Join Our WhatsApp Group

ASP ZARAH Complete Hausa Novel Document by ASP ZARAH


ASP ZARAH

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 36289



ASP ZARAH

Reading Time: 3 Hours

Added On: 13, Aug 2023

Author: Asmau Bint Abubakar ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : MANAZARTA WRITTERS ASSOCIATION

Author Phone : 07048961623

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 200.06 kb

File Type: txt

Views: 2276+

Download: 851+

Last download: 2 days ago

Description/Story:  *MANAZARTA WRITTERS ASSOCIATION*📚🖊️
*M*. *W*. *A*
_Putting smile on our readers faces._
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsapp
___________________________________

*ASP ZARAH*👩‍✈️

_Daga Alƙalamin_✍🏻
_Asmau Bint Abubakar_
_Jasmine_🌸🌸

*Da sunan Allah mai rahma mai jinƙai, dukkan yabo da godiya su tabbata gun Allah maɗaukakin sarki daya bani lafiya, ilimi, basira da kuma lokaci dana samu daman rubuta wannan littafin. Allah yaƙara dubun salati a gun mafificin halitta annabinmu Muhammad S. A. W da ahlinsa da sahabbansa dama dukkan masu bin tafarkinsa har zuwa ranar tashin alqiyama.*
*Ina roƙon Allah ya tsaremin alƙalamina daga rubuta duk wani abu dazai kawo ɓatanci a cikin al'umma. Allah ina roƙonka yadda nafara rubuta wannan littafi lafiya Allah kabani ikon gamashi lafiya, kurakuran dazanyi ciki Allah ka yafemin da wanda nasani da wanda bansani ba.*

*Littafin ASP ZARAH na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da biya ba. Idan kinji kinason cigaba da karantawa toh ki biya kuɗi N300 kacal domin karantashi cikin kwanciyar hankali, idan kinsan zaki dinga yimin sharing ɗin littafi dan Allah kada ki biya kuɗin banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntu6eni a 07048961623 domin biya da kuma shiga group*.

*Jan Hankali*: _Ƙirƙirarren labari ne. Ban yarda a canjamin littafi ta kowace siga ba batare da izinina ba. A bi doka a zauna lafiya_ .
👩‍✈️
👩‍✈️
👩‍✈️
👩‍✈️
👩‍✈️

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_

*Free PAGE 1*

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un".
Shine abinda matashiyar yarinya wacce ke sanye da kayan ƴan sanda take maimaitawa, alamu sun nuna cewa suma tayi aka watsa mata ruwa ta farfaɗo duba da yadda take a kwance a ƙasa idanu a rufe ga fuskarta data jiƙe da ruwan da aka watsa mata. Jin ana ƙoƙarin ɗagata a ƙasan ne yasata buɗe ido domin ganin mai taɓatan, Ammi ce wacce take matsayin ƙanwa ga mahaifinta.

Kallon fuskar Ammin tayi wacce ta kumbura tayi jazir saboda kukan da tasha domin hatta idanunta sun koma can ciki ba'a ganinsu sosai saboda kumburin da fatar idon nata tayi.

"Zarah kuka ba shine mafita ba a yanzu, kizo kiyi sallama dasu domin a samu damar kaisu makwancinsu da wuri." Ammin ta faɗa cikin dasasshiyar muryarta.

Buɗe baki tayi domin magana amma kukan data kasayi tun farko ya riga maganartata fitowa, take kuwa ta fara rera kukan mai taɓa zuciyar duk wani mai sauraro.
Hannunta Ammi ta kama ta ɗagota tare da nufar inda gawarwakin mutane takwas dake sanye da suturarsu ta ƙarshe a cikin makara, koda ta iso da ita wajen sake hannunta tayi tare dayin baya domin kukane yakeson ƙara kece mata.

Cikin rawar hannu ta fara yaye mayafen daya lulluɓewa gawarwakin fuska tundaga kan gawa ta farko.
"Mahaifina, Mahaifiyata, Kakannina uku, ƴan biyun ƙannena sannan ƙaramar ƙanwata. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." ta ƙara fashewa da wani sabon kukan mai taɓa zuciya, lokaci ɗaya kuma ta tsagaita tare da gyara rufuwar mayafan sannan ta ɗaga hannu sama ta fara addu'a.

