Join Our WhatsApp Group

BASHEER Complete Hausa Novel Document by BASHEER


BASHEER

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 21752BASHEER

Reading Time: 1 Hours

Added On: 25, Apr 2024

Author: Mrs Sadauki ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : +22795045822

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 106.91 kb

File Type: txt

Views: 269+

Download: 192+

Last download: 2 days ago

Description/Story: [07/10 à 09:24] MRS SADAUKI 💫: *BASHEER...*🌼*PAGE 1_2*


Ƙarfe sha biyu na dare agogon hannunsa ta nuna wacce tsabar tsufa yasa ba'a ka iya tantance kalar ta.
Kwanciyarsa ya gyara ya na mai tallabe haɓar sa mai ɗauke da ƙasumba dusu-dusu,jajayen idonsa masu cike da sha'awa ya fara lumshewa sai dai sam barcin ya gagara ɗaukarsa.
A sannu ya fara sauke ajiyar zuciya ya na sa'ilin da yake tabi'a mafi muni wacce Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yayi nuni da haramcinta wato istimina'i.
Tsawon lokaci ya na masturber kansa kafin ya samu nutsuwa marar amfani, nan take ya ji wata irin nadama ta saukar masa wacce ita ma ba ta da amfani.Wanka ya ke son yi amma sanyi da ya luluɓe garin ba zai basa dama ba wannan yasa sai da asuba ya daure yayi wankan.Ya na fitowa daga banɗaki hannunsa riƙe da bokiti hasken fitilar Inna ya haskesa,kamar wani munafuki haka ya saki bokitin ƙasa kafin murya na ɗan rawa yace "Inna har kin tashi?yanzu ne ma ake kiran assalatu" Innar ba tace komai ba,ta koma ɗaki shi kuwa Basheer jiki ba ƙwari ya cika buta ya soma alwala kafin ya tafi masjid.Lokacin da ya dawo gida tuni gari yayi haske ,zaune ya tarar da Inna kan sallaya ta na jan casbi.Bisa tsohon bancin da ke aje a falon ya zauna,Inna ta dube shi yayi saurin sauko wa ya na mai cewa "ina kwana Inna kin tashi lafiya?" "Alhamdullah !"ta amsa masa a takaice kafin ta kawar da kai sai ƙara haɗe fuska take.
Basheer ya ja doguwar ajiyar zuciya yace "Inna ki yi haƙuri"ba tare da ta dube shi ba ta tambaye shi "da aka yi mi fah?"ya sosa ƙeya yace "da kike fushi da ni" ta girgiza kai kafin ta juyo ta kallesa tace "Basiru duk abin da mutum yayi Allah na ganinsa,sannan bai haramtawa ɗan Adam abu ba har sai ya kawo masa halalcin sa.Ba zargin ka nake ba amma ka ji tsoron Allah,ka yawaita yin azumi"
Basheer ya sunne kai tun da ya ke bai taɓa jin nauyin Inna ba in ba yau ba,duk da a baya ta na yawan yi masa jirwaye mai kamar wanka na dangane da tabi'arsa wacce kusan kullum sai yayi wanka kafin sallar asuba wani sa'in kuma har wasu sallolin muddin ya kaɗaice shi ɗaya a ɗaki.
Ganin bai da niyyar tashi yasa Inna ta miƙe ta shiga ɗaya daga cikin ɗakunan biyu da ke jere da juna,ya bi bayanta da kallo ya na jin tausayin ta tabbas da ace Inna na da kuɗi da tuni ta yi masa aure.
*Basheer Amadu* shine cikakken sunan shi,matashin yaro ɗan shekaru talatin da biyu a duniya.Ya kasance baƙi ƙirin mai yawan ƙasumba haɗi da gargasar ƙirji,dogo ne marar jiki amma ya na da cikar zati.Rashin kuɗi shi ya ɓoye sihirtacen kyawunsa sai kuma ya ƙara rinar masa da fata, Basheer ya kasance Mutum mai riƙo da addini ya hardace Alƙur'ani mai girma sai dai duk da wannan Allah ya jarabce shi da muguwar sha'awa wacce ba ta da lokacin taso masa ko a wane irin yanayi zuwar masa ta ke musamman in ya na cikin kaɗaici.
Tun kafin yayi wayo mahaifinsa ya rasu wannan yasa kulawarsa ta dawo a hannun Inna kaɗai wacce rashin ƙwaƙwara sana'a yasa ta kasa ci gaba da biya ma Basheer kuɗin makarantar boko,na islamar ma a Maiduguri yayi shi inda yayi yawon almajiranci wannan kenan.
"Basiru ?Basiru?tashi maza rana ta yi amma sai barci kake koko yau ɗin ma ba za ka je kasuwa ba?"Inna ke faɗa yayin da hannunta ke ɗauke da ƙaramin kofi cike da kunu.
Sai da yayi miƙa kafin ya fita,gawayi ya samu ya wanke bakinsa kafin ya wanke jiki ya zo ya karɓi kunun ya shanye .
"Yau kasuwa ce fah ko ka manta?" Inna ta sake tambaya,Basheer ya girgiza kai yace "na sani Inna yanzu zan tafi"cikin jin haushi Inna tace "shine kuma kake a zaune?" Ya dubeta da sauri karon farko kenan da ta ɗaga murya a kansa.
"Sai ƙarfe goma motocin ke zowa fah Inna ,yanzu ko na tafi zaman jira ne zan yi" Basheer ya faɗa a shagwaɓe kamar zai yi kuka Inna ta haɗe rai ba tace komai ba,a doli ya fita ya nufi babbar kasuwa ta Maradi.


