Join Our WhatsApp Group

RIJIYA GABA DUBU 5 Complete Hausa Novel Document by RIJIYA GABA DUBU 5


RIJIYA GABA DUBU 5

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 11104



RIJIYA GABA DUBU 5

Reading Time: 0 Hours

Added On: 07, Dec 2023

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 58.09 kb

File Type: txt

Views: 1026+

Download: 444+

Last download: 3 days ago

Description/Story: RIJIYA GABA DUBU
Littafi Na Biyar (5)
Part A

Na Abdulaziz Sani M Gini
AA Misau ke Magana

Ina Yima Daukacin Mutanan wannan gida barka da wannan lokaci Dafatan Muna lafiya
Mun kammala littafi na hudu a baya yanzu zamu cigaba Insha Allah

Labari Ya isowa Shagala Cewa🥰
Marubucin yaci gaba da cewa...

KO DA GANIN HAKAN SAI DAKARUN SARKI TARYAN SUKA BISHI domin su kamoshi, dan su a zatonsu ma so yake ya gudu.
Nan fa aka kasa tsere tsakani jarumi Imhal da dakarun sarki Taryan.
Su kuwa dakaru birnin Kisra masu rakiyar gawar gimbiya Lamirat ko da suka ga jarumi Imhal ya durfafosu a guje rike da takobi da garkuwa sai su ma suka zare makamansu suka tsaya cak suna jiran isowarsa.
Da isowar Imhal sai ya tsaya cak ya dubi dakarun sarki Gurzalu ya ce, ba yakı na zo yi ba kawai nazo ne na ga gawar gimbiya Lamirat. Ko da jin wannan tambaya sa sarkin yaki ya yi wuf ya matso gaban jarumi Imhal ya dubeshi a fusace ya ce, sarki bai bamu umarnin mu bar wani ya ga wannan gawa ba don haka sa dai kayi hakuri.
Ko da jin haka sai jarumi Imhal ya juya kamar ya hakura amma sai ya juyo cikin bazato ya daka tsalle sama ya doki kirjin sarkin yaki yayi sama da baya ya fada kan sauraran dakarunsa, ya sake daka tsalle sama da nufin ya dira akan keken doki dake ɗauke da gawar Gimbiya, kawa sai yaji an yi masa wani wawan naushi a kirjinsa, saboda karfin naushin sai da yay sama sosai sannan ya fado kasa tamkar takarda aka jefo sannan ya fado kasa tim yana kakarin amai.
Yana dago da kansa yayi arba da sarki Gurzalu tsaye a gabansa cikin shigar yaki. A cikin tsananin mamaki Imhal ya mike tsaye ya kuma kurawa sarki Gurzalu idanu ya kasa cewa komai.
Kawai sai yaga hawaye ya zubowa sarki Gurzalu ya dubeshi ya ce akan wane dalili zaka bukaci ganin gawar 'yata alhalin kai ne ka kasheta. To ka sani cewa ka rura wuta kiyayya a tsakaninmu ninkin ta da sau dubu kuma lallai sai na đauki fansar kisan da ka yiwa "yata a gobe idan har ka rayu a wannan gasa.
Ko da sarki Gurzalu ya Zo nan a zancensa sai kan jarumi Imhal ya daure ya kamu da tsananin mamaki. Shi dai a saninsa bai kashe gimbiya Lamirat ba to amma kuma yanzu ga ta a cikin akwatin gawa.
Ai kuwa in dai tana raye babu yadda za a yi a sata a cikin wannan akwati a rufe tunda ba za ta shaki numfashi ba.
Nan take jikin jarumi Imhal ya yi sanyi ainun ya juya da baya a lokacin da dakarun sarki Taryan masu tsaronsa suka karaso daf da shi suka kewayshi.
Nan dai suka sashi a gaba suka har aka isa filin gasar da shi a lokacin da sarki Gurzalu ya bisu da kallo kawai.
Filin gasar ya cika ya batse da 'yan kallo, attajirai, sarakai da manyan masu fada aji a nahiyar gaba daya.
Babban abin da ya daurewa kowa kai shine tun da aka fara wannan gasar kambun jarumta ba a taba cikowa irin ta yau ba domin har akan katangar filin gasar mutane ne a zazzaune, ko ina ka duba babu masakar tsinke sai dai kaga kawunan bil adama rututu ba adadi.
A wannan lokaci sarki Taryan na zaune a can saman gini inda ya saba zama tare da 'yarsa gimbiya Shumaira amma sai hangen bakin kofar shigowa yake domin yayi matukar mamaki da bai ga sarki Guzalu ba a filin gasar. Har ya yunkura zai kira wani badakare nasa ya.aikeshi yaje ya dubo sarki Gurzalu sai ga sarki Gurzalun ya shigo cikin filin, dakaru na take masa baya, daga can kuma sai gashi an shigo da jarumi Imhal, ai kuwa sa filin gasar ya rude da shewa, aka fara buga ganguna ana kodasu gami da yi masa kirari.
