Join Our WhatsApp Group

LADINGO NA MODIBO Complete Hausa Novel Document by LADINGO NA MODIBO


LADINGO NA MODIBO

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 42307LADINGO NA MODIBO

Reading Time: 3 Hours

Added On: 15, May 2024

Author: Shamsiya Adam ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08160375544, 07043185799

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 267.69 kb

File Type: txt

Views: 116+

Download: 106+

Last download: 2 hours ago

Description/Story: ο»Ώ"LADINGO NA MODIBBO " 2018
Bismillahir Rahmanir Raheem.
🌱🍯🌱🌱🍯🌱🐝🌱🌱🍯🌱🌱🍯🌱🌱🌱
🌱🍯🍯🍯🍯🌱🍯🌱🌱🍯🌱🌱🍯🌱🍯🌱

🌼🌱 by Shamsiyya adam 🌱🌼

'Yanmata ne uku sukajero kowacce da faranti akanta tafe suke suna hiransu kowacce tasha kwalliyarta da dige dige irin na 'yan kauye afuskansu daya gyadane akanta dayarkuma aya ta ukun kuma dakuwa, mai ayance tadubi abokan tafiyar tata bayan sun tsallaka titi tace
lami waikuwa kinsan 'yar bala in nan batada lafiya? harsuna hada baki wajen cewa ke haba LADINGO kike nufi , dariya tayi tana cewa eh yo inba itaba wacece ta damemu agarin nan,
wacce aka kira da lami ta yi dariya tanacewa shegiya aigwarana ta mutu kowa yahuta ,don wlh inabala in jin haushin LADINGO kiri kiri MODIBBO yakini ba wacce yake so kamar ta ,
indo wacce tundaa suka fara magana batace komaiba tace uhum aiko iya haushinta kukeji kawai nikuwa wlh ALLAH ALLAH nake muhadu nakamata nayimata dankaran duka,
ke metayi miki suka tambayeta
ta girgixa kai tana kallonsu , abindatayimun baxan mantaba ke ai lami ranan laraba naxo gidanku ko? lami tace eh
indo tacigaba, toh bayan bafito xani gidan su mairo ahanyana inatafiya kawai naji anjamin mayafi najuya banga kowaba saidana kara juyawa xantafi akatadeni goshina yadaki kasa ina daga kai naga ladingo tana kwasar dariya, kodanaje nafadama innanta hkri tabani batayi mata komaiba , dan haka wlh saina rama
cijan baki lami tai tana cewa aikubari mune maganinta agarin nan
mairo tagyara xaman gyadarta kwarai kuwa kawayena mukoya mata hankali inda baxata kara kuskuren shiga layinmiba agarin nan
tohm kuxo mukarasa kasan bishiyan can da muka saba xama lokaci natafiya
tare suka karasa tare da a a aje kayan kansa kowacce ta xauna kan takalminta,

