Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

TRIPLETS Complete Hausa Novel Document by TRIPLETS


TRIPLETS

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 197442TRIPLETS

Reading Time: 16 Hours

Added On: 22, Oct 2023

Author: Star Lady ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 09162620621

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 980.85 kb

File Type: txt

Views: 3950+

Download: 4353+

Last download: 1 day ago

Description/Story: 💞💕
💕💞💕
💕💞💕💞
💞💕💞💕💞


*_💋 TRIPLETS 💋_*
     *_( ROMEO )_*
*Story & Written*
           ⬇️
     *Star Lady*The writer of
*DUK KARFIN IZZATA*    
And now
*_💋 TRIPLETS 💋_*       
     *_( ROMEO )_*


_Assalamu alaikum warahmatullahi taala wa barkatuhu masoyana masoyan *DUK KARFIN IZZATA* masoyan Hiyana da Brigadier general Safras ina muku fatan alkhari da godiya mai tarin yawa ba zan taɓa mantawa da kuba har kullun kuna rai na ya Allah ya tsaremin ku daga sharrin duk wani abun halitta_.

Da farko dai wanna littafi book 1 sadaukarwa ne ga My dear Amira My sister kuma my P.A😹ina kaunar ki lodi lodi 🥰


BOSS BATURE!!!much kauna 💖 masoyiya munarh much love ❤️

Kamar Yadda na fara littafin nan lafiya ina rokon Allah subhanahu wata'ala daya bani ikon Kammala shi lafiya Allah ya bani ikon faɗakarwa da kuma ilmantarwa harma da nishaɗantarwa Ubangiji Allah ya kare ni daga rubutu abunda bazai amfani al'ummar Annabi ba.

🤲Ya Allah ina rokon da ka tsaremum alkalami na daga rubuta abun da zai lalata tarbiyyar ƴa'ƴan mutane Allah ka bani ikon isar da sakon da nake son isar wa

*Gargarɗi*

_Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book ɗin nan ba ta kowace siga, ko akaranta mun shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba ko a haɗamun document ko amin Edit Idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutun zaibi mun haƙƙina_


San nan ina jiran daɗaɗan comments naku masu karamin karfin gwiwa ta hanyar daddaɗar comments naku ne zan iya gane ya kuka ɗauki littfin Ina godiya Allah ya bar zumunci 🥰

Share fisabilillah👏👏

Mai neman karin bayani ya min magana ta wan nan number 09162620621 or 09075846926 Please iya WhatsApp ban da kira💋THE BEGINNING 💋

Let's get started


Episode 1

KATSINA STATE

Unguwar farin yaro

Misalin karfe 4 na yamma anguwar tayi shiru babu wani motsin kirki kyakkyawar yarinya ce Chocolate colour doguwa tana da kyakkyawar fiska ɗan ma dai dai ci mai ɗauke da dogon kyakkyawar hanci mai tsini har baka ga manya manyan dara daran idon ta masu design na kifi farare ne tas kamar madara masu ɗauke da dogayen gashin ido kamar wadda tasa eyelashes bakin ta ɗan karami dai dai da face nata lallausan laɓɓan ta launin pink color, lips nata nasama design of heart ne tana da baƙi lallausan saje kwance a gefen lalausan kumatun ta lallausan kwantaccen bakin gashi siɗif a goshin ta kamar na larabawa tana da gogayen yatsun kafa masu ɗauke da kunba (farce) farare tas kamar madara sanye take cikin blouse gown pink color mai bala'i kyau ta sanya ɗan karamin hijabi baki a kanta a shekaru bazata wuci 13 years ba kallon ɗaya zaka mata ka san tafito daga gidan hutu da jin daɗi amma sai dai ga fuskar ta ɗauke da bushesshen hawaye alamar tasha kuka. Rike dake da matches (ashana) a hannun ta kyakkyawar kafar ta na sanye cikin kyakkyawar flat shoe baki kalan hijabin ta kyakkyawar gaske ce dan idan nace zan tsaya zayyana muku kyan yarinyar nan to sai mu kwana mu wuni bamu gama ba dan ta ko ina ta haɗu.

Sauka tayi daga kan titin da take tafiya ta keta ta cikin wani lungu taci gaba da tafiya tana tangal tangal alamar ta gaji.
Dai dai zata shiga wani kwana wani matashin saurayi yace "Jimana ƴanmata" Juyowa tayi tana kallon sa zaune yake cikin motar sa kofar motar a buɗe ya zuro kafafunsa waje, Ji tayi kamar kar taje sai kuma ta tuna da zancen mum ɗin ta in da take cewa "Ba kyau wulakan ta ɗan adam dan baka san in da zaka haɗu da shi gaba ba" tuna hakan ya sanya ta nufesa tana ɗaure fuska.
Da ga ɗan baya ta tsaya da zazzakar voice nata tace "Gani nan" tayi maganar rai a ɓace fitowa yayi daga cikin motar ya juya gabas ya juya yamma lungun babu kowa shiru cikin sauri ya zaro handkerchief daga aljihun sa ya kaɗa mata a fuska, nan take ta yake jiki zata faɗi cikin zafin nama ya taro ta ya turata cikin mota gidan baya, ya shiga gidan gaba ya tada motar da gudun gaske ya fito daga lungun ya miƙi hanyan. Gudu yake zubawa sosai kamar zai tashi sama yara uku ne a cikin bayan motar da ita 4 dukkan su a sume kuma dukkan su mata ne.

