Join Our WhatsApp Group

MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN Book 3 Complete Hausa Novel Document by MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN Book 3


MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN Book 3

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 30120



MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN Book 3

Reading Time: 2 Hours

Added On: 31, Jan 2024

Author: Aliyu Abubakar Sharfadi ,

Ebook Compiler : Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 151.03 kb

File Type: txt

Views: 713+

Download: 372+

Last download: 13 hours ago

Description/Story: MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN
Littafi na biyu 3
Fassarar Aliyu Abubakar Sharfadi
Typing by Shuraihu Usman
published at www.TaskarNovels.com.ng

MALUKUSSAIF
idan mai karatu bai manta ba, a littafi na baya, mun tsaya a inda Kamriyya ta kara sace allon Iluru yayin da Malukussaifi yake barci a dakin matarsa Nahidu ta koma gidanta da shi. To yanzu bari mu ji kuma abin da zai wakana bayan komawarta.
A wannan daren Kamriyya ta goga allon nan, nan da nán Iluru ya zo gabanta ya tsaya da zuwansa sai ta umarce shi da ya je ya ďauki Malukussaifi ya kai shi can birnin Malam Afaladinu. Ya aikata kamar yadda ta umarce shi. A wancan karon, ickin jimami Iluru ya fita ya je ya dauki Malukussaifi ya yi sama da shi, saboda tsananin sauri da yake har ya farka daga barcinsa ya shafa dantsensa ya ji bai ji allonsa ba kuma ya duba ya ga Iluru ne ya ke dauke da shi sai ya san lallai wani ya mallaki allon nan sai ya ce “Ya Iluru ina kuma aka umarce ka da ka kaini? Kuma waye ya mallaki allon nan ya sa ka ka daukc ni?" Iluru cikin fushi ya amsa masa da cewa ya shugabana wallahi baka san muhimmanci na ba wajenka shi ya sa ka ke sakaci da allona ake sani ina ta kaika ga halaka,wallahi banda na san akwai sabanin da zai sa na. dawo hannunka to wallahi da ni kaina tuni na halaka ka saboda na huta da wahalar da ni din da ake saboda kai, ka tuna fa nima ba matsiyacin aljani ba ne kuma ba bawa ba ne nima dan sarki ne kamar kai, ka kan kasamu ya sana'anta maka allo na domin kai kadai na rika yi maka hidima amma kana sakaci da ni har wasu suna samun damar bautar da ni. Yanzu ma mahaifiyarka ce ta sake mallakar allo na kuma ta umarce ni da na kaika garin Maļlam Afaladinu garin da,ka samo hula na aikata maka kamar yadda ta umarce ni a baya”.
Da jin wannan magana ta Iluru sai ya yi nàdama ya ce “Ya Iluru to yanzu idan wadannan mutane suka daga tsinin masu sama ka jehoni ai ba makawa na mutu ke nan". Iluru ya ce “Sakacinka kai ka jiyo”. Bayan wasu sa'o'i suka isa garin.
Iluru ya aikata kamar yadda aka umarce shi sai ya yi duba ya ga inda jama'ar birnin nan suka yi sahu-sahu sun daga tsinin masu sai yasan lallai idan ya jeho shi haka za su tsire shi sai ya karyr wata bishiya ya hura ta ta rarake sai ya zurashi a ciki,sannan ya luluka can sama da shi cikin ice sannan ya sako shi,ya tafi cikin gaggawa zuwa gidan Akisa ya gaya mata “Maza ki je ki ku6utar da dan'uwanki domin yanzu gashi can uwarsa ta sa na kai shi na jefawa mutanen birnin Afaladinu shi za su tsire shi da masukan su” Ko da jin wannan magana ta Iluru sai Akisa ta yi wuf ta tasi ta kama hanya cikin hazari tana gaggawa irin wadda bata taba yin irinta ba jim kadan ta isa birnin ta tarar sanhon bishiyar nan