ladingo ce kwance kankafar innanta sai xabga shagwaba take ,abinka da tabararre dama bare kuma batajin dadin jikinta, inna duk hankalinta yatashi takalleta "wayyo shalelena ince ko jikin ne? yamitse fuska take tana rirrike kanta ita ala dole xafin ciwo, dakyar ta daga kai tana cewa inna na kaina wayyo ni inna na xan mutu banga modibo ba, lallamata tashigayi tohh aixaki ganshi daxuma yaxo kina barchi nasan anjima xaidawo kinji , ahakan saidatayi murmushi tana sinke kai , inna toh ki taimaka kimun wanka karyadawo yaganni haka,
kallonta inna tayi cike da mamakin wannan soyayya ta ladingo da modibo tindata kwanta rashin lfyn nan batason wanka amma yau daknta take maganar wanka lallai abin babba ne,
inna ta ce
hum tohm amma kinsan jikinki har yanxu ba kwari ko?
turo baki tayi gaba tana cewa
nidai inna ba ruwanki da kwarin jikina kimin wankana kawai nidai kar modibo ba yaganni kaxama ,
murmushi inna tayi tana jinjina yarinta irin ta ladingo ,
tohm shikenan amma kinsan kwana uku kenan yanaxuwa dubaki bakyama cikin hayyacinki kuma ahaka yake ganinkin dakika dauka kaxanta,
aikafin inna ta rufe baki ladingo tafasa kuka harda tirjiya tana tashiga uku shikenan ita anvari modibo yaganta akaxanta , baffa dake daki yafito aa aa shalelena xo muji menene kike kuka 'yar babanta,?
dakyar ta iya jan jiki ta matsakusa da baffa tana kwantar dakanta ajikinsa saikuma wani sabon kuka,
dakyar ya lallasheta hartafara bacci ajikinsa yadauketa yakaita daki ya kwantar da ita,ana kiran mangaruba modibo yayi sallama gidansu ladingo, inna taimasa ixinin shigowa kan 'yar yaloluwar tabarman da dake shinfide tsakan gida gaisawa sukayi kasa yayi dakai irin abinda samarin kauye keyi yana wasa da gefen rigansa yace
inna ina ladingo yakuma jikin nata?
inna tashi tayi tana cewa
tana ciki barchi take amma bari naduba naga kota tashi,
toum yace yana murmushi xai ga abarkauna kwana biyu baiga ladingon nasaba, da gudunta tafado waje tana xubewa gabansa
laaa modibbo ahe da gaske kai din ne
shima dik yaware hakwaransa yana dariya
nine ladingo ta ai hankalina atashe yake tinda akacemin baki da lafiya kullun burina inxo inganki yajikin
sosa kanta tafarayi tana murmushi,
ni ai dama ban warkeba sai yanxu sabd naganka
dariya sukayi suduka modibbo nadaga kai yaga inna tana tsaye akofa danhaka da gudu yafita hannunsa abaki sbd kunya
kunjifa
baiji kunyar xuwa hargida ya tambayetaba sai kunyar taji shiransu, ladingo tatashi tana turabaki gaba takalli inna
"ni inna kinga ko kinkorar mani shiba
DaΖ™uwa inna taimata
"uwaki ladingo ke bakyajin kunyata,shito yanaji kingatashi kibani gu bisa wajen
tashi tayi tana xunburar baki gaba "xandawo ai wlh saina gayama baffana
"ku koreni karna kwana agidan,kinji 'yar banxar yarinya da iyayin tsiya
dariya tayi tana ficewa , tsaye tasamesa yana wasa da wani sanda ahannusa
"kai gaskiya naji kunyan inna
tayi dariya "saikuma ka gudu aibansan kafitoba fa "kinsan wani abu kuwa ?
"aa modibbo na saika fada yayi murmushi "inasonki dayawa dan allah karki taba barina ,
hararansa tayi "humm aikaima kasani duk wanda yacema nabarka yayi aikin banxane
yayi dariya "gaskiya nagode sosai dawannan kulawan dakikemani kwarai,
cikin shauki da farinciki masoyan suka yi firansu xuwa wani lokaci sukayi sallama da juna kowannesu yatafi,🌱🍯🌱🌱🍯🌱🐝🌱
🌱🍯🌱🌱🍯🌱🌱🌱
🌱🍯🍯🍯🍯🌱🍯🌱
🌱🍯🌱🌱🍯🌱🍯🌱
🌱🍯🌱🌱🍯🌱🍯🌱
🌼🌱 kunatare dani MATAR YAYA. aCikin littafina na ladingo na modibbo, makaranta inafatan wnnan littafi yanayimaka daΙ—i daΖ™ayatarwa, kucigaba da kasancewa dani insha Allahu mu assalama 🌱🌼

