Join Our WhatsApp Group

GUDUN TSIRA Complete Hausa Novel Document by GUDUN TSIRA


GUDUN TSIRA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 107696



GUDUN TSIRA

Reading Time: 8 Hours

Added On: 17, Jul 2023

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 326.5 kb

File Type: doc

Views: 1035+

Download: 552+

Last download: 17 hours ago

Description/Story: a cikin kwanciyar
hankali
wanda bama tunanin fuskantar wata
barazana
daga
sarkin Birnin nan.Sharwan ya dubi
Siyama
yace,abinda kika fada gaskiya
ne,amma ai bamu
isa
muyi Yaki da sarki Ruguzan ba.Saboda
yawan
mayakansa kuma gashi ya kasance
Azzamuli mara
tausayi.Mu kuwa a matsayinmu na
kabila kawai ba
kasa guda ba,babu wanda zai bamu
gudunmawar
dakarun yaki saidai ma a kuramu da
matsayin 'yan
tawaye ayi mana taron dangi a shafemu
gaba
daya.Yanzu dai abinda ya kamata ayi
shine,mu
zauna tare da yan majalisata da kuma
tsofaffun
kabilartamu domin ayi shawara bisa
abinda muke
ganin zai fishshemu.Koda jin wannan
batu sai
Jikin
Siyama yayi sanyi tayi shiru batace
komai
ba.Kamar
yadda shugaba Sharwan ya fada hala
al'amarin ya
kasance,wato saida aka zauana taron
yin shawara
aka shafe sama da sa'a bakwai ana
kace nace
kowa
na fadin albarkacin bakinsa,sai daga
karshe wani
tsoho wanda yafi kowa yawan shekaru a
kabilar
wanda yaga zamani da yawa ana
kiransa da suna
Wamhas ya daga hannu alamar yana
son yace
wani
abu,dama shi kadaine baice komai ba
tunda aka
fara
taron.Koda shugaba Sharwan ya hango
tsoho
Wamhas ya daga hannu sai yayi tsawa
akayi tsit
sannan ya baiwa Wamhas umarnin yayi
magana.Wamhasa ya yunkura da kyar
saboda
tsufa
yana mai dogara sandarsa ya mike
tsaye sannan
ya
fuskanci shugaba sharwan yace ya
shugabana ina
son ka sani cewar Yaki ko Hijira duk
bazasu
kubutar
damu ba saboda duk sarakuna na
wannan zamani
basu da wani adalci,azzalumai ne duk
inda muka
je
zamu tarar da abinda muke
gujewa.Bamu da wata
mafita face mu nemi sulhu da sarki
Ruguzan.Dole
ne mu tashi wakilinmu guda daya
wanda zaije har
fadar Sarki Ruguzan ya kaskantar da
kansa ya
nemi
alfarmar ya sassauta mana wannan
haraji izuwa
yadda ba zamu rinka takura ba,sannan
kuma idan
za'aje gareshi aje masa da kyautar
shanu da
tumaki
kamar guda dari dari,manya manya
kuma
kosassu.Tabbas idan aka je masa ta
wannan siga
a
gaban fadawansa zaiji nauyin yaki
amincewa da
bukatarmu musamman daya kasance
mutum mai
son abin duniya.Ya shugaba na kai da
kanka ya
kamata kaje ka gana da sarki Ruguzan
amma
tunda
yanzu bakada cikakkiyar lafiya kamata
yayi ka tura
'yarka Siyama ta wakilceka yin hakan
zaisa Sarki
Ruguzan ya dauki abin da
muhimmanci.Koda jin
wannan batu sai Majalisar ta rude da
kace
nace,wasu suna goyan bayan shawarar
da tsoho
Wamhas ya kawo wasu kuma basa
goyon
baya.Kawai sai Siyama ta mike tsaye ta
tako
kafafunta ta
zo gaban Sharwan ta risina cikin
girmamawa tace
Ya
shugabana,Wamhasa ya gama
magana,shawarar
sa
itace kadai mafita a garemu tunda idan
