Join Our WhatsApp Group

YAR HANNU Complete Hausa Novel Document by YAR HANNU


YAR HANNU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 44445YAR HANNU

Reading Time: 3 Hours

Added On: 15, May 2024

Author: Shamsiya Adam ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08160375544, 07043185799

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 264.77 kb

File Type: txt

Views: 176+

Download: 249+

Last download: 5 hours ago

Description/Story: 'YAR HANNU
Aiki dana zari domin farincikin makaranta (readers) story and written by shamsiyya Adam MATAR YAYA

Shekarar :2021

BISMILLAHI YA ALLAH

Mallakin SHAMSIYYA ADAM
Dasunan Allah........

Gudu take iya kar karfinta tana nishi harta karasa ga dan madaidacin gidan danaga tanufa jikin wata tsohuwa tafada tana sakin wani marayan kuka xuciyar ta nawani tukuki da wani lallausan muryanta mai cike da rauni naji tafara magana duk da har yanxu tsohuwar nan bata ce mata kala ba binta kawai take da ido tana shafa kanta dahannunta daya alamun rarrashi
Dada banga mami ba har yanxu naduba kaf gidan babu ita kuma tunsafe tataho nan gidan nakira bahba yace bataxo ba dan Allah dada kitaimaka min dama tunjiya mamina batada lfya shiyasa naso narakota amma taki tace naxauna nayi abincin gida,
Wacce ake kira da dada naga tafara sharar kwalla tana yunkurin tashi saita yanke jiki tafadi kwallah kara budurwar tayi tana rumgumar ta
Wayyo Allah dada kitashi karki mutu kitashi muje munemo mami kune kadai gatanmu dada pls pls dada open yur eys pls dada
Amma shuru kofar gidan tafita tamkar wata mahaukaciya dan kwalinta ahannu hawaye kuwa tamkar anbude famfo batasanma takamai mai ina xata dosaba hango baba datayi yasa ta ruga garesa tana ehu ruko hannunta yayi suka shigo gidan sbda takasa gayamasa abin datake faruwa sbda tsagwaron kuka
Da sauri baba yakarasa yana yayyafawa dada ruwa aikuwa dakuka ta farfado tana dafe gefen xuciyar ta
Malam har yanxu ba aga Jamilar ba
Dada tajefawa bahba tambaya kasa yayi dakansa yana gyara xamansa
Yaxa ayi abin sai addu ah kulu wlh tunda fujjilat takirani tafadamun nabaxama nemanta cikin gari kinganni nine har gangare akafa naje gidan maigari naba da cigiyanta in ansamota yanxuma dawowar danayi naji yaya ake ciki anganta kokwa nakai gidan redio nibabban tashin hankali na da batajin dadin jikinta da mutum ma klau yake toh dasauki fargabar Allah dai yabayyana mana ita
Amin suka amsa kowacce na sharar kwallah
Ke yanxu fujjilat ki koma gidan naku kisanarwa alhajin don balailai yasaniba kikafara yonan
Tarausayar dakai tana share kwalla
Tohm bahba amma kome ne ne yasami mami wlh dakamason Abba aciki sbda inajinta jiya dasafe tanafadamasa bata jin dadi tanakuma jin ciwon mara sosai yabata kudi taje asibiti suduba ko cikin badai dai yake ba amma Abba yayimata banza yace taxauna in haihuwa ce agidama ai xata iya haihuwa haka ta hakura kuma ranar kwanatayi juyi tana hawaye naje nafadawa abban yakoroni saiyau dasafe tace min xataxo gida kugaisa tunda tasamu sauki dakyar nabarta tataho ita daya amma duk dahaka jikina bai yadda da lfyn nataba haba dan Allah baba yanxu mu haka rayuwa xaicigaba datafi acikin macutanmu shikenan bari naje
Dada tace
Fujjilat wannan kaddarar muce muduka bakeda mamanki kawai ba karfa kimanta taku kika sani bakisan tamuba kowacece rayuwa dakike gani sai anyi hakuri da hakuri ne kadai ake cin nasarar rayuwa xa aga mamanki insha Allahu
Tohm dada
SOME WEEKS LETAR
Yau kusan wata guda kenan ba aga mami ba ankai cigiyanta gurare dadama amma jikake shuru yanxu addu ah muka dage da ita kawai game da Abba kuwa kamar baida muba da batan nata dik da ba abin mamaki bane hakan sbda kosanda take gidan ba agabansa takeba da ita ko ba ita duk daya ne awurin sa haka abokiyar xaman mami itama ko Allah yakyauta baitaba hadamu da itaba tunda mami tabata saima wani sabon farinciki da jindadi data bude acikin gidan maganar aikin gida kuwa tuni yadawo wuyana nikadai domin kuwa kubrah sa ar haihuwa na tasaki yin komi dai dai dashara wannan kubrah baxatayi ba saidai taci takoshi tatafi school ko ta kwanta inyakasance ranar batada lacter nikuwa ummansu tuni tasa Abba yatsaidani daga xuwa makaranta sbda bakin sharrin datayimun nacewa inabin maxa atakaice rayuwa ta nacikin wani hali kowanne kuma dan adam nason farinciki arayuwarsa amma ni narasa ga rashin mami na wanda nadora xargina akan umma
Wannan
KUCI GABA DA KASANCEWA TARE DANI SHAMSIYYA ADAM Matar yaya IN SHA ALLAHU XAKU KARU XAKU FAHIMTU XAKU GAMSU XAKU JIDADIN WANNAN LABARI NAWA
MAI SUNA 'YAR HANNU
Kiran da umma ke kwala min ne yafuto dani daga dakin mami na wanda nake kwana aciki nikadai
