Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

BAKAR TA'ADA Complete Hausa Novel Document by BAKAR TA'ADA


BAKAR TA'ADA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 42018



BAKAR TA'ADA

Reading Time: 3 Hours

Added On: 06, May 2024

Author: Surayya Dahiru Gwaram ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08032773332

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 218.87 kb

File Type: txt

Views: 529+

Download: 768+

Last download: 2 days ago

Description/Story: *BAK'AR TA'ADA*
*NA*
*Surayya Dahiru Gwaram*
*(Mrs M.I. Nashe)*
*Marubuciyar Halin yau da Sabo da kaza*.


•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•


*Rok'on addu'arku*!
*A irin wannan ranar ta 09 ga wata 09 shekarar 2000. Ubangiji ya karbi ran mahaifiyata. Dan haka ina baran addu'arku dan nema mata raham da gafarar Allah daga bakunanku masu albarka dan Allah*.

*Haka nan ina mika sak'on ta'aziya ta ga dukkan musulmai bisa babban rashin da muka yi na bijimin malaminmu kuma uba*.
*Sheikh Abubakar Giro Argugun*
*Allah ya jikan magabatanmu gabad'aya kwata.*

*JAN KUNNE*
*KADA A TA'BA MINI LABARIN NAN, KO KARANTA SHI A KOWACCE IRIN KAFA TA SADARWA BA TARE DA IZININA A RUBUCE BA*.
*IDAN KUMA AKA YI KARAMBANIN TABAWA, ZA'A FUSKANCI TUHUMA DAGA LAUYANA BAR MUSTAPHA ISA GWARAM*.


*GARGADI*.
*WANNAN LABARIN KIRKIRARREN LABARI NE*
*BA SHI DA ALAKA DA KO WANNE MAHALUKI*.
*IDAN KIN CI KARO DA RAYUWAR DA TA YI KAMANCECENIYA DA TA KI, KO WANINKI, TO ARASHI NE*.
*DOMIN MANUFAR MARUBUCI ISAR DA SAKO DA HANNUNKA MAI SANDA A CIKIN ZAMANTAKEWARMU*.
*LITTAFAN SURAYYA BASA NUFIN HABAICI KO SHAGUBE GA RAYUWAR WANI KO WATA.*
*NA GODE*.

*GODIYA GA*
*SADIK ABUBAKAR*
*NA GODE MADALLAH*.

*GAISUWAR GIRMA GA IYAYENA KUMA MARUBUTA*
*HAJ SALIHA ABUBAKAR ABDULLAHI ZARIA*.
*HAJ HAFSAT C SODANGI*.
*HAJ MARYAM KABIR MASHI*.
*HAJ HABIBA ABUBAKAR IMAM*.


*YABO GA*
*K'AWATA JAMILA JANAFTY*
*IDAN DA WANDA NA GAMSU DA TULIN SOYAYYARTA GA RUBUTUNA DA CIGABANSA TO KE CE*
*DUK WATA KALMA TA YI KA'DAN TA FAYYACE GIRMAN SHA'ANINKI A WAJENA*
*INA FATAN UBANGIJI YA SHIGA AL'AMARIN KI, YA BAKI MIJI NA GARI*.

*GAISUWAR SADA ZUMUNCI GA MARUBUTA*
*Sumayayyah Takori*
*Binta Umar Abbale*
*Fadilah lamido*.
*Hassana D'anlarbawa*
*Zainab MAZAWAJE*
*Lubna Sufyan*
*Nazifa Nashe*
*Ayusha Muhd*
*Nana Diso*.
*Kulsum Baffah*.
*Safiyya Um Abdul*
*Umm Asghar*.
*Aisha Dansabo*
*Aisha jos*
*Zee Kumurya*
*Da dukkan y'an kungiyarmu ta lafazi*.

*FATAN ALHERI GA IYAYEN D'AKINA*.
*HAJ HALIMA D'ALHA SHEHU*
*HAJ RABI SANI*
*HAJIYA HALIMATUS SA'ADIYA*
*HAJIYA HADIZA FARI*.
*HAJIYA ZAINAB ABDULWAHAB*
*ALLAH YA HA'DA Y'AY'ENKU DA MUTANAN DA ZASU MUSU KARAMCI FIYE DA YADDA KUKE MINI, INA MATU'KAR GODE MUKU*.