Har sai da sarki Gurzalu ya je ya zauna kusa da sarki Taryan, shima jarumi Imhal ya shiga tsakiyar filin gasar ya tsaya sannan aka buga tamburan fara gasa.
Nan fa kowa ya zuba idanu izuwa kofar da jaruman gasa ke fitowa domin a ga ko wanene jarumin da zai kafsa da jarumi Imhal a wannan zagaye na hudu na gasar.
Tsawon dakika casa'in da biyu shiru ba a ga kowa ba. kwatsam sai ga sadauki Marrasu ya fito yana taka kasa kamar wani toron giwa, yana rike da wadansu zabga zabgan adduna guda biyu.
Ko da ganinsa sai gaba dayan "yan kallo suka mimmike tsaye suna bude baki saboda tsananin mamaki. Kai wasu ma firgita suka yi suka fara yunkurin guduwa domin a zatonsu fatalwa ce ta shigo fili.
Abu daya ne ya sa mutane suka dan nutsu suka fasa gudu, ba komai bane face ganin tabon katon dinki akan makoshinsa. Nan fa hankalin attajiran caca ya dugunzuma musamman wadanda suka zabi jarumi Imhal a matsayin gwaninsu.
Ko da jarumi Imhal ya yi arba da sadauki Marrasu sai ya firgita ya ji Zuciyarsa ta buga da ƙarfin gaske a karon farko tunda ya shiga wannan gasa. Ga shi dai sauran jaruman da ya fafata da su a baya sun fi sadauki Marrasu girma da kwarjini amma kuma kallo daya mutum zai yiwa sadauki Marrasu ya gane cewa sadauki ne na gaske domin kirar zaki gareshi saboda yana da kirji mai fadi da tudu cike da gashi kuma gaba dayan jikinsa a murde yake cike da jijiyoyi da kwanji.
Kai tsaye sadauki Marrasu ya durfafi inda Imhal ke tsaye, ko da ganin haka sai Imhal ya fara dan ja da baya baya. Ai kuwa sai attajiran gasar da suka zabi Marrasu suka fara ihu suna murna saboda sun san waye sadauki Marrasu, sun san irin tsananin zafin namansa da karfin damtsesa.
Yayin da marrasu ya ga jarumi Imhal ya tsorata da shi sai ya kyalkyale da dariya, lokaci guda kuma ya turbune fuska ya dakawa Imhal tsawa, ya ce, guje gujen me kuma kake yi. Shin ba kai ne jarumin da ya kashe sadauki Darwaz da sadauki Zambaru ba?
AA Misau ke Magana Wadannan sadaukai manyan yarana ne na jikina
don haka zan dauki fansar ransu a yau a kanka, a gobe kuma na dauki fansa mafi girma akan maigidanka sarki Gurzalu.
Ko da gama fadin hakan sai sadauki Marrasu ya daga kansa sama ya dubi inda sarki Gurzalu yake, suna hada ido sai suka hau hararar juna, kowannansu jikinsa ya kama tsuma, fuskokinsu na yatsiñewa kamar su rugo izuwa kan juna su kacame da yaki.
Kai da ganin irin kallon da suke yiwa juna kallo ne na tsananin kiyayya da gaba.
Sadauki Marrasu ya dauke kai, ga barin kallon sarki Gurzalu ya dawo da hankalinsa izuwa kan jarumi Imhal sannan ya gyara tsayuwarsa yana mai bude hannayensa rike da wadannan adduna guda biyu.
Shima jarumi Imhal sai ya gyara, tsayuwarsa ya rike garkuwarsa daidai kirjinsa kuma ya daga takobinsa sama, duk su biyun suka kame kamar gumaka kuma suka kurawa junansu idanu sunamnazarin irin harin da zasu kai.
Ko da ganin haka sai jama'a suka rude da shewa kowa na koda gwaninsa.
Ba zato b a tsammani kuma sai jaruman biyu su ka taso da gudu a lokaci.guda izuwa kan juna. Suna haduwa sai suka kacame da azababben yaki, ya zamana cewe suna kaiwa junansu sara da suka ciki i tsananin zafin nama, juriya da jarumta ka ta ban al'ajabi da ban sha'awa.
Al'amarin da ya yi matukar burge kowa ke nan, aka yi tayi musu tafi da jinjina.
Ana fara wannan gumurzu ne hankalin jarumi Imhal ya dugunzuma ainun domin tunda yake karo da maza bai ta6a jin sadauki mai karfin damtse gami da zafin nama ba kamar sadauki Marrasu. Tababs idan har suka dan jima a cikin wannan yanayi zai iya galabaitar da shi ainun, ya gama dashi farat daya.
