Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

FUSKA BIYU Complete Hausa Novel Document by FUSKA BIYU


FUSKA BIYU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 68848



FUSKA BIYU

Reading Time: 5 Hours

Added On: 14, Jun 2024

Author: Halima K Mashi ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 340.41 kb

File Type: txt

Views: 3249+

Download: 4299+

Last download: 15 hours ago

Description/Story: [1:27PM, 13/10/2016] 🌹@lh@ji🌹 A R: FUSKA BIYU Part 1
NA
HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
Fuska Biyu 1-----1
NA leko a hankali ina sanda bana son mama ta
ganni nasan sae tace na saka hijabi, in har kin
ganni da hijabi, to ki tabbata islamiya ko sallah,
don ko an matsa min nasa dana fita waje zan
aiko dashi. Anyi fadan , anyi dukan , an gaji an
barni sai addua inji mama. Na kusa kofar fita
inajin mama tana fadin "ke! Ke!! Ke!!! Asma'u ai
tuni na falla da gudu. Gidansu aminiyata Rahma
zan je, ina sonta gashi ta juri zama da halina na
masifa da tsokana, duk da ana cewa sai hali yazo
daya ake abota, amma ni da Rahma ba haka
bane, ita tana da gudun zuciya sam batason fada
haka nan ita ma'abociyar sanya hijabi ce, duk
kawar danayi sai mun bata, amma banda Rahma.
Na kalli gidan dake kallon namu, maza ne zaune
a barandar gidan kusan su hudu. Yaya Ali ne da
abokansa a raina nace sarakan sa ido , riga da
wando ne a jikina na jeans da farar shirt ko ince
top, ta dame ni sai dan karamin gyale irin shigar
da nakeso kenan a duniyata, kuma a ganina ban
wuce wannan shigar ba, tunda yarinya ce ni 'yar
sha biyar.
zan sha kwana layin su kenan sai gata, nace
gidan ku fa zanje Rahma. kefa sai ina ? tayi
dariya , nima gidanku zanje . nace to mu koma
naku gidan wai ta ce a'a ni fa da shirin islamiya
na fito , lokaci nayi sai mu wuce. naja tsaki to zo
muje , amma Allah ban so komawa gida yanxun
ba , tace saboda me? nace kin san Allah Rahma
ban san me na ma yan gidanmu ba , duk sun
tsane ni. tace ba tsana ba ce Asma'u , don nasan
bai wuce ana miki fadan natsuwa ba. Na harare
ta bansan me nayi na rshin natsuwa ba, kina
nufin ban da natsuwa ko me? Ganin yanda na
hayyako mata yasa tace , "Allah ya baki hakuri
Asma'u , ba ina nufin ba ki da nutsuwa bane , kin
san....."na katse ta "nidai yi min shiru malama zo
muje in zaki. "muka taho sungun-sungun babu
mai magana da wani, don ta mantar min da
fushina sai tace ina Suraj? nan ko na soma
murmushi , nace daxun shine ya dauko ni daga
makaranta. hirar suraj muke har gidanmu , ta nufi
gurin su mama ni kuma na nufi dakinmu, don na
daura zani akan wandona, nasani na nufi mama a
haka laifin zai zama biyu
sai dai kash! ina isa dakin na samu su yaya yina
masu cin ubana Anty Ainau da Anty fati da Anty
salima, zan juya Anty salima tace "ke zo nan 'yar
iko zo gidan uban wa kikaje a haka? nace "ni ba
fa inda naje" na nufi sasansu mama ina yan
kunkunai ku kun cika takura gara naje gun mama
a haka bata da saurin hannu ku kam yanxun kun
duki mutum. na samu Rahma su nata gaisawa da
mama ta amshi rezar da mama ke yanke farce
tana yanke mata. na shiga na dan rabe mama
tace dago ta dube ni tace "yanxun Asma'u ba za
ki taba jin magana ba? kin fi son kina yawo haka
sai kace arniya? haka kika ga yan uwanki koko
haka ki kaga Rahma tana yi? ko Aisha da take
kanwar ki ta fiki hankali. na bata rai sannan na
ce "to ni me nayi mama? ni ba a sona a gidan
nan kowa sai yayi ta min fada" mama tace to sai
ki rama mara kunyar banza , ba'a son naki me
ake da mara ji? ki canja halinki mana ki gani in
ba'a daina miki fada ba, karamarki dake sai
shegiyar kafiyar tsiya , tace uban me aka miki
zaki tsira min kuka? bansan shigowar yaya
usman ba sai dai
sai dai rankwashi naji kus a kaina, yace shegiyar
yarinya daxun uban wa na ganki da shi a mota ya
dauko ki daga makaranta? ya kama kunne na
baza ki rabu da dan iskan suraj din nan bako sai
kin sha wahala? cikin kuka nace bafa ni bace ya
usman, ya kara kai min mari ina wasa dake ne?
ban sanki bane kenan? yasa kafa ya shure ni na
saka ihun da duk yan gidan suka taru amma abin
takaici babu wanda yace yaya usman yayi hakuri,
saidai suce ya kara min gara ma su umma da
hajiya sunce kece ai rashin jinki yayi yawa
Asma'u, ace ayi ta fama da mutum? yi hakuri
Usman, yace haba hajiya yarinyan nan ta fita
zakka a gidan nan in dai kaji an kawo kara nan
gidan to ita ce. dazun fa motor yaron nan suraj
na ganta ya dauko ta daga makaranta bayan
