Join Our WhatsApp Group

MASEEFAR SOO Complete Hausa Novel Document by MASEEFAR SOO


MASEEFAR SOO

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 83885MASEEFAR SOO

Reading Time: 6 Hours

Added On: 28, Apr 2024

Author: Rahma Muh'md Rufa'i Nalele ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 07038260028, 09051533739, 08085342390

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 496.63 kb

File Type: txt

Views: 413+

Download: 316+

Last download: 7 hours ago

Description/Story: [10:42PM, 02/11/2016] Rahamat Muh'md Rufa'i Nalele.: 🌡🌡🌹🌹🌡🌡
MASIFAR SOO.....🌹
🌡🌡🌹🌹🌡🌡

Na
Rahamat Muh'md
Rufa'i Nalele
Bismillahir-rahamanurrahim
Part 1
07038260028


Tafiya suke Cikin tsanaki. Kansu 'daya yanayin jikinsu 'daya. Kallo 'daya xaka musu kagane nutsattsune. Kayan jikinsu tsaf dashi na islamiyar dan yasha goga dashi
Suna hanyarsu tadawowa daga islamiyane
Bakin 'daya daga cikinsu ne Ni Rahamat naga yana motsi alamar xatama 'yar uwarta magana. Shine naga bai cancanta tayi maganarba harsai nafa'da muku kosu Su suwaye....

Fara da jah suke
Aisha-Labibah jar yarinyace mekalar sanyi da nutsuwa.
Tanada kyau tamkar ita tayi kanta batasan hayaniya sosai Amma tana'dan magana idan kukasan juna. Tanada hanci xirr baki madai daici mefa'din fuska ka'dan da kuma gashin kai yala yala Sannan ma'abociyar dariyace da fara'a.
Tanada shagwa6a da halin yanayin yara tare da xaqin murya

Yayinda Fatima-zarah takasance fara soll me gashi da hanci me doguwar fuska da dogon hanci bakinta me'dan fa'di.
Ma'abociyar Murmushi da surutu da iyayi batasan raini shiyasa batasan sakewa mutane kamar Aisha-Labibah

Aminan junane Su biyunnan wato Aisha-Labibah da Fatima-zarah
Aranar da Fatima taxo duniya dasafe aranar Aisha ma taxo duniya da yamma

Gidansu Aisha na manne danasu Fatima
Iyayan Fatima dana Aisha aminan junane hakan yasa xumuntarsu har tagangaro kan 'ya'yansu

Iyayan Fatima-zarah Fulanin gwambe ne xamane da yanayin rayuwa ya kawosu kano unguwar Kurna da xama
Anan suka ha'du da iyayan Aisha-Labibah wa'yanda damasu mah Fulanin Yola ne
Ganinsu makwafta yasasu ha'de kansu kamar xuri'a 'daya

Gidansu Aisha-Labibah Su uku iyayansu suka haifah
Suleiman da Usman sai ita Aisha-Labibah
Suleiman yanada mata Zainab sunada yara uku
Yayinda Usman ya maida hankalinshi kansana'ar shi bayi da ra'ayin aure yanxu

Gidansu Fatima-zarah ko Su hu'dune tanada yayu biyu maza Bashir da Nasuru
Wa'yanda sukeda mata bibbiyu
Sai ita da qanwarta Sumayya
Bashir yaransa hu'du. Nasuru ko uku

Shekarun Aisha-Labibah da Fatima-zarah goma Sha bakwai yanxu
Sungama secondary skull tuni
Amma dake iyayan nasu sunfiba karatun mahammadiya mahimmanci tohakan yasa basu barsu sunci gababa. Suka barsu a islamiyarsu da suke xuwa

Wannan shine asalinsu labarin wa'dannan bayan Allah

Aisha-Labibah kalli Fatima Tace kinko ga rashin mutuncin da Malam Auwal yamana yau
Fatima-zarah Tace hmm ina hangoshi ta ajinmu yasaku tsallan kwa'do


Tace Ashe kinganmu Wallahi natsane shi. Fatima-zarah Tace kika tsaneshi ko natsaleshi
Aisha-Labibah Tace aishikam baiji da'diba ayi mutum mugu azzalimi me Baqin hali
Fatima-zarah Tace hmm gaskiya baiyiba Amma nan gaba zaigane kuskuransa daxaran yasamu futsararrun 'dalibai.......

