Join Our WhatsApp Group

ANJANE Complete Hausa Novel Document by ANJANE


ANJANE

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 25842



ANJANE

Reading Time: 2 Hours

Added On: 26, Oct 2023

Author: Ouummey ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 09013101854

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 132.13 kb

File Type: txt

Views: 656+

Download: 296+

Last download: 3 days ago

Description/Story: [12/13, 10:35 PM] Maman kalisat Novel: Ouummey 01 [ 12/1/2022 1:10 PM ]

★★★ *ANJANE* ★★★
(Rashin sani)
★★★★★★★★★


_*PAID BOOK*_


Story/written by Ouummey.

Wattpad @ouummey.



From The author of:

*HAƘORIN DARIYA*
*ƘASAR MU A YAU*
*BA NI DA LAIFI*
*SARAKI (the accused prince)*
*ABOTA CE KO SOYAYYA*
*And now.......ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*





                     *FREE PAGE 001*



Ina the name of Allah the most beneficient, the most glorious and the most merciful.

Dubun salati ga fiyayyen halitta Manzon tsira Annabin mu Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam.

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki mai kowa me komai da ya Wada ta ni da rai da lafiyar da na sake dawowa gare ku cikin wani salon rubutu na daban, Allah yadda ka bani ikon fara rubutun nan lafiya kasa in gama lafiya, Allah ka bani ikon rubuta abinda ze amfane ni ya amfani al'umma gaba ɗaya, ya Rabb ka hane ni rubuta abinda ze cutar dani ya cutar da ƴan uwa musulmai.

At long last nake cewa hellooooooo to You my fans💃💃💃💃💃.

Gani dai na sake dawowa, Ouummey ce dai taku tafe cikin wani sabuwar tafiyar da nake fatan ku so kuma ku ƙauna ce shi fiyeda littattafai na na baya, soyayyar da kuka nuna min a littafin *SARAKI da ABOTA CE KO SOYAYYA* is really amazing and unpredictable, am using this opportunity to say thank you once again, Ouummey loves you so dearly 💖.

Sedai fa ba kamar baya ba this novel isn't FREE kamar na baya, it's a *PAID BOOK at ₦300 ONLY!!!.*

Na sani you guys won't make me feel unloved or ashamed, nasan zaku nuna min ƙaunar da kuke min ta hanyar siyan littafina dan rubutu na ba abin yar wa bane, isn't so??!.

Kar dai na cika ku da surutu, ga duk me buƙata zai/zata biya kuɗin ta ta wannan account ɗin, RABIATU ABDULLAHI
2391368231 ZENITH BANK tare da turo shaidar biya ta 09013101854
Ko a turo katin MTN ta wannan number
09013101854.

Son so fisabilillah 💋💋.


WANNAN LITTAFIN SADAUKAR WA NE GARE KU MY FAMILY, HEART U ALL AND ALLAH YA QARA MANA ZUMUNCI DA QAUNAR JUNA, AMEEN💞💝💖💗.















________________________📖 Gudu take cikin fitar hayyaci cikin dokar dajin dake da shegen duhu duk kuwa da cewa ba wai dare ne ba dan lokacin bai wuce ƙarfe huɗu da rabi zuwa biyar ba, takun mutanen da take jiyo wa a bayan ta yasa ta tabbatar basu daina bin ta ba haka suna daf da ita, wani irin kuka ne ya kubce mata ta shiga yin shi tana sakin numfarfashi, bata san me yasa azzalumai suka yi yawa ba a duniya, bata san me ita ko ƴaƴan ta suka tare wa maƙiyan ta ba da suke san se sun shafe labarin su ta kowace hanya, a rayuwar ta bata da abokin gaba tun daga yarinta har zuwa girman ta, kai har zuwa yanzu da take wannan gudun na ceton ranta da na ƴaƴan ta bata san dalilin neman kashe su ba.

Kukan da yarinyar bayan ta fara ne yasa na gane jaririya ce sedai ba wai ɗanyar haihuwa ba dan zata kai watanni, bata rufe bakin ta ba wani kukan ya shiga tashi, se a lokacin na lura goyon gaba da baya ne matar tayi kuma da alama ƴan biyu ne dan itama ta gaban macece, wannan kukan shi ya kuma ruɗar da uwar ta saki nata kukan me sauti tana cigaba da gudun da take yi.

