Join Our WhatsApp Group

MUTUM DA DUNIYARSA Complete Hausa Novel Document by MUTUM DA DUNIYARSA


MUTUM DA DUNIYARSA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 231925



MUTUM DA DUNIYARSA

Reading Time: 19 Hours

Added On: 16, Sep 2023

Author: Billyn Abdul ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Zafafa Biyar

Author Phone : 08030811300

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 994.5 kb

File Type: doc

Views: 1307+

Download: 1812+

Last download: 3 hours ago

Description/Story: *_=Ø¡ÜHASKE WRITER'S ASSO...._*



*_=اÜMUTUM DA DUNIYARSA....!!=اÜ_*
_(ya dace ya gyara kansa)_



*_Bilyn Abdull ce>ØÝ<Øûß_*


*_©2019_*


*(P3REP qDDQNGP qD1QN-RENpFP qD1QN-PJEP*

_In the name of Allah, the Entirely Merciful, the Especially Merciful._



*[1......]*


............Tafe take tana zirar da hawaye masu d'umi da saka k'unar zuciya. Kasantuwar Nikab d'in dake sakaye da fuskarta ya hana bayyanuwar kukan nata ga mutane, dukda dai hakan bai hana wasu kallonta ba, musamman wad'anda sukeda tabbacin itace.
Cikin Nutsuwa da sanyi take tafiya, kanta a k'asa dukda kuwa tana sanye da dogon hijjab da nik'ab. Isowarta inda zata yasa ta tura murfin k'ofar gidan kalar madara ta shiga da sallama.
Dattijuwar da bazata gaza shekara hamsinba ta d'ago daga d'ibar ruwan da take a rijiya ta amsa Mata.
“Wa'alaikissalam, yanaga kin dawo dandanan? Kobaki iskeshi a gidan bane?”
Nik'af d'inta ta yaye, kamilalliyar fuskarta ta bayyana, ta d'an sakin guntun murmushi tace, “Eh Umman mu, na tarar har ya tafi kasuwa”.
Batareda ta jira amsar Umman tasuba ta wuce gaba. Binta da kallo Umma tayi, ko kad'an bata yardaba, tasan ta 6oye mata ainahin abinda yafarune acan kamar yanda ta saba gudun kar ranta ya 6aci. Ta d'an sauke ajiyar zuciya tana girgiza Kai, sannan ta ajiye gugan hannunta ta d'auraye hannun da ruwan data jawo ta nufi d'akin da yarinyar ta shiga.
Zaune ta isketa ta zabga uban tagumi tana cigaba da kukan, amma jin sallamar Ummansu sai tai saurin share hawayenta ta maye gurbinsu da murmushi. Da kallo kawai Umma ta bita tana mamakin zurfin ciki irinna y'ar tata, ita har tausayinta take gameda zaman gidan aure, idan bata sami miji na gariba sai dai aita cutarta........
Maganar budurwar ya saka tunaninta katsewa.
“Umma wai su Zarah basu dawoba har yanzu?".
Zama tayi kusa da ita tana fad'in “Basu dawoba Nafisar ma ta kirani tace sai zuwa yamma zasu dawo, zasuyi Mata wani d'an aiki”.
“Humm ni dad'ina da Aunty Nafisa kenan, baka isa kaje gidanta kafito bata nanuk'a maka aikiba, son jikinta yayi yawa wlhy ita da Zarah Umma”.
Murmushi Umma tayi kawai, amma batace komaiba. Sai da taga budurwar zata mik'ene tace, *“JIDDAH!,* dawo ki zauna muyi magana”.
Babu musu ta dawo inda ta tashi ta kuma zama, “To Umma gani, wacce magana ce?”
Numfashi Umma ta sauke, kafin ta tsare Jiddah da idanu, “Jiddah ya kukayi da Abbanku?”.
“Lah Umma aina cemiki ban iskeshiba, yatafi kasuwa sanda naje”.
“Ban yardaba Jiddah, nifa mahaifiyarku ce, duk d'inku nasan halin kowanne, ki daina k'ok'arin 6oyemin abinda ba sabo bane a gareni da rayuwata”.
