Join Our WhatsApp Group

GIMBIYA ZAJLAT Complete Hausa Novel Document by GIMBIYA ZAJLAT


GIMBIYA ZAJLAT

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 16492



GIMBIYA ZAJLAT

Reading Time: 1 Hours

Added On: 06, Jan 2024

Author: Sanah S Matazu ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 90.33 kb

File Type: txt

Views: 753+

Download: 266+

Last download: 21 hours ago

Description/Story: GIMBIYA ZAJLAT
Gaba ɗaya garin ya yi wani irin yin baki kirin da shi da kyar mazauna garin ke ganun tafin hannuwansu, a hankali duhun ya yayye sai wata irin gugguwa ta taso jajjur da ita ta soma shawagi da mutane tana makawa a bango. Duk wanda hakan ya kasance a kansa to kuwa baya faɗowa da rai sai ya sheka barzahu, shekaru goma sha uku kenan wannan annoba na adabar ɗaucin mazauna birnin bisa wani gaggarumin laifi da suka aikata babban tashin hankaƙin Sarkin garin duk sanda hakan ya kasance ya kan rasa dakaru da yawa abu mafi muni ya kan rasa ɗan da ya haifa a cikinsa yau kimanin shekara goma sha uku kenan wanda ya yi daidai da rasa yaransa guda goma. *ZAJLAT* Ita ce yar da yafi so fiye da sauran yaransa shi yasa yake takaicin rasata a wannan *GUGGUWAR ANNOBAR*. A yau da wannan iska ke kaɗawa gaba ɗaya hankalinsa ya yi masifar tashi jikinsa ko ina rawa yake tamkar mazari zuciyarsa ta cunkushe tamkar bakar kwalta idanunsa sun kaɗa sunyi jajjur kamar ɗan buda a cikin ruwan barkono.
Bayan kurar ta lafa ne, kuma katangun birnin suka fara girgiza kamar zasu rufta inda sabo sun saba da hakan sai iface-iface ke tashi da guje-guje tare da kukkan kanannu yara da sauri ya faɗa cikin gida ga mammakinsa Zajlaht zaune tana karanta wasu surutai da kunnuwansa suka juyo masa tamkar na makiyansa tabbas kunnuwansa basu suka jiyo masa karya ba ya shiga tunani yaushe ne Zajlah ta samu keɓewa da makiyansa?. Bai bi takanta ba ya sureta bai zame ko ina ba sai ɗakin mahaifiyarsa bokanya Sharmila ya direta tare da juyo wa a fusace ya bar gidan sarautar.

Nan ne ya zama wajan ɓoyan Gimbiya Zaljah duk shekarar da hakan ƴya kasance sabida hakane take kuɓuta daga wannan gugguwar annoba.
***

Fuskarta ɗauke da matsanancin fushi, tamkar wadda aka aikowa sakon mutuwa take duban dakarun dake zagaye da ita wanda babu komai a jikinsu sai shigar silken yaki baki yana walwali. Kowa ne daga saman kansa akwai hular karfe baka an mata ado da zaiba mai kyau tare da ɗamarar adon wani gunki a rike da mashi. Ta cigaba da zazzare idanu tana muzurai.

“Na rantse da abin bauta bazan ɗauki wannan ba, a haifi ya a a gabana a tafin hannuna tazo ta na neman gaggarata ina karya ne! Abin bauta! Abin bauta!!”.

Haka muryarta ta cigaba da amo da amsa kuwa har zuwa lokacin da wasu dakaru suka gurfanar da wata matashiya yar shekaru kimanin goma sha biyu zuwa sha uku a gabanta. Suturarta ta bambanta da tasu sossai doguwar riga ce a jikinta fara mai faɗi an mata adon da koron launi da kuma zaiba mai daukar idanu kanta sanye da wani kambu na sarauta mai ɗaukar idanu gashinta ya zubo baki siɗik da shi tana da idanu manya sossai a kwai kyawu tare da ita duk da karancin shekarunta tana da girman jiki sossai.
A hankali ta sauke idanunta a kan kakkaurar matar wadda sabida muni in a ka ce ka yankata hatta wukar saika ɓoyeta, hancinta kato idanunta kulu-kulu jajjaye kamar idanun ɗan buda a cikin ruwan barkono. Ta sunkuyar da kai,

“Zajlat!”.

Bata ɗago ba ta cigaba,

“me kike zuwa yi wajan waɗancan ɓatattun mutanan? Ko kin manta fushin da abar bauta ta yi damu a zuwanki na wancan karon?”.

“Kiyi hakuri ya ke Kakata bazan kuma ba”.

