Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

KA SAKE TA NA AURA Complete Hausa Novel Document by KA SAKE TA NA AURA


KA SAKE TA NA AURA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 10532



KA SAKE TA NA AURA

Reading Time: 0 Hours

Added On: 08, Sep 2023

Author: HausaEbook ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 54.91 kb

File Type: txt

Views: 1008+

Download: 320+

Last download: 3 days ago

Description/Story: KA SAKE TA NA AURA
Hausaebooks.cf
Ebook creator:- Shuraih Usman
Domin download na wasu kayatattun littatafan Hausa a matsayin Hausaebooks tayadda zaku iya saukewa ku karanta acikin wayoyinku sai ku ziyarci wannan shafi www.shuraih.waphall.com Sannan ku zabi littafin da kuke so

For more download of some non- fictional hausa books as a hausaebooks so that you can download it to your phone and read it at any time (offline reading) then visit our wepsite at www.shuraih.waphall.com Adress and select your books for offline reading
Gargadi:- wannan ebook din bana sai ruwa bane kuma ba anyishi bane don batanci ga wani koh ga wata
Sannan ni shuraih Usman 99% bana tura littafi ta private kuma bana whattsapp sannan banda group a whattsapp ga wanda yaga wani kuskure da muka making acikin wannan littafi sai kiramu akan wannan nombar 08170707521

Ga duk wanda baisan yadda ake downloading na littatafanmu ba sai ya ziyarce mu akan wannan adireshin yanar gizo gizon http://keffians.xtgem.com/forum Sannan yayi tambaya in sha'Allah muku ma zamu mai bayani dalla dalla akan yadda ake sauke littatafanmu
Sannan ina kara maimaitawa bana whattsap kada wani ya ha'ince ku ta hanyar amfani da sunana a whattsap asha karatu lafiya
Hakkin mallaka (m) http://hausaebooks.cf


=>ma'auratane,
Suna manne da juna tamakar wasu tif da taya sobada tsabar tsantsar kaunar da sukewa juna wacce ta zarce ta Laila da Majnun...
Zallan so wanda ba mis ko na kwayar zarra shi ke tasiri a wajen ma'auratan.. Kai duk yadda mutum ke zaton wadannan masoyan sun shige nan. Auren cikar buri sukayi da juna wanda suka shafe sama da shekaru biyu suna zuba 'yar ubansun soyayya, karshe kuma Allah yayi ikonsa a kansu ya cika musu barinsu suka mallaki juna a lokacin da suke muradin hakan.
Mako biyu cif-cif da yin auren masoyan, amma basu taba rabuwa da juna na sama da minti goma ba. Kullum suna tare komai tare suke yi...
Kai! Wadannan masoya fa sun wuce kwatancen mai kwantance, sun zama ma'aurantan da kowa zaiyi sha'awar inama shine?
A hankali kuma cikin shagwaba Amarya Safina ta dago ta dubi angon nata sai ta wani cuno baki kamar wata yar bebi. Ta kara lafewa a faffadan kirjin sa.
Ya sunkuyo da kansa ya kalle ta shima cike da nashi salon na soyayya yace da ita
"Sweety kiyi hakuri dan Allah ki saki ranki, wallahi ba dadewa zanyi ba, dan dai ma Kawu ne yake kira na amma wallahi da babu inda zani kema kin sani."
Ta kara mannewa a jikin shi kamar tana so ta tsaga kirjin shi ta shige. Muryarta bata fita sosai saboda shagwaba ta ce dashi.
"Ka san fa in ka tafi ba zanji dadin gidan ni kadai ba.... Wallahi dan dai kawai Kawu ne da kanshi amma da bazan barka ka tafi a lokacin da nake tsananin bukatarka a kusa dani ba wallahi..."
Ta kare maganar cikin matso hawaye. Yayi saurin sa hannayensa ya soma share mata hawayen, ya cigaba da bata baki har dai ya samu ta rabu da shi ya mike ya fice, sai da ta rako shi har bakin gate, a nan ma rike shi tayi, sai da kyar ta sake shi ya fice.
Kai tsaye gidan kawun nasa ya nufa cike da tararradin kiran da Kawun ke yi masa.
*
A babban falo ya iske kawun shi kadai, ya harde a bisan doguwar kujera, kai da ganinsa kasan babban gwaska ne mai shuni a hannu.
Ya nunawa Abdul wajen zama ya zauna, suka fuskanci juna sosai.
Shiru ne na wasu yan dakikoki ya ratsa tsakanin su kowa na taraddadin abinda zai ji daga bakin kowa....
Daga can dai Kawu ya katse shirun nasau ta hanyar yin gyaran murya, kana ya karkace babbar rigar sa ya zaro rafar kudi yan dubu dubu har guda biyar ya dire a gaban Abdul...
Gaban Abdul ya fadi rass! Cikin zazzarowar idanu ya kurawa kudin ido gabansa na cigaba da bugawa. Daga can kuma ya dago ya dubi kawu wanda fuskarsa ta yalwatu da murmushi, sai faman girgiza kai yake ya kadangare...
Ya gama nazarin Abdul din sosai ya fahimci yadda ya rude, abinda yakeso kenan.
Cikin sarkewar harshe Abdul ya shiga inda indar cewa.
"Kawu.... Me....wannan kudin.... Na mene....ne?"
Kawu ya tuntsire da dariya harda kyakyatawa, saida yayi mai isarsa sannan yayi shiru. A nutse kuma yace da Abdul "Wadannan yan kudaden ba komai bane matukar zaka yi amanna da bukata ta, to ni kuma naci maka alwashin ninninka
maka su har sai kai da kanka kace sun isa....."
Ko kadan Abdul bai taba tsammanin kudi zasu iya rudashi haka ba, sai gashi da saurin bakin cewa.
"Wacce irin bukatace wannan Kawu?"
"Me kake ci na baka na zuba? Kabi sannu zan sanar dakai kamai" Inji Kawu, sannan ya dora da cewa.
"Bukatace mai sauki kuma mai wahala, abinda yasa nace haka kuwa shine, na san a duniya a wannan zamani kudi suna tasirin siyan komai musamman ma idan aka hada da bude kwanji....
Wadannan kudin da kaga na baka su a yanzu na baka sune a matsayin toshiyar baki kafin inji amincewar ka in baka mamaki da kyautar da baka taba jin anyiwa wani ba a iya tsawon rayuwarka....
Zan baka kudade masu yawa muddin ka ce ka amince zaka saki matarka Safina......"
Wata irin zabura Abdul yayi cikin dimuwa da gigitar jin abinda kawu ya fadi, amma kafin ya tanaka kawun ya rigashi da cewa.
"Hold on abdul! Bance ka daga hankalinka ba akan wannan batu, shi yasa na cemaka bukatar tana da sauki tana da wuya, kuma a karankanka in kaso a kana iya daukarta mai sauki ko akasinta...
Na sani kwarai rabuwa da masoyi yana da wahala da ciwo a rai, amma kar ka manta nace zan baka arzikin da sai ka bada labari. Mata suna da yawa a duniya, ko ina kaje
zaka same su birjik kamar kaji, ledar fiyowata ma tafi su wahalar samu. Kana iya zuwa ka nemo ko wace irin mace ko yar waye a duniya ni kuma nayi maka alkawarin zanyima komai dan ka aure ta... Ni dai kawai buri na matarka KA SAKETA NA AURA!"
Tunda Abdul yazo duniya bai taba cin karo da bakar rana irin ta yauba, bai taba jin kalaman da suka munana ransa irin na yau ba.
Kau! Zufa ce ke keto masa ta ko ina
gashi dai falon cike yake da na'urar A.C amma bai hana shi jikewa shakaf da gumi ba...
Ya laluba ya rasa kalaman da zai mayarwa da Kawun nasa, kansa ya
dau caji, kwanyarsa tayi zafi rau! Ba dan Kawu ya kasan kani a wajen mahaifinsa ba yau da ko buzunsa bazai bari ba. Maimaita abinda ya fada kawai yake a zuciya...
Ya mike a fusace ya dubi Kawu cikin tashin hankali yace da Kawun.
"Wallahi kawu duk duniya babu wanda ya isa ya rabani da matata wallahi........."