"Yauwa gata can, ku ƙara gudu mu cin mata tun kafin ta kai ga ficewa dajin nan dan na gaban sa ya fishi duhu ba lallai mu iya ganin ta ba".

Cikin azama ta ƙara gudun ta dan jin abinda wani da take zaton shine babban su yace, burin ta a lokacin be wuce ta fita daga nan ta faɗa dajin gaban ba dan tsira da numfashin su sedai bata kai ga hakan ba taji saukar katako ta bayan ƙeyar ta, su ne suka jefo mata ko kuwa daga ina yake ba ta sani ba.

Faɗuwa tayi sedai da sauri tasa hannu ta dafe ƙasa dan gudun kar ƴar ta taji ciwo, jin takun su daf da ita yasa ta hanzar ta miƙewa duk kuwa da yadda taji jini na bin wuyan ta ban da kuma jirin da take gani, neman wajen fakewa take yi sedai kamar babu wani loko a dajin, a lokacin ba ta rayuwar ta take yi ba ta rayuwar ƴaƴan ta ne, ta sani ba lallai su tsira daga hannun wadan nan azzaluman ba sedai tana fata ƴaƴan ta su tsira ko da kuwa ita zata hallaka, yara ne da basu san komai ba basu kuma fara komai a rayuwar su ba dan yanzu ne suke watanni na uku da haihuwa, ba zata so rayuwar su ta tsaya iya nan ba haka kuma ba zata so maƙiya suyi galaba akan ta ba, ta sani saboda yaran ake neman kashe ta saboda kada uban su ya sami wani haske ko ƙanƙani a rayuwar sa.

Bata san me yasa marasa imani suka cika faɗin duniya ba sedai tana tausayin mijin ta kuma uban ƴaƴan ta, yaran ne dukkan wani farin ciki, jin daɗi da walwalar sa shiyasa mahassada ke neman ganin sun raba shi dasu har itama ta samu nata rabon ƙaddarar, rayuwar su cike take da baƙin duhun da bata taɓa tunani ba se a yau da take wani siraɗi na mutuwa ko rayuwa, se a yanzu ne abubuwa da dama suka dinga dawowa kanta da yaci ace ta ankare da su tuntuni sedai tsabar pious heart ɗin ta yasa bata taɓa zargi ko kawo wani mummunan lissafi ba, se a yanzu ta tabbatar da tabbas tayi kuskure, kuskure kuma mafi girma na ɗaukar cewa kowane ɗan Adam kyakkyawar zuciya gare shi.

Wani ɗan haske da take hangowa yasa ta nufi wajen cikin matsanancin gudu cikin fatan Allah ya kawo mata matserata ko da ta rayuwar ƴaƴan ta ne kaɗai, ta yarda ita ta mutu in har zasu rayu, tana fatan suyi kyakkyawar rayuwa ba dan saboda komai ba se dan kwaɗayin samun addu'ar su, Manzon Allah yace addu'ar ƴaƴa salihai ga iyayen su karɓaɓɓiya ce haka kuma sune kawai arziƙin da mutum ze mutu ya bari a duniya ya tadda shi a ƙiyama bayan sadaƙatul jariya wanda tasan bata da rabo a wannan ɓangaren dan ko tunanin hakan bata taɓa yi ba.

**********

Kamar ko wane hutun makaranta in an yi, yau ma tafe take da ƙafa kamar yadda ya zame mata jiki ba kamar ragowar ƴaƴa masu gata ba da za'a je ɗaukar su a mota, mashin ko keken amalanke ko kuwa motar ƙurƙura, ita da ƙafa take takawa har zuwa ƙauyen su wanda tsakanin shi da makarantar tafiyar awa huɗu da mintuna ne a ƙafa, bata taɓa jin ba zata iya ba dan tana matuƙar son karatun kuma ta san in ma ba tayi ba kanta kaɗai ta cuta dan shine kaɗai gatan da take tunanin zata iya samu da ze zama sanadin canjuwar rayuwar ta da ma duniyar ta gaba ki ɗaya.

