Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

BASMA Complete Hausa Novel Document by BASMA


BASMA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 26261



BASMA

Reading Time: 2 Hours

Added On: 15, Apr 2024

Author: Ummu Maher ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 07068606171

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 139 kb

File Type: txt

Views: 545+

Download: 407+

Last download: 16 hours ago

Description/Story: [08/08, 14:11] Miss Green🍀: _*🔖BASMA*🔖_

📄Littafi na 1


*UMMU MAHER*
(MISS GREEN)🍏


*arewa book*
*PROFILE NAME* Rabiattu0444
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

*LINK*
https://arewabooks.com/chapter?id=62d10b94e4924f3d434fb7f9

*Wattpad*
*PROFILE NAME*
Rabiatu333

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
*LINK*
https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_campaign=invitefriends

*Matso kiji*
mu yawaita karatun alqur'ani mai girma don yana wankr cutukan zuciya dana bayyane.
------------------------------
2🟢

A hankali Abeed ya zagayo ta gaban mahaifiyarsa ya kalleta sosai sannan ya Ɗago haɓarta ya ce"ya ke ma'abociyar ƙyau da haiba ina neman gafararki ya ke mahaifiyata abin tinƙaho na,ta gaban goshin sarki babu wani a gabanki ko a bayanki,ke ce agaba ke ce a farko babu wani mahaluƘin daya isa ya tsaya a gabanki ya ce bake bace don cikar izza da kuma Ƙyau da Ƙawa."dun gure kansa ta yi tana dariya ta ce"kai yarima gaskiya ka raina ni sai kace wata matarka?".murmushi ya yi sannan ya ce"ai babu wata mace a guna data fiki ya ke mahaifiyata babu wanda ya isa yaja da ke matuƙar ina wajen ba tare da na cire masa yatsanta guda ba,don haka ni ke ce abar ƙauna ta har abada".

wani irin jin daɗi ne ya sauka a fuskar sarauniya Jidda don arayuwarta tana matuƙar son taga an yabe ta kuma duk abinda ta ce ayi to ya zama dole a yisa,don tun a masarautarsu ta sudan babu mai ɗaga mata hannu ba tare da ta saka anyi mata maganinsa ba.sarauniya Jidda tana da izza da kuma mulki bata yadda a kawo wani abu a masarautar ba wanda ba ita ce ta kafa sa ba,don haka kishiyarta fulani Khadija binta ta ke sau da ƙafa don aƙwai lokacin da ta mari Fulanin akan ta karya mata doka,tun Abeed yana ƙarami ta ke sonsa tunda ita alokacin Allah bai bata haihuwa ba sai daga baya ta haifi namiji sai kuma mata 2 ƴan biyu daga nan bata ƙara haihuwa ba.


Sarauniya Jidda kuwa tana da ƴara guda5 ɗaya namiji huɗu mata ta aurar da biyu matan Hasiya da Husna,yanzu kuma aƘwai Hajara da Bilkisu.


Hajara ce kawai tayo halin Sarauniya Jidda saboda tana da izza da mulki da kuma wulaƙanta ɗan adam babu ruwanta komai girmanka yanzu zata zageka ta saka aci maka mutunci.



Washe gari da sassafe Fulani da kanta ta isa ɓangaren ɗanta Yarima Abeed yana ta karatun alqur'ani mai girma ta shigo,ta kalli ɗan na ta cikin burgewa aranta tana ƙara son ɗan na ta don aƙwai addini sosai kuma kullun ba shida abokin hira irin qur'ani ya yi karatu a turai na shekara 15 amman ko da yaje ɗin ma bashi da wani aboki sai wani abokinsa Al'amin shima Al'amin irinsu ɗaya da Abeed don yana da matuƙar taka tsantsan sosai da addininsa.
tsayar da karatun Yarima Abeed ya yi sannan ya gaida mahaifiyarsa cikin girmamawa sannan ta ce"yarima anjima ƴan matan nan na masarautu daban daban zasu zo gidannan ka zaɓi wacce ka ke so daga cikinsu kaima ka yi aure ko ns ji daɗi araina".ransa yaji ya yi masa zafi ammzn saboda mahaifiyarsa taji daɗi sai ya ce"babu komai mai babbar fada insha'Allah ina nan ina jiran zamansu Allah ya zaɓa min tagari a cikinsu."

murmushi ta yi sannan ta ce"Ina alfahari da kai ɗana,saboda ban taɓa baka umarni baka bi ba don haka ina maka fatan alheri a rayuwarka ta duniya ya wanke maka dukksn abinda ke damunka na zuciyarka ya cikamin burina na ganinka a matsayin Yariman ƙaisa babu abinda zai sani farin ciki irin ganin wannan ranar".

murmushi ya yi sannan ya ce"ummi na Allah ya kaimu lokacin yasa muna da rai da lafiyar gani".murmushi ta yi ta ce"amin".


tana fita yabi hanyar da tabi da kallo yana masifar son mahaifiyarsa amman kuma aƙwai wani mummunan hali irin na mahaifiyarsa wanda baya sonsa,yasha yi mata wa'axi akan hakan amman sai ta nuna masa fushinta don haka yana ji yana gani sai dai ya yi shiru ya ƙeleta don mahaifi yafi gaban wasa.

Kallon ƙaton mudubin da ke ɗakinsa ya yi,ya kalli kansa ya kalli irin halittar da Allah ya yi masa,amman fa sai dai kash ya rasa wani abu a zuciyarsa wanda ya ke ji kamar ba zai taƁa samunsa ba.