Sam Aisha-Labibah bataji qarashen furucinta ba sakama kwan ganin wani ha'daddan saurayi datayi Cikin motarsa mekyau na'daukar hankali wanda kuma Fatima-zarah bata lura dashi bah

Kallo 'daya Aisha-Labibah tamai tagano abu uku agareshi
Me kyaune naqarshe irin tsaftacaccan kyau 'dinnan na larabawa mesanyi da shigarai lokaci 'daya
Me ajii ne me tattare da ilimi da wayewa dajin gayu da tsafta ha'de da yanayin taqama
Gashi xaiyi muskilanci dabin ra'ayinsa
Qara tsaida idanta tayi akansa nan taqara hango wani sirri nashi wato me fara'ane da 'dan sanyi ka'dan yanada fa'din qirji sannan shiba qatoh bane. Kuma baxa'a sashi sawun masu qananan jikiba yanadai tsaka tsaki

Tun daga motarshi Aisha-Labibah taji qamshinsa ya bigeta yayinda talumshe idanta. takuma bu'de ahankali. karab suka ha'de ido dashi
Gabanta yayi wani mummunan fa'duwa nan take kuma taji tanasan suqara ha'de idan
Tamkar ya ankare yaqi yarda sukuma ha'da idan. Saima maida hankalinsa dayayi gurin kallan Fatima-zarah
Yayi faking dai-dai inda suke dayin saurin fitoh da kansa daga motar Yace jimana 'yan mata dan Allah karku shareni ina tambaya ne......
Ya subhanallah abinda Aisha-Labibah tace kenan aranta dan tunda take bata ta6ajin da'din muryar saurayi kamar nashiba mesanyi da da'din sauraro ha'de da taushin 'daukar hankali
Atare suka juyo gareshi gaban KAMAL yaqara fa'duwa akaro nabiyu dan qara ha'da ido dayayi da Aisha-Labibah hakan yasashi saurin maida kallanshi ga Fatima-zarah
Yace dama tambayar sunanki xanyi my luv

Fatima- zarah tatsaida idanta akanshi dakyau Tace ayya banda suna. Yace kice ke 'Yar baiwace Tace ba mamaki kam yayana.
Sauri muke kaga baifi taku hamsin xamuyi ba mushiga gidanmu. Dan haka kasamu damar daxaka iya tambayar cikakken gaskiyar xancanka nabaka minti 'daya.
Yace gaskiyar xancan shine tunda na'dora ido akanki xuciyata takamu da soyayyarki inasanki my luv
Tace tab kamakara dan isiyaku yarigaka shiga birnin soyayyata dan haka sai'anjima......

Aisha-Labibah wacce ta kafeshi da ido takasa matsawa saboda yanda takejin da'din muryarshi da sanyin dayake shiga xuciyarta. Sam batasan Fatima-zarah tayi gababa.
Ya maida kallanshi kanta ganin shitake kallo hakan yasashi 'dan Murmushi
Innalillah taqara cewa aranta saboda wani kyau murmushin yaqara mai
Yace ayya qanwata nabaki tausayi ko. nasan shiyasaki kallona. Plx kifa'damin sunanta da naki Amma fah nata xaki fara fa'damin dan hankalina ya kwanta
Wallahi tatafi da xuciyata inasanta