da Malukussaifi yake ciki ya kusa zuwa kasa saura bai fi zira'i biyu ba ya tarar da tsinin masukan mutanen nan sai ta yi wuf ta fauce shi cikin sanhon nan ta yi sama da shi ta koma da shi izuwa gidanta ta kwantar da shi a kan gado sai taga ai sam baya motsi sai ta yi zaton ya mutu sai ta kara kunncnta a kirjinsa sai ta ji bugawar zuciyarsa nan sai ta tabbatar bai mutu ba. Kasancewarsa cikin wannan hali sai Akisa hankalinta ya tashi ta rude ta rasa inda zata sa kanta nan sai ta sabi wata waka baiti ashirintana kuka cikin wakarta tana addu'ar Allah ya kawo sababin da zai warke ya samu lafiya. Bata gama wakarta ba sai ta ga wani mutum akan wata taguwa mai fukafukai ya sauka a cikin gidan.
Da saukar mutumin ya yi mata sallama sai ta tambaye shi “Kai kuwa mutum ne kai ko aljani dan'uwana kuma daga ina kake kuma yaya sunanka kuma mc ya kawo ka nan gidana?"Mutmin non ya amsa mata da cewa “Ai yanzu ba lokacin zance ba ne, ni dai na zo ne domin na taimaka miki na baiwa wannan dan'uwana naki magani, saboda haka kar ki tsawaita mini zance daga baya zaki samu labari na". Ya dauko wata 'yar batta daga cikin wata jaka dake rataye a kafadarsa ya bude ya debo wasu jajayen kwayoyi guda uku ya mika mata ya cc "Rike wadannan domin dan'uwanki yanzu baya ji baya gani kuma ya samu sagewar jiki sakamakon bubbugewa da ya yi cikin icen nan, saboda haka yanzu ki jika daya daga cikin
Kwayoyin nan ki diga masa ita a idanuwansa za su warke,daya kuma ki jika ki diga masa a kunnuwansa za su warke sannan kuma dayar ki jika ta ki shafe masa duk jikinsa da ita zai samu lafiya kamar wani abu bai taba samun sa ba." Akisa ta kar6a cikin farin ciki shi kuma mutumin ya hau taguwarsa ya tashi sama ya yi tafiyarsa.
Cikin hanzari Akisa ta aikata kamar yadda aka umarceta,jim kadan sai ta ga Malukussaifi ya yi hamma ya yi mika ya yi juyi ya ta shi zaune sai ya ganta a zaune a gefensa sai ya ce “Ya 'yar'uwata nan kuma a ina nake?" ta amsa masa ta ce "Ai nan a gidana ka ke". Ta kwashe labarin abin da ya faru kaf ta gaya masa sai ya yi mata godiya kuma ya nemi ta kawo masa abinci ya ci, ta kawo masa abicni iri-iri na alfarma ya ci ya sha ya koshi sai ya nemi da ta dauke shi ta mayar da shi birnin sa sai ta ce “Ai ya dan'uwana ba zan mai da kai kasarka ba domin ina gudun kada uwarka ta sake kulla maka wani makircin da zata halaka ka. Ni dai na fi so ka zauna nan tare da ni domin in kana nan gidan ba bu aljanin da ya isa ya zo ya dauke ka ko ya cutar da kai”.
Jin wannan zance na ta sai ya ce allaburan shi bai yarda ba ba zai zauna wajenta ba, suka yi ta jayayya ta yi- ta yi ta shawo kansa ya yarda ya zauna amma ina sam ya ki yarda. Da ta ga ya ki yarda sai ta ce "Na rantse da Ubangiji maďaukakin Sarki ba za ka bar nan gidan yau ba sai ka zauna ka dan yi kwanaki a wajena domin idan uwarka bata son ganinka ai ni bengen ganinka nake”. Da ya ji ta rantsuwa a kan sai ya zauna sai ya ce mata "Na yarda zan zauna matsawar wasu 'yan kwanaki,amma yanzu ki tafi izuwa kasata kizo min da labarin halin da ake ciki domin yanzu ban san abin da uwata zata aikatawa jama'a ta ba. Akisa ta amsa ta tashi ta tafi izuwa Yemen domin ta zo masa da labarin mutanensa.
Bayan kimanin sa'a biyar Akisa ta koma masa da labari ta ce“Na je kasarka na zo maka da labari”. Ya ce “Ke na ke saurare gaya min naji”. Ta ce “Lokacin da uwarka ta umarci Iluar va fauke ka va kaika birnin Afaladnu bavan va kai ka va