A hankali ta shiga takawa lokacin dan ta gaji, tsakanin ta da ƙauyen su be wuce tafiyar mintuna Talatin ba dan ta kawo kusa sosai sedai a yadda ta gaji se take ganin in tayi yanke ta cikin daji zata fi saurin zuwa gida maimakon ta bi ta hanya sosai, ba ɓata lokaci ta danna kai cikin dajin cikin dajin ba tare da tsoro ba dan shiga daji a jinin su yake dan sun saba, in basu shiga yin itace ba sa shiga tsinkar magunguna ko kuma kayan marmari ko kuma yawon su.

Ƙarar gudun da taji yasa ta ɗan dakata tana tunanin anya lafiya, jin kamar gudun ba na mutum ɗaya ba yasa ta ɗare wata doguwar bishiya da sauri ta yadda zata samu damar ganin abinda ke faruwa, mace take hangowa da goyo har biyu wato gaba da baya tana gudu yayinda wasu mutane masu riƙe da makamai suke binta, hankalin ta taji ya tashi duk da bata san me tayi musu suke bin ta ba sedai a ƙananan shekarun ta tasan ba abu me kyau yasa suke bin ta ba tun da har ga makamai banda haka kuma mutane da yawa na shiga wannan dajin dan aiwatar da munanan ayyukan su saboda duhuwar dajin na basu kariya daga idanun jama'a, bata san me yasa ba sedai kawai taji a ranta ya zama dole ta taimaki wannan matar, ba zata bar wannan azzaluman su yi galaba a kanta ba.

Da sauri ta ɗirko daga bishiyar tareda nufar wajen matar da saurin ta dan gasu da suka saba da dajin bawa wani ganin duhuwar sa, da sauri ta fizgi hannun matar daidai lokacin da wani yayi nasarar sakar mata harbi a ƙafa ganin yadda take wahalar dasu, wani kogo ne na bishiya ta shigar da matar haka kuma da sauri tasa hannu ta since goyon bayan ta ganin wuyar yarinyar na reto alamun ta suma ko ta mutu, a galabaice matar ta kwanto ta gaban ma ita kuma tayi saurin tare ta.

Numfarfashi kawai matar ke yi dan ta galabaita to the extent da bata iya ko da buɗe idanun ta sosai balle tayi magana, hannun yarinyar da bata san wacece ba ta ruƙo da sauri tana fizgar numfashi kamar me asthma, da ƙyar ta buɗe baki da idanun ta tayi magana mara tsayi

"A...am..maa..naa, su..su..tsira..dan.. Allah".

Wani irin duka ƙirjin yarinyar ya shiga yi jin abinda matar ke faɗa, da sauri ta shiga jijjiga ta,

"Ki tashi Aunty mu gudu, kar ki rufe idanun ki ni ban san inda zan kai yaran nan ba wallahi".

Bata iya tace mata komai ba se yatsun ta duka goma ta ɗaga mata kafin ta shiga nata nuni da zobunan dake jiki wanda guda biyar ne, uku a hannun dama biyu a hannun hagu, da sauri ta sa hannu ta cire mata dan a tunanin ta sun dame ta ne, wuyan ta ta sake nuna mata nan ma ta cire mata sarƙar jikin ta da ɗan kunne, ajiyar numfashi matar ta saki tana buɗe ido sosai cikin ƙure ƴaƴan ta da kallo kafin wannan karan cikin cikakkiyar magana tayi magana

"Ki kula min dasu dan Allah, ban bar komai ba a wannan duniyar se su, sune fitilar zuciyar mahaifin su, kije dasu na baki halak malak amma dan Allah su tashi cikin kyakkyawar tarbiyya kamar kowane cikakken bahaushe musulmi, kije dasu ki kula dasu da wannan kayan sarƙar na hannun ki dan Allah kar su cimma na su kashe mu gaba ɗaya, kar ki tsaya wata magana dan ni tawa ta ƙare ko basu kashe ni ba mutuwa zan yi dan bana jin akwai ragowar jini a jikina, fatana ƴaƴana su tsira kuma alhamdulillah Allah ya turo min ke dan cetar su, ki tafi, ki tafi gasu nan, dan Allah ki tafi".