“Umma kiyi hak'uri, aganina yawan maimaita magana bashida amfani, hak'uri da mantawa da abinda yawuce shine dai-dai”.
“Duk nasan da hakan Jiddah, kedai fad'amin”.
“Shikenan Umma tunda kin matsa. Na iske Abba a gida yanama Karin kumallo, bayan mun gaisa dashi da aunty Amarya, saina sanar masa nazone ya taimakemu da kud'i su zarah sun koma hutu, gashi kuma basu biya kud'in makaranta ba belle su kuma, gashi su waleeda Jsce zasu zana a wannan shekaran. Wlhy Umma bakiga yanda Abba da Aunty Amarya suka hayayyak'o minba, har Abba yana fad'i bazai gaji da takaicin *HAIHUWAR y'ay'a mata* ba harya koma ga ALLAH, wai mune muka dabaibaye DUNIYARSA shiyyasa yakasa gaba ya kasa baya, shi baiga amfaninmu ba inama laifin ciyar damu abinci da yakeyi, yariga ya rantse sisin kwabonsa bazai ta6a kashewa akan muyi karatu ba, gara ya sayama su kalifa ice-cream yasan duk tsiya nan gaba zai amfana dasu...........” kuka ya sark'eta takasa k'arasa maganar, saima fad'awa datai jikin Umman.
Shiru Umma tayi takasa cewa komai, sai k'ok'arin Had'iye wani Abu daya tsaya Mata a mak'oshi takeyi, yayinda hannunta ked'an bubbuga bayan Jiddah.......
Jiddah takuma katse Mata tunani da fad'in “Umma wlhy Duniyarnan tama fitarmin akai, wataran nakanji tamkar zancen Abba gaskiyane mu Mata bamuda wani amfani acikin wannan al'ummar, kowa gani yake amfaninmu daga a haifemu sai muyi aure mu haihu, babu wata gudunmawa da zamu iya kawowa a duniyarmu, mune muke d'aukar ciki, muyi goyonsa, mu haihu, muyi raino, muyi tarbiyya mutum yakai wani matsayi, amma MACE itace zai fara k'ask'antarwa, MACE itace zai fara d'auka mara muhimmanci, itace zai Fara kira mai k'aramar k'wak'walwa, itace zai Fara kira mai k'aramin tunani, itace wadda yake Fara kallo takalminsa abar takawa ako yaushe, mune jagororin AL-UMMA amma mu ake maidawa MAK'ASK'ANTA, Umma Abbanmu namana haka to yaya Miji zaimana muji haushi? Anya kuwa Umma Abbanmu y..........”
Da sauri Umma ta rufe bakin Jidda tana fad'in “Kul jiddah karna sakeji, koma dai minene shi mahaifinku ne, bai cancanci kowanne irin furiciba, addu'a itace kawai makaminmu da hak'uri kinji”.
Kai Jiddah ta d'aga Mata tana share hawaye.
Umma tace, “Inaga kawai Zan samu Na saida Kujerunnan su koma makarantar, dan duk suna a ga6ar dabai kamata ayi wasa da itaba, kodai karatun secondary d'in suka samu ALLAH ya amfana, mutum dai yasamu abin fidda kai aduk inda ya tsinci kansa, kema da bakiyiba keda y'ar uwarki ALLAH ya baki miji nagari dazai kula dake kamar yanda y'ar uwarki ta dace”.
“Ameen Umma, amma baikamata a saida kujerunnan ba, mudai jira muga kozai biya d'in kokuma Uncle zai dawo da wuri, dan nasan shima hankalinsa Na nan”.
“Humm Jiddah kenan. Kema dai kinsan hali basai nafad'aba indai Abbanku ne, mudai jira yahayan kawai”.
Shiru Jiddah tayi tana had'iye wani Abu mai d'aci daya tokare mak'oshinta, ji take da zata samu wata dama akan MAZA masu irin halin Abba, to lallai shine Wanda zata Fara hukuntawa domin na bayansa su Shiga hankalinsu da koyar yanda zasu *MARTABA Y'AY'A MATA*.