"Ya rabbi, Ya rabbi, Ya rabbi. Ya Hayyu ya Qayyum ya Allah ina gode maka a cikin kowani yanayi dana tsinci kaina. Ya Allah kaine shaidata ban shiga aikin ƴan sanda ba saidan na taimaka gurin gyara ƙasata, Ya Allah kasani ina tsare duk wasu dokokinka bana saɓawa da gangan saidai a rashin sani. Ya ubangijina nasan ka fini son waɗannan bayi naka shiyasa ka karɓesu daga aron daka bamu, na karɓi wannan jarabawa hannu biyu sannan ina ƙara gode maka.
Ya Allah ga bayinka nan zasu iso gabanka Ya Allah kayi musu gafara ka yafemusu zunubansu wanda sukasan sun aikata dama wanda basu sani ba, Allah kayi musu rahama, Ya Allah ka tsare daga duk wata fitina dake cikin kabari Allah ka karɓi shahadarsu. Ya Allah kabasu wani ɓangare a cikin Aljannarka.
Ya rabbi baka aikata zalunci sannan baka barin masu aikawa, Ya Allah na kawo ƙarar duk wani wanda yake da hannu a cikin mutuwar bayinka muminai."

Hatta mazan dake farfajiyar wajen saida suka zubda hawaye tare da jinjina jarumtar Zarah.
Batare da ɓata lokaci ba aka sallaci gawarwakin sannan aka tafi sadasu da gidajensu na gaskiya.

_Kafin faruwar wannan al'amarin_.


Tsantsar abota da aminci ne a tsakanin Malam Usmanu da Malam Adamu wanda ya rikiɗe ya kuma ƴan'uwantaka hakan ya samo asaline tun daga iyayensu da sukayi zaman aminci tare, hakan kuma ya ƙarayin sanadin da yaransu suka taso cikin shaƙuwa da son juna tamkar iyayen nasu sakamakon gidajensu dake maƙotaka da juna.
Asalinsu mutanen garin Deba ne a jihar Gombe kuma a nan suke da zama da iyalansu, da sana'arsu ta noma suke rufawa kansu da iyalansu asiri.
Malam Usmanu yanada mata ɗaya Faɗimatu da ɗansu Abdul_Jalal wanda shi kaɗai suka haifa. Yayinda Malam Usmanu keda yara biyu Sulaiman da Rumaisa sannan matarsa Aishatu.
Yaran sun taso cikin so da kulawar iyayensu, tare sukeyin komai tun yarinta har zuwa girmansu.

Sulaiman shine babba cikinsu wanda a yanzu haka yake zaune a cikin garin gombe tare da yaransa biyu Muhammad Jawwad da Nusaiba dakuma matarsa Safiyat wacce yaran ke kira da Momi. Inda ya kasance ɗan kasuwane a fannin ma'adanai.
Sannan Abduljalal dake zaune a garin bauchi da nashi iyalan inda yake aiki a babban asibitin tarayya dake jihar bauchi. Yanada matarshi ɗaya mai suna Zainab (Mami) sai yaransa uku Abubakar Sadiq, Rahma, sai Fatimah Zarah.

Rumaisa kuwa(Ammi) a ƙasar Cairo take zaune da mijinta wanda ya kasance ɗan kasuwa da ƴan biyun ta Muhammad Adil da Muhammad Shahid.

Duk da kasancewar ba guri ɗaya suke rayuwa ba, sukan ware lokuta domin zuwa ziyartar iyayensu a garin Deba. Hakan yasa yaran sukayi sabo da juna sosai in banda Muhammad Jawwad da tun bayan kammala karatunshi na firamari aka kaishi England domin ya cigaba da karatunshi a can.
Haka wannan familyn suke kasancewa koda yaushe cikin so da ƙaunar juna.

Mafarkin Zarah nason zama ƴar sanda ya fara tun lokuta da dama da take ganin ana zaluntar talakawa sannan ƴan sanda suƙi ɗaukan mataki, hakan yasa tasha alwashin zama ƴar sanda.
Daƙyar iyayenta suka aminci da wannan buƙatarta ta domin saida ta kaita ga kwanciya a asibiti tamkar bazata rayu ba, ganin haka ne yasa suka amince tare da kafa mata sharuɗɗan kare mutuncinta dana danginta.

Wani al'amari daya faru a rayuwarta wanda ta kasa mantawa shine.

_Garin Bauchi_
12:30nr

Gosulo ne sosai akan titin wanda ya kasance ana yawan samun cunkuson ababen hawa duk ranar juma'a saboda tare wasu hanyoyi da akeyi sakamakon sallar juma'a da ake gabatarwa. Cikin waɗanda gosulon ya tsayar harda direban daya ɗauko Zarah daga makaranta.
Saidai gabaɗaya hankalin Zarah dake cikin motar ya koma ga wata tsohuwar almajirah dake gefen hanya zaune da roba tana bara, sosai ta bata tausayi ganin babu wasu masu bata sadaka dayawa. Jakar makarantarta ta duba saidai naira ɗari biyu ne aciki..

"Baba Sule akwai kuɗi a hannunka ne". Ta tambayi direbansu dake jan motar.

"Ehh baza'a rasa ba".