Tafiyar minti asharin ta kawo shi,direct inda motocin dankali suka parker ya nufa da alamu isowar su kenan.
Da abokan aikinsa ya gaisa kafin su fara jidar buhuhuwan dankali su na shiga da su can cikin kasuwa,haka Basheer ke duƙawa a ɗora masa ƙaton buhun dankali a baya ya na zufa da fitar da hucin wahala.
Tun ƙarfe goma har sha biyu na rana ya gota aikin kenan,bayan sun gama Alhaji wanda ya kasance uban gidansu ya sallami kowa.
Innuwa Basheer ya samu ya zauna,ruwan sanyi ya fara zuba ma kansa ya ji daɗi.
Badiya wacce tun ɗazu ta ke kallonsa ta ɗauki robar abinci ta zuba shinkafa da wake kafin ta kai masa,yayi murmushi ya karɓa yace "wannan na nawa ne?na ga kamar ya fi na kullum yawa to ni 300 zan baki yarinya" yadda ya ke magana ƙirjinsa na ɗagawa haɗi da buɗewa ta ke kallo kafin tace "a'a yau na kyauta ne dama ban taɓa yi ma alkhairi ba a matsayin ka na Yayana"
Basheer wanda ya cika baki da lomar farko ya zaro manyan idonsa ya na kallon Badiya wacce tuni ta juya ta koma inda ta ke sana'ar ta.Bayan ya ci ya ƙoshi ya kai mata robar ta,sai da yayi godiya kafin ya wuce shagon wani abokinsa da ke cikin kasuwa."Ango ka sha ƙamshi" Basheer ya faɗa lokacin da ya isa shagon ya na mai zama akan kujerar roba,Lawan ya ɗan haɗe rai yace "ba wani ango kai da har yanzu ka ƙi zuwa cin abincin amarya"
Basheer ya murmusa yace "har ku gama cin amarci zan je in shaa Allahu, Allah sa dai ƙanwata ba ta yi fushi ba" Lawan ya sauke ajiyar zuciya yace "ƙanwar ka ko raguwa " Basheer ya kece da dariya yace "mugu! Halan cutar ta kake?" Lawan yayi masa hararar wasa yace "yau wajen 2week fah da auren amman bai wuce sau biyar ba da na kusanceta"
"Banda ƙarya abokina sau biyar fah?"
"Ai sai ka yi! Ta cika sangarta da zarar ta gan ni ma wani sa'in sai ta fara koke-koke doli na ƙyale ta"
Basheer ya ja tsuki yace "kaji banza!to a hakan ta yaya za ta saba?kace kawai laifin ka ne, billahil azim da ni ne toshe kunnuwa na zan yi na kwashi galima" dundu ya kai masa a baya kafin yace "auren soyayya mu ka yi ai,sam ban iya supporter kukanta yanzu dai gaya min ya zan yi?"


"Kawai ka bar ganin tausayinta in ta na kuka ka sa tayi mai mafari ka gurji amarcin ka malam,a haka za ta saba"cewar Basheer ya na mai jawo asusun da ya ke ajiyar kuɗinsa.
Lawan yace "to shikenan zan gwada yin hakan,ya ne da kuɗin za ka tafi?" Basheer ya gyaɗa kai yace "eh Inna tace na zo da su"nan suka ci gaba da hira kafin Basheer ɗin ya dawo gida.A tsakar falo Inna ta baje kuɗin ta na lissafawa yayin da Basheer ke cin ƙanzo wanda Inna ta gyara ta saka mai da magi da albasa.
"Kuɗin jika ɗari biyu da goma ne sai wannan ƴan canjin"cewar Inna bayan ta gama lissafi,sai da ya sha ruwa sannan yace "ga kuma 7000f nan wacce na samo yau" Inna ta karɓa tace "to yanzu ya za'a yi ina son a kai kuɗin auren ka ne"wani irin tari ne Basheer ya shiga yi sam bai yi zaton haka daga Inna ba.