“Karya ki ke, indai waɗancan mutanan ne ba zaki barsu ba sau nawa kina faɗa?. Ta karasa tare da sunkuyowa ta ɗago fuskarta suna jin numfashin juna,

“ba zaki gane ba amma zan koya miki hankali ku tafi da ita ɗakin azaba!”.

Ta faɗa da matsananciyar tsawa mai firgitarwa, kafin kiftawar idanu sun kwasheta sun tafi da ita ta kyalkkyale da dariya tare da ɗaukar tambulan giya dake kusa da ita ta soma kafa kai tana sha tana yi wa kanta kirari.
2
GIMBIYA ZAJLAT
MASARAUTAR SAMBASU
Birnin *SAMBASU* babban birnine dake ɗauke da mutane kimanun miliyan dubu goma. Birnin kewaye yake da kayan jin daɗi da more rayuwa, gari ne daya shafe shekaru sama da shekara ɗari da ashirin da tara ana mulki a cikinsa mulki irin na bakin zallunci. Sarkin dake mulkar wannan gari ya kasance takadiri kuma gawurtacan sadauki wanda ake matukar tsoronsa halima asalin sarautar kwacanta ya yi ba gada ba, babu abinda ya tsana a duniya irin musulmi da musulunci.

Asalin Sarkin garin sunansa Sarki Markahu yana da matar aure mai suna Sharmila tare da yara goma sha biyu dukkaninsu maza kuma babu wanda ba gawurtacan sadauki ba cikinsu daga mafarauta sai mayaka yana alfahari dasu sossai. Matarsa kuwa gawurtaciyar matsafiya ce wadda ta amsa sunanta asalinta ɗiya ce ga sarkin sarakunan bokayan garin kafin ya rasu ta haye kujerarsa, Sarki Markahu ya aureta ne sabida ita jaruma ce kuma da taimakonta ya kwaci sarauta yana matukar ji da ita kuma baya tsallake duk abin da ta gindaya masa. Tsanar da ya yi wa musulnci ta shahara matuka hakan yasa bida shawarar mai ɗakinsa ya gidana *GIDAN AZABA* kawai sabida azabtar da musulmi. Mutanan masarautar Sambusa basu da abin bauta face wani katon taswirar suffar wani gunki ne da aka kera wato JARBUBA. Duk wata bukata tasu idan ba ranar bauta ba sukan kawota ne ga SHARMILA ita kuma ta mikata gareshi ko kuma mutum ya hakura sai ranar bauta wato kowace Talata.
Al adar mutanan Sarki Sharmil shi ne, duk Talata suke halartar ɗakin abin bauta don mika bukatunsu, a irin wannan rana sukan yi shigar data bambanta da shigar kasarsu maza da mata akan sha giya a kuma bada yara jarirai masu ciki da dama kuma kan yi ɓarinsa mudun sun hallata. Hakan yasa masu ciki da dama kan kaƴracewa ɗakin bauta a asurce domin mudun Sarki ya samu labari to kuwa hukuncin kissa ne ga matar mijin kuwa korarsa ake daga garin. Yan mata kan yi shiga ta fitar da tsuraici wanda da damarsu a ɗakunan samari suke kwana, da dare kuma akan kunna wuta a tsakiyar gari a zagayeta ana tikar rawa har zuwa wayewar gari.
Asalin suffar gunki JARBUBA ta mahaifin Sharmila ce wato Boka Jarbuba bayan mutuwarsa suka sassaka suke bauta masa aka yi katari wani aljani cikin hadimansa ya shiga jikin gunki yana kara dulmiyar da su.
*GIDAN AZABA*
Babban waje ne dake ɗauke da ɗakuna a kala sama da guda ɗari da hamsin, kowa ne ɗauki nau in azabar da ake yi wa laifi daban daban cikin kowane ɗaki akwai ɗakuna guda huɗu a ciki masu tsaninin duhu sai itacen da suke ajiyewa wanda ya zamo shi ne abun haske ko wane ɗaki. A ciki akwai ɓangaran mata dama maza, sai kuma banɗakuna wanda suka kasance a cikin kowa ne ɗaki a kwai. Akwai babbar magirkar abincin masu laifi wadda keda ma aikata sama da mutun dubu suna aikin shige da ficen rarraba abinci.