baka
manta
ba kasha gaya min cewa abinda na
gaba ya hango
na baya ko ya hau kan tsaunin dayafi
kowanne
girma da tsayi a duniya bazai hangoshi
ba.Sannan
kuma ance Durkusawa wadai ba gajiya
bane.Sa'adda
Shugaba Sharwan yaji bayanin Siyama
sai
hankalinsa ya dugunzuma har ya budi
baki zaice
wani abu sai gaba dayan 'yan majalisar
suka rude
da cewa sun amince da shawarar tsoho
Wamhas.Don haka sai ya kasa cewa
komai.Nan
take
aka yanke hukuncin kashe gari da safe
Siyama tare
da dakaru arba'in zasu tafi izuwa fadar
saki
Ruguzan
dauke da shanu da tumaki dari
dari.Kashe gari
kuwa
da sassafe Siyama da dakaru arba'in
suka hau
dawakai kuma suka tusa dabbobin a
gaba suka
nufi
cikin birnin Kisra.Bayan tafiyar rabin
sa'a kacal
suka
iso fada.A wannan lokaci Siyama da
dakarunta duk
sunyi shiga ne da fatun dabbobi.Siyama
tana
sanye
da riga da wando na fatar damisa
wadanda suka
kasance matsattsu don haka duk suka
fito da
kyawun surar jikinta.Babu wani 'da
namuji dazai
ga
Siyama a wannan yanayi bai kidime ba
saboda
tsananin kyawun kirar da Allah ya
bata.Siyama ta
kasance doguwar mace mai
madaidaicin kaurin
jiki,wato ita ba siririya bace kuma ba
mai kauri
bace.Tana dogon hanci da kuma dan
karamin baki
tamkar da wuka aka yanka mata
shi.Kirjinta a cike
yake kuma kugunta a bude yake,cikinta
a shamule
kamar bata ciin abinci.Gashin kanta
dogo ne kuma
baki sidik yana haske da walwali tamkar
madubi.Siyama bata kasance Farar
fatar jiki
ba,kuma
bata kasancewa baka ba,ita dai
madaidaiciya ce a
haske,.Wani irin launin fata gareta na
musamman
mai tsananin ban sha'awa wanda irinsu
a duniya
ma
kaf basufi a kirga ba.A wannan lokaci
Siyama na
rike
da wani dogon mashi a hannuta,a
kuibin cinyarta
ta
hagu kuwa ta daure wata zabgegiyar
takobi.Su
kuwa
gaba dayan Dakarun dake take mata
baya su
arba'in
sunyi shigar yaki ne suna rataye da
Takubba da
Garkuwoyi.Da isowarsu Siyama kofar
gidan
sarautar
birnin kisra tare da wadannan dabbobi
sai dakaru
suka taresu suka hanasu wucewa akaje
aka
gayawa
sarki Ruguzan zuwansu.Jim kadan sai
ka manzon
ya dawo,da zuwansa sai ya dubi
Siyama
yace,Sarki
yace na kaiku gareshi amma dole ne ku
ajiye
dukkan makaman dake jikinku anan sai
kum fito da
kayanku.Koda jin wannan batu sai jikin
dakarun
Siyama yayi sanyi kuma hankalinsu ya
dugunzuma
suka rasa abinda zasuyi.Ita kuwa
Siyama sai ta
dubesu tayi murmushi batace komai
ba,kawai sai
ta
fara mika mashinta sannan ta cire
takobinta ta
bayar.Bisa dole suma dakarun suka
bayar da
dukkan
makamanus sannan akayi musu jagora
izuwa
gidan
sarautar har aka iso cikin fadar Sarki
Ruguzan.Fadar
ta cika makil da mutane duk inda mutum
ya duba
saidai yaga kawunan bil'adama
fululu,babu
masakar
tsinke.Sarki Ruguzan na zaune akan
Karagar
Mulkinsa yana ta nishadi bisa kallon
wadansu 'yan
mata dake faman tika rawa,makidansu
suna gefe
daya suna ta buga ganguna.Sarki
Ruguzan sai
kyalkyala dariyar farin ciki yake domin
shi a
rayuwarsa babu abinda yake so sama