*In na ga comment zan cigaba in shaa Allah*
[07/10 à 09:25] MRS SADAUKI 💫: *BASHEER ...*🌼

*PAGE 3_4*


"Miye kuma na tari?to ni dai na riga na gama yanke hukunci.Ka ga dubu ɗari na sadaki sauran kuma sai a tsara yadda za'a yi da su" Inna ta faɗa ta na mai kallon Basheer wanda yayi suman zaune.
"Inna to ni ina na ga budurwa?dan Allah ki bar wannan zancen don ba yanzu zan yi aure ba sai na tara kuɗi sosai yadda kowa zai yaba " Inna ta girgiza kai tace "ta yaro kyau ta ke ba ta ƙarko!To in ba abun ka ba Basiru kai da ke talaka ina ruwan ka da wani tara mutane balle su yaba,sannan maganar budurwa kuma ga Badiya nan ƴar gidan Iya mai wake tunda dama ta jima ta na sonka"
Basheer ya gyara zama yace "haba Inna duka-duka Badiya nawa ta ke?ba ta wuce 19years ba da ita ɗin ce za'a min aure?maganar kuma ta na sona a'a ƙauna ce sam babu zancen soyayya"
Inna ta kwaɗa masa kofin roba a kai tace "in an kai kuɗin auren ka je ka karɓo,yarinyar da kullum sai ta kawo min abinci kawai dan jan ra'ayin ka in ba ma jiya da na bata shawarar kai ya kamata ta bai wa ba ni ba" sake da baki ya ke kallon Inna kafin yace "au !dama wake da shinkafar da ta ban yau ba na tsakani da Allah ba ne?hum!to ni dai ban son ta "ya na gama faɗa ya miƙe ya nufi ɗakinsa Inna kuwa ta take masa baya."Kirawo min Kawun ka ina son yin magana da shi"Inna ta faɗa cikin bayar da umarni, Basheer ya kumbure fuska ya ciro Nokia wayar sa daga caji yayi ƴan danne-danne kafin ya miƙa ma Inna,ana ɗaga kiran ta bar gun.
Shi kuwa zagayen ɗakin ya fara ya na tunanin rummacen mahaukaciyar da Inna ke shirin yi,ta yaya ma Badiya za ta iya ɗauke nauyin
sa?Yarinyar da a gaban shi aka haifeta ita ce zai haɗa shimfiɗa da ita?