Nan fa jarumi Imhal ya rude kuma ya kidime domin ya ma rasa irin dabarar da ya kamata ya yi domin ya ceci kansa daga hannun sadauki Marrasu har ma ya sami nasarar kasheshi.
A can bayan garin birnin Misra kuwa lokacin da dakarun birnin Kisra wato suka ci gaba da tafiya sai da suka shafe rabin sa'a suna tafiya cikin kwanciyar hankali ba tare da fuskantar wata matsala ba.
Kwatsam sai suka jiyo motsi mai yawa ta gaba ta baya kuma gabas da yamma, kudu da arewa an durfafosu ta cikin duhuwar ciyayi.
Sarkin yakin Gurzalu ne ya fara zare takobinsa kuma ya bada umarnin da a tsaya.
Nan take kuwa, sauran dakarun nasa suka tsaitsaya suna masu zare takubbansu kuma suka yiwa keken dokin dake dauke da gawar Gimbiya kawanya don bashi tsaro.
Faruwar hakan ke da wuya sai wadansu dakarun sumame suka dako tsalle daga cikin duhuwar ciyayi suka dira daf da su.
Gaba dayan dakarun suna sanye da bakaken tufafi ne kuma sun rufe fuskokinsu, idanunsu kadai ake iya gani, kowannasnu na dauke da makaman yaki. Hatta takalman kafafunsu bakake. Sai da dakaru suka gama dirga a gabansu sarkin yaki kimanin su dubu shida suka yi musu kawanya ba tare da sunyi yunkurin cutar da su ba, sannan sarkin yaki ya dubi shugabansu cikin nutsuwa ba da fargabar komai ba ya ce da shi.
Me kuke bukata daga garemu Dukiyarmu kuke so ko rayuwarmu?
Ko da jin wannan tambayar sai shugaban dakarun Sumamen ya yi murmushi a cikin boyayyiyar fuskar tasa ya ce ba ma bukatar daya daga cikin abubuwa biyun da ka fada. Abin da muke so kawai shine ku bude mana akwatin gawar da kuke dauke da shi muga gawar da ke ciki domin mu tabbatar da ko gawarce ko mai rai.
Ko da jin wannan batu sai sarkin yaki Gurzalu ya bushe da dariya sannan ya ce, ai cire silin gashi a cikin tandun mai yafi wuya akan abin da kuke bukata.
Ko da gama fadin hakan sai sarkin yaki ya sa aka dauko wannan akwatin gawa aka bude ta, ai kuwa sai ga gawar Gimbiya Lamirat a ciki ko alamar rai babu a tare da ita.
Shugaban dakarun sumame ya zo Kan gawar ya tsuguna ya kara hancinsa daidai hancin gawar har tsawon yan dakiku amma sai ya ji shiru babu alamar numfashi. A sannan ne ya mike tsaye ya juya da nufin su tafi shi da yaransa sai sarkin yaki ya sha gabansa ya ce da shi idan ka koma wajen maigidanka ka gaya masa cewar maigidana murucin kan dutse ne bai fito ba sai da ya shirya.
Ko da jin haka sai shugaban dakarun sumamen yayi murmushi ya ce, ai ba a sanin maci tuwo sai ta kare, daga haka Shugaban dakarun sumamen bai sake tankawa ba kawai sai yayi wa yaransa yaransa inkiya suka ruga izuwa cikin duhuwar bishiyoyi suka bace bat tamkar basu taba wanzuwa ba a wajen ba.
AA Misau ke Magana
A can filin gasa kuwa al'amura sun sauya sai kuma suka rincabe domin kuwa lokacin da aka shafe kusan rabin sa'a ana wannan bakin artabu tsakanin jarumi Imhal da sadauki Marrasu sai jarumi Imhal ya fara gajiya ya zamana cewa da kyar ma yake iya kare hare haren sadauki Marrasu har takai cewa ma yana faduwa kasa. Cikin hanzari yake mikewa tsaye ya ci gaba da kare kansa.
Shi kuwa sadauki Marrasu lokacin ne ma yake kara zage damtse
tamkar a sannan ya fara yakin kuma a sannan ne ya fara samun damar kaiwa Imhal naushi da bugu, hannu da kafa har ya hada masa jini da majina a hanci da baki.
Nan fa jarumi Imhal ya fara shiga wani irin mugun hali, ko da sadauki Marrasu ya ga yana samun wannan nasara sai ya ji kansa ya kara girma wato ya dauki girman kai, maimakon ya yi amfani da makami ya kashe Imhal sai ya ci gaba da dukansa gami da naushinsa, duka yake mashi na nuna bambanci tamkar
babba da yaro. Sai dai kaga Imhal yana layi jini na feshi ta cikin bakinsa.
Ko da gimbiya Shumaira taga jarumi Imhal ya shiga wannan hali sai ta kamu da tsananin bakin ciki ta kuma fashe da kuka. Gaba daya mutanen dake filin gasar ma sai da suka lura da halin da take ciki.