mahammad MODIBBO, shine babba awajen mahaifinsa saikannensa guda uku biyu mata sainamiji maibinsa, mahaifiyarsa inna marka macene maikirki da kyautatawa mutane nayaban halinta domin sambata da hayaniya, mahaufinsa malam buba danfulanine na asali,mahaifin buba shine sarkin rigan tasu mai suna mahammad modibbo tinkafin sarkin rigan yarasu malam buba damatansa tahaihu yasama dansa muhammada ake kiransa modibbo,donhaka yagaji wannan sunan kuma ake kiransa dashi ,wannan kenan
nawwara (ladingo) shine sunan ladingo na asali kuma tasamu sunan ladingo ne daga wajen masoyinta modibbo,domin haka ake kiransuma akarkaran LADINGO NA MODIBBO har sunan yabita mutanen karkarar ma haka suke kiranta da shi, ladingo 'ya awajen malam ibraheem itakadai suka haifa kuma awajen haihuwarta mahaifiyarta ta rasu, bakaramin gigita mlm ibraheem yayiba yayinda mutuwr tatabashi sosai shima yakwanta rashin lafiya ciwo yayi tsanani daga karshe shima yabi matarsa , yayin da rainon nawwara (ladingo )yakoma hannun kakanninta inna da baffa iyayen mahaifiyarta kenan, inna da baffa na son ladingo sosai shiyasa suke nunamata gata kuma basa son laifinta ko kadan, koda tsokana ladingo tayo basa bari adaketa, saida in abindaxa abiyane baffa yabiya in hakurine subada amma basa so ataba musu jikarsu,komai takeso ladingo iyakarfinsu sunayimata,dan haka ta taso cikin farincciki da walwalar rayuwa babu damuwa atare da ita ko babu,don haka take abindataga dama akauyen babu wata budurwa daxatadagawa ladingo hannu ta kyalle saita saukeshi kasa ,tana son rawa da waka don haka dik inda taji kida xata ruga wajen koda kwa tatafi makarantane saita aje jakar ta ruga wajen da ake bikin tashiga fili tachashe jakar makarantan kuwa saidai akawowa inna gida ace ba aga ladingo ba, haka xata fito har saita nemota tukunna sutafi gida, duk da randa taje deban ruwa sai ta barar dana 'yanmata dayawa kafin tadebo nata taho,kuma bamai binta tace xata rama domin yanxu takifa miki ruwan kanta takuma watsa miki yashi ta gudu ko ta kyaleki saikina xance adandali ta lallaba ta kwace miki mayafi ta gudu tana dariya,,
dan haka ansanta sosai akarkarar,sun hadu da modibbo ahanyarta tadawowa daga kasuwa dayake ranan ranan kasuwace kowacce budurwa burinta shine tachi kwalliya tashiga kasuwa siyesiye sbd wani lokacin har 'yan birni nashigowa siyayyan masarufi, don haka ladingo nadaga daga ciki, masu chaba wannan kwalliya ansha powder irin jarnan 'yar xaxxaga ,janbaki ja ankwabashi har yana hawrawa labban saijagira dataja da kwallin masoyi, tasa less dinta doguwar riga takawo mayafi tachi damara dashi , bayan dankwallin data daura mai santsi tafito "inna na shirya tsaf banikudin tsami gayen
inna dke dubanta samada kasa ta ce "oooo ni 'yasu yanxu ke nawwara da wannan shirmen xaki fita agidan nan?
tirjiya tafarayi tana turabaki "nini ni baruwanki da kwalliyata wlh kawai kibani,
"naji toh dame dame xaki siyo ,
dariya tayi tana gyara daurin damararta "yawwa ni tsami gaye xansiyo da dan tamatsitsi
salati inna tafarayi tana tafa hannayenta "yanxu ke dan jan dalilin yawo kawai kan wadannan kayan banxa da wofin xaki daukafa harkasuwar kaura ,
"ni ni toh nace xanje wlh kiban ko yanxu yanxu nafasa miki kuka wlh

