Join Our WhatsApp Group

ME MAGANIN MATA Complete Hausa Novel Document by ME MAGANIN MATA


ME MAGANIN MATA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 90522



ME MAGANIN MATA

Reading Time: 7 Hours

Added On: 15, Mar 2024

Author: Zahra Muhammad Mahmud Surbajo ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 07044600044

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 471.9 kb

File Type: txt

Views: 331+

Download: 579+

Last download: 15 hours ago

Description/Story: [10/18, 2:48 PM] Sis Asma: 🦚🦚 ME MAGANI🦚🦚
COPY BY ZAINAB BUTALAWA






1







Official





By
AsmaBaffa






BISMILLAH






Mun godewa Allah da ya kawo Mu sabon Novel Dina, Ina muku fatan Alkhairi fans,Fatan zai fadakar,ilmantar da nishadantarwa,nice dai AsmaBaffanku fans.

Yanda muka Fara lfy Allah yasa mu Kare lfy.

Comments dinku nake bukata pls,sannan Ina neman Afwar duk wacce ta min comment ban Mata reply ba,wasu comments Yana sa min waiting bana gani,wasu Kuma Allah Bai sa na kula ba,sai Wanda ke min Sharhi na manta ban Basu page kuyi hakuri Kar kuyi fushi aci gaba da min Sharhi Dan Allah hakan shi ke sawa novel ya tafi dai dai,sannan na samu kwarin gwiwar typing.






Wannan Page na JIDDER ZARIA ne da Kuma SUBBY tawa.








Yar wata matashiya ce zukekiyar gaske Fara ce Amma ba Fara kwal kwal ba,ka rantse Yar Ethiopia ce baza ta wuce 17yrs ba, rike take da sandar wani Dattijo makaho Wanda baya gani ko kadan,hannunsa daya a shanye yake nakasshe ne sosai Yana
rataye da Jakar maganin sa cike dam,wannan Dattijo ba bara yakeyi ba,magani yake siyarwa iri iri, Khairat da sandarta tana Masa jagora daya hannunta Kuma speaker ce katuwa irin ta maroka, Rana ta kwalle a kansu suna zaga kasuwa kasuwa a cikin birnin Kano.

Sandar ya samu ya kwala Mata a kanta Dan ubanki baza kiyi tallan maganin ba sai dare yayi bamu samu komai ba,Kawu to wlh Ni bazan iya Furta kalaman tallan Nan ba,ace kamata mace budurwa Ina Furta kalmomin batsa,Ina ka taba Jin mace da tallan magani iri wannan? Ai gwara ka barni irin da na dinga Shiga gida gida Ina musu talla ba a kasuwa ba,Taya Zan iya Furta wannan kalmomi,Kuma kasan Ni ban iya ba yauce ranata ta farko Dana rakoka kasuwanni.

Dan ubanki sai kinyi ko Kuma idan na koma gida wlh na fadawa talatu taci ubanki,Zaki min asara Allah ya Baki nasibi idan kinyi talla yanzu Nan Zaki ga an siye maganin Amma idan nine ko yarona Haka muke yini Babu ciniki wlh ko kiyi ko sai kinyi sati cur ba a Baki abinci a gidan ba kin San Halina kin San Kuma wace ce Talatu.

Jin za a hanata abinci tace to Bari zanyi yanda kakeyi ai Allah ya gani bani da laif...kafin ta Karasa ya sake rafka Mata sanda yana Fara yi Dan ubanki,shegiya, tsinanniya ke dai Allah wadaran halinki.
Ba shiri ta kafa speaker a bakinta cikin zazzakar Muryarta me dadin saurare ta fara tallan magani kamar Haka...

Ga Magani...ga...magani,nice me magani, sai an gwada Akan San na kwarai da yardar Allah zaku warke,ba mune muke warkarwa ba,Allah ne, da Iznin Allah idan ka siyi wannan magani cikin hukuncin Allah zaku warke,ga maganin waraka,Mata da maza Hajiya ko Alhaji Azo a siyi magani araha garabasa,maganin warakar dukkan wasu cututtuka,ga me gani tazo ga araha ga aiki...da masifa Makahon yace Baki Fadi na ko wacce cututtuka ba? Fadi Yar iska,ta jinjina nauyin Maganar Amma Haka ta jawo gyalenta me zarnin fitsarin yaran gidansu ta rufe Fuskarta sabo da kunya tace.

