Join Our WhatsApp Group

BAKAR GABA Complete Hausa Novel Document by BAKAR GABA


BAKAR GABA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 61603



BAKAR GABA

Reading Time: 5 Hours

Added On: 26, Sep 2023

Author: Habibullah Muhammad Kabara ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 352.23 kb

File Type: txt

Views: 904+

Download: 320+

Last download: 23 hours ago

Description/Story: BAKAR GABA
littafin Habibullah Muhammad Kabara
Kashi na daya 1
Ebook created by Shuraih 99%
Published at WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG







BAKAR GABA
PART 1
LBR
HABIBULLAH KBR
rungume suke da juna suna masu kukan
rabuwa kamar bazasu daina ba.
inda uban ya dubi dansa mai suna yarim
saiman.yace yakai dana bakomai ne yasa
boka ulumanu yakeson yakarnuba face
tsananin zalunci irin nasa.
saboda haka nake umartarku da kuyi shiri
kai da matarka kubar wannan gari ku tafi
izuwa kogon darul sihir kuci gaba da rayuwa
acan
shidai wannan kogo asalin mallakin wani
kasurgumin boka ne.wanda ya kirkiri
tsatsuba guda dubu.
saidaya shekara dari yana aikin bokancinsa a
ciki sannan ajali ya riskishe tundaga lokacin
da ajali ya riskeshi aka rasa mahalukin da
zai shiga wannan kogo yafito a raye .
saboda haka nake umartarku da kuyi shiri ku
tafi izuwa kogon darul sihir ku ci gaba da
rayuwa.
koda yazo nan a zancensa dai hankalin
yarima ya dugun zuma.sannan ya dubi
yarima yace.bawai inaso ku durfafi kogon
darul sihir kai tsaye bane.yanzu haka na
hada maka dakaru guda dari wadanda zasu
zamo yan rakiya agareka.
sai kuma kuyangi hamsin wadanda zasu kula
fa lafiyar gimbiya har zuwa sa'ar da gimbiya
zata haihu.
a lokacin ne zata haifi ya mace ko namiji
wanda zai zama gagara badau kuma
sadaukin da da'a taba kamarsa kuma
gwarzon mayaki.
a lokadaya cika shekara ashirin aduniya
alokacin ne zai mallaki duk wani sihirin tsafi
da boka awaisul masawi ya bari.kuma
alokacin ne zaku mallaka masa wata takobin
sihiri da zaku dauko.yanzu hakazaku tafi
dajin kurusul saudam domin dauko ita
wannan takobi amfaninta shine komai karfin
sihiri tana iya karya shi.kuma idan tana tare
da kai inzaka shekara kana yaki bazaka gaji
ba.
abu na biyu da zaku samo shine tsumin
dodo harjaju.
shikuma dodo garjaju yanzu haka yana can
wani daji wanda akewa lakabi da dajin ajali.
shi wannan dodo shikadai ya isa ya mallaki
duniya saboda karfin damtsensa dana
sihiri.du wanda yasha。i tsumin dodo garjaju
babu wani kaifi da tsini da zai kara tasiri
ajikinsa da ku
sai kuma abu na uku wanda zaku samo
shine makullin kogon darul sihir wanda
dashine za'a iya bude kofar kogon darul
sihir.
shi kuma wannan makullin ana kiransa da
miftahul sihir.
yanzu haka yana hannun sarkin aljanu na
birni hamshak.
ayanzu haka wadannan aljanu sun mai da
wannan kuba a matsayin abin bautarsu.kuma
akwai tsaro a tattare da ita na sihirtattun
aljanu masu tsnanin karfin damtse.
koda abu saiman yazonan abayaninsa sai ya
dada rungume yarima ajikinsa.sannan a sake
dubansa yace hakika bincike ya tabbatar
mana cewa matarka gimbiya suhaila nada
ciki na wata biyu saboda haka kasan yadda
zakayi ku takaice wannan tafiya acikin wata
goma.
yanzu haka na samar muku yan gudun hijira
mutun dari hudu da kuma kayan guzurinsu.
ba komaine yasa mukayi hakaba face don
asami raguwar kashe kashen da za'ayi a
wannan yaki.da kuma burin sake kafa
wannan birni sabida haka yaune ranar bakin
ciki agareni wacce ban taba tunanin zuwanta
ba.
yanzu bada dadewa ba ina mai umartarku