Sai da Sarki Markahu ya shafe shekaru tamanin yana mulki sannan matarsa ta ci amanarsa ta kashe shi ta hanyar sa masa guba a abinci ya mutu, bayan kwana arba in ta ɗora babban ɗanta mai suna *SHAMFALI* kwanansa goma ƴya mutu aka ɗora kaninsa shi ma haka a haka sai da kaf yaranta suka kare ciki shekara goma ya rage saura autansu mai kimanin shekaru ashirin da tara wanda ya kasance sadauki na gaske. Hankalinta ba karamin ta shi ya yi ba da wannan al ammari nan da nan ta shirya ta shiga halwar tsafi wanda sai da ta shafe kwana arba in cif sannan ta fito cike da tashin hankali domin abin da ta yo karo dashi babban al ammari ne.
MASARAUTAR SAMUWARU
Daga hagu cikin birnin akwai wasu mutane cikin wani ɗan karamin gari mai suna *SAMUWARU*. Garin samuwaru mazauna cikinsa sun kasance suna bautar JARBUBA ne kamar yadda mazauna *SAMBUSA* ke bautawa *JARBUBA* shi dai wannan abin bauta duk shekara ka ida yana shan jinin ma abota addinin musulci kimanin mutu ɗari da goma sha biyu da sunan *SADAUKARWA*. Sarkin dake shugabantar wannam gari aminine ga Sarki Markahu matansa huɗu ya tsufa sossai duk da Markahu ya girmeshi bai taɓa haihuwa ba sai shekarar da aka haifawa Markahu autan ɗansa wato Sharmil a shekarar matarsa ta haihu aka sawa yaron Sharbusa. Sharmil da Sharbusa sun taso jarumain kuma aminan juna har zuwa mutuwar mahaifin Sharbusa ya ɗare karagar mulkin mahaifinsa yana shimfiɗa mulki cike da umarnin Sarki Markahu har zuwa mutuwarsa. Komai nasu irin na mutanan Sarki Markahu ne har shiga zuwa horan yaki da cima. A shkekarar Sharbusa ya yi aure ya auri yar sarkin yakin garinsu, wata tara ta haifi ɗa Namiji ya ci sunan *SHAM UNU* shekara biyar tsakani Sarki Markahu ya mutu. Yaran ya taso da tsagwaran jarumta sossai.
GARIN BAITUL NUR

Daga damansu kimanin tafiya kilomita ɗari da saba in, akwai karamin kyauye wanda ya kasance mutanan cikinsa rumawa ne, kyakkyawa dasu masu tsayi da kirar sadaukantaka ma abota zama a wannan kyauye mai suna *BAITUL NUR* ma biya addinin musulunci ne. Masu tsantsani tare da bautar Allah, sukan fita gari-gari don yaɗa addinnin Allah. Shugabansu mai suna Malam Tahir yana da mace ɗaya da yara tagwaye guda biyu maza, Hassan da Hussaini sai mahaifiyarsu Khadijatul Kubrah. A kwai alakar siye da siyarwa tsakaninsu da mutanan Sarki Sharbusa da kuma kuma na Sarki Sharmil kafin daga bisani su haramta hakan sabida yadda suke yi wa yaransu mata aika-aika kuma i sun kai kara babu wani kwakkwaran matakin ɗauka.
Garin Baitul nur garine da ake shimfiɗa adalci kowa na jin daɗin yadda suke zamansu,babutsangwama bare kyara babban tashin hankalinsu shi ne cikar shekarar garin dake makwabtaka dasu wato masarautu guda biyu. Domin suna asarar rayukan mutaneda daa kama daga kan yaransu musamman jarirai sai da takai ta kawo ko cikine da mace in dai ya shigo shekarar cikar shekara sai ta yi ɓarinsa sabida mugun tsafinsu da suke aikowa da shi. Malam Tahir ne ya yi tsaye wajan kauda wannan cuta da karfin addu a hakan yasa sai dai su dinga farautarsu idan shekarar ta tunkaro sabida basu da damar shiga garin basa samun nasara sabida karfin addu’a . Malam Tahir babban Malamine dake da almajirai sama da mutum ɗari, bayan karatu yana basu horon yaki ta fanni daban-daban kasancewar mahaifinsa shi ne asalin Sarkin yakin garinsu karɓar addinin musulunci yasa aka kashe shi su kuma suka samu suka tsere suka kafa karamin gari. Bayan haka suna yin sana o i na hannu da dama, noma da kira da kuma kiwo a cikinsu ma akwai mafarauta da maɗinka. Malam Tahir gwanine kuma hafizin alkur ani mai ruko da addinni sossai ya sha kawo wa birane da dama dake makwaftaka dasu tallar addininsa suna watsa masa kasa a ido, suna matukar jin haushinsa gashi kuma sun rasa yadda zasu yi da shi sun sha kai masa hari basa samunsa ko kuma su iske garin ya zama daji ko ruwa haka suke hakura su juya. Kullum muradinsu shi ne ta ya ya zasu kauda shi a doron kasa su mulki mutanansa?.

