Join Our WhatsApp Group

MATATACE Complete Hausa Novel Document by MATATACE


MATATACE

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 168576



MATATACE

Reading Time: 14 Hours

Added On: 31, Oct 2023

Author: Meemartjj ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 953.09 kb

File Type: txt

Views: 806+

Download: 1088+

Last download: 13 hours ago

Description/Story: [14/08, 14:28] Dala Grp: 🕯🕯🕯
            _*MATATACE*_
     🕯🕯🕯

     

story&written by Haleematu💕meemartjj💕

   *Dedicated to lovely sisters*
_Jameela ja'afar yakubu_
_Fateema ja'afar yakubu_
_Fa'iza ja'afar yakubu_

   _Godiya_

   _*DUkkan yabo su tabata ga Allah, wanda ya bani daman rubuta wannan littafi, ubangiji Allah yasa a amfanu dashi a fadaku dashi, fiye da komai, kuskuren da xanyi kuma, Allah ka yafe mun, Ameen ya Allah*_

    _Tunatarwa_

    _*A rika amfani da abin da ake nuni shine mai kyau, kaima kaga ya dace kabi, bisa hanya madaidaciya, plss a watsar da marasa kyaun ciki, a ije karatu lokutan ibada, makaranta, da ayyuka masu muhimmaci, tnx*_

   _Gargadi_
   _*Ban yarda wani ya juya mun labari ta ko ina ba, plss a kiyaye.......✍🏻meemartjj💕*_

   _jinjina na musamman *sist Dala,* hakika ba abin da za muce, sai Allah ya saka miki da alkhairi......daga taki haleematu sa'adiya._


Da sunan Allah mai Rahma mai jin Kai


_*Page 1&2*_

――――Tun daga saman stairs take kwallo da ita, ta mirgino ta fado bisa tyles din dake falon, kadan ya rage kanta bai bugu da karfen stairs din ba, cike da razana ta kauda kan nata, wanda yayi sanadiyar haduwan bakinta da stairs din karshe, duk da wannan bai hana ummeeta mikewa ba a gigice, bakinta na fidda jini, tare da ja da baya, tana wani irin kuka macin rai take fadin,,,

  aunty suhymah don Allah kiyi hakuri bazan kara, don Allah na rokeki, na tuba bazan karaba, wani irin dogon tsaki taja tana sakkowa down stairs din, har wani tukukin huci na zalunci takeyi, tare da nufa wajen socket tana zaro wani wayan caji mai kaurin gaske, wannan ne ya sanya ummeetah kara kidimewa tare da gigita, tana saka wani sabon kukan, don tasan yau a gidan mai ceton ta sai Allah, gadan gadan tayo kanta tana fadin,,,

  yau saina illataki mai sosai, ban taba miki dukan daya sumar dake ba ko?zan tabbatar dan tuna miki da matsayinki a gidan nan, ta daga bulalan kenan aka danna door bell din dake kofan shigowa, ta saki ajiyar zuciya, tana yarda wayan nan, tare da nufa kofa don ta duba ko waye, mainat ce tsaye bakin kofan tasha rolling da farin gyale, sai blushing takeyi, alamar taji dadin zuwa gidan, itama suhymah cike da murna take bude kofan da fadin,,,

   oyoyo yer halas, sai yau nake ganinki koh?tana walwala da farin ciki take karisowa ciki, amma sai me, annurin dake fuskantane ya dauke, ranta kuma ya baci, sanda tausayin yarinyar kebin jini da tsoka na jikinta, ta rasa ko yaushe suhymah zata daina ganawa yarinyar azaba, itama ummeetah rage sautin kukanta tayi tana bin mainat da kallo, tasan koba komai, Allah ya kawo mai taimakonta, ta wani hada fuska tana kallon inda ummeetah take da fadin,,,

    banxa, jaka, bace mun da gani useless girl, da sauri tabar falon tai wani dan corridor inda tayi hanyar daxai kaita kitchen daga nan ta futa backyard din gidan,,,

  mainat ta dubi suhymah da wani dacin zuciya take fadin,,,

  sist what's going on, me yake damun kine har yanxun, har yaushe zaki daina zaluntawa yarinyan nan, yaushe ne zaki sanja halin nan, wani murmushi ko in kula tayi tana fadin,,,