Jama'a kuzo ga maganin Basir,Ciwon sanyi me cutar da mace ko Namiji,fitar farin ruwa a gaban mace ko Namiji ya rage Masa karfi ya Sa Masa kasala Wanda baya iya gamsar da Matarsa baya iya tsinana Mata komai ya rasa Kuma ya gagara gane Dalilin to sanyi ne ke damunsa, ga waraka tazo kuyi maza ku garzayo domin siyen wannan magani.
Naira dari biyu ne kacal anyi shi da ingattun Yayan itatuwa.

Murmushin jin Dadi Makahon yayi yace yawwa Khairat ci gaba,tace Namiji gabansa na kankancewa kamar an roko Masa yazo ga Magani,mace wacce Bata Jin dadin saduwa da mijinta tazo tana da cutar sanyi ga Magani ya samu,bamu mukeyi ba Allah ke warkarwa ta silar Amfani da maganin Kawu Mai baiwar makanta,Makaho ne Amma Allah ya bashi baiwar Ilmin hada magunguna,Makahon ya sake Mata rada a kunne Aiko ta karo karfin Muryarta jikinki na Miki kaikayi mace taji wani Mar mar kamar tsutsa na yawo ajikinki maza zo ga Magani,Amarya wacce ake Shirin aurenta tazo ga Magani Kar Ango yace an cuceshi, rada a kunne Makahon ya sake yi Mata,tace Muna da Sa Ango kuka,muna da makale Mata,Mannau shima muna dashi,Amarya Kisha kiga aiki ke da kishiya sai dai ki gani a makwafta.

Duk wannan tallan da Khairat ke yi kusan Abubuwa kadan take gane me ake nufi,kawai dai tana yin yanda Makahon kawunta ke yi.
Da yawan mutane maza da Mata kallonta akeyi wasu suna dariya,wasu na zaginta a ransu Bata da tarbiya,Bata da gata,wasu Kuma ganin Makaho Dattijo sun gano shi ya tirsasawa budurwar irin wannan tallan sai suke Jin tausayinta suna Jin haushin Makaho,ta wani bangaren Kuma wasu Makahon ya burgesu akan ya dinga bara da roko to gwara ya nemi na kansa wannan ya nuna me zuciyar neman na kansa ne sakamakon wasu daga nakasa ta samesu ko yayane sai zuciyarsu ta mutu kawai sanaarsu bara da roko.

Khairat taci gaba da Magani....azo a garzayo a siyi magani zaku ga amfaninsa,ta fara bada labarin karya wani saurayi matashi yazo wajen Kawu Makaho yace Kawu na Shiga uku ka tallafa min gaba daya gabana kullum ja baya yakeyi,Kawu na ya tambayi matashin yace yaro idan ka tashi da safe Yana motsawa? Matashin yace Kawu kamar lagwanin resho Haka yake,Kawu yace yaro na gane komai matarka ma Bata ko saurarenka sai dai kullum fada ko? Yaron yace exertly Kawu Nan Kawu ya bashi wannan Magani tare da Furta maza jika a ruwa kasha har kwana uku zaka ga aiki,Bayan sati daya sai ga saurayin Nan ya dawo Yana Godiya tare da yiwa Kawu kyauta me tsoka sabo da yaji dadin wannan magani,Mun gaji Wannan magani tun iyaye da kakanni...Alumma ku garzayo ga maganin gaskiya ba algus.Makaho sai washe Baki yake yaji khairat ta zage tana sambada karya yanda yake yiwa mutane Ana siyan maganinsa yayi ta bayar da labarin karya,ya Jinjinawa Khairat data iya yanda yake tallan har ma ta fishi iyawa dake tana da basira.

Kafin wani lokaci mutane irin Wanda suka shigo kasuwa daga kauye Mata da maza da Kuma Yan Tasha suka Fara rubibin siyan magani Nan da Nan sai ga Magani ya kusa karewa kaf,Makaho kuwa murna kamar zai tashi sama Yana wani lallaba Khairat.
Khairat kuwa kamar ta saki Ihu Haka take ji ga kunya ta rufeta bata iya kallon mutane,kwalla ta cika Mata Ido,Idonta yayi ja sabo da bacin Rai ji take kamar ta kashe kanta ta huta,Kawu Makaho kuwa ko a jikinsa kudi kawai yake Tarawa abinsa.