da
mata.Saboda tsananin son matansa
nema ya kasa
zama da matar aure daya,a shekara
daya yakan
auri
mata kala ashirin.Da zarar mace tayi
sati biyu ko
uku sai yaji ta isheshi don haka sai ya
saketa ya
auro wata saboda da ruwan
idonsa.Koda Siyama
da
dakarunta suka shigo cin wannan fadar
kowa yayi
arba da ita akaga tsananin kyawunta sai
kowa ya
kame.'Yan matan da suke rawa ma sai
suka
daina,masu kida suka kasa ci gaba da
kidansu.Shi
kuwa Sarki Ruguzan dimaucewa yayi
bai san
sa'adda ya mike tsauye ba ya kurawa
Siyama
idanu
jikinsa na Tsuma ko kifta ido ba yayi sai
kace
Gunki.
Ko kifta ido
bayayi sai kace gunki.har Siyama da
dakarunta suka iso daf da karagar
mulkin tasa suka zube kasa gabansa
suka kwashi gaisuwa bai iya cewa
komai ba.Siyama ta mike tsaye ta
dago kanta sukayi arba ita da Sarki
Ruguzan a lokacin da da fuskarta ya
cika da annuri gami da murmushi mai
taushi tace ya kai wannan sarki mai
daraja gami da cikar mulki kayi sani
cewa mu kabilar Banu Hanzar mun
kasance talakawanka masu rauni da
kaskanci don haka mun zone neman
alfarama a wajenka bisa harajin da
muke biya a duk wata guda. Muna son
Sarki yayi mana adalci ya rage mana
kaso biyu daga cikin kaso ukun
abinda muke biya saboda tattalin
arzikinmu ya fara lalacewa.Koda
Siyama tazo nan a jawabinta sai Sarki
Ruguzan ya bushe da dariyar farin ciki
a lokacin da yaji wani irin girman kai
ya shigeshi.Lokaci guda kuma ya
hade fuskarsa ya dubi Siyama cikin
nutsuwa yace,yake wannan budurwa
ma'abociyar kyawu.Ke kuma wacece
a cikin mutanen Banu Hanzar kuma
me kuka zo mini dashi wanda zai sa
na amince da bukatarku?Siyama ta
dukar da kanta kasa tace Sunana
SIYAMA BIN SHARWAN 'ya ga
shugaban kabilar Banu Hanzar.Nazo
ne bisa wakilcin mahaifina.Ya
shugabana ba komai muka kawo
maka ba face Shanu da Tumaki guda
dari dari kacal don amfanin miyar
gidanka. Bamu da wani abu wanda
zamu iya baka amma muna neman
aldalcinka da jin kanka.Koda Sarki
Ruguzan yaji wannan batu sai ya bsue
da dariya a karo na biyu sannan ya
dubi wani babban hadiminsa yace
dashi a kai Siyama da jama'arta izuwa
masauki inda zasu huta kafin ya
zauna da 'yan majalisarsa su tattauna
dangane da bukatar datazo masa da
ita.Koda jin wannan batu sai hankalin
Siyama dana dakarunta ya tashi suka
fara tunanin cewa lallai akwai wani
abu wanda Sarki Ruguzan yake so
yayi na yaudara a garesu. Nan take
Siyama tayi dan guntun tunani sannan
ta dubi dakarun nata tayi musu inkiya
dasu kwantar da hankalinsu babu
abinda zai faru.Nan take aka tafi dasu
Siyama izuwa wani gida na
musamman inda ba a saukar kowa sai
manyan sarakuna da manyan
attajirai.Shi dai wannan gida an
kawata shi ainun ya cika aljannar
duniya babu abinda babu a cikinsa na
jin dadi.Da shigarsu suka iske an
kawo masu abinci na alfarma irin
wadanda ma basu taba ci ba sama da
kala ashirin an shirya shi akan tebur
sannan ga kayan shaye shaye ma iri
iri cikin tambulan- tambulan wanda
akayi shi daga 'ya'yan itatuwa nau'i