('('('('('('('('('('('


*ASALIN LABARIN*

*Alhaji Zakari yaro* d'an asalin jihar Adamawa ne, amma mazaunin kano, dan acikin kano ya bud'i ido yagansa tun a zamanin k'uruciya, ALLAH yayima Mahaifinsa rasuwa tuni, amma sai mahaifiyarsa taci gaba da zama bata koma Adamawa ba, ita tacigaba da kula da al'amuransa harya kai munzalin aure. Da kanta tabashi damar nemo matar aure, anan kano kokuwa cikin y'ay'an dangi dake Adamawa.
Cikin ikon ALLAH ya za6o matarsa cikin dangi, dankuwa acan Adamawa tushensa ya d'akkota, hasalima auren zumincine a tsakaninsu. Sosai mahaifiyarsa tayi murna da za6insa tai ta sanya masa albarka. Babu 6ata lokaci aka shiga shagalin biki Na y'an gata, domin kuwa su biyu iyayensu suka Haifa, dagashi sai k'aninsa yahaya. Ansha biki amarya Aminatu ta tare anan cikin birnin kano. Zamane akeyi mai cike da nagarta da k'aunar juna, dan kuwa suna son junansu, sai da Aminatu ta shekara uku a gidan miji sannan ALLAH yabata ciki, zokaga murna wajen Zakari da mahaifiyarsa da k'aninsa yahaya, a kullum fatan Zakari Aminatu ta Haifa masa d'a Namijine, wataran har takanji haushi a yanda yake nuna k'iri-k'iri yafison a Haifa masa y'ay'a maza, to idan ta haifi mace kenan bayaso? Idan wannan tambayar tazo mata a rai hankalinta yakan tashi, domin tarasa yanda zuciyarta zata iya kar6ar amsar.
ALLAH da ikonsa ciki ya isa haihuwa, a wani daren lahadi Amina ta tashi da nak'uda, gabannin asuba da taimakon ALLAH dana surukarta ta haifo y'arta mace. Tunda mahaifiyar zakari ta sanar masa abinda aka Haifa saiya canja fuska, murnar da yaketayi takoma ciki, batare da yako d'auki y'ar ba ya buga takalminsa ya fice, bai dawoba sai da daddare, wasa-wasa dai Zakari yak'i d'aukar yarinya, hud'uba ma sai wani makwafcinsu yahaya yakira bisa umarnin mahaifiyarsu akaima yarinya. A kayan shagalin suna da ya saya saiya raba uku yabada kashi d'aya, mahaifiyarsa batasan abinda ke faruwa ba, dan a gabanta 6oyewa yakeyi, sai a daren sunan da taga kayan daya kawo takaici ya kamata, kiransa tai ta nema ba'asi, nanfa yashiga kame-kame, itako ta balbaleshi da fad'a, ta inda take shiga ba tanan take fitaba, yayinda shikuma yaketa bada hak'uri da neman afuwa. A daren yakawo sauran kayan, washe gari akasha shagalin sunan baby dataci suna SAUDA.