komo wajenta sai ta sashi ya fito da bokayen nan guda biyu da aka kullesu a kurkuku tare da su ta kuma sa shi yadebe su ya mai da su kasarsu garin Sarki Saifu'aradu. Bayan da gari ya waye jania'a suka ga ba su ganka ba sai suka je suka gayawa bokan nan naka Barnuhu nan danan ya buga kasa ya fahimci lamarinka sai ya umarci mutanenka da kowa ya kwantar da hankalinsa babu abin da zai faru shi zai kiya ye su cikin yardar Allah daga sharrin Kamariyya. Sai duk jama'a suka kwantar da hankalinsu.
A wannan lokacin dai ya umarci Sarki Abuttaj da Sadaukansa ya ce su hau dawaki su tafi wani waje amma ban sami labarin in da ya tura su ba, shi kuma Barnuhu ya yi wani sihirinsa ya daddaure ga6obin Kamriyya bata da ikon motsa su sai ya zamto yanzu dai bata da ikon goga allon nan kuma ya aika mata da matsananciyar cuta wanda a yanzu bata iya fita koina,to ka ji wannan shi ne labarin mutanenka” Ya yi murna da jin yadda wannan lamari ya gudana ya ci gaba da zama tarc da 'yar'uwarsa Akisa 'cikin farin ciki, tana ba shi labarai iri-iri masu ban sha'awa domin ta shagaltar da shi ya dade tare da ita.
Amma abin da ya faru ga Kamriyya kullum sai ta yi nufin ta goga àllon nan amma ina sai ta kasa kuma ga cuta ta tsananta a tare da ita, wata rana sai ta yi kiran wani daga cikin bayinta sai ta sake rubuta takarda ta ce “Zuwa ga babban Sarki Saifu'aradu, kai sani fa ni kuyangar nan taka Kamriyya nai nufin halaka dan nan nawa Malukussaifi saboda biyayya bisa umarninka amma yanzu ga wani boka wai shi Barnuhu kamar yadda na san ka samu labari daga bokayenka, shi dai wannan boka yanzu shi ya rage min domin kuwa dana na tura a halaka shi, shi ne nake so da ka turo min da bokayen nan guda biyu don su taimake ni mu kama wannan bokan domin ka tuna fa kai ne sarkin lardin nan gaba daya. Idan kabar wannan bokan har ya yi galaba a kai na to sauran manyan sarakunan duniya za su aibata ka da cewa duk fadi da karfin mulkinka wani boka guda daya ya gagareka”.
Da ta gama rubuta wasika ta baiwa bawan ta ce "Maza ka je ka shirya ka tafi garin Sarki Saifu'aradu ka kai masa wannan takardar, cikin daren bawan ya daura sirdi ya hau ya sulale ya fita ba tare-da kowa' ya ganshi ba ya kama hanyarsa ta zuwa Kasar Babban Sarki Saifu'aradu, kwanci ta shi har ya isa kasar da zuwansa bai zame ko ina ba sai fada. A ka yi masa iso ya fadi. gaban Sarki ya yi gaisuwa sannan ya mikawa Sarki wasikar Kamriyya, sarki ya bude ya karanta sannan aka karanta a fada kowa ya ji a nan sai Sarki ya ce "Kamriyya fa-ta yi gaskiya saboda babu shakka sauran sarakunan duniya sai su aibata ni a bisa wannan.
Sarki ya yi umarni ga bokayen nan guda biyu da Sakaradisa da Sakaradiyyuna da su sake komawa Yemen su taimaki Kamriyya su gama da Barnuhu. Sakaradisa ya duka gaban Sarki ya ce “Zahlu ta baka nasara zamu koma Yemen kamar yadda ka umarce mu lo amma fa mu ba za mu tafi mu biyu kawai ba saboda kuwa ba wai wannan bokan muke tsoro ba mu Sa'aduninzamji muke tsoro domin kuwa wancan zuwan da muka yi mun tarar da shi yana can”. Sarki ya ce “To yanzu me kuke so ayi muku?” Sakaradisa ya ce “Muna so cikin sadaukan ka ka bamu mutum dubu goma cikin su ka hada mana da manyan sadaukan nan naka guda biyu da Sabikussalasa da Hurulwashi, domin kaga idan muka je su su yaki Sa'aduninzamji da sauran jama'a, mu kuma mu yaki wannan bokan Barnuhu”. Sarki ya amsa ya ce zai hada su da su su tafi.