3
Tunda Sharmila ta fito daga halwa babu wanda ta sake yi wa magana tsayin kwana ki goma lamarin daya dugunzuma hankalin Sharmil sossai kenan yasan tabbas a kwai matsala gaggaruma, sai ranar kwana na sha biyu ne ta kaɗaice dashi cikin sirri fuskarta babu annuri ta dube shi,

“Yaƙkai Sharmil ka sani abin bauta JARBUBA ya nemi mu yi masa gaggarumar SADAUKARWAƁwadda zai yi alfahari da ita, ba komai ya bukata ba face yana son ya sha jinnin wancan mai taurin kan na birinin *BAITUL NUR*”.

Koda ta zauna a zancanta, sai gabansa ya yanke ya faɗi, kansa ya sara idanunsa suka yi jajjur kamar gauta jijjiyoyin kansa suka mummurɗe suka ɗago raɗa-raɗa ya dinga huci kamar mesa.

“Ya kike gani ya ke mahaifiya ta?”.

.

ƘKunnuwansa ta rankwafa ta yi masa raɗa koda ta zauna a zancenta bai san lokacin da ya takarkare yana ɓaɓɓaka dariya ba, ita ma ta soma kyalkkyalawa tana mai taya shi. Hakan yasa ɗakin ya dinga girgiza daga bisan ta tsagaita tare da daka masa tsawa ya daina. A ranar an yi busha-busha da yawa an sha giya an yi wa kananan yara fyaɗe da yawa da sunan murna tun daga ranar suka soma shirin tunkarar birnin baitul nur da mutanansa. Ya rage saura kwanaki bakwai su je, suka aika masa da takarda ɗauke da bayanin suna son ƙshiga musulunci, lokacin da ɗan aiken ya iske shi sun fito sallahr la asar ne suna zaune a kofar bukarsa yana yi musu wa’azi ya karaso ya isar da sakon, Hassan lokacin yana da shekaru goma shi ya mike ya karantawa mahaifinsa takardar kasancewar Allah ya yi masa baiwar jin yare kala-kala ciki kuwa hadda larabci. Bayan ya gama jawabin ne Malam ya yi shiru, wani dattijo wanda ya fisu yawan shekaru ya numfasa tare da furta,

“bamu yarda ba yaudara ce kawai Malam!”.

Murmushi ya yi masa ya ce,

“babu komai Baba, Allah ne kaɗai yasan gaskiya abun alfaharine ace birni kamar wannan zasu karɓi addinin musulunci”.

Take yasa aka rubuta musu martani kan cewar suna maraba da su, ɗan aike kuwa aka haɗa masa sha tara ta arziki ya koma garinsu. Tafiya mai tsayi ya yi sai cikin dare ya isa gari ya samu fada dankam shi ake jira bai wata-wata ba ya bayyana musu komai sun ji daɗin yadda Malam Tahir ya amince sossai. Bayan ƙkwanaki goma da faruwar hakan su Sharmil suka karɓi addinin Musulunci sai da Malam Tahir ya shafe kwanaki ashirin yana koya musu ibada da sauran abubuwan da suka danganci musulunci sannan suka yi sallama ya dawo gida. Matarsa Khadija kwata-kwata ta kasa yarda da abinda suke faɗa kawai dai ta zuba idanune sabida wasu mugayan mafarkai take marasa kan kyau.

*** *** ***

Kwanaki ɗari da ashirin da musuluntarsu, suka aiko musu da katin gayyata na murnar cika kwanakinsu da musulunta. Malam ya yi jim yana tunanin wannan sabuwar bidi’a amma daya tuna basu gama sannin addinin ba sai yasa a ka shirya tafiya da zumar zai daɗa wayar musu da kai. Ana gobe zasu tafi ne da dare Khadija ta sameshi da batun da yake damunta,

“Malam ina hango matsala a tafiyarmu da waɗanan mutane, mai zai hana kaki amsa wannan gayyata tasu”.

Sai da ya dade sannan ya dubeta,

“Khadija kyautatta zato abune mai muhimmanci kuma duk abin da ya faru da bawa kaddararsa ce bazai kauce mata ba, imani da cewar komai kika ya samu bawa daga ƴubangiji ne abin alfahari ne garemu ace mun jagoranci wata runduna masu yawa zuwa tafarkin gaskiya”.

Koda ya zauna a zancansa jikinta ƴya yi matukar sanyi harta gaza bakin magana ya numfasa,

“ki kasance mai addu a garemu ki zamo mai karfafa guiwa kamar mai sunanki mana, kinsan fa ta yi wa addinnin Allah hidima fiye da tunaninki Sayyada Khadijatul Kubra ita ce wadda ta hudimtawa addinni da dukiyarta da lafiyarta kuma alhamdullilahi tabbas ta yi rawar gani”.

“Malam...


Read / Download GIMBIYA ZAJLAT

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album