Lokacin da sadauki Marrasu ya ga yayi laga laga da jarumi Imhal yanda ba zai iya kare kansa da komai ba sai ya cafi makoshinsa da hannu daya ya dagashi sama ya shakeshi. Nan da nan idanun Imhal suka yi luhu luhu ya fara kakarin mutuwa.
A daidai wannan lokaci ne sadauki Marrasu ya dubi sarki Gurzalu suka hada idanu ya yi masa nuni da cewar shima haka zai yi masa.
Nan take ran sarki Gurzalu ya baci ainun, zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone. Jikinsa ya kama kyarma ya ji kamar ya mike zumbur ya ruga izuwa cikin filin gasar a yi dashi.
Ko da lmhal ya ji numfashinsa na neman daukewa gaba daya sai ya yi wani irin mugun yunkuri iya ragowar karfinsa ya doki fuskar sadauki Marrasu da tafin kafarsa ta dama. Saboda karfin dukan sai da Marrasu yaga taurarin wuya kuma ya dimauce a lokacin da hancinsa da bakinsa suka fara zubar da jini, bai san sa'adda ya saki wuyan Imhal ba ya tsuguna kasa yana ganin dishi dishi.
Imhal ya fadi kasa a matukar galabaice yana numfashi, da karfi kamar ransa zai fita.
A wannan lokaci ne filin ya rude da shewa da tafi kuma aka cika da tsananin mamaki bisa ganin yadda jarumi Imhal ya sami karfin da ya ceci rayuwarsa.
Cikin tsananin karfin hali jarumi Imhal ya mike tsaye yana dafa kasa kuma ya sunkuya ya sunkuci garkuwarsa da takobinsa amma sai ya kama rangaji a tsaye saboda tsananin jigatar da ya yi don idanunsa ma lumshewa suke yi yana gani dishi dishi.
Shi kuwa sadauki Murrasu sai da ya shafe sama da dakika arba'in sannan ya dawo cikin hayyacinsa. Ko da ya sa hannunsa guda ya shafi hancinsa da bakinsa ya ga jini sai ya takarkare ya kwarara uban ihu cikin tsananin fushi da kunar zuciya.
Cikin hanzari ya ruga izuwa inda ya yarda addunansa guda bıyu ya suresu sannan ya sake rugawa izuwa inda jarumi Imhal ke tsaye.
Ko da jarurni Imhal ya ga sadauki Murrasu ya nufoshi gadan gadan rike da makamansa a fusace sai shima ya tareshi suka ruguntsume da sabon azababban yaki tamkar ma a sannan suka fara gumurzun.
Wohoho bala'i ba a sa masa rana, kuma wanda ya iya ya huta. Tunda aka kirkiri wannan gasa ta kambun jarumta ba a taba yin wasan da 'yan kallo suka more ba irin wannan domin sun ga inda tsagwaron yaki, karfi da jarumtaka ke aiki.
Sai da jarumi Imhal da sadauki Marrasu suka dada shafe wata rabin sa'ar suna kaiwa juna sara da suka cikin bakin zafin nama, ammna a tsawon rabin sa'ar sau daya jal jarumi Imhal ya sami nasarar saran sadauki Marrasu a cinya.
Shi kuwa Marrasu sai da ya sari Imhal sau shida ya sareshi a kirji, gadon baya, cinyar hagu da ta dama, sannan a damtsen hannun
hagu da na dama.
Ga...


Read / Download RIJIYA GABA DUBU 5

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

5 Comments On RIJIYA GABA DUBU 5
avatar
abdulmudallib-8

5 months ago

Reply

I already paid N1000 why don't you allow me to download the document

avatar
abasu-kala

5 months ago

Reply

Replying to abdulmudallib-8

I an sorry this is a technical issue i am resolving it now you can download

avatar
abasu-kala

5 months ago

Reply

Replying to abdulmudallib-8

I an sorry this is a technical issue i am resolving it now you can download

avatar
abasu-kala

5 months ago

Reply

Replying to abdulmudallib-8

I just check now i am unable to saw your payment can you send me receipt if the payment through WhatsApp 08140419490

avatar
taskar

5 months ago

Reply

Replying to abdulmudallib-8

Alhamdulillah now you can check and see that your subscribtion is active, and you can download any of your desire book here. feel free to contact me anytime you face any minor or big issue related to our site Thanks for using our services

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album