Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

INA ZAN GANSHI Complete Hausa Novel Document by INA ZAN GANSHI


INA ZAN GANSHI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 48660



INA ZAN GANSHI

Reading Time: 4 Hours

Added On: 06, Feb 2025

Author: Xarah Bukar ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 271.6 kb

File Type: txt

Views: 179+

Download: 209+

Last download: 1 day ago

Description/Story: [10:00PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: *INA ZAN GANSHI*💖
Rubutawa
©Xarah Bukar

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION {NWA}

xarahbukar.wordpress.com

1 - 5

 Banko k'ofar d'akin da k'arfin gaske ya firgita Hajjo dake k'ok'arin had'e tabarmin dake yashe gefe guda. Fuska murtuk'e ta sak'alo k'afa ciki d'akin tana gunguni. Cike da k'unin rai Mahaifiyarsu Hajjo ta zuba mata idanu.
"Batula baki iya Sallama ba?"
Haushi ne ya kuma turnuk'e ta da sunan Batula da Hajjo ta ambata, tafison akirata da Fatima Zarah ainihin sunanta.
"gaskia Hajjo ana shiga hakkina a matsiyacin gidan nan, saurayina yazo daga fita ta Baba ya izo k'eyata, da alamun kuma da d'an maik'on sa, oh ni Fati naga samu naga rashi" karashe maganar tayi cike da tashin hankali, hannuwan ta biyu bisa kanta.
Tak'aici ne ya cika Hajjo, wana irin k'aramar kwak'walwa yarinyan nan keda shi, "Batula miyasa baki da hankali, talauci ba hauka bane, ki kuma iyawa bakin ki, matsiyacin gidan nan gidan uwarki da ubanki ne ba yadda kika iya"
Shuru Batula tayi zuciyar ta na tafasa, banda harara talautaccen dakin da take.
"Maza jeki rumfar babanku ki amso kayan miya kafin ya kasa na kasuwa" acewar Hajjo batare data kula da yanayin ta ba.
Ware idonu tayi, tayi tace "nikam bazani niba, ajira dawo wan su Hassan saisu karb'o"
"Dole kije dan bazan tsaya jira harsai sun dawo makaranta zan aza abinci ba, wuce ki karbo kafin na mazge ki" Hajjo ta fadi da niyyan kai mata dundu
Gunguni tahau yi bata da alamun tafiya saida Hajjo ta hada mata tsawa mai dauke da ashariya sannan ta fice ak'ufule bayan ta tsuri mayafin ta dake lank'aye bisa taga.
Gaban karamin gidan nasu dako fenti babu ta iske wani yaro tsaye.
"Baba mai kayan miya na nan ? Yaro ya tambaye ta.
Idan akuya na magana to ta tanka bangajesa tayi ta wuce abunta cike da haushin yadda Baba ke zubar mata da aji, wai itace diyar mai kayan miya, dogon tsaki taja ta k'arasa can gaba da gidansu inda runfam Baba yake, bata kai ka zuwa rumfam ba ta mak'ale daga gefe inda baba bazai hango taba, amma tuni ya ganta ya dauke kai, Lawali ta kira yaron auguwan su ta aikesa amso kayan miyan.
Sabo da halinta yasa Baba bai nuna yaganta ba, jinjina kai kadai yayi, albasa batayo halin ruwa ba. leda taf ya cikawa Lawali sannan ya damk'a mai.
    Hankalin ta gabadaya ya shagala da kallon wasu yara da Mamansu cikin wata arniyar jeep, sai kallonsu take ji take dama itace acikin motar da tafi ko wace ya mace morewa, sai dai kuma aka samu akasin Baba talakana ne saidai su k'are da tumatur da albasa.
"Butula gashi" taji yaro na fadi, harara takai ma sannan ta warce ledar tayi gaba, Hajjo na iza wuta a gindin murhu ta shigo ta dire ledar tayi cikin kusurwar daki.
Girgiza kai Hajjo tayi, tunanin barkatai ke yawan mata a kwakwalwa, inda ba a gidan ta haifi Batula ba tana iya cewa an mata musanye, amma ba daman fadin haka kamarsu daya da Baba kamar an tsaga kara.