*TUKUICIN LABARIN SUKUTUM GA*
*AISHA MUHD LAME*
*ALLAH KA SO AISHA, KA FARANTA MATA, KA BIYA MATA BU'KATUN TA NA DUNIYA, KA BATA BABBAN RABO A LAHIRA*.
*IDAN AKWAI WANDA JINI BAI HA'DAMU BA, NA KE DAKACEN INA MA JINI YA RATSA TSAKANINMU TO AISHA LAME CE MAI KAYAN Y'AN GAYU TA ORIFLAME*
*SURAYYA DEE TA GODE, TA YABA MIKI, UBANGIJI YA TAYA NI GODE MIKI*.


*Doka mi lamba ta 68 ta nuna cewa satar fasaha Babban laifine da yake dai-dai da satar Dukiya*


*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*.

*1&2*.

*SHIMFI'DA*.
Sunana Asiya Sani Toro.
Amma mafi yawa da Yabi ake kira na a dalilin mahaifiyata ta yi aikin Hajj da ni a cikinta.
Mama ce kawai bata kira na da hakan sai Asiya saboda tana adawa da Yabi tunda ana nufin nima Hajiya ce.
Gidanmu babban gida ne a garin na Toro domin ko yaro k'arami ka tambayi gidan Marina zai nuna maka. A dalilin asalin kakanmu da ya zo daga Kano ya fara kafa wannan sana'ar a garin. Fiye da shekaru saba'in kenan, amma har yau ba'a juya wa sana'ar baya ba, duk da dai an zamanantar da ita, ba kuma cikin gidan ake yin ta ba saboda warinta.
Gidanmu babban gida ne k'warai da gaske.
Idan na ce babban gida ina nufin mai d'auke da ahali daban daban masu yawa.
Ko a k'ofar mahaifinmu Alh Sani (Baban Marina) da shi ne babba mata uku ne.
Hajiya Habiba ita ce uwargidan mahaifinmu, mace mai k'ifadi da kutunguila. Duk wani rikicin da yake k'ofarmu, dama cikin gidan tana da sa hannu, ta tsani ta ga ko wanne irin cigaban d'an wata sai nata yaran kawai.
Sannan komai cikin dabara da girma ta ke yinsa, ba kowa ne ya fahimci irin makircin da take k'ullawa ba. Sai mu da mu ke rayuwa da ita kullu yaumin.
Ta kanka ne komai, ta yadda komai ta shimfi'da akan haka za'a tafi, sai dai ranar da ta samu bacin rana Baba ya bijire mata.
Ya'yanta biyar.
Yaya Musa, Yaya Hadiza, Yaya Salamatu, Yaya Indo sai autarta da ta haifa bayan ta shafe shekaru masu yawa Nazira, wacce ita ce sa'a ta ta girme ni da wata uku.
Sai Mahaifiyata Hajiya Àsma'u wacce muke kira da Goggo. Ba dan tana mahaifiyata ba, amma mace ce mai sanyin hali da matsanancin ha'kuri. Idan na ce ha'kuri, ina nufin ha'kuri gangariya, irin ha'kurin nan da mai yinsa kan saka a alummar da suke kewaye da shi su halaka saboda hakkinsa da za suyi ta d'auka.
Yaranta takwas cif.
Yaya Salisu, Yaya Rabi'u, Yaya Ummi, Yaya Adnan, Yaya Ali, sai ni Yabi, duk dai bani nake bin Yaya Ali ba, akwai wani ya rasu ne, sai Anas da kuma autarmu Ikilima.
Wannan yawan yara da mahaifiyata ta tara a d'akinta, kuma maza, ya sanya Mama ta tisa ta a gaba da masifa da tuggu, kusan kowa a gidan ya tsani mahaifiyarmu, ba kowa ne yake mua'amala da ita ba.
Duk gidan bakinsu daya ne a kanta. Duk kuma Mama ce ta b'ata ta, take adawa da duk wanda zata ga ya mu'amalan ce ta
Shi yasa hatta mu yaranta bamu da wani kwarjini har a wajen Dada kakarmu da ita ma tana cikin gidan bangarenta daban.
Sai Hajiya Sahura muna k'iranta da Innah. Yaranta biyar Na farkon ma mun dan girme masa ka'dan Ubaid, Ubaida sai Abida, Hajara, Ismail da autarmu gaba'daya Saliha.
Duk yadda Mama ta so wajen raba zumunta a tsakaninmu bai yi tasiri a tsanina da Nazira ba.
Duk yadda bata kula ni, bata sakar mini fuska hakan bai hana ni yin dabdala a dakinta ba a dalilin Nazira.