  pls sist have a seat, ki zauna ki huta kafun muje ga wannan zancan, mainat taji kaman hawaye zai zubo mata tana fadin,,,

  ina miki magana mai muhimmaci kina maganan in zauna, cikin kasaita take zama daya daga cikin mayan kujerun da suke falon, tare da daukan trow pillow tana  rungumewa, ta daura kafa daya kan daya, tana girgixawa da kallon mainat take fadin,,,

  hmmm dadina dake mainat rashin ganewa, amman ina son ki sani, nan gida nane, gidan mijina, zanyi abin da nake so, kuma abin dana gadama, da komai dake cikin gidan, ta yamutsa farin fuskanta da fadin,,,

  kie gane mana, na gaba fa yayi gaba, na baya sai labari, kuma abin da kika gani a yau ba komai bane akan na kullum, da sauri cikin zafin murya mainat ke fadin,,,

  sist what nonsense are yhu saying, ummeetah fa yarinya ce, she is just 13years old, har yashe ne zaki daina mal treating dinta, itama fa mutum ne kaman kow...... zaraf ta mike da wani irin tsawa take fadin,,,

  No!never, ummeetah ba kaman kowa take ba, akwai mutane daban daban a cikin duniyar nan, kuma ita tana cikin mafi kaskantantune, ma rasa usuli, ma rasa galihu, har abada ummeetah ba zata taba zama dai dai da niba, never ever in ithis life, da sauri mainat ke fadin,,,

  why can't she, kin mant.....

   da Allah malama dakata mun, taja tsaki kafun ta cigaba da fadin,,,

  mainat kin manta matsayina kenan, tayi shiru tare dayin wata yer dariya, tana cigaba da fadin,,,

  nie suhymah ina auran mijin da yake da company har biyu, sannan yana da strong shares, a companyn da kowa yasan da ita, cikin birninUSA, gidajen gonaki, ke da dai sauran su, duk cikin zuri'ar mahaifinku kunsan dashi kuke takama, sannan kixo kina hadani da wannan banxan who didn't even have a real family, mainat karki mantafa dad dina ministerne na kudi, and what about my mum, she is a professor, and my aunt, manager director, a daya daga cikin  companyn mijina, and what about this rascal...... da sauri mainat ke dakatar da ita da fadin,,,

  enough, ya isa haka, na lura lamarin naki kullum dada gaba yake, to bari na tuna miki wani abu, shin kin manta da wanda ya halicce mune, mai maida yini ya koma dare, mai jujjuya al-amura, ya maida matalauci ya koma mawadaci, in yaso kuma ya maida mawadaci ya koma matalauci, yaushe kika manta da dukkan wadaddan abubbuwan, when?wani kallon raini wayyau tayi mata, kafun tace,,,

   nice explanation, nie kike nuna ma bansan religion dina ba, thanks, amman inaso ki sani, irin su ummeetah haka suke girma cikin bauta, sannan su tsufa a bauta, kai ko sun koma village dinsu sunyi aure, sai sun kasoshi sun dawo, ta tako har gaban mainat murya kasa kasa take fadin,,,

  kinsan me yasa? saboda kwadayin abin duniyansu, da rashin zuciya irin nasu, kema kin sani mainat, sai dai ki boye gaskiya, amman gasu nan a gidanku, tsofaffine amman har yau su suke muku a''iki, kuma ba yanxun suka fara ba, tasowa ki kayi kika gansu, ke wasu ko shelter harsu mutu basu dashi, dole sai sunyi a'iki zasu samu inda zasu zauna, so as for ur information, ta numfasa da fadin,,,

    ina son kisan cewa nie suhymah na tsani house maids, ke koma menene, na tsani masu a'iki, munafukaine, abin da suka iya kenan, nasan haryau baki manta da abin da yer a'iki tayi ma rayuwa nah ba, dana iyayena, duk akan yer a'iki, don haka na fada na kuma kara fada miki, kadan kika gani akan ummeetah, and last warning daxan miki, shine, karki kara zuwa mun gida kie shiga harkan nida house maid dina, mai a'ikine kuma haka zata dauwama abadan da'iman din rayuwanta, jiki a sanyaye da hawayen daya sakko bisa kuncin mainat take fadin,,,

  yanxun laifin tane, don taxo a yer a'iki, cikin tsawa kamar wata mahaukaciya take fadin,,,