***
K'asak'asa suke zantawa da alamun wata muhimmaciyar magana sukeyi, nisawa Hajiya Fatima tayi tace "Safara ya kikeso nayi kinsan Rasheed wani irin murd'add'en mutum ne da baa iya tank'wara shi, tun rasuwar ubansa ya koma hawainiyar da babu kala"
Murmushin dabai kai zuci ba Hajiya safara ta mata sannan tace "yaron nan dai d'an kine ke kika haifeshi bashi ya haifeki ba sai kisan yadda zakiyi ya amincin da kudirin mu.."
Turo kofar tafkeken palon ne ya katse masu zance, sanye yake cikin black suit, haunna sa rike da karamin brief case, ciki ciki yayi sallama, basu amsa ba banda kallo da suke bisa da shi, maihaifiyar sa hajiya Fatima ce tayi karfin halin cewa my boy ka dawo.
"e" kawai ya amsa mata agajarce ya wuce hanyar dakinsa cike da haushin Hajiya Safara dake hakince kan babban kujerar palon, idan bai manta ba tun yana yaro yake ganinta saidai jininsu bai taba haduwa ba, ya rasa mai suke yawan zantawa tare da momyn sa akullm idan suka hadu, tsaki kawai yaja ya cusa kai ciki had'add'an dakinsa.
Fitowa tayi daga kitchen, hannuta ruke da kwalin exotic ta karasa cikin palon cike da yauki da iyayi. "Mardiyyah mutumin ki fa ya dawo"
Acewar hajiya Safara,
"Dagaske " Mardiyya ta fadi tare da kwalalo ido tana kallon Momy dake mata murmushi, sai kuma ta kalli ogogon hannuta tun 4 tabaro office amma shi sai yanxu 8 ya dawo.
Tashi tayi da azama, zata bar palon, hajiya safara tace "kardai ki dade, dare yayi kar Abban ki yajimu shuru"
"Toh Umma" ta fadi tayi rushing zuwa kitchen ta sanya ruwa a glass cup sannan ta nufi kofar dakinsa gabanta na dukan uku, tasan sarai xai iya korota shiyasa tayi dabarar kaimai ruwa, ahankali ta tura kofar dakin ta shiga.
Tsaye yake yana kokari cire neck tie bayan ya ajiye coat din gefe, ganinta da yayi ya dakatar dashi yanai mata kallon kina bukatar wani abune, kaman tasan abunda yake aynawa, girgiza kai tayi tace "Mr Rasheed sai yanxu ka kawo, ga ruwa kasha" ta fadi at once hade da mikamai glass cup, bai karba ba balle ya tanka, closet ya nufa yadau towel yabar ta tsaye ya shiga bandaki, ya rasa wace irin mayyace Mardiyya, at work bai tsira ba sai taxo har office yimai shishigi ya dawo gida kuma ta biyosa, wace irin rayuwace wanan, most annoying part of her shine yadda take kura mai manyan idanuwan ta da mak'e muryarta tamkar wata sabuwar farar kura.
Rashin tankata da yayi ko a kwalar rigarta, inda sabo ta saba, sukanyi shafe awa hudu biyar ko tari bai yiba, duk wannan ba matsalarta bane koda ace ma wuka zai dauka yana datse naman jikinta bata damu ba, tana sonshi kuma ganin kyakyawan fuskar sa ya ishe ta farin cikin shekaru ashiri. Murmushi tayi ta kwank'wade ruwan tas sanna ta fito palo, hajiya safara na ganin empty glass cup din taji farin ciki ya ziyarceta, komai yafara kankama tsakanin yarta da Rasheed kenan tunda har ya iya amsan abu gareta. Duk aganinta shiya sha ruwan.
Sallama sukayi da Momy, ta rakasu har bakin motar su sannan ta dawo cikin gida ta wuce dakinsa.
Gefe gado yake zaune yana brushing lausassiyar kashin kansa bayan ya fito daga wanka, zama tayi kusa garesa heda da amsan brushern tahau tazarmai lufluf tana fadin,
"my boy ya aikin ?
"fyn" ya amsa mata, fuska ba yabo ba fallasa.
"My boy ka girma, ga kudi ka tara ta ko ina, yanxu miya rage ?"
Anxo gurin, daure fuska Rasheed yayi tamau, tacigaba
" sa'anninka masu shekaru talatin da uku duk sunyi settling banda kai, ya kamata kayi aure"
Murya can kasa yace.
"am not ready, infact ban samu wace nakeso ba har yanxu"
"wannan ba excuse bane, kana da alot of yammata masu sonka, ga Mardiyya yarinyar kirki masu hannu da shuni, itace daidai dakai, naira na gugan naira"
Kai ya girgiza "bana son Mardiyya infact banason ya'ya masu kudin nan yawanshi basu da isheshen tarbiya, it better nasamo wata can cikin talakawan nan"
B'ata rai Momy tayi, inda akwai alumma data tsana bai wuce talaka ba, mikewa tayi tsaye tanai mai wani mugun kallo, cike da karaji tace "talauci badai a xuri'ata ba, na gwamma ce mutuwa ta akan naga ka auri dangin tsiya, ban haifi dana dan talaka suci arzikin saba, tunda ubana ya haifeni bansan miye talauci ba kayi na farko kayi na karshe koda wasa karka kuskura ka ambata kalmar talauci a gidan nan, Mardiyya kuma saika aureta" karashe maganar tayi cikin huci sanan tai wurgi da brushen ta fuce dakin afusace.
Murmushi mai sauti yayi,
ya lura dai dabiar Momy bazata gyarabu, hatred dinta towards talakawa bazai canxu ba, ya rasa miye tsakanin dinta da takala, same story dinta kenan tun yana karami shiyasa yake da burin aurar talaka dan ganin miye illarsu da Momy ke masu kara tsana. Wayarsa dake kusa dashi ya dauka yayi dailing numbern Daddy Malam, bugu daya ya dauka suka gaisa. Yace "Mr Rasheed kwana biyu, fatan kana cikin k'oshin lapia
"Am good, Aikuwa suka min yawa a office, kayi ready din komai gobe xan zo na cigaba a inda na tsaya"
"Toh sir, Allah ya kaimu"?
"Amin ya amsa mai sanan ya katse call din ya shingid'e bisa gado hade da lumshe idanu.
Safa da marwa Momy
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download INA ZAN GANSHI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album