Gaban Aisha-Labibah yaqara fa'duwa danjin yanda Yace yanasan Fatima
Ahankali tasaukar da kanta qasa. Yayinda shikuma yamaida kallanshi ga Fatima-zarah wacce take dawowa da'alama jan Aisha taxoyi
Cikin firucin dabai wucce sakan uku ba Tace sunanta Fatima-zarah.......
Da sauri ya maida kallansa kanta dajin da'din muryarta. Dan Ba shakka tafi Fatima da'din murya
Amma yanasan qarajin muryar tata Yace toh naki sunanfah
Takalleshi ka'dan suka ha'da ido. Abin dai dataji daxu shita kumaji
Dan haka Cikin sakan biyu Tace Aisha-Labibah
Yayi saurin runtse ido hakan kuma yaxo dai-dai da qarasowar Fatima
Taja hannun Aisha tana cewa da ganinshi dan jarida ne mesace sirrin mutane baxan barki yamiki wayo kisaki baki kigaya mishi sirrinmu bah
Yace Allah yahuci xuciyar my luv niba'dan jarida bane. Bayanma qawar taki rowar magana take dashi
Yafa'da hakanne dan Aisha-Labibah taqarayin magana ko ya qarajin dadda'dar muryarta. Amma saitayi 'dif tabi Fatima-zarah tamkar raqumi da akala

Shima ganin haka yasashi binsu ahankali da motarsa. Haryaga gidan da kowaccansu tashige. Amma kan Aisha tashiga gidansu sanda tajuyo takalleshi Sannan tashige gidan
Yaqurama gidajen nasu ido ba shakka Su talakoki ne dan kaf layin gidajensu ne marasa kyau
Ya Shafah kansa Yace naga gidanku zarah tare dana qawarki Allah ya bani ke Zarah.
Yana fa'din haka yaja motarshi gaba ka'dan gidansu abokinsa dake kusa da gidansu Aisha
Yafitoh atsanake da wayanshi ahannu Yana neman abokin nasa Auwal Nanko yasameshi Yace dan uwa kafitoh gani kofar gidanku
Yana fa'din haka ya kashe wayan
Ko cikakken motsi baiyi bah saiga Auwal yafitoh da fara'arshi Yace wow 'dan Uwa Ashe da gaske kana tafe yace ga zahiri
Nan suka tafah sukayi Cikin gidan nasu Auwal
Bayan KAMAL yagaisa da Hajjiya mahaifiyar Auwal . Yace Ashe mutumin nawa baiji da'diba Tace aiyama yasamu sauqi tunda Yana fita
Da sauri KAMAL yakalli Auwal Yace wato ka warware shine katasoni
Yace eh kawai inasan ganinka ne Yace Allah ya kyauta maka Allah yasa maganar arxiqice kuma Yace itace
Hajjiya tace aikam gwara ka tambayeshi dan kasanshi da shiririta Yace hakane hajjiya
Tatashi takawo miki abinci Tace dan Allah kaci karkace kaqoshi nasan halinka Yace ahaba Hajjiya yau ai banci Komai ba nace abincinki xanci saboda karmiyi fa'da dake yau
Cikin farinciki Tace yauwa ai kakyauta
Auwal ya 'dauki abincin nasa Yace muje ko
Nan suka shige 'dakin Auwal
Bayan KAMAL yaci tuwan shinkafar miyar taushe Yace naji da'din tuwannan Auwal Yace qila ka kwan biyu bakaci ba Yace hmm yaufah nayi gamo da soyayya acikin layinkun nan


Auwal Yace kai habadai
Yace da gaske
Auwal yagyara xama Yace tab abinda da mamaki waiyau Kaine dacin karo da soyayya ina yara'ayinka yake.
Kodai yau kakah tamaka kukane shine yasaka jin tausayinta
KAMAL ya girgixa kai Yace ko 'daya kaima Kasan bayau tasabamin kuka ba
Kawaidai Allah yayi yau xanci karo da sone. Shiyasa nadingajin fa'duwar gaba tun agidan kakah.
Wallahi Auwal Naji San yarinyar ne kamar yanda kasan ake harba kifiya haka santa yashiga xuciyata
Amma kasan meyaban mamaki
Auwal Yace aa
Yace dana kalli wacce zuciyata takar6i soyayyarta banji bugun xuciyata ba.
Amma dana kalli 'kawarta sanaji mummunar fa'duwar gaba takamani
Yace idan nacanki wacce xuciyarka ta kamu da Santa xan'iya cewa Aisha-Labibah
Da sauri KAMAL Yace Fatima-zarah nakeso wannan karan tubaninka baixo dai-dai ba.
Auwal yayi dariya Yace kace zarah ta camke xuciyarka
KAMAL Yace sosai mah. Tayima xuciyata mugun kamu