daku kama hanya kutafi aikin dake gabanku.
nan take kuwa yasa hannu ya bude wata
barauniyar hanya dake kusa da gadon mulki.
wata katuwar rijiyace wacce akalla sai
mutum dubu sun shiga cikinta kuma wani
abin mamaki shine acikin wannan rijiya cike
yake da haske yadda ko allura ce ta fadi
zaka ganta.bude wannan rijiya keda wuya sai
sarki abu saiman ya juyo ya dubi yarima
yace acikin wannan rijiya zakuyi ta tafiya har
tsawon mako guda inda zaku iso wani daji
mai tsananin ban tsoro.
da kun iso wannan daji sai ka zare zobenka
na sihiri ka cillashi sama to duk hanyar da
kaga ya nuna itace hanyar da zata kaiku
dajin kurusul saudam sai kubi hanyar.bayan
kun dawo daga dajin kurusul saudam sai ka
sake cilla zobenka sama.zai sake nuna maka
hanyar da zata kaiku dajin ajli.
to haka zaku dinga yi aduk wani abu daya
shige muku duhu har ku karasa kogon tsafin
boka awaisul masawi.
sannan yaci gaba da cewa da zarar kakama
hanyar tafiya karka sake kace zaka sake
juyowa ka kalleni don yin hakan kan iya
janyo tarwatsewar shirin mu baki daya.
koda yazo nan abyaninsa sai ya daga
hannunsa sama ya tafa.
faruwar hakan keda wuya sai ga dakaru guda
dari dauke da guziri akan dawakai da kuma
kuyangi dauke da ginbiya suhaila.
sai kuma jama'ar gari maza da mata.lokacin
da wadannan dakaru da jama'ar garin
ramlatul saif suka suka shigo turakar sarki
abu saiman sai dukkansu sukayi sujjada
agareshi.
sarki ya dubi jama'ar garin yace yaku
jama'ar garin ramlatul saif kuyi sani cewa
yaune zaku fara tafiya mai tsananin hatsari.
saboda haka nake umartarku dakubi duk
wani umarni da yarima saiman zai baku idan
kuka bishi zaku tsira don munaso ku dawo
ku sake kafa wannan birni bayan wasu
shekaru masu zuwa.yana zuwa daidai nan
abayaninsa sai ya taka da kafafunsa yaje
wajen wata akwatin zinareya budeta ya dauko
wani gunki wanda aka kerashi da zallan
zinare.sannan ya juyo ya bawa yarima ya
damka masa ahannunnsa yana mai cewa.
wannan gunkine wanda aka kera mai
siffata.dama nasa an kerashi ne saboda irin
wannan rana.yana zuwa nan azancensa sai
ya sake rungume yarima ajikinsa suna masu
bankwana.
sai bayan dakiku sannan ya sake janye
jikinsa daga jikin yarima idanunsa cike da
hawaye.nan take ya juyawa yarima saiman
baya tare da fadin cewa yanzu haka na
umarceka daka gaggauta kama hanya ka tafi
aikin dake gabanka don cika burin dake
gabannu baki daya.don haka ina gargadinka
kada ka sake juyowa da zummar kallona don
yin hakangangancine a garemu.yana gama
fadin haka sai wani irin hawaye ya zubowa
yarima saboda bakin ciki amma bisa dole ya
kama hanya ya tafi don cika umarnin
mahaifinsa.ma'ana suka shiga cikin wannan
rijiya.
yarima ne a gaba sannan kuyangi,gimbiya
suhaila,mutanen gari.sai dakaru don
tabbabtar da tsaro.
lokacin dasu yarima saiman suka shiga cikin
wannan rijiya sa isarki yajuyo yaje ya sake
rufe wannan rijiya.
WANNAN SHINE ABINDA YA FARU A FADAR
SARKI ABU SAIMAN
a can fadar boka ulumanu kuwa yau yana
cikin farunciki sakamakon binciken da yayi
na rushe birnin ramlatul saif kuma binciken
ya tabbatar masa da samun nasara a
wannan yaki.
dalilin hakanema yasa ya baiwa dakarunsa
hutu na jinsin mutane da aljanu don nuna
farin cikinsa.don hakane ma ya hada walima
afadarsa tsakaninsa da hadimansa.bangaren
aljanu daban na mutane daban.
abisa karaga kuwa boka ulumanu ne ya
zauna bisa karagar mulki yaci ado irin na
manyan bokaye. kai wannan fada ta kawatu da kayan alatu
sosai.hatta iskar da take kadawa acikinta
tatacciyace ba irn wacce aka saba shaka
bace.