nau'i.Koda ganin wanna daula sai
dakarun Siyama suka dimauce basu
san sa'adda suka hau kan teburin ba
suka dasawa abincin wawa.Kawai sai
sukaji Siyama ta daka mus tsawa.
Cikin razana suka mike tsaitsaye
suka sunkui da kawunansu kas.A
sannan ne Siyama ta dubesu a fusace
tace shin a tunaninku Sarki Ruguzan
zai yi mana wannan kyau tane a
banza?Ku tuna cewa iyayenmu da
kakanninmu basu taba shigowa gidan
sarautar nan ba fiye da shekaru dari
da suka gabata.Basu taba dandanar
abinci mai dadi ba irin wannan kuma
sunyi zamaninsu tafiya sun tafi.Mu
hakura da irin yanayin rayuwarmu da
muka saba da ita kada a rudemu da
dadin duniya a cutar damu.Na lura da
wani irin kallo wanda Sarki Ruguzan
ya dinga yi mini,kallo ne na sha'awa
don haka idan harma zai biya mana
bukatarmu bada zuciya daya zai
taimakemu ba.Lokacin da Siyama tazo
nan a zancenta sai dakarun nata suka
shiga taitayinsu sosai.Babban cikinsu
wanda ake kira da Ilmar ya dubeta
yace,ya shugabata yanzu mene ne
abinyi kenan?Siyama ta numfasa tace
zamu jira daga nan zuwa yamma muji
irin shawarar da sarki Ruguzan yayi
da jama'arsa. Idan ban gamsu da ita
ba nasan abinda zanyi.Amma abinda
nake so daku shine dayanku ya zauna
a cikin shirin komawa can daji
sansaninmu nan da cikar dakiku
kadan bayan na gama rubuta wasikar
dazan bayar a kaiwa mahaifina.Koda
jin wannan batu sai su Ilmar suka cika
da tsananin mamaki kuma suka kasa
gane abinda Siyama ke kokarin
shiryawa.Har Ilmar ya budi baki zaiyi
mata tambaya sai ta daka masa
harara tace kada kuyi mini tambayar
komai kawai ku zamo masu bin
umarnina.Tana gama fadin hakan ta
bude jakarta ta fata ta fiddo alkalami
da tauwada gami da takarda ta koma
nesa kadan dasu Ilmar ta zauna ta
rubuta wasika. Bayan ta gama rubuta
wasikar sai ta nannadeta ta mikawa
daya daga cikin dakarun ya karba
sannan ta dubeshi tace Ya kai Muzaru
ka boye wannan wasikar a jikinka
yadda duk duban da za ayi baza a
ganta ba a lokacin da zaka fice daga
cikin garin nan.Lallai ka ruga izuwa
sansaninmu ka kaiwa mahaifina ita a
cikin kankanin lokaci kuma ka bashi
wannan wasikar a sirrance ba tare da
kowa ya sani ba.Koda jin wannan batu
sai Muzaru ya risina yace An
gama.Nan take Muzaru ya shiga cikin
bandaki ya kimtsa kansa sanna ya fito
da sauri yana fitowa sai Siyama ta
dubeshi tace duk wanda ya tuhumeka
dalilin tafiyarka yanzu ka gaya masa
cewar nice na aikeka wajen mahaifina
domin ka gaya nasa halin da ake ciki
don kar yaga mun dade bamu dawo
ba ya zata ba lafiya. Muzaru ya sake
risina yace An gama.Kawai sai ya
juya ya fice daga gidan gaba daya da
sauri.Kafin Muzaru ya fice daga cikin
gidan sarautar saida ya ratsa ta cikin
kofofi tara,kuma duk inda ya iso sai
an caje ko ina a jikinsa ba aga
wannan wasika ba da Siyama ta
bashi,kuma sai an tuhumeshi dalilin
dayasa ya fito shi kadai ba tare da
sauran abokan tafiyarsa ba,daya
basu amsar kamar yadda Siyama ta
umarceshi sai a bude masa kofar ya
wuce.Yana fita daga cikin gidan