  what ever, nadai fada miki, house girl dai ba wanda ya kawo mun, mijina yaje musamman ya samomun don karni matarsa na wahala, don haka zaki iya tafiya in kin gama insulting dina, ta juya tai saman upstairs din fuww, hartai taku biyu, taja ta tsaya tana juyowa da fadin,,,

     nagode Allah, kwanan nan, zamu bar kasan, sai inga mai zuwa har inda nake, ana bata mun rai, sannan zaki iya kulle mun gidan da kyau inkin futa, daga haka tayi upstairs ranta bace da kalaman mainat, share hawayenta mainat tayi tana futa ranta bace, da ayyana,,,

  lallai ya kamata ta dakatar da tafiyan da zasuyi da ummeetah, inba haka ba, tabbas suka tafi sai ummeetah ta zama gawayi, a nan ma kenan, bare wani nisan duniya, da wannan ta shiga motarta, mai gadi ya bude mata gate, tana barin gidan.  


Ta rika kaiwa tana dawowa tsakar dakin, ranta ya baci matuka da kalaman mainat, ta futo sanye da wani doguwar mai tsada, amman kirjin nan a shafe, hakama kasan babu wani abin azziki, gadai girman jiki har jikin, amman fa babu diri, tun daga kitchen take faman kwalla kiran,,,

  ummeetah!ummeetah!yarinyar dake bakin fanfo tana wanki ta witsulo da sauri tana karisawo sukai karo bakin entrance din kitchen din, ta wani wanketa da mari, a rude taja baya tana dafe kumatunta da dukar da kanta, cikin zafin murya take fadin,,,

    kije site dina kie kwaso bedshee..... no barshi ma, kinga cikin ranan can, can zakije kie kama kunninki, babu lunch tsakanina dake a gidan nan, yer iska kawai, baku iya komai ba, sai munafunci da haddasa fitina, wuce nace!da sauri tayi baya tana nufa inda rana ta fara kwallowa ta kama kunninta, babu hawaye a idanunta, inda sabo ta saba, sai dai dafin yana cikin zuciyarta, marainiya irinta a haka zata kare, sai kuma daga baya hawaye zai zubo kuncinta da fadin,,,

    Affah nah, zata rika zubar hawaye, tana tuna mahaifinta.



                       *****

Wurin karfe 8:30pm, driver yayi packing din motar a haraban gidan, tare da futowa yana bude ma mai gidan nashi kofan baya, wanda ya ziraro kafansa waje, wanda ke cikin black cover, ya futo rike da briefcase tare da black suit rataye a hannun, ya rage jikinsa daga shi sai wani tsadaddan blue shirt mai long slip din hannu, wanda yaji toking da wani tsadaddan belt a black trouser din, driver na fadin,,,

  barka da dawowa yallabai, ya dan daga kai fuska ba annuri da daddan muryansa yake dadin,,,

  yawwa, mal.nura, barkan mu, kai a kasa yake mika mishi ledojin daya ciro mai na galaxy mall a bayan both, ya amsa lokacin da yake nufa cikin gidan a gajiye, dai dai sanda take sakkowa down stairs, da wani murmushin farin ciki, yana danna door bell din, tana bude kofan,,,

   ido kawai ya zuba mata kyakyawan shigarta yana daukan idanunsa, ya koma kaman wani mutum mutumi, tana sanye cikin wani yellow skinny vest, da black mini skirt, tayi packing din gashinta mai dan tsawo babu cika da yellow band, ta saka dangling earring, sai wet lips din dake faman spackling, ta juya jikinta, tare da juyowa tana kashe mishi ido daya, kafun ta shige jikinsa tana rungumesa da fadin,,,

  welcum my bby boo, ta dan juma kwance a hot chest dinshi, wanda shi kawai tsaye yake komai ya kwace mai, ta sassauta rikon da tayi mai tana dagowa da amsan ledojin dake hannunsa, cikin farin ciki yakai mata wani hot kiss a gefen kumatu, tare da sakalo hannunsa ta kugunta yana rufo kofan  suka shige ciki.

