Join Our WhatsApp Group

TSATSUBA Complete Hausa Novel Document by TSATSUBA


TSATSUBA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 91030



TSATSUBA

Reading Time: 7 Hours

Added On: 18, Jul 2023

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 494.55 kb

File Type: txt

Views: 1883+

Download: 1108+

Last download: 1 day ago

Description/Story: TSATSUBA
Littafi na daya 1
Na Abdulaziz sani m gini
Ebook creator::- Shuraih 99%
You can download more hausa novels ebooks At http://shuraih.waphall.com
Zaku iya downloading na wasu littatafan mu amatsayin ebook ta hanyar latsa wannan blue din rubutun www.shuraih.waphall.com

TSATSUBA
Littafi Na Daya (1)
Part A.
Marubucin littafin Abdul aziz sani madakin gini
the king of Adventure story
Marubucin ya fara da cewa....
SARAUNIYA LARBISA TA KASANCE GAGARUMAR ATTAJIRA kuma gagarumar mayakiya mai mulkin wata kasa
babba wacce tafi dukkan sauran kasashen duniya
girma da yawan jama ah a zamaninta
sarauniya larbisa ta tara zakakuran mayaka
wadanda suka kasance GUGUWAR ANNOBA domin duk kasar da suka durfafa
da yaki sai sun murkusheta komai karfin mayakanta
babbar matsalar sarauniya larbisa itace
bata tsafi kuma tsafi baya cinta bokaye sun
tabbatar mata da cewa ba zata taba haihuwa ba
sai ta lalata dukkan tsafin dake duniya gaba daya
idan kuwa tana son ta lalata dukkan tsafin duniyar dolene ta tura a nemo
mata wani littafi mai suna TSATSUBA
wanda aka rubutash sama da shekaru dubu arbaIn da suka gabata
A salin wannan littafin mallakin sarkin bokayan
Aljanu ne na farko wanda shine ya kirkiro
dalasiman tsafi guda miliyan dubu Arba'in daya
rubucesu tsaf a cikin wannan littafi kuma yayiwa
littafin lakabi da suna TSATSUBA
Duk wani tsafi na duniya mafarinsa kenan kuma
makarinsa na cikin wannan dalasimai tsawan shekaru dubu Arba in din da
suka gabata bokayen duniya da yawansu
suka bazama neman wannan littafi har suka hallaka bisa wannan tafarki
kuma duk wanda ya tsananta nemansa hallaka sukeyi
saboda tsananin tsaron da aka yiwa littafin
lokacin da sarauniya sarauniya larbisa taji wannan
batu na littafin TSATSUBA sai hankalinta ya dugunzuma ainun ta rasa abinda ke mata dadi a duniya
bayan tayi dogon tunani da nazari saita watsa shela a ko ina a cikin duniya cewa duk
wanda ya samo mata wannan littafin na TSATSUBA shi zata aura kuma zata raba
kasarta da dukiyarta ta bashi kaso daya
shidai wannan littafi na TSATSUBA duk wanda ya
mallakeshi sai ya mulki komai da kowa na duniya
hatta dabbobi da tsuntsaye kuwa domin
zasu rinka bin duk umarnin da ya basu bisa wannan
dalili ne matsafa da sarakai da manyan jarumai
suka bazama neman littafin TSATSUBA suka rinka mutuwa a kokarin neman nasa.
Abin tambaya a nan shine waye zai iya baiwa
sarauniya larbisa littafin TSATSUBA alhalin yasan
cewa idan yana tare da littafin ita kanta zai iya
mallakarta kuma zai sami kowace irin dukiya da yake so ko matsayi
?
Masana da matsafa sun tabbatar da cewa babu
wata mai kyan fuska da kyan jiki tamkar gimbiya
larbisa a zamaninta kuma a wannan lokaci
data bayar da shelar a nemo mata littafin
TSATSUBA shekaranta ashirin daidai A duniya
kuma tun tana da shekara goma sha biyu ta hau kan karagar mulki sarauniya larbisa