sarautar ya zaburi dokinsa da gudun
tsiya ya nausa izuwa cikin daji,bai
tsaye a ko ina ba saida ya iso
sansaninsu inda suka kafa
tantuna.Tun daga nesa aka hango
Muzaru shi kadai ya dawo daga cikin
Birnin Kisra,sai hankalin kowa ya
dugunzuma aka fara tunanin ko wani
abu ya sami siyama da sauran
mukarrabanta.Koda isowar Muzaru
sai ya tsaida dokinsa a daidai kofar
tantin shugaba Sharwan ya
sauka,wani badakare ya kama dokin
nasa yaje ya daureshi. Nan take akayi
masa iso ya shiga cikin tantin.Da
shigarsa sai ya iske Sharwan tare da
mahaifiyar Siyama a zaune sunyi
jugum fuskokinsu a cike da alamomin
matukar damuwa da tashin
hankali.Koda ganin Muzaru sai
mahaifiyar Siyama ta mike zumbur ta
tareshi tana mai rike kafadunsa a
lokacin da idanuta suka ciko da kwalla
kamar zatayi kuka tace,ya kai Muzaru
ka gaya mini iyakar gaskiya,menene
ya faru ga 'yata?Muzaru yayi dan
guntun murmushi yace,Siyama tana
nan lafiya kalau kamar yadda kuka
ganni,yanzu haka itace ma ta bani
sako na kawowa shugaba,amma tace
sai na kadaita dashi.Koda jin wannan
batu sai shugaba Sharwan ya dubi
Matarsa Ilela cikin murmushi yace
barkanmu.Yanzu hankalinmu ya
kwanta.Yake matata bamu wuri na
gana da babban hadimi Muzaru.Ba
tare da gardamar komai ba kuwa Ilela
ta mike tsaye ta fice daga cikin
tantin.Fitarta ke da wuya sai Muzaru
ya kwance kitson kansa guda ya fiddo
wata takarda wadda take a kanannade
ya warwareta sannan ya mikawa
Sharwan cikin sauri kuma hannunsa
na karkarwa.Shugaba Sharwan ya
warware takardar ya karantata.Yana
gama karanta wasikar sai ya kurma
uban ihu ya durkushe kasa bisa
guiwoyinsa.Koda jin ihunsa sai
Mahaifiyar Siyama ta shigo cikin
tantin a firgice,ta rungumeshi sannan
ta fashe da kuka tanace yakai mijina
mene ya faru?Shugaba Sharwan ya
dubeta fuskarsa cike da damuwa
yace,yake matata kisani cewa damu
da dukkan 'yan kabilarmu muna cikin
babban tashin hakali. A wasikar ta
Siyama ta rubuto tace dukkanmu mu
hada inamu inamu mu bar wannan
daji mu kara gaba,sannan tace mu
hadu a wajen wannan katon dutsen,so
take mu bar wannan nahiyar gaba
daya.Bansan abinda take shirin
shiryawa ba,amma naji a jikina abin
ba dadi,in bamuy da gaske ba 'yan
kabilarmu guda daya bazata tsira da
ranta ba.Don haka yanzu mu fara
shirye shiryen barin wannan
waje.Koda jin wannan batu sai Ilela ta
sake kankame Sharwan tana mai
fashewa da matsanancin kuka. WANE
ABU SIYAMA TAKE SHIRIN AIKATA
WA? ME ZAI FARU A ZAMAN DA
SARKI RUGUZAN ZAIYI DA 'YAN
MAJALISARSA AKAN YANKE
WANNAN HUKUNCI? KABILAR SU
SIYAMA ZASUYI HIJIRA KO ZASU
ZAUNA,IDAN SUNYI HIJIRAR MAI ZAI
FARU DASU A GABA. Muhadu a
GUDUN TSIRA kashi na biyu don jin ci
gaban wannan kasaitaccen labari
Gudun tsira
Littafi na daya 1
Na Abdulaziz sani m gini
Ebook creator::- Shuraih 99%
You can download more hausa novels ebooks At http://shuraih.waphall.com
Zaku iya downloading na wasu littatafan mu amatsayin ebook ta hanyar latsa wannan blue din rubutun www.shuraih.waphall.com