Sarki ya juya wajen Wazirinsa Baharu ya ce “Waziri da na san ka da yawan hikimomi da himma wajen ba ni shawara amma yaya kwana biyu bokayen nan kadai ke ba ni shawara”.Waziri Baharu ya cc “Ai da kana neman shawarata amma yanzu ba ka nema sai ta bokayén nan kawai, to ka ga kuwa ni da ba'a tambaye ni ba mai zan-ce aikawai sai dai na yi shiru”.
Jin wannan magana ta Waziri sai Sarki ya ce haba Waziri kada ka yi fushi amma yanzu mene shawararka a kan wannan lamari?"Waziri ya ce "Shawarata a nan ita ce ka sani dan fashi Sa'aduninzamji sadauki ne wanda babu kamarsa duk
lardin nan,wadannan sadaukai duk da yawansu ba za su iya kama shi ba”, Ko da Sarki ya ji wannan magana ta waziri sai ya yi tunani ya ce "Kai Waziri gaskiyarka Sa'aduninzamji shege ne, ba za su iya kama shi ba, to yanzu Waziri yaya za'a yi?” Waziri ya ce “Ya kai Sarki ka tuna da wani Sadaukin dan fashin nan mana mai suna Maimunulhinjab wanda yake dajin Asadu wanda shi kadai yake tare ayari ya yi musu fashi kuma sarakuna da dama sun aika da rundunar mayaka don su kama shi amma ya yi tumbe abin ya gagara. Ai wannan sadauki shi kadai zai iya kama Sa'aduninzamji”.
Ko da Sarki ya ji wannan magana ta Waziri sai ya ce "Kai babu shakka waziri ka yi gaskiya wannan magana taka haka takè,to amma yanzu yaya za'a yi muga shi wannan mutumin Maimunulhinjab har mu gaya masa wannan bukata tamu?”Waziri ya ce “Ai dabara a nan ita ce yanzu ka tashi manzanni ka base dukiya mai yawa su kai masa ka ce gata nan kyauta ce a gare shi ka gaya masa kuma kana so in ya yarda ya zo ya taimaka maka akan wata bukatarka ta ya kama maka wani mutum da ya buwayi sadaukanka kuma idan ya aikata haka zaka aura masa 'yarka kuma zaka Kara masa dukiya mai yawa,to na san babu shakka idan ya ji haka zai yarda ya zo mu tura shi”.
Sarki ya kar6i wannan shawara ya sa aka loda dukiya bisa dawaki sannan ya umarci bokayen nan guda biyu ya ce “To na san ba bu mai iya gudanar da wannan aiki sai ku, saboda haka yanzu ku tafi da wannan dukiya zuwa ga Maimunu kuma ku gaya masa kamar yadda Waziri ya fada". Nan da nan cikin rawar jiki bokayen nan suka hau suka tafi suna fargaba domin sun san ba'a ido hudu da Maimunu a ci gaba da rayuwa ba makawa sai an halaka, haka dai suka daure suka ci gaba da tafiya bisa ga umarnin Sarkinsu, bayan wasu 'yan kwanaki suka isa wannan dajin na Asadu.
Cikin dajin akwai wani katon dutse dogo wanda akansa ne Maimunuthinjab da yaransa su goma suke zaune. A wannan lokaci Maimunu yana zaune. Kai in ka ganshi ka ce mutum ne
a tsaye saboda girma, girmansa ya kai kamar zira'i arba'in ga fadin kirji da bakar fuska mai muni ga shi da farkeken goshi kamar kwarya, idanuwansa kuwa jajaye ga su manya kamar shacen katuwar kabewa ga shi da manyan damatsa kamar tulu,cikinsa kuma kato kamar ya sha ruwan tsari, ga kaftara-kaftaran kafafuwa kamar allo.
Maimunu yana zaune akan dutsne nan sai ya hango bokayen nan biyu tafe da dukiya, ko da ya hango su sai ya yi dariya ya ce a zuciyarsa ga ganima nan tafe” Ya mike tsaye kai ka ce wani kyami ne aka tsayar. Saboda girmansa kuwa baya hawa doki si giwa domin kuwa samun dokin da zai dauke shi...


Read / Download MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN Book 3

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album