Bayan haihuwar Sauda zaman Amina da Zakari ya canja alk'ibla, ya janye mata sosai, dukda ta damu amma saita danne zuciyarta darajar mahaifiyarsa dake k'yautata mata, da gudin tsinka igiyar zuminci. Shekarar Sauda biyu takuma samun wani cikin, nanma dai Zakari yakuma k'wallafa rai ga haihuwar d'a Namiji, yakoma ririta Aminatu. Itadai mamakinsa take ainun, amma bata ta6a cewa dashi uffanba har cikinta yakai haihuwa.
Tab an da6a kenan, inji masu iya magana, dan kuwa wannan karonma Aminatu Mace ta sake haihuwa k'yak'yk'yawa San kowa k'in Wanda bai samuba, itadai murna tai tayi da kuma godema ALLAH da wannan k'yauta. Amma ga zakari ba haka bane, dankuwa jiyay yakuma tsanar Amina, wai danmi zataita cika masa gida da y'ay'a Mata. A wannan Karon koda ya takalota da fitina bata d'aga masa k'afaba, tai masa tatas, wannan shine silar guntulewar aurensu, sai a gidansu aka rad'ama jaririya suna Hannatu, dan kuwa Zakari yace yabar mata bayaso. Ran mahaifiyarsa yakai k'ololuwar 6aci, ta tattara kayanta takoma Adamawa ita da yahaya.
Shekarar su d'aya da rabuwa da Aminatu yasake aure, Wanda da k'yar mahaifiyarsa ta amince, saida ma Baban Aminatu ya saka baki.
Saidai wannan karonma auren Zakari da Ai'sha baiyi k'arko ba, dankuwa tun a haihuwar farko suka raba jaha, sakamakon haihuwar d'iya mace mai suna Zulaiha. Itama yace bayaso ya barmata. Ananma sosai mahaifiyarsa ta fusata, amma bisa hak'urin da dangi sukaita batane yasata hak'ura. Zakari yakuma auren Rammah. A haihuwar farko Rammah ta haifi mace itama, tashin hankali kenan, dankuwa Zakari yakai k'arshen fusata da haihuwar Mata da ake masa, a cewarsa haihuwarsu batada wani amfani sai d'orama mutum nauyi (=ØAÞhumm).
Itama dai batakai labariba ya 6alleta tareda bar mata y'arsa mai Suna Nafisa tace bazata rik'eba. Dole ruk'on Nafisa yakoma hannun mahaifiyarsa dake Adamawa.
Bayan Aurensa da rammah saida ya shekara hud'u bai k'ara zancen aureba. Sai kuma rana tsaka ALLAH ya had'ashi da Y'ar Shuwa wato Yagana, Zakari ya had'u da Yagana ne a Adamawa, lokacin yazo gaida mahaifiyarsa, yayinda Yagana kuma sunzo biki makwaftansu mahaifiyar Zakarin. Dandanan soyayya ta k'ullu a tsakanin yagana da Zakari, dukda sukarsa Na auri saki da k'in haihuwar y'ay'a Mata da akaita kawo Mata. Ba awani ja lokaciba manya suka shiga magana, akaje har Maiduguri aka d'auro auren Yagana. Saida tayi sati biyu a Adamawa sannan suka taho kano, bisa ga dogon gargad'i da mahaifiyarsa tai masa, takumace inhar ya Saki Yagana ALLAH ya isa bata yafeba koda a bayan rantane...........
'<Øûß