Auwal yaja numfashi
Yace gaskiya na tayaka murnar samun Fatima-zarah amatsayin wacce xuciyarka keso
Gidansu sunada tarbiya sosai
Musamman gidansu Aisha-Labibah. Wallahi KAMAL duk aguwannan ba nutsattsun yara kamarsu
Ammafa Labibah tafi Zarah sanyin hali bata cika San hayaniya ba. Amma Zarah tanada surutu bata san raini. Sam tayi fa'da bai dameta ba idan kashiga gonarta
KAMAL Yace koma dai miye naji Santa fiye da tunanin me tunani. Ashe dama haka Masoya sukeji idan suka fa'da soyayyah
Auwal Yace kwarai ai ingayama wasuma sunaji fiye da yanda kaji yanxu
Yace toh yanxu dai xantafi dan yau nakesan komawa
Cikin Takaici Auwal Yace meyasa kakemin hakane bayan Ni bahaka nake makaba
KAMAL yatashi da dafashi Yace habah 'dan Uwa Kasan halin aikina
Jiya da yaune kawai ranar samun hutuna idan Nace xankwana yau kaima Kasan akwai matsala plx kafahimce
Yata6a baki badan ransa yasoba Yace na fahimceka
Yayi Murmushi Yace yauwa muje ko
Haka suka fitoh Hajjiya nacewa tunyanxu kafitoh KAMAL meyasa baxaka bari sai gobeba
Yace ina
Ai idan nace xankwana akwai matsala gun aiki Tace hakane Allah ya temaka ka gaishemin da kakah Larai
Yace AmEEn xataji

Nan KAMAL ya bata ku'di me'dan dama takar6a tana xubamai gidiya
Kaidai baka gajiya Allah yasaka ya albarkaci dukiyarka
Yayi Murmushi Yace AmEEn Hajjiya
Nan suka fitoh

KAMAL Yace yanxu dai saikaxo.......
Malam Sanih ne yafitoh daga gida mahaifin Aisha-Labibah
Da sauri Auwal Yace ga mahaifin qawar Zarah wato Labibah
Kallo 'daya KAMAL yanasa yaji qaunarsa yashiga xucitarshi

Dan haka sukayi gunsa da sauri suna kwasar gaisuwa
Cikin fara'a Malam Sanih ya amsa.
Ya tsaida idanshi kan Auwal Yace ina kasamo aboki nagari me ladabi kamarka
Da Murmushi Auwal ya kalli KAMAL Yace
KAMAL kenan babah yama fini kyan hali
Shima Murmushin yayi Yace toh Allah ya muku albarka......
Kansu amsa saiga magaifin Fatima-zarah yafito yamiqama mahaifin Aisha -Labibah hannu suka gaisa
Yace yanxu nake rayawa araina koka fito Yace eh. fitowata kenan
Maihaifin Zarah Malam Sallau ya maida hankalinsa kansu KAMAL Yana niyar yimusu magana suka rigashi wajan gaisar dashi
Ya amsa da walwala yaha'da da tsokaci da akan KAMAL ganin hankalinsa
Auwal Yace dama yaga Fatima-zarah ne yana Santa shine mukace bara mufara neman ixini Allah yasa alamunce mana....
Yaqarashe maganar da sosa qeya alamun kunya

Cike da farin ciki Malam Sanih da Malam Sallau sukace an lamunce muku karkuji Komai aikai Auwal Fatima-zarah da Aisha-Labibah qannanka ne wannan Bakomai Allah dai ya tabbatar mana da alkairi
Cikin murna sukace AmEEn