"Zasu kai nawa ne."

"Inajin zasu kai dubu biyar ko sufi haka". Ya faɗa sanda yake ƙoƙarin ƙirga kuɗin daya zaro a aljihunshi.


Karɓa tayi tare da fita a motar ta nufi inda matar ke zaune.

"Sannu Baba ya zaki zauna a rana ki koma inuwa mana". Cewar Zarah lokacin data ƙaraso gurin.

"Ƴar nan idan kayi nesa da jama'a wasu bazasu zo inda kake su taimaka ba dole sai mutum yazo inda suke."

"Allah sarki to baki da mai taimaka miki ne.? "

"Da inada mai taimakamin ba zaki ganni ni ɗaya ba ƴata."

"Sunana Fatimah Zarah ne, ga wannan sadaka ce babu yawa." ta miƙa mata kuɗin.

"Allah ya saka da alkhairi Batula, Allah ya albarkaci rayuwarki ya kareki daga sharrin maƙiya. Allah ya bani ikon taimaka miki watarana kamar yadda kika taimakamin."
Cike da jindaɗi Zarah ke amsa addu'o'in kasancewarta mutum mai son taga babba nayi mata addu'a.

"Bari naje direba na jirana zan dinga tsayawa wani lokaci mu dinga gaisawa."

"Toh nagode Allah ya albarkaci rayuwarki." Almajirar ta faɗa a fili amma cikin zuciyarta cewa take "Bazaki ƙara ganina ba yau ɗinma na fito ne da niyyar taimakon mai taimako ne, kuma gashi kinyi sa'ar kasancewa wacce zan taimakawa.

Tun daga wannan lokacin sai ya kasance duk dare Zarah zatayi mafarkin wannan almajira sannan kullum zancen da take maimaita mata a cikin mafarkin shine. _Zaki haɗu da ƙalubale da dama a rayuwarki, ki zama mai hakuri da juriya tare da fauwalawa Allah lamuranki a duk lokacin da kika tsinci kanki cikin tsanani, sannan ki zama mai gaskiya a dukkan lamuranki. Kada kiyi zalunci kuma ki bari wasu su aikata, ki jajirce wajen bada gudumawar da za'a kauda zalunci a cikin al'umma._

Da farko abin baya damunta amma bayan tayi satikai tana neman wannan almajira a inda ta ganta sai abin yafara tsorata ta musamman da mutanen wajen ke faɗin basusan wata almajira ba, hatta Baba Sule data karɓi kuɗi a hannunshi wancan ranar yace bai san ina taje ba bayan ta fita a wannan rana. Lamarin na matuƙar damunta saidai ta kasa tunkarar kowa da lamarin.

A wata ranar lahadi ne tayi mafarkin ƙarshe da almajirar wacce bata kuma zuwa mata ba saidai maganganun data gayamata a wannan rana sun tsorata ta.
_Ni ba mutum bace ALJANA CE! kuma lokaci yayi dazan koma nahiyarmu, BATULA nayi miki alƙawari bazan ƙara zuwa miki a mafarki ko a zahiri ba amma kamar yadda na alƙawaranta zan taimaka miki idan lokacin taimakon yayi. Kada ki manta da nasihata a gareki domin zata taimaka miki sosai._
Tundaga wannan lokaci bata ƙara mafarkinta ba wanda ya gaskata mata cewa aljana ta taimakawa.

Lokacin data fara aikin ƴan sanda sai ya kasance ta jajirce sosai wajen ganin ta ƙwaci duk wani haƙƙin talaka da ake dannewa, hakan ya jawo mata farin jini tare da ƙarin matsayi akai-akai har zuwa yanzu da take matsayin ASP.

Alhaji Sulaiman, wato ɗan'uwan mahaifin Zarah nada tarin dukiya sosai da baisan adadinta ba. Babba kuma sanannen kamfaninshi shine _M.J JEWELS_. Kamfanin ya samu sunan ne daga Muhammad Jawwad wato ɗan shi na fari.
Ana sarrafa duk wasu nau'ika na kayan ƙaleƙale a wannan kamfani kama daga kan ƴan kunnaye, sarƙa, awarwaro, zobuna, agogo da sauransu wanda ake sarrafasu daga ma'adanai daban daban danginsu zinari, azurfa, lu'u lu'u da dai sauransu.
A shekarar data gabata ne yasamu nasarar mallakar lu'u lu'u wanda ya siya a hannun turawa da darajarshi takai dallar amurka miliyan talatin, an sakashi a wani akwatin tsaro na musamman wanda babu wani abu dazai iya fasashi koda guduma ne da bindiga dole sai mabuɗin shi wanda yake tamkar flash na jikin laptop. Kasancewar sai yayi shekaru da dama a ajiye kafin a iya sarrafashi yasa ya ɗaukeshi daga gidanshi inda yake da farko aka maida kamfaninshi saboda hare-haren ƴan fashi. Inda aka ajiyeshi a wani ɗakin sirri dake kamfaninshi, amma duk da hakan ba'a daina barazanar satar shi ba.
Ganin hakan ne yasa shida ɗan'uwan shi Alhaji Abdul_Jalal suka yanke shawarar maida shi gidansa dake bauchi bayan an damƙa tsaronshi a hannun Zarah.