˙ūGudun tsira
Littafi na biyu 2
Na Abdulaziz sani m gini
Ebook creator::- Shuraih 99%
You can download more hausa novels ebooks At http://shuraih.waphall.com
Zaku iya downloading na wasu littatafan mu amatsayin ebook ta hanyar latsa wannan blue din rubutun www.shuraih.waphall.com

&GUDUN TSIRA&
Littafi Na Biyu (2)
Part A
&A-H Physicist&
A CAN gidan sarautar sarki Ruguzan kuwa bayan
tafiyar Muzaru sai Siyama ta umarci sauran
dakarunta su talatin da tara dasu dauko abincin
guzurinsu dake cikin jakunkunansu su ci.Ba tare
da
gardamar komai ba kuwa suka cika umarnin suna
ji
suna gani suka hakura da wannan abinci mai
dadin
gaske na alfarma wanda aka shirya musu.Itama
Siyama nata abincin guzurin taci bayan sun gama
cin abincin kowa ya kimtsa sai Siyama ta dubesu
cikin nutsuwa tace,abinda nake so daku shine
lokacin da sarki ya turo a kirawoni ku biyoni a
baya
amma kafin mu iso inda zan gana da shi,ku sulale
ku fice daga cikin gidan sarautar nan gaba daya ku
nausa daji,zan hadu daku a can Dajin Zamhar inda
kabilarmu gaba daya zasu yi zaman jiranmu na
tsawon rabin sa'a kacal.Idan har muka wuce sa'a
daya bamu riskesu ba a can to abu ne mayuwaci
ni
daku ya kasance mun tsira da rayuwarmu.Koda
Siyama tazo nan a zancenta sai hankalin gaba
dayan
dakarun nata ya tashi ainun domin a sannan ne
suka gane abinda take shirin yi.Cikin alamun firgici
daya daga cikinsu ya dubeta yace haba ya
shugabata saboda me zaki durfafi wuta alhalin
kinsan cewa baki sha maganin konewa ba?Siyama
tayi ajiyar numfashi sannan tace,ai abinda ya koro
bera ya fada cikin wuta yafi wutar zafi.Sau tari sai
mutum yayi kundumbala ya tari fadan da yafi
karfinsa sannnan yake fita daga wata
masifar.Nasan
irin jarumtakarku kuma nasan iyakar irin abinda
zaku iyayi.Ku jajurce duk wuya duk rintsi ku fice
daga cikin garin nan a raye,kada ku damu dani
don
nasan duk yanda zanyi na kare kaina.Ku sani cewa
daga yanzu mun daura damarar yakin ceto
rayuwarmu data jama'armu gaba daya da kuma
gyara rayuwar 'yan bayan mu don haka ranmu da
lafiyarmu ba a bakin komai suke ba.Siyama ba
gama fadin haka sai suka an kwankwasa musu
kofa.Take Siyama ta dubi daya daga cikin dakarun
nata tayi masa inkiya yaje ya bude kofar saiga
hadimin Sarki Ruguzan wanda ya kawosu
masaukin
ya shigo da sauri fuskarsa cike da annuri.Koda
yaga
alamar su Siyama basu ci abincin da aka kawo
musu ba sai nan take fuskarsa ta sauya yanayi ya
dubi Siyama cikin alamun tsananin damuwa yace
yake wannan ma'abociyar kyawu da kwarjini mene
ne dalilin da yasa bakuci wannan abincin da aka
kawo muku ba alhalin sarki ya karbeku hannu biyu
a matsayin manyan bakinsa ya karramaku kuma
ya
baku masaukin da yake baiwa sauran abokansa
sarakai.Koda Siyama taji wannan batu sai tayi
murmushi mai taushi ga hadimin wanda ya
kidimashi ya sukurkuce bisa ganin yadda kyawunta
ya karu ainun tace,yakai wannan babban hadimi
na
sarki ka sani cewa mu mutanen daji ne wadanda
suka saba da abincin 'ya'yan itatuwa da naman
tsuntsaye da dabbobi,bamu saba da irin wannan
abincin naku ba don haka idan muka cishi da
yawa
zai iya lalata mana cikinmu.Yanzu menene ya
kawoka garemu?Hadimin ya maidawa Siyama
martanin murmushin yace,Sarki ne yace nazo na
tafi
dake izuwa inda zaku gana dashi,domin ya gama
zantawa da 'yan majalisarsa.Koda jin haka sai
Siyama
da dakarunta suka mike tsaye suka fito daga cikin
dakin,amma sai wannan hadimi ya yasha gabansu
ya dubi Siyama yace,ai ke kadai sarki yake son
gani
don haka dole ne masu tsaron lafiyarki su jiraki a
anan.Koda jin haka sai Siyama ta sake murmushi
tace,ai bazasu shiga cikin dakin da zan gana da
Sarki ba saidai su tsaye a waje.Koda jin haka sai
Hadimin ya juya ya wuce gaba yana mai yiwa su
Siyama jagora suka nausa izuwa wani bangaren
dabam na gidan sarautar,suka...


Read / Download GUDUN TSIRA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album