inna tasan halin rigimarta yanxu ta hadata da baffa tarasa kanshi danhaka tadauko dari tadanka mata , dagudunta ta kwasa tana tsalle da murna
"ko kefa innata
tafiya take cikin farinciki tana wasa da gefen dankwallin kanta harta isa kasuwar bataja kowa dafadaba hartayo siyayyarta tajuyo hanya annan ne tahango wani saurayi tareda abokansa biyu saihira suke shikuma yayi shuru yana kallon mutanen dake shige da fice akasuwar dayake axaune suke akan benchi gefen wani runfa, itama takallesa kyakkawa dashi kamar badan kauyenba ya dan fita daban acikinsu harta fuskar nutsuwa ma, karaf idanuwan modibbo suka fada kan nawwara , baisan sanda yafashe da wata dariyaba har yana rufe bakinsa ,bakidaya yarinyar tabashi dariya yanayin yadda ta cika fuskarta da xane xane kamar baxatabar fili afuskarba, jallata yake yana nunawa abokan nasa "kai kuga wata ladingo can da allah kamar aljana,
suma me xasuyi inba dariyaba , bakinciki yacika nawwara tayo kansu tana masifa kafinta karaso tadau dutse tanaxuwa tabugawa modibbo akafa ta ruga kafarsa yarike yana juyawa awajen domin bakaramin dutse bane takwadamasa har targade yayi saida suka rakasa gyara, game da itakuwa dakyar taje gida sbd gudu sai haki take inna tai tambayar duniya amma taki tafadamata komai ,shi kuwa modibbo tunda yasata a idansa yaji yanasonta shi tayimasa domin ko abindayafaru yasan shine yajata amma duk da tacika fuskarta da kwalliya haka bai hanasa gano kyanta ba, don haka cikin karamin lokaci yanemo gidansu , atakaiche dai ranan dayafara kiranta bataxuwa guduwa take domin gani take kamar xairamane dahaka hartagane baramawa xaiba domin cikin gida yake shiga har wajen inna yace ina ladingon sa tace wacece haka yace "nawwara
tayi dariya aitafi kama da hakama yarinya sai shirme,
sunsaba sosai amma kafin tayarda da sunan ladingo anjima, ansa soyayyarsu sosai agarin na TSADA, domin basa boye kansu game da yadda suke son juna koda agaban waye,
WANNAN SHINE TUSHEN LABARIN LADINGO NA MODIBBO,ATAKAICE ,YANXU NE XAMU SHIGA CIKIN CIGABAN LABARI GADAN GADAN,MUJE XUWA TAKU ...AKULLUM (MATAR YAYA)
.yammacine maicike da sanyi da iska na karkadawa ko inaka kalla mutanene xaune karkashin bushiya suna shan iska ana hira,kamar yadda yaxamaa al adan mutanen karkara taruwa arufan maishayi anahira ko kasan bushiyo musamman lokacin xafi, inlokacin sanyine kuma ataro ahura wuta anajin dimi, ladingo ce hannunta rike da boket na roba tana tafiya domin isa rafi, wani matashi yakalli nakusa dashi "sani kaga waccan yarinya mara kunya tana tahowa ,
wanda akakira da sani yakarasa tashi "au ladingo wlh kamar kasan nemanta nake sbd na sanar da ita irin Ι—inbin Ζ™aunar danake mata
"kai wlh karkasoma tararta da wannan maganar domin ladingo na modibbo ne kawai kowa yasani akarkarar nan,bata sauraran kowa inkuma rabon kasha xagine saikaje don wlh masifar tsiwace da waccan yarinyar ,
hara rar manu sani yayi yana mikewa tare da kakkabe rigarsa yana gyara xaman kodaddiyar hularsa wacce taji jiki har xane yafara bata, "ko xata mareni yau saina bayyana mata sirrin xuciyana allah,
YamiΖ™e yana hararar manu tareda nufar ladingo
yanaganin takaraso wajensu tagifta yabi bayanta ,yana kara sauya taku irin dangayen nan itakam kodata lura dashi yanabinta ko dakallo bai ishetaba tindata hangosa bayanta take xabga tsaki yayin dayakaraso dai dai itasukajera yashagabanta tare da yajan birki "aa ladingo 'yanmata rafi xa ah,
taja tsaki tareda kauda kai gefe "toh idan rafi xani saime? Takai maganar tana farida ido
"ah haba ladingo babukomai rakiya daikawai xanyi kawo bokitin,