Bare ita kuma da dakin Goggonmu take kwana..
Sau dubu gara Inna akan Mama. Domin dai ba yadda za'a yi Inna ta ha'da wa Goggo sharri, ko ta tsokane ta da gangan, amma bata wani girmama ta a dalilin Mama ta dabarbarce ta, ta hana ta yin mu'amala da Goggo ta hanyar fa'da mata Goggo ce da gida, duk yaranta maza ne, idan Alhaji ya mutu duk su din y'an kallo ne.
Da na fara mallakar hankalina sai nake tambayar kaina wai mene ne mahaifinmu ya mallaka da har ake fatan ya mutu?
A da kam ya yi arziki k'warai da gaske, domin duk girman Gidanmu shi ya zaga ye ya gine shi, sannan mafi yawa na cikin zuri'arsu shine ya biya musu suka sauke farali.
Amma tun shekarar da aka haife ni ya ha'du da y'an damfara suka yi masa sanadin karayar arziki, har yanzu da muke da shekaru goma sha biyar bai farfad'o ba.
Yan'uwansa kuma kowa ya zuba masa ido ya zama abin tausayi.
Amma a hakan Mama take fa'din Goggonmu ce zata ja komai.
Wannan kenan.
Sai k'ofar Alh Badamasi(Baban Tsakiya).
Matansa biyu da yara sha biyu.
Na uwargidan Hajiya guda bakwai . Babban d'anta Yaya Jabir, Zakiya, Jamila, Hauwa, Firdausi, Aisha sai k'aramarsu , Basira. Nan Firdausi ce warinmu.
Sai amaryar Momi tana da yara biyar, Nasiru, Naziru, Sararu, Rumanatu da Kubrah.
Anan ma Saratu ce sa'armu.
Sai kofar k'arshe ta Alh Iliya (Baban kasuwa).
Matarsa daya da yaransu shida.
Amina, Aminu, Maijidda, Kaltume Abba andda Aliya.
Maijidda ce sa'armu
Sai wajen kakarmu Hajiya Binta! wadda Yaya Umminmu sunanta ta ci. Kowa Dada yake ce mata, wata irin tsohuwa mai wahalar sha'anin gaske.
Tana daga zaune rikicin da take yi ba dan ka'dan bane, haka nan bata damu da ha'din kai a tsakanin ahalin gidan ba.
Domin bayan su Babanmu akwai yan'uwansu mata biyu.
Bangaren Dada ma hawa biyu ne, domin akwai wata k'ofar a can ciki bayan ka wuce k'ofarta ta farko, sannan ana iya fita waje ma ta wannan wajen Sai dai kofar a rufe take. Amma ba kowa ciki sai kayan ajiye ajiye da dangin kayan noma da tarkace.
Babar Bulkachuwa(Hauwa) ita ta biyo Baban Tsakiya, tana aure a Bulkachuwa, mijinta Alh Yusufu babban d'an kasuwa ne a kasuwar kayan miya ta Muda lawal a Bauchi.
Ita ce amarya amma sai a kanta ya samu haihuwa ta tsaya masa, uwargidan wabi take yi, ma'ana idan ta haihu sai su koma.
Tijjani ne babba sai Aliyu, sai Nasir. Sai bayan haihuwar Nasir ne uwargidan ta haifi Maryam da kuma Hafsa.
Daga nan sai Babah ta sake haifar Ihisan. Kenan yaranta hudu na uwargidan kuma biyu.
Tijjani ya taso cikin wani irin gata a wajen mahaifinsa a dalilin tsawon lokacin da ya shafe babu haihuwa.
Sai dai kash gatan ya zame masa d'an zani domin gaba'daya sai ya kangare, tun yana karaminsa ya ko yi fitina iri iri, shine kame kaji da awakin jama'a yana siyar wa, gaba'daya ya ki kar'bar tarbiyar da ake ba shi a sanadin duk abokansa lalattu ne.
Duk yadda Baba ta Bulkachuwa da mahaifinsa suke son fige masa wannan dabi'ar abin ya ci tura.
Akan dole suka raba shi da garin, suka dawo da shi wajen Mahaifinmu da Baban Tsakiya, tunda su din zafi ne da su ainun.
A lokacin bai fi shekaru sha biyar ba.
Sa'an Yaya Salisu ne,...


Read / Download BAKAR TA'ADA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album