Nansu suka tafi
KAMAL na yaba sauqin kai irin nasu iyayan Aisha-Labibah da Fatima-zarah

Yacema Auwal gaskiya Naji da'din yanda kashigar dani garesu
Auwal Yace karka damu natabbata idan momy taji Nina shige gaba wajan kawo mata surukarta daga gareka ba qaramin farin ciki xatayibah
KAMAL yayi Murmushi Yace hakane kam
Amma maganar gaskiya naji San tsofaffinnan araina
Auwal yace tukunna ma KAMAL saika mallaki 'daya daga Cikin 'ya'yansu

KAMAL Yace madallah da kawo maka xiyara ta wannan ranar
Yace tunda kayi gamo bah
Atare suka bushe da dariya.
KAMAL dai ya tafi badan Auwal yaso ba
Tsohuwa ce Amma ba tukubba tana tare da 'yan aikinta sunkai biyar. suna hira Cikin farin ciki da annushuwa
KAMAL ya shigo Cikin farin ciki
'Yan aikin suka ficce
Kakah takalleshi Tace yadai naganka haka da'alamar farin....
Baibarta taqarasa bah Yace ina Cikin farin ciki kakah
dan yau nasamo miki kishiya
Tawashare baki tamkar taha'diyi TV tana kallanshi Tace ikwan Allah a ina take 'dan nan
yau Allah ya amshi addu'ata
Yace aikuwa dai
Nan unguwarsu Auwal naganota
Kyakkyawa da ita dan tafiki kyau
Tace a lalle xanyi kishi da ita
Yana Murmushi yatashi yana kallan agogo Yace toh xanhucce dan saura minti tanatin jirgi yatashi
Tace toh Allah ya kaika lafiya yayi maka albarka yakaremin kai daga sharrin mahassada
Yace AmEEn kakata takaina. Ba wani abunda kuke buqata Tace Bakomai ai kasani
Yace toh ga wannan koxaki buqaci wani abun
Tace kabarshi bana buqatar Komai
Yace um umfah kar farincikin xuwan kishiya ya mantar dake abubuwan da kikeso Tace aiwannan farin cikin ya cancanci ya mantar dani Komai
Yayi Murmushi Yace Toni natafi
Tace gashi Jamilu bai dawo ba
Yana tafiya Yace shareshi kawai sai kinganni Tace karka da'defa wajan dawowarka gareni
yace toh
Nan KAMAL ya tafi birnin taraiya Abuja inda yake


Aisha-Labibah nashiga gidansu tatarar da mamah na shara dake haka suke kiranta. Ta xauna a 'Yar kujeraisu 'yar tsugunno

Cikin sanyin jiki Tace mamah sannu da gida Tace yauwa kundawo Tace eh
Da sauri mamah tasaida idanta akan 'Yar tata tana naxarinta dan bata ta6a shigo mata a irin wannan yanayin ba
Taji muryarta tacanja alamun da damuwa acikinta Tace lafiya naganki wani iri haka
dafe goshi tayi Tace kaina ke ciwo.
Tace toh kije kicire kayan naki kiyi sallah inkinci abinci akwai panadol anan Cikin kwallah saikisha ki'dan kwanta Tace toh
Bayan tacire kayan tayi Sallah dacin abincin. Saitasha maganin tamiqe a'yar katifarta tashiga tunani KAMAL

Tatuno lokacin da yayi Murmushi. Tayi saurin rungumar fitoh dan tatuno farin Cikin data shiga awannan lokacin
Taqara tuno muryarshi. Saita lumshe ido tana Murmushi
Can kuma kome tatuna saitayi cilli da filan tana tafe qirji tace nashiga uku
Meyake shirin faruwa dani
Ban san saba saiyau Amma meyasa xuciyata tacika da San qara ganinsa meyasa

dame bata amsa dan haka tadafe kanta tanasan sanin dalili

Fatima-zarah...


Read / Download MASEEFAR SOO

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album