bayan yan dakiku kadan boka ulumanu ya
tashi ya fara bayani kamar haka.
yaku hadimaina duk cikinku babu wanda
baisan burina ba.
burin nawa kuwa shine na mallaki na hiyar
nan baki daya.
Adalilin hakane na shiga bincike,kuma
tsafina ya tabbatarmin bazan taba samun
nasara ba.har sai naje na yaki wani birni
wanda ake kira da ramlatul saif na rusheshi
baki dayansa na debe dukiyar kasar.
sannan na shiga dakin bautar su in hallaka
macijiyar da suke bautawa nasha jininta.
da zarar nasha jinin wannan macijiya to
awannan lokacinne duk wani boka dake
nahiyar nan zai dawo karkashina,saboda
babu wanda zai kaini karfin sihiri aduk cikin
wannan nahiyar.
koda yazo daidai nan a zancensa sai ya juya
yayiwa wasu yammata da makada inkiya.
nan take kuwa wadannan yna mata suka
shiga tsakiyar fada suka fara tikar rawa,su
kuwa wadannan makada suka fara kade kade
da bushe bushe.
nan take kuwa fadar ta cika da hayaniyar
mutane da aljanu.
bayan wasu yan dakiku sai wasu kuyangi na
jinsin mutane da aljanu suka fara debo
tulunan giya da kuma kayan abinci suka fara
rabawa hadiman gidan.
koda wadannan hadimai suka ga wannan
abinci sai suka dasa masa wawa hannu baka
hannu kwarya sabo da sun dade basu sami
abinci kamarsa ba.kai wasuma har faduwa
kasa suka dingayi basu saniba saboda
tsananin dadin abincin.
koda boka ulumanu ya lura da abin dake
faruwa sai ya fusata sannan ya dakawa
hadiman nasa tsawa,nan take kowanne ya
dawo cikin hayyacinsa.
sannan yaci gaba da cewa
bawai nataraku bane don ku dinga yin
shashanci ba,nataraku ne don kutayani
farinciki,don haka yanzu zan rubuta wasika
naba daya daga cikinku ya kaita fadar sarki
abu saiman.sanan ya dawo fadata.
nan take boka ulumanu ya bude tafun
hannunsa tare da karanta wadansu
dalasiman tsafi guda uku,yin hakan keda
wuya sai wata farar takarda ta bayyana
ahannunsa,koda bayyanar wannan takarda
sai boka ulumanu ya nuna wani aljani mai
suna markazulu da wannan ta kardar.nan
take wannan takardar t koma hannun wannan
aljani.sannan boka ulumanu yace na
umarceka daka tafi kakaiwa sarki abu
saiman wannan wasika cikin abin da bazai
gaza kwana guda da yini daya ba.
cikin biyayya markazulu yace angama ya
shugabana
nan take ya bude fuka fukansa ya luluka
cikin srarin samaniya cikin azababben gudu
tamkar tauraruwa mai wutsiya
WANNAN SHINE ABIDAYA FARU AFADAR
BOKA ULUMANU
al'amarin yarima saiman kuwa tun lokacin da
suka bar birnin ramlatul saif ta cikin wannan
rijiya sai suka wanzu suna tafiya cikin
karkashin kasa har suka isa bakin wannan
rijiya.
sai ganinsu sukayi cikin wani makeken daji
mai ban tsoro.
daga bayan wannan rijiya kuma wasu
ingarmun dawakai ne sunata faman harbin
iska.
koda su yarima suka tsinci kansu awannan
daji duksai suka ji wani tsoro ya darsu a
zuciyarsu..yarima saiman ne kadai hankainsa
bai tashi ba,kai tsaye ya durfafi inda
wadannnan dawakai suke ya zabi daya ya
mikawa gimbiya suhaila sannan ya umarci
dakarunsa suje su zabi nasu dawakan.nan
take suka je babu hayaniya kowa ya zabi
guda daya ya hau.
bayan kowanne badakare ya hau nasa dokin
sai yarima saiman ya umarci jama'ar gari da
suma suje su hau nasu dawakan.
batare da bata lokaciba suma sukaje suka
cika umarni.saida kowa ya zabi nasa dokin
sannnan shima yaje ya zabi nasa dokin
yahau sanna ya zaburi dokin zuwa gabashin
dajin batare da sanin inda ya nufaba.
nan da nan suma dakarun suka saki
linzaman dawakansu suka bi bayansa cikin
tsananin gudu mai tada hankali.
hakika alokacin da yarima saiman kejan
wannan zuga tasa duk irin halittar da tai karo