A fili ya ja tsuki kafin ya cire rigar sa ya saka jallabiya,fitowa yayi ya cika bokiti da ruwa ya shiga banɗaki.Ɗan tunanin auren da ya shigo masa a rai tuni yasa hankalinsa tashi .
An ɗauki lokaci sosai kafin ya samu nutsuwa,sai kuma ya fara wankan Tsarki a gaggauce jin Inna na ƙwala masa kira.
Sam ruwan basu ishe shi yin na sabulu ba hakan yasa ya wanke soson wankan dan kar Inna ta zarge shi.Ya na fitowa kuwa Inna ta ƙure sa da ido dan kuwa sun fi minti talatin su na waya da Kawu wanda ya kirata bayan kuɗin wayar Basheer sun ƙare.
Cikin rana ya aje kwandon sabulun ya na mai ɗan jingina shi nan ruwan soson suka shiga tsiyaya,yayi fuska dan kar ma ya ya bada ƙofar zargi.
"Har kun gama wayar?"ya tambaya ya na mai aje bokitin "eh mun gama yace zuwa jibi zai zo in shaa Allah a yi komai a gama"cewar Inna ta miƙa masa wayarsa.
Ya duba yace "Inna duk kin canye kuɗin wayar ma ko?"ta taɓe baki tace "wa za ka kira da su kai da ba ka da budurwa?"bai ce komi ba ya shige ɗaki.
Bayan kwana biyu Kawu Laminu ya zo,wanda ya kasance Ƙanen mahaifin Basheer .Sosai ya yi wa Basheer faɗa kafin ya ƙara da "duk abin da ka ga mahaifiyar ka na yi saboda goben ka ne, Basiru ka dube ka da kyau ka girma tubarkallah inda a ƙauye kake da yanzu ka na da Ƴa budurwa.Duk halin da kake ciki mahaifiyar ka na ankare da kai,kawaici ta ke yi ma a matsayin ta na mace ba ta iya fitowa fili ta faɗa ma,amman yanzu tunda Allah yasa ka tara ƴan kuɗin ka sai akai ma sadaki"
Basheer ya sauke ajiyar zuciya yace "Kawu ita yarinyar da Inna ke magana inda fa ka gan ta ƴar ƙanƙanuwa da ita babu wani girman jiki" kawu yayi murmushi yace "girman mace ai ba daga nan yake ba Basiru,ana auren nan da wata shekara za mu zo suna" da sauri Basheer ya sunne kai ya na jin kunya.
Bayan magrib Kawu Laminu ya shiga gidan su Badiya,bayan sun gaisa da mahaifinta ya shaida masa abin da ke tafe da shi.Baban Badiya yayi gyaran murya yace "to babu damuwa za ku iya kawo sadakin ku amman kafin nan zan tambayi ita yarinyar in ta amince" Kawu Laminu yace "to ba matsala a duk lokacin da kuka shirya za mu kawo kuɗin sadakin in shaa Allah"
Iya mai wake da ke laɓe ta na sauraren su da sauri ta ƙarasa shiga ɗakin ta na mai cewa "yarinya ta amince tun tuni na yi mata tambayar,kasancewar ɗazu Innar Basirun ta zo nan"
Duk da Baban Badiya ya ji haushin matarsa hakan bai hana sa cewa "Masha Allah to ka ji dai,ko yanzu kuka shirya za ku iya kawowa daidai abin da Allah ya hore" a haka kawu ya dawo gida ya shaida ma Inna yadda suka yi da iyayen Badiya." DATTIJON ARZIKI(Ummu Fareesa)ai dama bai taɓa yanke sadaki ga duk ƴaƴansa da ya aurar shiyasa na ke kwaɗayin haɗa zuri'a da shi"Inna ke faɗa ta na goge ƴar guntuwar ƙwalla.
Duka kuɗin ta bai wa Kawu Laminu shi kuwa ya cire 100mill/100k ya mayar mata da sauran,kafin yace "wannan ne na sadaki,su kuma sauran sai ya sayi kayan abinci da sabbin kaya,gidan da za su zauna kuma zan biya masa kuɗin shekara guda" Inna tace "na zata nan za su zauna sai a buɗo ƙofa daga waje"
Kawu yace "a'a ba za'a yi haka ba gwara dai su zauna wani gun" haka dai suka ta tsara yadda komai zai kasance Basheer kuwa ya na ɗaki ya na jin su.Washegari
Tamkar da wasa sai ga shi an kai kuɗin auren Basheer wanda zuwa yanzu shi ma ya fara ɗan jin son lamarin,ita kuwa Badiya tsabar murna har sai da ta taka rawa .
An tsayar da biki wata uku cur lokacin kaka, Basheer sam ba haka ya ke tsara aurensa ba amman babu yadda ya iya a zuciyarsa kuma ya ɗauki alƙawarin sai ya yi wa Badiya akwati mai taya ko bayan aure ne kamar ko wace amarya.
Yau ta kasance Laraba tun da safe Basheer ya tafi chantier kamar yadda ya saba duk sati sau biyu kawai a bai zuwa ranar Litinin da kuma juma'a ranakun kasuwar Maradi.
Da isar shi tuni ya tarar ana ta aikin kwaɓa ƙasa,kayan jikinsa ya cire ya saka na aiki uwanda duk suka ɓace da siminti.
Kwagirin da ake zuba kwaɓaɓen siminti nan shi ma ya fara aikin lebarancin ,tsawon wuni guda babu hutu sai cin abinci da suka tsaya.Daf da magrib duk suka wanke jikin su,ogan su ya fara raba masu kuɗi sai dai duk wanda aka ba sai ya ɓata fuska.
Basheer ya juya 2000f ɗin kafin yace "oga yau kuma 2k a maimakon uku?" Ogan ya tamke fuska yace "eh yanayi ne ya zo da haka,yau ai ba ku yi ma wani aiki ba duk surutu yayi yawa" Basheer zuciyarsa tuni ta kawo ga wuya yace "amman oga sam hakan ba adalci ba,duk kowa ya san lebaranci 3k ko ina wasu ma har 4k suke bayarwa dan gudun shiga haƙi" a hasale ogan yace "Basheer ni kake gaya ma magana?tsawon shekaru nawa yanzu...


Read / Download BASHEER

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album