Hatta iyayen basuda masaniyar a inda lu'u lu'un da akwatin tsaronsa suke tun bayan da aka damƙa mata ajiyarshi.

*ALPHA*👽

Alpha wani taƙadirin ɗan ta'adda ne dayayi ƙaurin suna a Nigeria dama maƙotanta, ya shahara sosai wajen sace-sace da fashi gami da kisan kai. Saidai abinda yake matuƙar damun al'umma shine babu wanda ya sanshi bare inda yake zaune domin yanada yara da dama masu yimasa aiki saidai hatta wasu daga cikin masu yimai aiki basu sanshi ba.
A duk lokacin da suka yi wani gagarumin laifi suna barin tambarinsu wanda yake sunan ALPHA ne haɗi da zanen bishiyar kwakwa🏝️, ta hakane ake ganewa idan sun aikata laifi saidai har yanzu ƴan sanda sun kasa kama koda ɗaya ne daga cikin masu yimasa aiki sakamakon manyan gwamnati da suke tare dashi.

Tun bayan daya samu labarin wannan lu'u lu'u daga bakin wani yaronshi na sirri wanda yake aiki a _M.J JEWELS_. Yasha alwashin sace shi saidai matakan tsaron dake jikin akwatin ne ya hanashi samun damar satarshi amma yana kan shiri wajen ganin ya mallaki wannan kadara tare da ɗaiɗaita kamfanin _M.J JEWELS_.

Bayan ya samu labarin inda aka maida lu'u lu'un sai yafara kiran Alhaji Abdul_Jalal tare da yimasa barazanar kashe wani nasa muddin bai sanya Zarah ta damƙa mishi akwatin da lu'u lu'un ke ciki ba, ganin bai samu nasara ba sai ya maida akalar barazanar shi ga Zarah ganin ita mace ce saidai yayi mamakin taurin kai irin nata domin akoda yaushe idan ya kira musayar maganganu marasa daɗi ne yake wakana a tsakaninsu duk da barazanar dayake mata na rasa wani daga cikin danginta.
Dalilin dayasa ya yanke shawarar taɓa wani a cikin danginta ko zata saduda.
_____________________________

Ciwon ciki mai tsanani ne yake damun Rahma wanda yayi sanadin harta kwanta a gadon asibiti, satinta biyu aka sallamota bayan jikinta yayi sauƙi sosai.
Kasancewar lokaci ne na hutu yasa Ammi dake ƙasar Cairo ta yanke shawarar zuwa duba jikin Rahman tare da samarin ƴan biyunta, a garin Gombe jirginsu ya sauka hakan yasa dole suka ƙarasa garin Deba domin kwana washegari sai su wuce Bauchi.
Bayan gaishe-gaishe da hirar yaushe gamo ne suma tsoffin suka yanke shawarar ayi tafiyar dasu domin suma dai basuje dubata ba tunda tayi rashin lafiyar, nan suka yanke cewa zasuyi sammako gabaɗaya suje domin a ranar tsoffin sukeson suje su dawo saidai tafiyar bazata yiwu da Baba Faɗimatu ba sakamakon ciwon ƙafa da take fama dashi.

Da daddare Momi matar Alhaji Sulaiman ta kira Ammi tayi mata ban gajiya inda ta roƙeta akan tabar tata tafiyar sai jibi domin su tafi tare saboda gobe zataje ganin likitan ido akan matsalar ido da take fama dashi. Nan Ammi ta yanke shawarar barin tafiyar sai jibi kamar yadda ta buƙata wanda hakan zai bata daman zama da Baba Faɗimatu da za'a bari a gida ita kaɗai a ranar.

Washegari kuwa kamar yadda suka tsara ƙarfe takwas suka ɗauki hanyar zuwa gari Bauchi bayan sun tsaya a cikin garin Gombe sun ɗauki Nusaiba a gidan Alhaji Sulaiman wacce itama za'ayi tafiyar tare da ita, Shahid ne ke tuƙa motar Adil na gefenshi yayinda Malam Usmanu, Malam Adamu, Baba Aisha...


Read / Download ASP ZARAH

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On ASP ZARAH
avatar
zainab-3-7-9

9 months ago

Reply

I need complete Asp zarah

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album