bata da wani buri wanda yafi ta sami magajinta kafin
tsufa ya risketa don kada mulkinta ya tafi hannun
wanda ba jininta ba kasancewar itace kadai ta rage
a irin zuri ar gidansu
wata rana sarauniya larbisa na zaune a fadarta
ana tafiyar da harkokin mulki kamar yadda aka saba
saiga wani almajiri ya shigo yana bara har
dakaru sun tareshi zasu koreshi waje sai sarauniya
larbisa tayi musu tsawa suka kyaleshi nan take
larbisa ta mike tsaye daga kan karagar ta taka taje har wajen almajirin
ta kama sandarsa ta rike ta dubeshi tace zan baka abinci kaci ka koshi
yanzu ya kai wannan tsoho amma ba zaka iya
biyana ba da komai domin ni bana bukatar abinci ko dukiya
koda gama fadin haka sai sarauniya larbisa ta juya ta ja tsohon har zuwa
cikin gidan sarauta
Al amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan hatta
mutanan gari da sauran masu fada aji saboda ita dai sarauniya larbisa bata kasance
mai tausayi da jin kan talakawa ba kuma tana da tsananin rowa bata bayar
da abin hannunta face akan bukatarta kawai
lokacin da sarauniya larbisa takai wannan almajiri
cikin babban falo na turakarta wanda girmansa
yakai na wani gida guda sai tsohon ya zama
cikakken dan kauye
ya kama kalle kalle domin bai taba tsintar kansa
a cikin waje mai ni ima da daula ba irin wannan
gaba daya falon a shimfide yake da wata irin dadduma mai tsananin laushi da zarar
ka taka daddumar sai kaji kamar zaka nutse a cikinta saboda taushi
kujerun dake zagaye a falon gaba daya anyi sune
da zinare kuma sun kai kamar guda dari biyu
A tsakiyar falon an ajiye wani katon gunkin tsuntsun dawisu akayi shi
da karfen jauhar mai launin kore da rawaya kuma anyi masa wata hikima
ruwa na ta zuba a cikin dawisun yana taruwa akan wani
katon faranti na lu'u lu'u
abin dai akwai ban sha awa da ban al ajabi.
A saman rufin falon kuwa wadansu irin fitilu ne sama da guda dubu daya
wadanda suma da lu u lu u akayisu sai sheki da walwali suke tayi
Baya ga wannan wani irin kamshi na tashi a cikin falon wanda mutum bai san ko daga ina yake fitowa ba
duk inda almajirin ya duba a cikin falon sai yaga
kuyangi ne tsala tsala sunata hidimar goge goge
da gyare gyare tabbas wannan wuri
Ya cika aljannar duniya
Almajirin ya dubi kujerar sai tayi masa kwarjini
ainun ya ga cewa shidai bai kasance basarake ba
ina shi ina zama akan irin wannan kujera
kawai sai ya zauna a kasa dirshan bisa wannan
darduma mai taushi
koda ganin haka sai sarauniya larbisa da kuyanginta
suka bushe da dariya domin basu taba
ganin wanda yayi wannan kauyancin ba
sarauniya larbisa ta dubi shugabar kuyangin wacce ake kira da suna HULAIRA tace
da ita aje a kawowa bakona duk irin kalar
abincin dake gidan nan
hulaira tace an gama ya shugabata nan take hulaira ta juya ta fice daga cikin falon
ita kuma sarauniya larbisa saita dubi almajirin
tace bayan ka huta zan dawo gareka da yamma
domin muyi yar hira kafin na sallameka
ka tafi saboda kazo mini da bayani wanda yaje fani a cikin wasi wasi
da kace idan na ciyar da kai zaka ciyar dani har abada
alhalin ni babu abinda na nema na rasa
na gada abinci ko dukiya lallai ba zaka tafi ka
barni a cikin duhu ba saika wayar mini da kai
koda gama fadin haka sai sarauniya ta wuce izuwa can cikin turakarta