Kash nasan masu karatu zasu so suji wannan wata irin matsala ce da Yarima,ku biyo ni ni miss green don kuji wata irin matsala ce haka.
****

Ina kitchen ina girki salimat ta shigo Ƙanwar Maryam ta ce"ke kurma har yanzu baki gama girkin bane?yunwaqq muke ji?".ban ma san me take cewa ba na cigaba da girkina kawai sai ta ɗebo ruwan zafin dana fara zubawa na shayi ta watsomin a kan kyalkyawar fuskata,tsananin zafin dana ji yatsa na ƙwala wani irin ihu ina yarfe hannuwa na don har hannu sai da ya zubar min,abinka da farar fata wajen ya tashi ya yi ja nan da nan,Mama da tazo wucewa ta kitchen ɗin taji ƙara ta da sauri tayo kaina,tana tambaya ta me ya faru?kasa magana na yi saboda tsabar azabar dana ji na rungume Mama ina kuka mai cin rai.

Da sauri Salimat ta fita don tasan bata da gaskiya da sauri Mama ta janyo hannunta ta ce"ai wallahi babu inda zakije Salimat don wallahi na gaji da abinda kuke wa yarinyar nan,ana cikin hakan Hajiya Saratu ta fito tana cewa"to wata wainar kuma ake toyawa,nasan babu munafukar data haɗa wannan abin sai kurma.

Faɗa sosai akayi ranar agidan don duk da Mama bata ramamin ba amman fa anyi masifa sosai kuma Salimat tasha duka wajen Mama da ƙer Hajiya saratu ta amshe ta tana kuka tana tsine mana ni da mama.


Alhaji Tasi'u ransa ya ɓaci sosai shine mijin mama yayar mahaifiyata dukanmu ya taramu ya kalli Salimat ya ce"idan na ƙara ganin wani mahaluƙi ya hantari Basma baiwar Allah marainiya,ku me yasa baƙwa tausayin yarinyar nan ne?da wanne zata ji da kurmanta ko da maraici ko da matsalarku,yarinyar nan a bata taɓa ganin mahaifiyarta ba ballanta ma taji Ɗuminta to wallahi bazan yarda a salwantar da rayuwarta ba,ke kuma hajiya saratu ki jawa mutumncinki don wallahi na Ƙara jin wani abu ya faru to tabbas ran kowa sai ya ɓaci".yana faɗar hakan ya yi tafiyarsa,Abubakar ya kalli Basma ya yi mata alama da hannu ta yi haƙuri baza a ƙara yin hakan ba".ɗan murmushi ta yi har ƙyawawan dimfil ɗinta ya lotsa ƙyaunta ya ƙara fitowa.

Abubakar ma murmushin ya yi yana ƙara jin son yarinyar acikin zuciyarsa ga ta kurma amman Allah subhanahu wata ala ya yi mata baiwa kala kala.

Shima faɗa sosai ya yi wa ƙannensa Maryam da Salimat,don su biyu ne yanzu yaran Hajiya Sara mata waɗanda basuyi aure ba ta aurar da mata uku,Abubakar shi kaɗai ne namiji shine kuma ɗanta na biyu.



*Miss green ce*
[08/08, 14:11] Miss Green🍀: _*🔖BASMA*🔖_

📄Littafi na 1




*Ummu maher(miss green🍀)*


_Noticed🛐:wannan littafin labarine akan wata yarinya wacce ta kasance kurma ce._

----------------------
*matso kuji👂🏻*
Babu abin ƙyama a ha
littar Allah matuƙar shi ya yi halittarsa don haka mu kiyaye don muma bamu fi ƙarfin ikonsa ba.

---------------

Bismillahir Rahmanir Rahim



1🟠


. . . .A hankali na ke share Ƙaton gidan a zuciyata ina ta istigfari don ban taƁa yin shiru da bakina akan ambaton Allah,shiyasa ko da yaushe zaka ganni cikin nutsuwa da kamala,wata sharar naji an watso min na ɗago kaina Maryam na gani a kaina tana ce wa"to uwar shara ga wata ƙarin sharar nan".bance mata ƙala ba na koma gefe na zauna don nasan tunda Maryam ta fara haka to tabbas tana son ɗebo rigima ne.

Cikin fushi ta ce"ikon Allah yanzu don na kawo wata sharar ki haɗa shine zaki koma gefe ki zauna ke ga ki uwar fushi ko?".sunkuyar da kaina na yi hawaye na bin kuncina Allah sarki baki yana da daɗi wani lokacin,yanzu da ina da baki da tuni ko da wataran banyi magana ba to tabbas wataran zanyi don sha'anin mutanen gidan sai a hankali.

Ana cikin hakan Hafsat tazo ta sameni ina kuka ta ce"Basma me ya faru ki ke kuka kuma?".tasan halina ba lallai in gaya mata ba don aƙwaini da haƙuri kamar dutse don haka ta juya kan Maryam don taga alamar ni da Maryam ne don ta juya ƙeyarta ta yi irin ɗaurin nan na ture kaga tsiya,don ƙarin neman rigima sai ce wa ta yi"to tsigarallahu to da kika zo rama mata zakiyi ko kuwa inji labari?".ran Hafsat ne ya ɓaci sosai ta ce"kin san ai zan iya rama mata ɗin saboda kin san Basma kurma ce shine ki ke mata duk abinda ki ke so don ki zalunce ta,to wallahi ba zaiyuwuba sai na tsaya tsayin daka na rama mata duk wani cin kashi banza kawai babbar kwabo".

Shaƙo Hafsat Maryam ta yi ta ce"ikon Allah yanzu Hafsa ni ki ke zagi saboda wannan kurmar banzar ko?ko da ya ke ƴan ubanci za ki nuna min saboda ita ƴar ƙanwar Mamanki ce dole ki nuna min haka?to wallahi ki maida hankalinki ko kuma inci ubanki...


Read / Download BASMA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album