janye bokitin tayi tana hararansa ta jallasa da yatsa "kaga sani kasan wacece nikuwa? toh nice nawwara ladingo budurwan modibbo jikan muhammad sarkin rugannan donhaka ka kiyayeni,
dariya yayi har da tafa hannu "toh menene soyayyace ai kowa yayi takansa wanda ya iya ruwa yafidda kansa shine kawai ladingon sani , yakarasa maganar yana gyara tattarewwar rigarsa dakarka de kurar dake jikinta sbd kwance yake awajendaya taso yatadakansa da takalmi, bakinsa kwa duk hakwaran sinja saboda sani akauyenma gaskiya shikaxamin gaskene bayakuladakansa, jatayi baya tana dage hanchi tare da yayyarfa hannu,"kaga ni kadaina kadamani datti malam maye haka
dariya yasakeyi akaro nabiyu " yi hakuri yi hakuri ai akwance nake cikin su manu,dana hangoki nataso sbd baxan iyabarin abindake damuna yamin lahaniba ladingo ki amshi tayin......
TaΙ—agamasa hannu
"kaga ka kama kanka,tin wuri sani karka soma ma yin takara da modibbo domin inkai kokarin yin haka toh ba inda gwabnatin ka xataje, kuma wlh kasake bina saina watsamaka yashi awannan mummunan fuskar naka,
tajuya tana rausaya tafice sororo sani yatsaya baki nayi hanchi nayi ido nayi kallon ladingo dariyar su manu da sauran samarin wajen shine yadawo dashi hayyachinsa, yana yin kwafa "kai wlh badan tayi saurin barin wajen nan saina babballata wlh,
suka kara kwashewa da dariya "kadai ka bari kawai amma aiba abindaban fadamakaba akan yarinyar can kaki ,yaciji lebe "wai harni take gayamawa mai mummunan fuska, ,
suka kara sa dariya manu kuwa harda tintsirawa yana buga kafa dan tani dake gabxar rake yace "haba kaima sani wlh da wani abu kake yaxaka dubi ladingo yarinyar yar gayu ga iya kwalliya,duk karkarar nan bamaitsaftar yarinyar nan kyakkykwa da ita haba malam kadubi jibeka dubeka da allah,dubi gwiwar wandonka wani dauda kalla rigarka duk ta tattre amma kaje wajen ladingo haba,,,
sani iya hasala yahasala yayi kan dantani yana kamo kwalar rigarsa,"saikasan kaci mutumchina wlh dantani,munafiki kawai kai kaf cikin kauyennan waye baisan wadannan kayan nawa nagadobane tin na babanane kafin yarasu,amma kai saboda bakinciki da munafinchi dama kasamusu ido sukake rainawa toh kai mai naka yabarmaka, kamar wannan din?
dantani yacakumi sani sai kokawa takaure atsakaninsu,"xancan banxa nixaka kalla ka kira munafiki kamanta abindakake akauyen nan duk inda gulmatake saika dauko ka kawo,toh kaxo muxagayamana baya kaga yadda xanmaidakai,banza dan saniya kawai, sani duka yakaimasa iyakarfinsa yayinda dantani yacukuikuyi sani,saikokawa takuma kaurewa dandanan mutanen dake gurin suka shiga basu hakuri anarabu amma dakyar akarabasu inda kowanne daga cikinsu yake xagin dan uwansa daga karshe sai kwasarsu akayi domin aje wajen maigari daganan suka dunguma sai wajen maigari,
game da ladingo kuwa gidansu modibbo taxarce tana aika yaro yakiramatashi ba ajimaba saigasa yafito cikin tafiyansa maicike da nutsuwa tundaya hangota yake fadada murmushinsa har yakaraso inda take atsaye tana wasa da bokitin dakehannunta, "rafi xaki ne
Tasaki murmushi
"eh inaso xan wanki ne anjima shiyasa nace bari nabiyo maka muje muΙ—ebo ruwa tare
tattare hannun rigansa yayi yana mika hannu ya amshi bokitin
"tohm muje narakaki gida ni xandebo maki ruwan kihuta kinji sarauniyar Ζ™yau tanoke kafadarta
"aa modibbo na muje tare kawai banaso nahuta alokacin dakake cikin aiki yakamata naΖ™ara kulawata akanka sosai
yayi murmushi irin wanda takeso taga yayi din nan
"ladingo kenan nasan kina tausayina ai kuma nagode muje lokaci naja yamma kuma shigowa yake,, "umhm muje
tare suka jera suna hira sai murmushi suke, abin gwanin sha awa,...


Read / Download LADINGO NA MODIBO

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album