Natsaya gabanta ina cewa umma gani
Kinga yau Muneeb xaidawo kishiga kitchin tunyanxu kifaramasa abinci dasauran 'yan kayan tande tande wadanda xa atareshi dasu, karfe biyar na yamma xai sauka kuma sannan kuma kidai shiga kitchin din xaki samu kubrah ababban falo saitamiki bayanin sauran abubuwan dayakamata ayimasa dafarko dai kifara xuwa kishare masa dakin nasa
Tohm umma angama
Tajuya kenan umma tasake kiranta tadawo tana kuma tsayawa inda tabari daxu
Sannan fujjilat kikula da dokokin danakafa miki agidan nan tunjiya wadanda nasanar miki idan Muneeb yadawo dafatan kinji dakyau kuma xaki kiyaye duk danasan ki dajin magana
Tana dan murmushi takalli umman tanacewa
Karki damu ummanmu insha Allahu mutkar kinga nafuto dagadaki wlh kekikayi kirana nai miki alkawarin xankiyayewa haduwar mu tunda baki aminta dahakan ba
Shikenan xanji dadin hakan indagaske kike yadameni dawani tambayar yaya kike yaya kike yanxu kungirma banaso yaxo kuma yasauya sheka yabar kubrah bayan tagama gina rayuwarta akan sonshi maxa basu da tabbs
Hakne umma sai anjima na tafi abuna babban falo ina tunanin wannan hali na umma ita kanta kawai tasani kanta kawai takeso yaji dadi batadamu da rayuwar kowaba da yayi farinciki mutkar ita tana ciki da 'ya'yanta tadauki rayuwa wata tsiya tadauki hassada da mugunta da xalinchi aikin yinta cutar dani take amma cikin rayuwan sanyi ba tsawa ba kuma wanda xaigane saitaso sbda batarageni da abinci ba kosa tufafi maitsada aa saidai tagama batani a idan mahaifina duk dadama bansan soyayyar saba nidashi tun ina yarinya kyarace da hantara tsakanin mu dagani har mamina jin nataka wani abune yasa na juyo ina dago kaina da idanuna wadanda ke cike da hawaye nakallesa, gamamakina haisam ne dan wajen yayar umma dayake bamu da nisa dasu kusan kullum saiyaxo gidan mu yay tajana dahira tun bana kulasa harsai dana saki jiki dashi muka saba sosai dayake shi din irin mutanen nan ne masu fara ah basa gajiya da barkwanci kuma baya kunchi koda yaushe xakasameshi cikin walwalar fuska sannan ga nutsuwa idan yasani agaba muna hira saikunga yadda nake shan dariya har darike ciki watarana in labari yakai labari abudayane yashiga tsakanin mu yasa kuma nadaina kulashi da watarana yaxo min dabatun soyayya tun daga lokacin nafita aharkar sa najanye jikina daga gunsa nafara kuma wasan buya washi sbda nasan baxaitaba yuwuwa ba aure na da Haisam sbda umma bazata taba bari ba ko magana abindayasa takyale ni mukeyi shine Haisam dan hayaniya ne yanxu yabirkice mata kuma baida kunya wajen fadar kowanne magana shiyasa bata taba tanka min ba dontaganmu atare
Dasauri na wuce ina sharar kwallar kan karamar kujera nasamu naxauna ina hadakaina da gwiwa nafara risgar kuka tamkar an aikomin da mutuwar mami bansan dalilin kukan nawa ba amma nasan bairasa nasaba da tuna mami na danayi dakuma tausayin irin rayuwar danakeyi agidanmu ni da abba na amma ba abindayake hadamu bayan gaisuwa itama dakyar tamkar bayaso ko yakashe ya huta haka nake gani afuskar sa narasa matsalata da Abba na
Fujjilat
Haisam wanda yadawo daga baya kenan yatsaya asaman kanta yakira sunanta
Ban amsa ba bankuma dagoba nafara kokarin mikewa domin barin falon gabaki daya ina jan majina alamun naci kukan nakoshi
Dan Allah fujjilat ki saurareni wai miyasa kike takura rayuwarki dakuka ne ke koyaushe at enytime kuka kike dan Allah kisawa xuciyarki salama ko kifadamun menene yake damunki wlh nai miki alkawarin kawo karshen damuwar ki mutkar xan iya
Bata tsayaba sai afarfajiyar gidan shima yaja yatsaya
Bakomai wlh Haisam kawai natuna da mami nane ganin yadda kowa ya manta da labarin ta tamkar wacce ta mutu haba wai memukayine aka tsanemu har haka duniya tai hannun baya damu Haisam?
Aa karkice haka fujjilat saikiyi Sabo wannan kaddara ce kuma kowa da irin tasa kuma waye yace miki kowa ya manta da mami toh bari kiji shi mutumin kirki aiba amantawa dashi amutum ci irin na mami wlh ba a isa amanta taba sbd tanada kirki da girmama dan adam batada wulakanta mutum tun ina yaro mami take bani alawa tai min wanka idan naxo mami takyautata min sosai har nagirma mami indai naxo gidan nan xatai tadawainiya dani harna tafi donhaka nima insha Allahu nixanxama silar gani mami ako inane take aduniya karki damu akullum inaba da bincike gurare daban daban xa aganta albarkar annabi s a w.
S a w, amin nagode Haisam Allah yasaka da alkhairi irin kulawar dakake bani Allah ne kadai xai iya biyanka
Kinga godiyar me kike min shiiiiiiiiiiiiii
Yadora hannu abakinsa yana kallonta
Dan murmushi ne yasubuce mata tana kasa dakanta
Haisam nabirgeta sosai ga kyau da siffa ta cikakken namiji bugu dakari yanada ilimi