dashi a wanna lokaci to kwananta ya kare
WANNAN SHINE ABINDA YA FARU GASU
YARIMA SAIMAN BAYAN SUN BARO BIRNIN
RAMLATUL SAIF
Al'amarin aljani markazulu kuwa bayan ya
baro fadar boka ulumanu da nufin kai sako
izuwa fadar sarki abu saiman
sai ya wanzu yana mai tsala azababben
gudu nagaban kwatance har sa'a uku ta
shude.
kwatsam ba zato ba tsammani sai yaci karo
da wani murgujejen dodo mai tsananin muni.
kafin markazulu yayi wani yunkuri tuni dodon
yasa hannu ya makoshi kasa.
nan take kuwa markazulu ya fadi kasa
sumamme.
koda faduwar markazulu kasa sai wannan
dodo yasa hannu ya dauki markazulu ya
dorashi akafadarsa sannan ya nufi wani
kogon dutse dake tsakiyar dajin cijin
tsananin farinciki domin yau shekararsa uku
rabon dayaci naman aljani,naman mutane
kuwa shekararsa goma sha biyar kullum sai
dai yaci naman dabbobi. Lokacin da dodon ya iso bakin kogon nasa
sIai ya kwankwasa wata kofa ta bakin
karfe,ita dai wannan kofa an sana'anta tane
da zallan bakin karfe,
fadin ya kai kamu hamsin tsawon kuwa yakai
kamu talatin.
amma bisa mamaki sai wata yar karamar
yarinya ta leko ta wata yar karamar taga.
koda taga mahaifinta ya dawo da wani
murgujejen aljani akafadar sa sai rugo da
gudu tazo ta budewa mahaifin nata kofa
tamkar yadda zaka janye murfi daga jikin
tulu.
nan take wata kara mara dadin ji ta cika
dajin baki daya sakamakon bude wannan
kofa.
ba tare da bata lokaci ba wannan shid
ge cikin kogon ya jwo wani kejin bakin karfe
ya jefa aljani markazulu ciki ya rufe
sannan ya juyo ya dubi yarsa yace
yake yata mafi soyuwa agareni ki sani cewa
yau nayo farautar da ban taba yin kamarta
ba
domin wannan aljani yana dag cikin manyan
dakarun boka ulumanu wanda ya kashe miki
mahaifiyar ki a shekarun da suka gabata
kuma ina mai yi miki albishir cewa kece da
kanki zaki kashe wannan aljani kisa mafi
munin da mukewa halittun da ke doron kasa
yadda zamu kunsawa boka ulumanu bakin
cikin da bazai taba mantawa da shiba
lokacin da dodo shrmanu yazo nan a
zancensa
sai yarsa samriya ta bushe da dariya har
zuwa wasu lokuta sannan tace ya abbana
hakika yau kacikan babbab burina koda ban
kashe boka ulumanu ba
sa'ad da samriya tazo nan a zancenta sai ta
mike tsaye cike da farinciki ta shige wani
daki dake cikin kogon ta kwanta.
kwanciyar samriya keda wuya sai barci ya
dauketa.
sannan shima dodo sarmanu ya tafi shima
ya sami guri ya kwanta nasa barcin don huce
gajiyw
kash hakika rashin sani ya fi dare duhu inda
dodo sarmanu ya san abinda zai faru da
baiyi gangacin kwanciya barciba domin ya
manta bai dauke makullin kejin dayasa aljani
markazulu a ciki ba.kwanciyasa jeda wuya
sai wani hadari mai karfi ya ta
so nan take aka tsuge da ruwan sama kamar
da bakin kwarya.
da ike kejin da aljani markazulu yake ciki
yana daga bakin tagar kogon sai nantake
aljani markazulu ya farfado daga dogon
suman da yayi sakamakon ruwan da yake
shigow ta cikin tagar
lokacin da markazulu ya farfado daga dogon
suman da yayi kuma ya ganshi cikin keji sai
ya cika da tsananin bakin ciki akan abu biyu.
abu na farko shine bai taba tunanin akwai
wani acikin duniya da zai iya yi masa irin
wannan kamu ba kamr dabba
abu na biyu kuma shine mai zai cewa boka
ulumanu idan ya koma can fadarsa alhlin
sunyi alkawarin zai kai wannan acikin kwna
guda da yini daya.
koda ya gama wannan tunani sai ya sake
cika da bakin ciki mara misaltuwa.
kwatsam ba zato ba tsammani sai yayi
kicibus da kubar wannan keji da yake ciki
koda yaga wannan kuba sai y sake jin murna