Yana washe Baki yace Khairat kwana Nan zamu Fara Shiga kauyukan Kano,Litinin zuwa Alhamis kauyuka zamu dinga zuwa sune Wanda suke da karancin wayewa zamu fi samun ciniki,Birni Kuma daga Jumaa zuwa Lahadi zamu dinga zagawa.
Harara Khairat ta zabga Masa tare da cewa Ni wlh bazan iya ba shike Nan tunda na taso bani da ishashen ilmi daga Talla sai talla,kwata kwata jss2 kuka katse min karatu na,Islamiyya ma Dan Ina kokarin zuwa ta dare ne da bazan San ko Fatiha ba,ga yaronku Nan su har ta Gaba da Secondary sukeyi,Ni kun maidani jakarku sabo da Baku Kuka haifeni ba,Kalleka Kawu kana kanin Babana Uwa daya uba daya Amma kaci Amanar iyalinsa baka iya yi min komai sai zaluntata da kukeyi,matarka ta cuceni,yaranka da Kai kanka Kawu tana Gama Fadi ta fashe da kuka,ko saurarenta baiyi ba yaci gaba da siyar da maganinsa ko a jikinsa Yana jinta ta kifa kanta a cinyarta tana ta kuka,idan mutane suka tambaya wannan lfy kuwa? Sai yace ai kanta ne yake ciwo yanzu Tasha magani Haka take yi idan tana Ciwon Kai.

Takaici yasa Khairat ta mike tace a Nan Zan barka Kawu in yaso ka mutu a Nan bazan maida ka gida ba gwara na Shiga bariki,Ta Kama hanyar tafiya kenan Kawu ya tabbatar da gaske ne idan ta tafi wa Talatu zata sai aiki,sannan shi kanshi wa zai tayashi tallansa, Aiko ya dauki speaker ya fara sanarwa jama'a ku taimakeni ga yarinyata can zata Shiga duniya a taimaka wlh mahaukaciya ce,tana da Ciwon hauka,kullum sai ta fito rannan ma sai da akayi sati Uku ba a San inda take ba,Nan take Khairat ta kwashe da gudu tana ihu,ganin Haka yasa mutane suka yarda da Zancen Kawu Makaho gata dama dukun dukun da ita,sai ko mutane sukayi Mata Tara Tara aka kamata.
Da kyar Kawu Makaho ya lallasheta ta rike sandarsa suka tafi gida tana Hawaye.

A hankali tace Kawu yunwa nake ji ka siya min ko yogourt ce na Sha tunda an yi ciniki,Kawu yace Dan ubanki nawa ne kudin? wasu na kirkine uwar son banza Zaki ce na siya Miki har yogourt Ashe Dadi kika zo ci,ko Ni ban Sha ba sai ke Yar gwal,ubanki me ya mutu ya Bari,uwarki data mutu zoben farin karfe kawai kika gada gayyar tsiya,to ko Zan siya bazan siya Miki ba,ban siyawa yarana ba su Zainabu ko matata Talatu sai ke,ke din banza ballagazar wofi.
To tunda baka siya min ba ai sai ka kyaleni ba sai ka zageni ka zagi iyayena ba,Kuma wlh duk ranar da Allah ya bani Rana nayi kudi sai na Rama abinda Kuka yi min,bazan ji wani tausayinku ba,Kuma yogourt sai na Sha Nan ta samu Kawu ta turmushe shi a kasa kamar ta samu yaro ta dauki Naira Hamsim Kawu Yana ta ihu Jama'a a taimaka min ga Yar fashi, ta siyi yogourt ta Hamsim me sanyi tana Sha tana yiwa Kawu jagora Wanda kayansa sukayi futu futu sabo da turmusheshi da tayi kasa suka dinga kokawa.
Khairat Allah ya Bata karfi ba yanda Kawu ya iya sai yace Allah ya Isa tsinanniya kinsha wuta Bal Bal.

Dariya tayi kyawawan hakoranta kanana suka bayyana,dama Dan bakinta cut kamar cokali bazai Shiga ba,lips dinta pink,Muguwa dama bakya dariya sai mugunta ta faru anan Zaki Shiga dariya Azzaluma.
Kawu wlh baka ji yogourt din ba Dadi ga sanyi tayi kankara,Banza yayi Mata suna tafiya sunzo dai dai majalisar samari Sai Kawu Makaho yaji wani Makaho Dan uwansa Yace Malam Sabi'u ya gari? Ai Ina Jin Muryar yarka na gane Kaine,Kawu Makaho yace Af Haladu Makaho ne? Sannu Dan Uwa,Haladu shima da yaronsa karami Yana Masa jagora yace Alhmdllh ya aka ji da Sana'a? Kawu yace Alhmdllh,Ai ka samawa kanka lafiya da baka bara barar Nan ko wahala gamu duk mun lalace cewar Haladu.
Kawu yace wuuuu rabani da bara,bara a Arewa musamman Kano ko wahala ba a sadakar arziki daga biyar sai goma Ina Zan iya wahala Haka,Kano sadakarsu daga biyar sai goma,sai dariya kake ji kyakyakya matasan Samarin Nan dake Majalisa suna ta dariya,Yan Jagora Kuma sunyi Miki Miki sabo da su suna gani sun San Kuma a majalisar Maza suka tsaya,su Kuma makafi basa gani.
Kunya ta rufe jagoran Haladu da Kuma Khairat jagorar kawu Sabiu Makaho,sai zungurin Kawu take da kafa tana da mutane fa Kawu Amma Bai gane ba yaci gaba da...