Toh kokefa kinga kwa yadda murmushi ke muki kyau kuwa? Yadace dakyakkyawar fuskarki kuma dakin sani dabaki bari yana yankewa daga fuskarki ba
Tayi dariya
Dadina dakai kenan abukadan raxanaka yake shin kai baka kula dakanka ne toh dakasan yadda kake dabaka dangantani da kyau nakomai ba, domin kuwa mata akasani dakyau axahirin xance na kuma idan akaxo gurinka har matan sai sun sara ma donhaka kaje kaduba mudubi kayi murmushi kaga me xakagani pls
Ta kai maganar harda hade hannu gu daya
Yayi dariya
Humm kinji ki fa kina wani tsarani tamkar kema kina gani natabbata da ina da duk abun dakika fada da tuni nayi nasarar chafke xuciyar ki tashin farko nafuri cina akanki sbda karfa kimanta fujjilat su fa irin masu suffar dakike fada hakanan ma sace xuciyar mata suke basai sun sha wahalar fadamusu suna sonsu ba amma dayake nidin bayan muni ni ragon maxane ai nakasa katamis gareki kuma mutkar narasa soyayyar ki natabbata duniya xatamin dariya.
Hum tace kawai tana cemasa
Sai anjima Haisam inada aiki acikin gida
Yakalleta idanunsa tamkar yasaki kuka cike da rauni
Nasan abinda xai futo daga bakinki kenan fujjilat sbda kullum amsata hakane baki mataba budabaki kinfadamun kinji ba kodasau dayane miyasa sbda me?
Sbda ni bakamar kowacce 'ya bace
Tafada tana dawowa gabansa tamkar tamaresa ranta amugun bace
Kana dagata kasamu soyayyar dukkan mahaifanka kana da iliminka da arxikin ka bakimar kabace neman mara gata irina amatsayin matar aure, karka manta wannan fa ita wacce ubanta ke daukar ta 'YAR HANNU sbda a i dansa ni lalatacciya ce. Dan Allah kajanye batun soyayya atsakanin mu sbda baxamutaba xama dai dai dajuna ba Haisam babu batun aure arayuwata wlh baxance banasonka sbda kai mutum ne ko acikin mutanen irin ku daban ne,
Taruga da gudu cikin gidan tana kuka kai tsaye dakin mamin tafada tana kuka mai ciwo sai wajen karfe shida darabi tafarka daga nannauyan baccin dayadauke ta bayan tagama shan kukanta ga xaxxabin daya rufeta hakan yasa takuma cikwikwiyewa acikin blnkt tana rawar sanyi jikinta yadau xafi sosai
Kubrah ce tadauko Muneeb a eapot sai wani uban rawar kai take sai surutu take masa taki shuru shikuwa bakidaya tadameshi daxa tai shuru ma dabakaramin taimakon sa tayi ba, can ya numfasa yace ya 'yar uwarki kuwa fujjilat
Tsit tayi tana jefomasa harara aikwa karaf yaganta
Dasauri tadauke idaninta ganin yadda yatamke fuska yana tsareta da ido
Ba tambayarki nakeyiba kinmin shuru ko ta mutu ne?
Aranta tace
Toh ai daduk ba hakan ba da ta mutun
Axahiri kuwa cewa tai
Umm umm tana nan lfy
Ok
Daganan kowa yayi shuru bawanda yasake cewa wani komai har suka karasa gidan
Mahmud da usman suka rumgume sa suna murna tare da oyoyo kubrah saifaman xabga murmushi datakeyi haka umma sai barka akemasa datambayarsa yakaratu bakaramin mamaki yayi ba sbda umma da batayinsa ko kallo bai isheta ba balle har taxauna dashi tana masa sannu da hanya shidai yanaganin ikon Allah gasabon wani fi ili yadda kubrah ke shishshigemasa kamar tasauyamasa halitta,