t akama shi har ta disa sar da bakin cikin da
yake ciki.
ba tare d bata lokaciba kuwa ya zuro hannu
ya dauki wannan kuba ya zura ta a cikin
gidanta sannan sannan ya murda nan take
kuwa wannan kofa ta bude.
nan take marlazulu ya fito daga cikin kejin
da yake ciki sannan ya zare takobi ya nufi
kan dodo sarmanu kai tsaye ba tare da
fargababa ya daga takobin ya caka masa ita
acikin ido
nan take kuwa dodo sarmanu ya kwalla uban
ihu
wanda yayi sanadiyar farkawar samriya daga
barci
koda taji karar mahaifinta sai tayi tsalle ta
zare wata sharbebiyar takibi dake jikin
bangon kogon ta rugo dq gudu izuwa inda
mahaifinta ke kwance kwatsam sai taci karo
da gawar mahifinta kwance cikin jini ga
kuma bakon aljanin da suka kamo rike da
takobi tana yoyon jini.sai ranta yayi matukar
tashi
nan take ta falfalo da azababben gudu tana
mai kwarara uban ihu koda tazo daf da
markazulu da nufin tai masa kwaf daya sai
aljani markazulu yayi tsalle ya tsallake harin
nata nan take aka ruguntsume da azababben
yaki na gaban kwtance tsakanin markazulu
da samriya
wohoho hakika fadan manyan dawa yayiwa
yara nisa domin ana fara wannan yaki
samriya ta toshewa markazulu kofofin tsira
amma saboda tsananin bakin naci irin na
markazulu sai yaki yarda yaje kasa
Azahirin gaskiya samriya tafi aljani
markazulu karfin damtse shi kuma markazulu
yafita juriya naci da iya yaki.
samriya ta wanzu tana mai kaiwa markazulu
sara da suka ta ko ina.
shi kuma ya wanzu yana mai kare saran nata
cikin zafin nama.sai da suka sahafe lokuta
suna wannan fada kowaya kasa samun
nasara akan dan uwan fadansa bisa dole
dukkansu suka ja da baya suna masu hararar
juna kamar zakaru.
daga can sai samriya ta dubi aljani
marjazulu tace
yakai wannan la'anannen aljani kayi sani
cewa yau ka tsokanowa kanka bala'in da ba
zaka iya fita ba domin mahaifina daka kashe
shine dan autan sarkin dodannin duniya wato
dodo garjaju
wanda yanzu haka yana can dajin ajali don
na tabbata yanzu yasan ka kashe dansa
don haka akoda yaushe zai iya turo yan
uwan mahaifina domin daukar fansa akanka .
koda samriya tazo nan a zancenta sai
markazulu ya bushe da dariya sannan yace
ke yarinya ki sai wanda ya rigaka kwana dole
ya rigaka tashi domin ni da kike ganina na
girmi mahifinki nesa ba kusaba don haka
koda yaushe ashirye nake dayin mugun gamo
ni da yanuwan mahaifinki
koda yazo nan abayaninsa sai ya shammaci
samriya ya cilla mata wata allurar sihiri
nan take kuwa samriya ta fAdi kasa ma
tacciya
faruwar hakan keda wuya sai aljani
markazulu ya sake bushewa dadariya akaro
na biyu sannan ya durfafi kofar kofar fita
daga kogon don ya budeta ya fita.
koda ya kai hannu da nufin budeta sai yaji
tamkar zai dauki duniya saboda tsananin
nauyi bisa dole ya saki kofar kogon cikin
tsananin ta shin hankalidomin yasan indai
yace zai zauna aciki wannan kogo bazai
dadeba zai mutu


LITTAFIN
BAKAR GABA
PART 2
TYPING HABIBULLAH KBR
Amma sai ya yanke hukuncin yakoma cikin
kogon kozaiga makullin kofar kogon.
nan take kuwa ya nausa cikin kogon batare
da sanin inda ya dosa ba.saida ya wuce yan
dakiku yana shige da fuce acikin kogon
sannan ya ido wani daki mai dauke da kayan
tsafi iri iri.koda isowar markazulu bakin
wannan daki sai ya cika fa farincikidomin
yasan cewa tabbas zai sami abinda zai
taimakeshi ya fita daga wannan kogo acikin
wannan daki.
nan take yashiga cikin dakin ya hau lalube
baji ba gani
kwatsam sai yaci karo...


Read / Download BAKAR GABA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album