Ai musamman matasan Kano Malam akwai son Kudi sai Yan Mata suke kashewa yanzu idan a kudu ne ba Arewa ba da tuni mun sauke Farali Munje Makkah Amma Nan Malam haba gayyar tsiya, Haladu ya karbe da musamman Ghana ko Uganda Hajji da Umrah sai mun ture,kaga sanda naje Nayi bara a Chadi sai da na Kai gyatimina da gyatimata aikin Hajji kafin su rasu Amma Nan sai dai ma su zageka suce ka fisu kudi.
Kawu yace ai Allah ya tsinewa Yan Arewa musamman Yan Kano Basu San mutunci ba Sadaka daga biyar sai goma,matasan Majalisa suka Kara kwashewa da Dariya, Haladu yace Sabiu nake Jin dariya ko a fillin kwallon kafa muke ne? Kawu yace to wa ya sani ke Dan Ubanki Khairat a Ina muke,Kawu a majlisa muke fa, sai kunya ta Kama Haladu yayiwa Kawu Sallama ya tafi Khairat ma suka tafi gida suka bar matasa suna ta dariya.

Suna zuwa gida Talatu ta fito da gudu kamar mahaukaciya jikinta na doyi da tsamin Dauda ta tarbi mijinta Kawu Makaho ko kunyar yaranta Bata ji ta rungume Kawu Wanda shima wari yake ga Rana ta buge shi,Kawu yace Talatu ta yau Kuma wani sabon salo ne Yana washe Baki,Talatu tayi fari warr da Ido Wai ita a Dole me kula da Miji tace Hmm Sabiu na yau karatun littafin Hausa naji Ahmad Isa na karantawa a radio soyayyar ta birgeni shine Nima nayi koyi da fadakarwarsa, dariya ce ta Kwacewa Khairat tsofai tsofai Talatu tana yiwa Makaho fari da Ido Bai San me takeyi ba ihu Bayan Hari kenan,ruwa me sanyi ta kawowa Mijinta da Abinci, Khairat Kuma ta watsawa Harara tana daka Mata tsawa Dalla malama fita can tsakar gida munafuka kin tsaya Mana a kai.
Can ta fita gindin bishiya ta tsaya,Zainab yarta wacce take B u k Jamia level 1 itace ta ebo kayan wanki ta zubewa Khairat a gabanta gashi Nan kiyi sauri ki wanke min anjima Zan koma schl Hostel maza sauri.

Fuska Khairat ta hade tace Ni wlh na gaji sai na ci Abinci daga dawowata....tas Zainab ta kwashe Khairat da Mari,dake Khairat itama Bata barin ko ta kwana Haka ta cakumi Zainab suka Fara kokawa tukuru Allah yasa Khairat karfi gareta sai ko ta fasawa Zainab Baki,Talatu ta fito tana ihu ta kwalawa danta Babba Kira ya fito da sauri daga dakinsa, tace Ammar Soja kalli yanda Khairat tayiwa kanwarka ta jini.
Ammar Wanda akewa lakabi da Soja ya zare belt ya Shiga dukan Khairat iya karfinsa kamar ya samu gardi Dan uwansa ya zaneta tas ya farfasa Mata jiki tana ta kuka har ta gaji bacci ya kwasheta a Nan yashe a kasa.
Sabo da Khairat sarkin bacci ce watarana ko aikenta kayi to tana Jin bacci sai ta nemi bishiya a waje kawai ta kwanta ta rushe da bacci.
Ba ruwanta da sai ta dawo gida ko ta nemi wurin bacci a wajen da bacci yazo Mata a Nan Zata kwanta.

Talatu...


Read / Download ME MAGANIN MATA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album