samu daidai ke duk da naki yafi namu amman munsan hanyoyin cuzguna maki yar banza munafuka."

Cigaba da danna mata kafar nayi ina hawaye kamar ruwa ba abinda suke mani bane,ke bani haushi ba,aaa ina hango girman rashin danayi na aminyata Asma'u,nasan na cancanci azaba agaresu tunda har zan iya aikata abinda suke mani kallan na aikata duk da nina fadi hakan da bakina,wannan kenan.


*Caranci*

"Ina bakin cikin ganin wannan ranar inama mutuwa nayi na huta da ganin wannan bakin ciki ni Yusuf yau nine ya'ta mafi soyuwa a wajena itace garkame a gidan Yari ni gani a gida inama ban kai wannan lokacin ba,wai Aminatu ita aka yankema hukuncin kisa,arasa wanda za'ace ta kashe sai Asma'u inalillahi wa'inna ilahirraji'un.
Tabbas bazan taba yarda Mamana zata iya kashe dabba ba bare kuma Asma'u wanda kowa yasan alakar su.!
Lallai Aminatu bakiyi dacen Uba ba,nagaza baki farin cikin ki nakafe na rabaki da duk wani farin cikin ki aganina ina maki gata ashe ba haka bane,miyasa na biye ta Alhaji Mukhtar muka dage sai munraba tsakanin ku da Taufiq miyasa na biyema zuciya ta,na rabaki da jinina Hussein dan kawai wani dalili namu marar tushe gashi munfarraƙaƙu,yanzun haka ba wanda yake da tabbacin Hussein yana raye ko ya mutu Allah masani."

Kuka Baba yasake saki mai tsuma rai sannan yaci gaba da cewa.
"Ga ya'ta a gidan Yari daurin rai da rai shikenan narasa ya'ta bani bata ban kara ganin ta,na cuceki Aminatu da nagaza yi maki uzuri a rayuwata kinmani biyayya matukar biyayyya amman ni Yusuf na gaza cika maki burin ki inalillahi wa'inna ilahirraji'un Allah ka kawo mani mafita Allahumma ajirni fi musibati wa'aklifni khairan minha."

Kuka suke baki dayan su dakyal Ahmad yace.

"Baba tabbas ba aima Anty adalci ba katabbata batazaƙi zabinkaba, koda ace da Ya Taufiq take waya, yaka mata ace kaji nata uzurin amman Qaddarace ba yanda zamuyi kuma haka Allah yaso."

"Ahmad kudaina ɗaura laifin nan kan kowa Allah yagama tsara komai dole sai Aminatu tayi gidan Yari,ni ba wannan yafi damuna ba rashin Asma'u yanzun zamu gaza sukuni a cikin jama'a da mun fita za'ace Yarmu ta kashe aminiyar ta,wane abune yafi wannan ciwo gashi abin takaicin da bakin ta,ta amsa laifi tace itace ta kasheta,yanzun mike garemu,Allah Sarki ƴata kiyi hakuri Aminatu mun gaza taimakonki *Haka Allah Yaso*"
Cewar Mama dake kuka kamar ranta zai fita.

Haka mutane akaita zuwa yi masu jaje wasu kam badan Allah suke zuwa ba.

Agidan su Husna kuwa zaman makoki akeyi gobe ake sadakar ukku gwanin tausayi lamarin ga ya'yan ta saibin kakar tasu, suke suna ina Momi musamman Minah dake kuka dayake tafi Haidar wayau sosai.

"Mama kikaini gun Momi na,tabani Sweet."
Irin wadannan maganganun suke dagama Mamar su Husna hankali hakama Mamanar su Minal intazo zaman makoki suke tada mata hankali duk da tazama bora abin hantara ga jama'a ana zaman makoki amman bai hana ai mata habaici ba saidai tayi kuka ta gode Allah saidai cikin ikon Allah iyayen Husna sun dauki Qaddara sun tabbata Amina baza taba kashe Asma'u ba saukin kenan ko ana maganar sune na farkon karyata lamarin saidai kunsan yawan maganar baida dadi,kuma haka mutane suke basu da gadonka sunada gadon maganar ka.

Haka rayuwa ta kasance hatta Abba da Mum su Tariq,Fatash duk sunzo dasu akai zaman makoki sosai suka tausayawa iyayen Husna halin da suka shiga dan Abba yai masu ihisani dan kusan abinda akaci na gaisuwa shi ya dauki nauyin shi daman halayyar mutane kenan, kana mutuwa sai afara ta ciki wani addu'ar ma bazai makaba saidai azo aci abinci Allah yasa mudace.

Rayuwa ba dadi ta kowane bangaren guda biyu gidan su Husna da Minal wanda suka zama yan uwa dangin juna masoya kuma aminai na hakika wanda suke sadaukar da farin cikin su dan cikar burin dan uwan su,sai ga yanda Allah ya hukunta wanda yake zartar da komai a lokacin dayaso yagama dama ga yanda yaso da Minal,Allah yabata ikon cin jarabawar da yai mata,wannan kenan.

*Prison*

Tunda gari ya waye babu abinda mukeyi sai.......

*Yar Mutan Kankia dan girman Allah kitaimaka ki cigaba da yimana posting din Haka Allah Yaso dan darajar Sayyidina Rasulillahi kitaimaka mana,wlh da labarin nan muke kwana muketashi dashi a ranmu munajin labarin nan na ratsamu musamman darussan dake cikin shi, pls Anty Jameey.....*


_Ire iren waɗannan maganganun da masu kirana waya duk akan cigaban book din nan, har masu magana ta Dm to kusani Yar Mutan Kankia taga sakonku saidai kamar yanda nace maku tabbas banda lokacin posting ina busy dayawa shiyasa amman duba da yanda akeson cigaban labarin nan insha Allah zakuna samun posting koda bani nayi post din kai tsayeba sannan ku dinga share dan saura su_ _samu,Comment dinku shi zaisa ku dinga ganin posting akan lokaci._

*Nagode da addu'oinku agareni na fatan alkhairi duk nagani kuma nagode Allah yabar so da kauna,ameen kardai ku manta.

_Yar Mutan Kankia ce❣️_
Share
Pls
❣️

_*HAKA ALLAH YASO❤‍🔥*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S4/E3&4




Tunda gari ya waye ba abinda muke sai jidar kattin duwatsu muna kaiwa cikin wani katon fili mai girman gaske ga rana ana kwalawa dan danan jikina ya saki zafi da kuncin da nike ciki suka bigeni ina cikin tafiya na rafka uban tuntube na fadi,ina tare da Shugaba Cakwai daka mani tsawa tayi har saida yan cikina suka koma gama gefe daya dan tsorota da nayi.

"tashi munafuka kinsan kina gudun wahala kika yarda kikazo gidan Ɗankade kadan kikagani indai rayuwar yari ce.
ba abinda kikagani da kanki saikin tsani kanki da kanki,yar banza maci amana."

Jini ke zuba a kafata amman gudun kada tasa a dagani ta bigeni dolena na mike ba wani dressing da zan samu duk da nasan girma da darajar treatment saidai yanda rayuwa tazo haka ake binta,nima tawa rayuwar kenan.

Haka muka wuni ana abu daya har nagaji saida aka kira salla mukaje mukayi salla sannan mukaje inda ake raba abinci muka ansa.

Yunwa nikeji sosai kamar zata halakani saka hannuna nayi cikin kwanon tasar dake...


Read / Download HAKA ALLAH YASO S4

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album