Can umma takalli kubrah
Aa yanaga kan table din bakomi sai jog ina girkinan danasa ayimasa kubrah?
Cike da iyayi da salo tafara magana kubrahn
Wlh Umma kinga dai kosuna kitchin batadauko takawo nandin ba bari naduba
Tamike tana wani taku Ahankali tamkar maijin tausayin kasa tafuce
Tabe baki shiko Muneeb yayi yana mikewa yabude firij din dake falon yadauko robar faro da glass cop yakoma yaxauna tare dafara shan ruwan sa
Dasauri kubrah tadawo tanarike baki wanda lebe ya mamaye
Umma Umma ai batayi komai ba
Kamar yayi batayi komaiba kina nufin bata girka masa komai ba balle taikokarin yin nagidan duka?
Umma ta tambaya ranta abace
Wlh Umma kitchin din ba alamun ma anyi aiki aciki
Ok kirawo min ita
Takalli Muneeb
Kaji fa wulakancin yannan ko tun karfe biyu nafadamata duk abin daya kamata ace antanada maka amma batayi komai ba bari tasameni kwa don ubanta
Aa dakin kyaleta umma ni naci abin ci ajirgi kafin musauka banajin yunwa don yanxu ni da cin abinci ma sainan da wajen 8,insha Allah
Yamike tare da daukar wayansa yafuce inda dakinsa yake cikin falon
Kubrah ce tadawo fujjilat abayanta sai rawar sanyi take tana kyarma sabda yadda takejin xaxxabin nashishshiga dukkan sassan jikinta datsokar jikinta don haka tsaiwarma gagarar ta take gaban umma taxube tana kyarma da rawar sanyi
Kafin takarasa xama kwa umma tafalleta da mari mai gigitarwa da rudarwa domin ta karya mata shiri akaron farko,
Kuma boka yatabbatar mata dacewa mutkar har yafara cin wani abu ba tare dawannan maganin dayabata ba tohm lallai fa baxai ce yanason kubrah ba
Dan Allah umma kiyi hakuri bada gayya nakiyiba wlh bani da lfy xaxxabi kedamuna ku..
Ke dalla rufe min baki wlh yau mairabani dake sai Allah kuma xakisan nikikayiwa haka ke baki isa ki layance min ba nasan abundake damunki bakinciki ne kawai da hassada sbd kinga yadda alkhairi yatunkaro mu toh ta Allah bataki ba wlh koke mayya ce haka xaki hakuri ayi abun
Tana sharar kwalla tace
Dan Allah umma kiyi hakuri
Nace karfa kisake bani hakuri agurin nan fujjilat inba haka ba wlh sainayi miki mugun dukan dakafar ki baxaki iya motsa taba wlh tashi fuce min dagani kije kitchin kinema mana abincin dare
Tohm umma
Ta tashi dasauri jikin ta narawa idaninta naruf rufewa tamkar wacce tasha wani abu bakidaya kafarta takasa daukarta ganin kowa take uku uku kanta nasarawa kamar yafashe tafara takawa baifi taku daya biyu taiba kafarta tai rauni tagaxa daukar nauyin jikinta bakidaya tayobaya luuuuuuuuuuuuuuuuuu
Caraf Muneeb dake tsaye tundaxu yanajin dik abun dake faruwa yatareta baitsaya jin wani abuba yasabe akafadar sa sai waje da motoci apaking space amma ba wacce yake da keyn ta ganin shugowar mota gidan yasa yaruga yana masa nuni da fujjilat Haisam dake kokarin shigowa dasauri yabude motar yashigo gidan
Aaa Muneeb lfy kuwa yaushe kadawo menene...


Read / Download YAR HANNU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album