  Wanka yayi yana shiryawa cikin wasu classy pyjamas, ya shirya komai need, yana kallon dakin daya kawatu da wuta lantarki, shima tsaf tsaf, ya kashe wutan dakin, yana kunna bedside lamp, bisa wata design white sofa, dake hade da wani glass table a gefe, ya harde kafa daya bisa daya, yana jawo remote, tare da kunna TVn dake daga can gefe jikin bango, yana kamo chanel din NTAi, don kallon labarun 9pm,,,

  ya lumshe idonsa a hankali, tare da saka yen yatsunsa yana shafar fine sashen dake gefen chocolate face dinshi, da alamu akwai abin da yake so, yafi 5minutes a haka, kafun ya budo ido yana kallon bakin kofa, yai dan tsaki da jawo ledojin daya shigo dasu, wanda ta zube a nan, dai dai nan ta shigo cikin wasu arnan night gown, wanda ya tsaya dai dai cinya, ba abin da ba'a gani, ya hadiye wani miyau da raya,,,

  inama bodyn nan, ina samun abin da nake so yanda ya kamata, tuni ya saki ledan yana faman kallonta, ta zauna gefensa da sakalo hannunta ta saman kafadansa, tana dada manna kirjinta a jikinsa, ya dan runtse ido, sanda yake jin wani yarr a jikinsa, ta sassauta mishi, da zuba yatsunta bisa sajen fuskanshi dake burgeta a rayuwanta, take shafawa da fadin,,,

  my bby boo, ba kayi dinnern kaba, yai dan tsaki yana fadin,,,

  bayan kinyi naki kin barni, tayaya zan iya cin wani abu, cikin wani lankwasan murya take fadin,,,

  haba boo nah, kar kayi ma kanka hora da yunwa, bana son kana fadan haka, plss have ur dinner, ta karisa maganan cike da nuna damuwa, yer murmushi yayi daya zama key din zuciyarta, tana matukar son murmushinsa, yana fadin,,,

   angel karki damu kinsa nie ba wani ma'abocin cin abincin dare bane, so ki bani plate, na taho da best snack dina, sai ki tayani cie, da murmushi ta mike tana lalankwasa jiki ta futa, sai gata ta dawo dauke da yer design plate da fork, nan ta zube bisa handle table din dake jikin sofan, cake ne hade da maltmilk, suka ci suka shayar da junan su, kafun su kammala, yana goge bakinsa da wata yer tissue yake fadin,,,

  Alhamdulillah, ya kishingida da kujera, yayin data daura kanta bisa kirjinsa, ya maida hannayensa a bayanta, yana kuma rungumota, lokacin daya fara yin wasu abun da suke dada fidda shi hayyacinsa, tsam ta rike hannunsa a kirjinta, kafun ta dan dago tana kallonsa, tare da yarfa hannunta bisa sumar kanshi mai tsantsi da laushi, tare da kamshi na musamman, tana wani tafiyar tsutsa da yatsunta, burinta kenan ita tayi yanda take so, amman bata san wani ya biya bukatun saba, can ta dan nisa da fadin,,,

   my boo ya office, hope lfy, yadan matseta da fadin,,,

  lfy ba lfy ba, yhu know why? girgixa kai tayi, ya numfasa da fadin,,,

  bcos each moment without yhu close to me, it very difficult, ta saki murmushi da fadin,,,

  me too, especially da yau aka xo har gida aka bata mun rai, my boo i feel like crying, missing yhu too muchchch, ya dan saketa da bata wani serious look yake fadin,,,

  meya faru, waye ya bata miki rai?ta dan daga tana zama da kyau rai bace take fadin,,,

   kasan ma ko wacece zata a'ikata hakan, kullum taxo sai munyi rigima akan abin da yake un important, my boo plss nidai ina son kayi ma mainat last warning, indai ba xata daina xuwa gida naba tana making trouble, just bcos of that useless girl ba, to ta daina xuwa, bata xoba bare raina ya baci, nata ma ya baci, ya dago daga kishingidan da yayi, da idanun da suka kankance da bacin rai, yana furta kalaman,,,

  mainat again, ta maida kanta bisa kafadansa, tare dasa hannunta daya, tana dafe hannunsa dake bisa gwiwansa, tana dan murzawa a hankali, idanunta sun sanja kala zuwa ja, take fadin,,,

    boo karka damu fa, inda sabo na saba da halin mainat, kawai dai this time, inason ka manta last warning, saboda bana son muna samun wani sabani a tsakanin mu,...


Read / Download MATATACE

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album