(Turkashi=ØFÞ<Øûß).






*_ya RABBI ka gafartama iyayenmu=Ø-Þ=ØOÞ<Øûß_*
[11/14/2019, 9:49 PM] =ØžÜNoorunnisa=ØžÜ: *_Typing=ØòÜ_*



*_=Ø¡ÜHASKE WRITER'S ASSO...._*



*_=اÜMUTUM DA DUNIYARSA....!!=اÜ_*
_(ya dace ya gyara kansa)_



*_Bilyn Abdull ce>ØÝ<Øûß_*


*_Ya rabbi kabani ikon fad'ar abinda zai amfanar da al'ummarka, ka tsare harshena daga fad'ar abinda zai cutar daku da ni baki d'aya._*=Ø-Þ=ØOÞ<Øûß


_Ya ALLAH ka gafartama mahaifina abin alfaharina da dukkan y'an uwa musulmai da suka rigamu kwanta dama=ØOÞ<Øûß=Ø-Þ_


*_Wannan littafi tukuycine a gareku my sweet sisters, ina gidiya da karamcinku gareni, alkairin ALLAH yakai gareku a duk inda kuke._*>ØpÝ>ØpÝ>ØÝ<Øûß

_Billy s Fari_
_Ummu Basheer_
_Fareeda Musa sweery_
_Ai'sha Manshat_
_Hafsat writer d'in Hafiz_


__________________________________


*_[2.....]_*


................ Zakari dai yataho da Yagana kano cikeda farin ciki, sunkumazo sun zauna lafiya har ALLAH yabata ciki itama, a lokacinne kuma yahaya shima yadawo kano suka cigaba da kasuwancin atanfofi da shaddoji shida d'an uwansa Zakari.
To a wannan Karon dai Yagana ta Haifa masa Namiji, wayyo zokaga murna da tsalle da shirin suna Na bajinta, ragoma biyu aka yanka kuma manya-manya. Ansha shagalin suna yaro yaci suna Nuhu. Sai dai kash bayan suna da kwanaki uku yarasu, wannan Abu yasaka Zakari takaici, harda kukansa rurus, kaikace wani babban mutumne yarasu.
Babu dad'ewa Yagana takuma samun wani ciki, Zakari ya shiga tattalin ta kamar zai maidata a ciki, dan a ganinsa Namijin za a kuma Haifa masa. Sai dai kuma shi Ubangiji babu mai masa shishshigi a lamarinsa. Koda Yagana ta haihu saiga d'iya mace. Babu kunya Zakari ya nuna tsantsar takaicinsa da haihuwar jaririya, gashi babu damar sakin Yagana. Yarinya taci suna *HAUWA'U (Jiddah)*, ko kad'an Zakari bai damu da Hauwa'u ba, koda ciwo takeyi babu ruwansa balle ya damu, ahaka takai yaye aka yayeta, Yagana takuma samun wani cikin. Nanma Zakari ya saka idon ganin namiji, amma saiga mace, itama kiri-kiri ya nuna bayaso, taci suna Fatima (Zarah), bayan an yayeta saiga wani ciki, a wannan Karo zakari baiwani damuba, hasalima ya maida hankalinsa ga kasuwancinsa ne daketa ha6aka gaba d'aya, ga shirin auren Yahaya da sukeyi kuma.
Ansha bikin yahaya da matarsa Zulaiha, itama ta tare anan cikin anguwar, amma haya ya kama kafin ALLAH yakawo kud'in gina d'an filinsa daya siya. Bayan auren yahaya da kwana ashirin da uku ALLAH yayma mahaifiyarsu rasuwa, takuma jaddada wasiyarta ga Zakari inhar ya saki Yagana bata yafeba. Sunsha kuka da alhini rasuwarta, kwananta tsara a k'asa Yagana tafara nak'uda, amma sai Zakari ya nuna halin ko inkula akanta, acewarsa bazai wahal da kansa da dukiyarsa ba ahaifa masa wadda bazata iya taimakonsa da komaiba idan ta girma. Haka Yagana tasha matuk'ar wahala kafin ta haihu dak'yar, wahalar da tasha yasaka jinjirin jigata yazo babu rai. Hankalin Zakari yatashi matuk'a, yakumaji haushin kansa ainun, dan aganinsa sakacinsa yasaka su6ucewar Abu mafi daraja da soyuwa a gareshi, ya rungume gawar yaron yayta hawaye da ALLAH wadai ga abinda yayi, daya kai Yagana asibiti da yanzu...


Read / Download MUTUM DA DUNIYARSA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On MUTUM DA DUNIYARSA
avatar
rukayya-yahuza

5 months ago

Reply

Kai book dinnan ya hadu iya haduwa

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album