www.shulaman.wapka.me

==>Kawu yayi zumbur ya mike ya sha gaban Abdul. Cikin zazzare ido da kausasa murya ya tari Abdul din da cewa. "kayi kuskuren yin wannan furucin yaro! Kuma ni kanin mahaifinka ni zan zama makarin furucin naka.... Bazan tausaya ma ba muddun baka tausayawa kanka ba ta hanyar sakkowa daga dokin nakin da ka hau, yaro kar ka bari buri akan mace ya kaika ga tafka babbar asara,domin kuwa biyu babu zakayi wato baka ga tsuntsu baka ga tarko! Na riga nayiwa kaina alkawarin ko ta wani hali sai na mallaki matar ka. Gwara ma ka yiwa kanka kiyamul laili ka karbi dukiya kayi arziki, sannan kuma kaje ka auri duk diyar da kake so... Na fada maka cewa mata basa wahala a wannan zamani kullum sabbi akeyi kuma masu kyau...." Gaba daya kam Abdul ya gama kullewa, hankalinsa ya kai kouwar tashi, wazu zafafan kalamai ne ke artabun fotuwa daga bakinsa, amma yaki bari harshensa su furta saboda sanin mutumin dake a gabansa. Matsayinsa ya wuce yayi masa rashin kunya, amma da yake bahaushe yayi azancin cewa tsohon da baiji kunyar hawa jaki ba, jiki bazai ji kunyar nika shi da kasa ba, sai da ya furta cewa. "Kawu bazan taba yin nadamar furuncin da nayi na cewa babu wanda ya isa ya raba ni da matata sai wanda ya bani ita... Kawu dukiyar ka bata isa ta fanshi soyayyar Safina a zuciya ta ba.... Kawu mai yasa kake son yi min karfa-karfa ne akan rabani da abinda ba karamain tashin hankali bane? Kawu kar kayi amafani da damar da Allah ya baka ta dukiya ka cutar dani a matsayina na da a wajenka?" Kawu ya tuntsire da dariyar mugunta, ya dinga kyakyatawa kamar ba zai daina ba, daga can kuma sai yayi dif ya kuma zubawa Abdul idanu. Gaba daya hankalin Abdul din a tashe yake, idanunsa sunyi jaja wur! Gumi na ci gaba da keto mishi ta ko ina. "Abdul! Tun farko kai kayi gangancin jefa kanka a inda ba ka kai matsayin da ya kamata ka jefa kan naka ba, ka je ka auri hamshakiyar mace irin wacce mu ya dace mu aureta, sam
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download KA SAKE TA NA AURA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album