Alhaji ya hana ta kula shi. mama ta fito tana
fadin sai ma an hana ta, ta dubi yayunta mana
su aina'u wa taga tana kula samari cikinsu? ina
ce tun suna secondary duk wanda yazo gurinsu
cewa suke yi je gurin mahaifinsu. amma ita da
yake ta sa maza a ranta 'yar kankannuwarta yau
ta tsaya da wannan gobe da wannan kai ranar
dai naci duka tamkar.
ranar dae haka naci duka kamar jaka sannan na
nufi dakinmu na kwanta a gadon mu ina kuka.
rahmace ta ke ta bani baki har aka kira sallah
nata tashi fuskata ta kumbura don kuka , nayi
alwala nayi sallah haka ma Rahma, ta nufi dakin
mama don shirin islamiya don can ta 'aje
kayanta, nima na saka nawa duk gidanmu nice na
dinka wando a kayan islamiya(not clear but ana
fadin yanuwanta duk dogowar riga suke sawa na
islamiya ita ta dinka wando ranar dae duk wanda
xae mata fada xaece ta ringa koyo da halin
kawarta Rahma har ta ji haushin ta ) ta biyo ta
tana kira na ban tsaya ba sae tayo gudu ta same
ni , muna fita lungun layinmu ta baya muka bi
sannan muka kama hanyar islamiya, kamar daga
sama nafa motar suraj na tsaya itama rahma ta
tsaya yayi parking ya fito kyakkyyawan yaro dan
masu kudi mai takamotoci na kece raini, ya nufo
mu baby lafiya? na soma hawaye ya kama
hannuna. oh please stop crying my baby
Rahma ta dube ni cikin takaicin yanda na tsaya
ya rikr min hannu zomuje ka da muyi latti fa
asma'u . nace ki tafi sai nazo. tace yanxun nan
fa ya usman ya ce ki daina kula samar, na daka
mata tsawa ina ruwanki? ta wuce yaja hannuna
muka shifa mota ya share min hawaye da
yatsanshi, fadamin me aka miki? nace wai ya
usman ne yace na daina kula ka hrda dukana,
yace to baby ke yanxun yaya kika gani zaki iya
rabuwa dani ko ko yaya? ni dai gaskiya baby ba
xan iya rabuwa dake ba, nace ai nima suraj ba
zan barka ba bayan duk garin nanm kai ne kadai
me sona, su fa ba wani sona suke yiba, yace to
mujr in kaki makarantar, yace bari mu dauki
rahma, nace barta kawai itama yau haushinta
nakeji. ina shiga ajinmu duk sauran yan ajin suka
gyara xamansu dan bani guri. nice na zabi gurin
kuma nace nan ne gurina duk da kasancewa
kowa yana zam a ko ina, amma ana shakkar
zama wurina , saboda masifata duk da karfi ne
dani ba suna tsorona kasancewarbamu taba
danbe ba shiyasa suke min kallon karfi.
na zauna ina tunanin yanda ba'a sona har zuwa
san da rahma tazo. malam ya shigo yana rubutu.
ba yabon kai ba, saidai ai min shaidar rashin ji,
amma in dai karatu ne daga boko har islamiya
nayi zakara. yanda malamai suka sanni da rigima
haka suka sanni da kokarin karatu, wannan shi ne
yas nake da farin jini cikin dalibai , suke kuma
shakkata. hour kofar gidanmu motar ta tsaya, na
fito tare da godiya tacemin zai zo anjima nace to
sai dai yatsaya daga farkon layin a wurin wani
gidan dake duban gidanmu ya Ali ne shi da wani
wanda ban tantance shi ba , sai dai ina ganin kila
shima dan gidan ne, yana ta min kallo mai kama
da harara na wuce ina ce ma wanda ya rago min
hanya sa anjima . yaya umar ya dubi kaninshi
Aliyu yace, Ali wannan yarinyar yau ganina da ita
na uku kenan, tana shiga gidan baba Alhaji itama
'yars ce? aliyu yace Asma'u? 'yarsa ce mana
itace mara jin gidan, yace na kula daga zuwana
shekaran jiya zuwa yau na lura bata da kamun
kai, su Abubakar suka barta ta baci haka? Aliyu
yace ai ya uwar yarinyar nan 'yar daru ce da
taurin kan tsya.
[1:28PM, 13/10/2016] 🌹@lh@ji🌹 A R: Fuska Biyu1-----2
suna iya bakin kokarinsu. ya umar yace 'yar
wacece a cikin matan gidan? Aliyu yace, 'yar
mama ce ka ko san albasa batayi halin ruwa ba.
ya umar yace 'yar mama? Ali yace kana mamaki
ko? wallahi 'yarta ce daga ita sai aisha auta, ya
umar yace lallai kam albasa bata yo halin ruwa
ba, mama da dukkan yayanta salihai ne kai kaf
gidan ma babu mai wata matsala shiyasa naje
mamaki kaya matsattsu jibi atamfar dake jikinta
yanxun tamkar tayi nishi su yage haka suke a
jikinta. Aliyu yace kaga kadan ma ba dan tana
shan wahala ba ma kila da tsirara xata dinga
yawo kuma ga smari kamar hauka yau
wancangobe wancan, 'yar karamar yarinya
jamilar gidan nan fa ta girme ta . ya uwar yace
kai haba? Ali yace wallahi bata wuce 14 ba, ya
umar ya mike ya nufi cikin gida yana fadin shi fa
ganinshi an barta ne
ina zaune bakin gado inayin note shema'u ta
shigo "Asma'u ki zo in
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download FUSKA BIYU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album