sai data jima tana tafiya sannan ta kule almajirin
ya daina hangota
nan fa almajirin ya shiga sakar zuci yana mai cewa
a ransa wai shin yaya cikin turakar sarauniya zai kasance a kyau
da kawatuwa?
Lallai dole ne ya ninka nan falon a komai
jim kadan da tafiyar sarauniya larbisa saiga
wadansu kuyangi daban su goma sha biyu
sun shigo cikin turakar kuma kowacce na
dauke da katon faranti abinci akan
kowanne faranti akwai abinci kala shida
nan take kuyangin suka ajiyewa almajirin farantin
abincin a gabansa suka juya suka fice
Al amarin daya firgita gaba dayan kuyangin
dake cikin falon kenan suka fara tunanin
anya kuwa wannan almajirin mutunne
a iya zamansu a gidan sarautar basu taba ganin
mutumin da ya taba cinye koda kwano daya na
abincin kasancewar kwanukan manya ne kuma
cike suke taf da abinci
sau tari sai mutane biyar sun taru suke iya cinye
kwano daya
lokacin da almajirin ya gama da abincin farantin
dake gabansa sai ya janyo wani farantin ya
gwamutsa abincin kwanon shidan akan farantin duka ya kama ci
nan da nan ya karar da abincin ya janyo faranti na uku
koda ganin haka sai gaba dayan kuyangin
suka firgice suka ruga wajen falon a dimauce
suna ihu kuma suka tsaya a can bakin kofar falon suna leken almajirin
nima kaina ganin wannan hadin nasa yasa na matsa daga kusa dashi.
Bari na dakata a nan domin jin ra ayinku game da
wannan littafi shin ya kayatar daku mu ci gaba ko kuwa
mu chanza wani
rince Auwal Auwzab > ‎MAZA GUMBAR DUTSE
TSATSUBA
Littafi Na Daya (1)
Part B.
.
nan take subauratu yayi sujjada ga sarauniya larbisa
yana mai bude fukafukansa ya kwashi gaisuwa sannan
yace da ita yake sarauniyar duniya fadi duk irin tambayoyin
da kike son ki gabatar dasu a gareni ko kuwa adadin
su yakai na yawan gashin dake jikin rago ko tinkiya
domin babu wata iska anan wacce zata dami tsufana. Lallai
zan baki amsoshin tambayoyinki ko da kuwa zan kwana
dubu a zaune ina yi miki jawabinsu
koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa ta
bushe da da dariya sannan tace aini tambayoyina
guda uku ne kacal tambaya ta farko itace naji
Huzallatul marwasu yace abokan tafiyarmu izuwa
inda zamu samo littafin Tsatsuba su hudu ne kuma ukun
cikinsu matane
na hudun kuma namijine to wai shin menene amfanin
kowanne daya daga cikinsu a cikin wannan tafiya kuma
a wane garuruwa zamu riskesu, Tambaya ta ta biyu itace akan wane dalili
wadannan abokan tafiya tamu su hudu zasu yarda suyi
mana rakiya zuwa wannan tafiya mai tsananin hadari?
Tambaya ta ta uku itace ta karshe shin kasan dalasiman
tsafin da za a karanta a lalata gaba dayan tsafin dake cikin
littafin tsatsuba?
Sa adda Aljani saubaratu yaji wadannan tambayoyi guda uku daga bakin sarauniya
larbisa sai yayi shiru yana mai kura mata idanu
cikin Al ajabi ba wani abu bane ya sa yayi shiru ba kuma
ya kura mata idanu ba face tsananin kyawunta da ya dimautashi
koda larbisa ta fahimci halin da Aljani saubaratu ya
shiga saita daka masa tsawa ta ce shin zaka bani amsar tambayoyina ne ko
kuwa zakaci gaba da kallona ne har saika gaji
nan take Aljani saubaratu ya shiga taitayinsa ya dubi larbisa
cikin nutsuwa ya ce ki gafarceni ya shugabata kiyi sani
kinyi mini tambayoyi ne masu matukar mahimmanci
a cikin wannan tafiyartamu kuma wadanda zasu dauki