Jin takun nasu da gaske kusa daf da bishiyar yasa yarinyar damƙe set ɗin sarƙar hannun ta ta zuba cikin jakar makarantar ta ta buhu dake hannun ta tare da saɓa yarinya ɗaya a ƙafaɗar ta ta goye ɗaukar tare da ɗaukar jakar buhun ta shige cikin dogayen ciyayin wajen cikin rarrafe dan kar su gan ta, seda ta ɗan yi nisa sannan ta tsaya jikin wata bishiya tana kallon yadda suka cimma matar a inda ta bar ta, haske haske sauka dinga yi da wayoyin hannun su cikin neman inda ta ɓoye yaran sedai basu ga komai ba, tsawon lokaci kafin suka koma wajen da suka bar uwar da mutum ɗaya na gadin ta,

"Yanzu ya zamu yi, me zamu cewa matar nan game da ɓatan yaran?".

Ɗaya daga cikin su ya faɗa kafin ɗaya ya kai ƙafar sa yana shurin matar da ke jingine har lokacin yana tambayar ta inda ta kai yaran sedai tuni ta faɗi rigija alamar rai yayi halin sa, tsabar jinin dake kwance a inda ta jingina zaka yi zaton wata ƙaramar dabba aka yanka, wani mugun tsaki mutumin ya saki kafin ya umarci ragowar su ɗau gawar tata sukai mota shi kuma ya cigaba da bincika wajen sedai dake ba sanin kan dajin yayi ba ko kaɗan be ko kai wajen da yarinyar take ba rungume da baby ɗaya a ƙirjin ta idanun ta na zubar da hawayen tausayin matar da kuma ƴaƴan dake hannun ta da yanzu suka zama marayu, bata san wane irin marasa imanin mutane ne yanzu ke rayuwa a wannan duniyar ba, ko ina cike da azzalumai, kowa ba ya tausayin kowa, kowa ba ya san kowa, kowa kan sa kawai ya sani, ya ilahi duniya ina zaki damu.

Ganin kuka me sauti na neman kufce mata yasa ta miƙe wa ta shiga tafiya a hankali cikin takatsantsan dan ba zata so abinda ze jawo hankalin mutanen cen ba balle har su kashe Innocent babies ɗin hannun ta, tafiya me ɗan nisa tayi kafin ta fita daga dajin ta yanka ta cikin gonaki ta shiga ƙauyen su, garin yayi luf luf babu rana se iska me daɗi kasancewar magrib ta doso kai dan yanayin na nuna alamun be fi karfe biyar da rabi zuwa shida na yamma ba.

Ba tare da  tunanin komai ba ta nufi gidan su da yake babban gida kuma ginin ƙasa ba, sallama ta shiga kwaɗa wa a ƙofar babban zauren su sedai ba wanda ya amsa mata kamar ko da yaushe, sa kai tayi ta nufi sashen da take rayuwa yayinda tsirarun mata da yaran dake babban tsakar gidan bin ta da kallo suna maganganu ƙasa ƙasa ganin ta goyon jaririya ga kuma wata a hannun ta.

Wata sallamar ta kuma yi a ƙofar sashen su sedai nan ɗin ma ba'a amsa mata ba se dogon tsakin da aka ja, kai a ƙasa ta shiga ƙofar tana tafiya a hankali kamar wata ɓarauniya ko wadda ƙwai ya fashewa a ciki, inna mariya dake tsugunne bakin malalallabta tana rege shinkafa ta tsugunna har ƙasa tana gaisar wa sedai maimakon amsa se zagi da yarfe ne ya biyo baya kamar yadda ta saba

"An dawo daga yawon ta zubar ɗin da sunan Makarantar boko, atoh mun dai sani ba wata wata boko se tambaɗewa da karuwa ci da ake yi ake fake wa da boko, wa ya sani ma ko an yi guzurin ɗan boko a ciki".

Bata wani damu da abinda Inna mariyar ta faɗa ba dan ba yau ta saba ba, ba ita ba kusan duk ƴan gidan ma haka...


Read / Download ANJANE

START READING

OR

DOWNLOAD TXT NOW
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album