Agogon Nigeria karfe 4:30pm ta buga.

Gidane ɗan ma dai dai ci mai ɗauke da ɗan ƙaramin kofar shigowa, bazaka kira gidan da gidan talakawa ba haka zalika bazaka kirashi da gidan masu kuɗi ba, za dai a sashi a layin gidan masu rufin asiri sai dai duk anguwar gidan tafi kyan gani da tsari da fasali. Ɗakuna biyu ne a cikin gidan sai yar karamar kitchen dake tsakar gidan ta ɓangaren hagu, daga gefen dama kuwa toilet ne awajen, gidan yana da ɗan filin tsakar gida mai ɗan girma.
Kyakkyawar mace ce zaune a tsakar gidan saman tabarma, kallo ɗaya zaka mata kaga jikin hutu ta mike kafa tana tsintar shinkafa a bai bai kana kallon yadda take tsintar shinƙafar kasan bata iya ba sanye take cikin dankareriyar lace baki mai ratsin ja hannun ta da wuyar ta sanye suke da sarkan gold mai matukar kyau da tsada farace tas kyakkyawa ajin farko, cikin sanyin murya ta ɗago kai tace"Jehan!! Jehan!!!"daga cikin ɗaki wata zazzakar murya ta amsa da "na'am Mum" "Kizo ki je ki dubamin Rimsha tun ɗazun da ta fita siyo matches bata dawo ba kin san dama ba wani sanin hanya sosai tayi ba, kiyi sauri dan mu samu mu ɗaura girkin nan yamma tayi sosai" "Mum ni gaskiya na gaji shekaran jiya fa tare da ita mukaje shagon na nuna mata hanya ba daman kince tafini ƙwaƙwalwa ba to sai ta gane hanya da kan ta ba sai na nemota ba ta dawo gida" tayi maganar cikin harshen turanci ta kai karshen maganar tare da fitowa waje daga cikin ɗakin.

```Jehan```
Kyakkyawa ce ajin farko farace tas doguwa mai kyakkyawar fuska dake ɗauke da dogon hanci har baka ga manya manyan idanun ta masu design na kifi farare tas kamar madara gashin idon ta dogaye a tsai tsaye bakin ta ɗan ma dai dai ci tana da lallausan laɓɓa pink color,sanye take cikin blouse gown pink color kanta ba ɗankwali ta zubo gashi har baya bakin kirin mai tsantsi da laushi an mata kananan kalba a kan nata a karshen kitson an sanya mata bit manya manya kowani kitso ɗaya bit uku aka sa idon ta abushe yake bata da tsoro ko kaɗan a shekaru ba zata wuce 15 years ba. Jehan yarinyace shagwaɓaɓɓiya a jin farko ga rashin tsoro iyayi rashin kunya rashin ji izza ba'a mata ta kyale rashin hakuri saurin fushi rashin son mutane.

***** "Ina ɗankwalin ki Jehan?" Cewar mum tayi maganar da ɗan karfi, turo baki Jehan tayi cikin shagwaɓa tace "Mum nifa nagaji da sanya ɗankwalin nan ni yanzu ma Mum fruits nake son sha" tayi maganar da harshen turanci "Jehan!! Jehan!!! Saunawa na kira sunan ki? Ki wuce kije ki sanya hijabi kije ki nemomin Rimsha kin san yarinyar nan ba in da ta sani tun da muka dawo nan bata taɓa fita ba sai shekaran jiya idan kika bari na mike Allah sai jikin ki ya gaya miki" "Kai Mum ni wlh kin takuramin yanzu fa mun kai 5 days da zuwa garin nan idan ma ban da dakikanci irin na Rimsha ko ba'a taɓa nuna miki waje ba ba zakije ki dawo ba bare mun taɓa zuwa to ni waye ma ya nunamin ba da kai na naje ba?" tayi maganar cikin kwaɓaɓɓiyar Hausar ta, Shiru Mum tayi bata sake cewa komai ba, ita kuwa Jehan waje ta samu saman dakalin soak away dake kusa da windon toilet ɗin ɗakinta ta zauna tana tura baki.

Wata kyakkyawar farar mata ce mai ɗan kiba ta fito daga cikin ɗaya ɗakin tana faɗin "Haba Jehan ɗin daddy yi hakuri kije ki dubo yar uwarki kinji idan ta ɓata fa? Ya zaki yi?" Tsaki Jehan taja kafin tace "Goggo ni fa I can't go anywhere ta ɓata mana ni ina ruwana da ita? Please Mum let's go back to our real house I don't like this house it's too local, I want to see my dad I miss him" Ta kai karshen maganar tare da miƙewa...


Read / Download TRIPLETS

START READING

OR

DOWNLOAD TXT NOW
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album