dogon lokaci ina yi miki bayaninsu
da farko dai abokin tafiyarmu wanda zamu fara
tafiya nema ba wani bane face JARUMA SHUMAIRA yar mafarauci IMSHAL, a halin yanzu duk
duniya babu wani mahaluki wanda yafi shumaira ibn imshal sanin sirrin daji da iya
farauta da kuma juriyar wahala kafin mu isa kogon
kitabul sihir inda aka ajiye littafin tsatsuba sai mun keta
ta cikin wadansu dazuzzuka guda uku a cikin daji na
farko sai mun shafe wata shida muna tafiya sannan zamuje
karshensa,
A cikin wannan daji wanda aka yiwa lakabi da shajarul shaljuma akwai
mugayen dabbobi da mugayen tsuntsaye wadanda kaifi da
tsini baya tasiri a jikinsu hakama tsafi baya aiki a kansu
babu abinda zai ceci mutum daga sharrinsu face wanda ya
san sirrinsu kuma ya kware a iya farauta gami da jurewa wahala
lallai idan babu jagorancin
jaruma shumaira bamu isa mu ratsa ta cikin dajin
shajarul shaljuma ba a raye
Abokin tafiyarmu na biyu kuwa ba kowa bane face jaruma
Larifat ma abociyar basira da hangen nesa gami da
jiyo takun sawu komai nisansa Daji na biyu wanda ke gaban
dajin Shajarul shaljun ana kiransa da suna Ujurul majnan
babu komai a cikin wannan daji face wadansu irin gabza gabzan dodanni masu cin
naman mutane da na aljanu da dabbobi suna
da kaifin basira wajan dana mugayen tarkuna kuma suna da tsananin gudun tsiya yadda komai tazarar dake
tsakaninsu da mutum suna iya cinmmasa
jaruma larifat ce kadai zata iya gano duk irin tarkunan
da wadannan dodanni suka dana kuma ta iya jiyo
sautin sawayen dodannin suke sannan ta iya jiyo
sawayensu a duk sa adda suka rugo don kawo farmaki,
Daji na uku wanda ke gaban dajin Ujurul majnan ana kiransa
da suna Darul Maut Babu komai a cikin darul maut face
wadansu mugayen kunamai da macizai bakake wadanda da zarar sun sami nasarar
sarar mutum ko harbinsa sau daya take jikinsa ke zagwanyewa
ya narke
Abokiyar tafiyarmu ta uku itace jaruma Lubaina Yar sadauki Sulzainu
Jaruma lubaina ce kadai zata iya yakar wadannan kunamu
da macizai ta hanasu cutar damu saboda duk duniya babu
wani jarumi mai zafin namanta kuma tana da wata
rantsatstsiyar takobi da babu abin da bazata iya tsargeshi ba
koda kuwa dutse ne ko karfe, muna fita daga cikin dajin darul maut Bayan tafiyar
wata Hudu zamu riski Kogon kitabul sihir inda aka ajiye
littafin tsatsuba
ya shugabata kiyi sani cewa shiga cikin kogon kitabul sihir
dai dai yake da mutum ya siyi ajalinsa da kudinsa
saboda tsananin masiful dake cikinsa da kuma irin
gagarumin tsaron da aka yiwa littafin tsatsuba
babu wanda zai iya samun nasarar shiga har cikin kogon kitabul sihir
ya isa har inda littafin tsatsuba yake a raye kuma cikin
kuzari face jarumi Ruhaisu ibn Zaiyanu daga Sarkin
Birnin Kufa.
A halin yanzu duk duniya babu wani jarumi mai karfin
damtsensa sannan kuma yana da tsananin sa a da rabo bisa
dukan abinda yasa a gabansa a yanzu haka yana cikin
tsananin bakin ciki bisa mutuwar masoyiyarsa wacce yake
tsananin kauna fiye da komai a duniya, duk da cewa
kama da wane bata wane
Ya shugabata ni ina da tabbavin cewar zaki iya yaudarar
jarumi ruhaisu da tsananin kyawunki ki nuna masa soyayya da haka ne kadai zaki iya
ribatarsa ya amince yayi wannan tafiya har ya shiga
cikin kogon kitabul sihir ya dauko mana littafin tsatsuba
Lokacin da Aljani subauratu yazo nan a zancensa sai
sarauniya larbisa tayi shiru tana mai sunkui da kanta
kas ta fada cikin kogin tunani mai zurfi har izuwa tsawon
wani dan lokaci
daga can kuma sai ta dago kanta ta dubi Aljani subauratu
tana mai ajiyar zuciya tace yakai subauratu kayi sani cewa
hakika kazo mini da babban al amari mai wuyar fahimta
da gamsuwa wanda dole sai dai mutum yayi kundunbala
ya aikata shi ni kam babu gudu kuma babu ja da baya a cikin
wannan Al amari amma ina da sauran tambaya guda
daya rak a gareka yanzu wacce idan ka gamsar dani
da amsarta bani da sauran fargaba tambayar tawa kuwa itace tayaya zamu hada
wadannan abokan tafiya tamu su hudu a cikin kankanin
lokacin Alhalin kowannansu yana can wani bangaren daban
na duniya harmuyi wannan tafiya tare dasu wacce takai ta tsawon
shekara guda?
Koda jin wannan tambaya sai Aljani subauratu ya
kyalkyale da dariya , lokaci guda kuma ya hada rai yace
ai riskar wadannan jarumai hudu a cikin yini daya jal a wajena dai dai yake da shan
ruwa a gareki makurwa daya don haka ki kwantar da hankalinki
kawai ki fara shirye shiryen wannan tafiya
koda jin wannan batu sai fuskar sarauniya larbisa ta
fadada da murmushi bata san sa adda ta kama kyalkyala
dariya ba koda ganin haka sai tsoho huzallatu marwasu da Aljani subauratu ma
suka tayata kyalkyala dariyar..
A yayinda ni kaina na tayasu kyakyatawa
kamar yadda sarauniya larbisa ta fada haka al amarin ya
kasance wato a cikin kwanaki uku dai dai suka kammala
dukkan tanadi na wannan tafiya ita da tsoho huzallatul marwasu
suka hau bisa wadansu ingarmun dawakai guda biyu
sannan aka debi dakaru mutum arba in kacal tare da kuyangi
goma masu yi mata hidima gami da isashshen guzuri
na abinci da dinare mai yawa aka kama hanya aka fice daga cikin
birninta
bayanta yiwa ta yiwa fadawanta da jama arta sallama akan
cewar ba zata dawo ba sai bayan shekara guda
sarauniya larbisa tayi shiga ne ta kayan yaki masu matukar kyau da kwarjini
kuma ta rufe fuskarta da wani bakin kyalle idanunta
kadai ake gani
shi kuwa tsoho huzallatul marwasu kaya na alfarma aka bashi ya sanya
irin na sarakai kai kace ma shine da mulkin ba Larbisa ba
lokacin da wannan tawaga ta shafe sa a uku ana
tafiya a cikin daji ba tare da sanin inda aka dosa ba kuma
dama larbisa ce akan gaba saitaja linzamin dokinta ta tsaya
cak, Al amarin da ya baiwa huzallatul marwas da sauran abokan tafiyar mamaki
kenan kowa ma ya tsaida nasa dokin, huzallatul marwas
ya risina a gareta cikin girmamawa yace
ya shugabata lafiya kuwa kika tsayar mana da tafiyarmu
a nan?
Koda jin wannan tambaya sai sarauniya larbisa ta dakawa
tsoho huzallatul marwas tsawa tace akan wane dalili
zamu ci gaba da tafiyar da bamu san inda muka dosa ba
ka yiwa Aljani Sabauratu ibn kimasasa magana ya gaya
mana inda zamu fara dosa domin nemo abokin tafiyarmu
koda jin wannan batu sai huzallatil marwas ya bugi jakar hannunsa take aljani
subauratu yayi magana yace ku nufi kudu zamu gajarce
muku tafiyar wata uku izuwa yini biyu da rabi inda zaku
riski Dajin Falmaz anan ne inda jaruma shumaira take
wacce ita ce kadai...


Read / Download TSATSUBA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album